Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Ta Yaya Za Ka Iya Kyautata Hadin Kai da Muke Mora?

Ta Yaya Za Ka Iya Kyautata Hadin Kai da Muke Mora?

“Daga wurinsa kuwa dukan jiki, haɗaɗe kuwa ta wurin taimakon kowace gaɓa.”—AFISAWA 4:16.

WAƘOƘI: 53, 107

1. Wane hali ne Allah da kuma bayinsa suka kasance da shi tun aka soma halitta?

JEHOBAH da Yesu suna da haɗin kai tun daga lokacin da aka soma halittan abubuwa. Yesu ne Jehobah ya soma halitta kuma bayan haka, sai ya halicci sauran abubuwa. Yesu ya yi aiki tare da shi a matsayinsa na “gwanin mai-aiki.” (Misalai 8:30) Bayin Jehobah suna kasancewa da haɗin kai sa’ad da suke aikin da ya umurce su su yi. Alal misali, Nuhu da iyalinsa sun gina jirgi tare. Bayan haka, Isra’ilawa sun gina mazauni kuma sun rushe shi tare. Ƙari ga haka, sun ƙaura da shi zuwa duk wurare a duk inda suka je. A haikalin, sun rera waƙa da kuma kaɗe-kaɗe tare don su yabi Jehobah. Mutanen Jehobah sun yi dukan waɗannan abubuwan domin suna da haɗin kai.​—⁠Farawa 6:​14-16, 22; Littafin Lissafi 4:​4-32; 1 Labarbaru 25:​1-8.

2. (a) Mene ne abu mai muhimmanci a cikin ikilisiyar Kirista a ƙarni na farko? (b) Waɗanne tambayoyi ne za mu tattauna?

2 Kiristoci da ke ƙarni na farko sun kasance da haɗin kai. Manzo Bulus ya bayyana cewa sun kasance da haɗin kai duk da cewa baiwarsu da ayyuka dabam-dabam ya bambanta. Sun bi umurnin Shugabansu, Yesu Kristi. Bulus ya kwatanta su da jiki da ke da gaɓoɓi dabam-dabam amma suna aiki tare. (Karanta 1 Korintiyawa 12:​4-6, 12.) Mu kuma fa a yau? Ta yaya za mu kasance da haɗin kai yayin da muke wa’azin bishara, a cikin ikilisiya da kuma iyali?

KU YI WA’AZIN BISHARA DA HAƊIN KAI

3. Wane wahayi ne aka nuna wa manzo Yohanna?

3 A ƙarni na farko, manzo Yohanna ya ga mala’iku bakwai da suke busa ƙahoni a wahayi. Sa’ad da mala’ika na biyar ya busa ƙahonsa, sai Yohanna ya ga “tauraro kuma wanda ya rigaya ya faɗo daga sama bisa duniya.” ‘Tauraron’ ya yi amfani da makulli don ya buɗe ƙofar wani rami mai zurfi. Da farko, hayaƙi ya fito daga cikin ramin, bayan haka sai fari da yawa suka fito daga cikin hayaƙin. Maimakon su yi ɓarna ga itatuwan ko tsiro, waɗannan fari sun kai hari ga waɗanda “ba su da hatimin Allah a bisa goshinsu.” (Ru’ya ta Yohanna 9:​1-4) Yohanna ya san cewa taron fari suna ɓarna sosai domin sun yi hakan a ƙasar Masar a zamanin Musa. (Fitowa 10:​12-15) Farin da Yohanna ya gani suna wakiltar Kiristoci shafaffu da suke shelar saƙon hukunci game da addinan ƙarya. Miliyoyin mutane da za su yi rayuwa a nan duniya suna wannan shelar tare da su kuma sun kasance da haɗin kai. Wannan aikin ya taimaka wa mutane da yawa su fito daga addinin ƙarya kuma su samu ‘yanci daga hannun Shaiɗan.

Haɗin kai da muke da shi ya sa muna yi wa mutane wa’azi a faɗin duniya

4. Wane aiki ne bayin Allah suke bukata su yi, kuma ta wace hanya ce kaɗai za su iya yin wannan aiki?

4 An umurce mu mu yi wa’azin ‘bishara’ ga mutane da ke faɗin duniya kafin ƙarshen ya zo. Wannan babban aiki ne sosai. (Matta 24:14; 28:​19, 20) Wajibi ne mu gayyaci dukan waɗanda suke “ƙishi” su sha “ruwa na rai,” wato muna bukata mu koyar da Littafi Mai Tsarki ga dukan waɗanda suke so su fahimce shi. (Ru’ya ta Yohanna 22:17) Amma, za mu iya yin hakan idan muna da haɗin kai a cikin ikilisiya.​—⁠Afisawa 4:⁠16.

5, 6. Ta yaya muke kasancewa da haɗin kai yayin da muke wa’azin bishara?

5 Muna bukata mu bi tsari mai kyau don hakan zai ba mu damar yin wa’azin bishara wa mutane da yawa. Umurnin da ake ba mu a cikin ikilisiya yana taimaka mana mu yi hakan. Bayan mun yi taron fita wa’azi, sai mu je wurin mutane muna musu wa’azin bishara game da Mulkin. Ban da haka, muna ba su littattafai da suka bayyana Littafi Mai Tsarki. Kuma mun rarraba miliyoyin littattafan nan a faɗin duniya. Wani lokaci akan ba mu umurni mu yi kamfen na wa’azi na musamman. Sa’ad da kake yin wannan aikin, kana yin hakan cikin haɗin kai tare da miliyoyin ‘yan’uwa a faɗin duniya da suke wannan wa’azin bishara! Ƙari ga haka, kana aiki tare da mala’iku da suke taimakon mutanen Allah su yi wa’azin bishara.​—⁠Ru’ya ta Yohanna 14:⁠6.

6 Muna farin ciki sosai sa’ad da muka karanta sakamakon wa’azin da muke yi a dukan duniya a littafin nan Yearbook of Jehovah’s Witnesses. Ka yi tunani kuma game da yadda muke kasancewa da haɗin kai yayin da muke gayyatar mutane zuwa manyan taronmu. Dukanmu muna sauraron umurni iri ɗaya a wannan taron. Jawabai da wasan kwaikwayo da kuma gwajin da ake yi a wannan taron suna ƙarfafa mu mu ci gaba da yin iya ƙoƙarinmu a bautarmu ga Jehobah. Ƙari ga haka, muna kasancewa da haɗin kai da ‘yan’uwanmu a duniya sa’ad da muka halarci Taron tuna da Mutuwar Yesu a kowace shekara. (1 Korintiyawa 11:​23-26) Ta wajen halartan wannan taro na musamman sau ɗaya a shekara bayan faɗuwar rana, a ranar 14 ga Nisan, muna nuna godiya ga Jehobah don abin da ya yi mana kuma muna yin biyayya ga umurnin Yesu. Ƙari ga haka, ‘yan makonni kafin ranar Taron tuna da Mutuwar Yesu, muna ba da haɗin kai wajen gayyatar mutane da yawa don su halarci wannan taro mai muhimmanci tare da mu.

7. Mene ne muke cim ma wa yayin da muke yin aiki tare?

7 Fara ɗaya ba za ta iya yin ɓarna sosai ba. Hakazalika, mutum ɗaya ba zai iya yi wa dukan mutane wa’azi ba. Amma da yake muna da haɗin kai, muna gaya wa miliyoyin mutane game da Jehobah kuma muna taimaka wa wasu mutane su soma bauta masa kuma su ɗaukaka shi.

KU KASANCE DA HAƊIN KAI A CIKIN IKILISIYA

8, 9. (a) Wane kwatanci ne Bulus ya yi amfani da shi don ya taimaka wa Kiristoci su kasance da haɗin kai? (b) Ta yaya za mu kasance da haɗin kai a cikin ikilisiya?

8 Bulus ya bayyana wa ‘yan’uwan da ke Afisa yadda aka tsara ikilisiyar, kuma ya gaya musu cewa kowa a cikin ikilisiyar yana bukatar ya “yi girma cikin abu duka.” (Karanta Afisawa 4:​15, 16.) Bulus ya yi amfani da gaɓoɓin jiki don ya bayyana yadda kowane kirista yake bukatar ya sa hannu wajen taimaka wa ikilisiyar ta kasance da haɗin kai kuma su bi umurnin Yesu wanda shi ne shugaban ikilisiya. Ya ce duka gaɓoɓin jiki suna aiki tare “ta wurin taimakon kowace gaɓa.” Saboda haka, ko da mu yara ne ko manya, ko muna da ƙoshin lafiya ko a’a, mene ne ya kamata kowannenmu ya yi?

Ta yaya za ka iya taimaka wa ‘yan’uwa a ikilisiya su kasance da haɗin kai?

9 Yesu ya naɗa dattawa su yi ja-gora a cikin ikilisiya kuma yana so mu daraja su kuma mu bi umurninsu. (Ibraniyawa 13:​7, 17) Hakan ba shi da sauƙi. Amma muna iya yi wa Jehobah addu’a ya taimaka mana. Ruhunsa mai tsarki zai taimaka mana mu yi biyayya ga duka umurnin da dattawa suke bayarwa. Ka yi tunanin yadda ikilisiyar za ta amfana idan muka kasance da tawali’u kuma muka haɗa kai da dattawa. Ikilisiyarmu za ta kasance da haɗin kai kuma za mu ƙaunaci juna sosai.

10. Ta yaya bayi masu hidima suke taimaka wa ‘yan’uwa a cikin ikilisiya su kasance da haɗin kai? (Ka duba hoton da ke shafi na 18.)

10 Bayi masu hidima suna taimaka wa ikilisiyar ta kasance da haɗin kai. Suna iya ƙoƙarinsu don su taimaka wa dattawa kuma muna musu godiya don wannan aikin da suke yi. Alal misali, bayi masu hidima suna tabbata cewa ikilisiyar tana da cikkaken littattafai da za a yi amfani da su a wa’azi kuma suna marabtar baƙi da suka zo taronmu. Ƙari ga haka, suna aiki don su gyara Majami’ar Mulkin da kuma tsabtace ta. Idan muka haɗa kai da waɗannan ‘yan’uwa, za mu kasance da haɗin kai kuma mu bauta wa Jehobah a hanyar da ta dace.​—⁠Ka gwada da Ayyukan Manzanni 6:​3-6.

11. Mene ne ‘yan’uwa matasa za su iya yi don taimaka wa ‘yan’uwa a ikilisiya su kasance da haɗin kai?

11 Wasu dattawa sun yi shekaru da yawa suna aiki tuƙuru a madadin ‘yan’uwa a ikilisiya. Amma wataƙila yanzu ba za su iya yin aikin da suka saba yi ba don su soma tsufa. ‘Yan’uwa matasa suna iya taimakawa a wannan yanayin. Idan aka horar da su, za su iya yin ayyuka da dama a cikin ikilisiya. Idan bayi masu hidima suka yi aiki sosai, suna iya zama dattawa. (1 Timotawus 3:​1, 10) Wasu matasa da suke hidima a matsayin dattawa sun yi aiki sosai don su sami ci gaba a ibadarsu ga Jehobah kuma a yanzu suna hidima a matsayin masu kula da da’ira. Suna ziyarar ‘yan’uwa maza da mata a ikilisiyoyi dabam-dabam don su ƙarfafa su. Muna farin ciki sa’ad da muka ga matasa suna ba da kansu da yardar rai don su yi wa ‘yan’uwa hidima.​—⁠Karanta Zabura 110:3; Mai-Wa’azi 12:⁠1.

KU KASANCE DA HAƊIN KAI A CIKIN IYALI

12, 13. Mene ne zai iya taimaka membobin iyali su kasance da haɗin kai?

12 Ta yaya za mu iya taimaka wa waɗanda ke cikin iyalinmu sun kasance da haɗin kai? Bauta ta iyali da muke yi kowace mako zai iya taimaka mana. Idan iyaye da yara suka haɗa kai tare don su koyi abubuwa game da Jehobah, hakan zai ƙara dankon soyayyar da suke yi wa juna. A wannan lokacin, suna iya gwada abin da za su faɗa sa’ad da suka fita wa’azi kuma hakan zai taimaka wa dukan su su kasance a shirye. Ƙari ga haka, idan suka ji wani a cikin iyalin yana magana game da Jehobah, za su ga cewa kowa a cikin iyalin yana ƙaunar Jehobah kuma yana so ya faranta masa rai. Hakan yana sa iyalin su kusaci juna sosai.

13 Ta yaya mutum da matarsa za su ba wa juna haɗin kai. (Matta 19:⁠6) Idan suna ƙaunar Jehobah kuma suna bauta masa tare, hakan zai sa su yi farin ciki kuma su kasance da haɗin kai a aurensu. Ya kamata su ƙaunaci juna sosai kamar yadda Ibrahim da Saratu da Ishaƙu da Rifkatu da Elkanah da kuma Hannatu suka yi. (Farawa 26:8; 1 Sama’ila 1:​5, 8; 1 Bitrus 3:​5, 6) Sa’ad da miji da matarsa suka yi haka, za su kasance da haɗin kai kuma za su kusaci Jehobah sosai.​—⁠Karanta Mai-Wa’azi 4:12.

Ibada ta iyali tana taimaka wa yara da manya su kusaci juna sosai (Ka duba sakin layi na 12, 15)

14. Idan mijinki ko matarka ba ta bauta wa Jehobah, mene ne za ka iya yi don ka ƙarfafa aurenku?

14 Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa kada mu auri wanda ba ya bauta wa Jehobah. (2 Korintiyawa 6:14) Duk da haka, akwai ‘yan’uwa maza da mata da suka auri wanda ba Mashaidin Jehobah ba. Wasu sun koyi gaskiya game da Jehobah bayan sun yi aure amma abokin aurensu bai zama Mashaidi ba. Wasu kuma sun auri wanda yake bauta wa Jehobah amma daga baya ya bar ikilisiya. A wannan yanayin, dukan Kiristoci suna bukatar su bi umurnin Littafi Mai Tsarki wajen kāre aurensu. Hakan ba abu mai sauƙi ba ne. Alal misali, wata ‘yar’uwa mai suna Mary da mijinta David suna bauta wa Jehobah tare. Daga baya, David ya daina zuwa taro. Amma Mary ta ci gaba da yi masa ladabi a matsayinta matar kirki kuma ta nuna halayen Kirista. Ƙari ga haka, ta koya wa yaranta guda shida game da Jehobah kuma ta ci gaba da zuwa taro da kuma manyan taro. Shekaru da yawa bayan haka, yaran sun yi girma kuma suka bar gida amma Mary ta ci gaba da bauta wa Jehobah duk da cewa yin hakan yana da wuya. Daga baya, David ya fara karanta mujallun da Mary take ajiye masa. Da shigewar lokaci, ya fara halartar taron. Jikansa mai shekara shida ne yake keɓe masa wurin zama kuma a duk ranar da David bai zo taro ba, yaron zai gaya masa cewa, “Na yi kewar ka yau a taro kaka.” Bayan shekara 25, David ya komo ga Jehobah kuma yanzu shi da matarsa suna bauta wa Jehobah tare.

15. Ta yaya ma’auratan da suka daɗe da yin aure da za su taimaka wa sababbin ma’aurata?

15 A yau, Shaiɗan yana kai wa iyalai hari. Shi ya sa ma’aurata da suke bauta wa Jehobah suna bukatar su kasance da haɗin kai. Ko da kun daɗe da yin aure, ku yi tunanin abin da za ku yi da zai ƙarfafa aurenku. Idan ku ma’aurata ne da suka daɗe da yin aure, za ku iya kafa misali mai kyau wa ma’auratan da ba su daɗe da yin aure ba. Kuna iya gayyatar su gidanku don ku yi ibada ta iyali tare. Za su ga cewa suna bukatar sun ƙaunaci juna kuma su kasance da haɗin kai ko da sun daɗe da yin aure.​—⁠Titus 2:​3-7.

“KU ZO, MU HAU ZUWA DUTSEN UBANGIJI”

16, 17. Wane bege ne bayin Allah masu haɗin kai suke da shi?

16 Isra’ilawa sun kasance da haɗin kai sa’ad da suka je bukukuwa a Urushalima. Sun shirya dukan abin da suke bukata don wannan tafiyar. Bayan haka, sun yi tafiya tare kuma sun taimaka wa juna. A haikalin, sun yabi Jehobah kuma sun bauta masa tare. (Luka 2:​41-44) A yau, yayin da muke yin shiri don yin rayuwa a sabuwar duniya, muna bukatar mu kasance da haɗin kai kuma mu yi iya ƙoƙari don mu yi aiki tare. Shin akwai wasu abubuwa da za ka iya yi da zai kyautata haɗin kai da muke da shi?

17 A duniyar nan, mutane suna rigima da kuma faɗa a kan abubuwa da yawa. Amma muna gode wa Jehobah da ya taimaka mana mu fahimci gaskiya game da shi kuma mu kasance da kwanciyar hankali! Mutanensa a faɗin duniya suna bauta masa a hanyar da yake so. Kuma mutanen Jehobah sun ci gaba da kasancewa da haɗin kai musamman ma a wannan kwanaki na ƙarshe. Kamar yadda Ishaya da kuma Mikah suka annabta, za mu hau “dutsen Ubangiji” tare. (Ishaya 2:​2-4; karanta Mikah 4:​2-4.) Za mu yi farin ciki sosai a nan gaba sa’ad da dukan mutane a duniya suna zaman tare kuma za mu kasance da haɗin kai yayin da muke bauta wa Jehobah.

Idan ma’aurata suna ƙaunar Jehobah kuma suna bauta masa tare, hakan zai sa su yi farin ciki kuma su kasance da haɗin kai a aurensu