Za Ka Iya Taimaka wa ‘Yan’uwa a Ikilisiyarku?
KAFIN Yesu ya koma sama, ya ce wa almajiransa: “Za ku zama shaiduna . . . har . . . iyakan duniya.” (Ayyukan Manzanni 1:8) Shin ta yaya za su iya yin wa’azi a dukan wurare a duniya?
Wani farfesa mai suna Martin Goodman a Jami’ar Oxford, ya ce “Kiristoci sun san cewa hakkinsu ne su je inda mutane suke don su yi musu wa’azin bishara, kuma hakan ya sa sun fita dabam da sauran addinai, har da Yahudawa da ke Daular Roma a dā.” Yesu ya je wurare dabam-dabam don ya yi wa’azi. Wajibi ne Kiristoci na gaskiya su bi misalinsa kuma su yi wa’azin “bishara ta Mulkin Allah” a ko’ina. Suna bukatar su biɗi mutanen da ke son sanin gaskiya. (Luka 4:43) Shi ya sa a ƙarni na farko, akwai “manzanni” wato waɗanda aka aika su su cim ma wani abu. (Markus 3:14) Yesu ya umurci mabiyansa game da hakan sa’ad da ya ce: “Ku tafi fa, ku almajirtar da dukan al’ummai.”—Matta 28:18-20.
Ko da yake almajiran Yesu sun mutu da daɗewa, bayin Jehobah da yawa suna bin misalin da suka kafa a yin bishara. A duk lokacin da aka tura su wa’azi, suna ba da kansu kamar Ishaya da ya ce: “Ga ni; ka aike ni.” (Ishaya 6:8) Alal misali, waɗanda suka sauke karatu a Makarantar Littafi Mai Tsarki na Gilead, sun je ƙasashe masu nisa. Wasu kuma sun ƙaura zuwa wani yanki a ƙasarsu. Da yawa sun koyi sabon yare don su taimaka wa wata ikilisiya ko kuma rukuni. Yin hakan bai da sauƙi, amma waɗannan ‘yan’uwa maza da mata sun yi hakan da son rai don suna ƙaunar Jehobah da kuma mutane. Saboda haka, sun shirya da kyau don su yi amfani da lokacinsu da kuzarinsu da kuma wadatarsu su je yin wa’azi inda ake bukatar masu shela sosai. (Luka 14:28-30) Abin da waɗannan ‘yan’uwa maza da mata suke yi yana da muhimmanci sosai.
Ba dukanmu ba ne za mu iya zuwa inda ake bukatar masu shela, kuma ba kowa ba ne zai iya koyan sabon yare. Amma dukanmu za mu iya yin hidima a ikilisiyarmu kamar masu yin wa’azi a ƙasar waje.
KA YI HIDIMA A IKILISIYARKU KAMAR MAI WA’AZI A ƘASAR WAJE
A ƙarni na farko, Kiristoci sun yi wa’azin bishara da ƙwazo duk da cewa yawancinsu sun kasance a garinsu kuma ba su je yin wa’azi a ƙasar waje ba. Bulus ya gaya wa Timotawus: “Ka yi aikin mai-bishara, ka cika hidimarka.” (2 Timotawus 4:5) Waɗannan kalaman sun shafe mu a yau kamar yadda suka shafi Kiristoci a ƙarni na farko. Wajibi ne dukan Kiristoci su yi wa’azin bishara kuma su taimaka wa mutane su zama almajiran Yesu. Akwai hanyoyi da yawa da za mu iya zama kamar masu yin wa’azi a ƙasar waje, a cikin ikilisiyarmu.
Alal misali, masu yin wa’azi a ƙasar waje sukan ƙaura zuwa wata ƙasa, inda tsarin abubuwan ya bambanta da na ƙasarsu. Saboda haka, suna bukata su saba da sabon salon rayuwa da suka sami kansu a ciki. Ko da ba za mu iya zuwa inda ake bukatar masu shela ba, za mu iya ƙirƙiro wasu hanyoyin yi wa mutane wa’azi. A shekara ta 1940, an ƙarfafa ‘yan’uwanmu su yi amfani da rana ɗaya a mako wajen yi wa mutane wa’azi a titi. Ka taɓa yi wa mutane a titi? Ka taɓa yin wa’azi da amalanken nuna littattafai? Abin da ake nufi a nan shi ne, za ka so ka bi wani sabon tsari wajen yin wa’azin bishara?
Idan kana da ra’ayin da ya dace, za ka kasance da himma da kuma sha’awar yin wa’azin bishara. Waɗanda suke zuwa inda ake bukatar masu shela da kuma waɗanda suke koyan sabon yare sukan zama da ƙwazo sosai kuma suna taimakawa a ikilisiya. Alal misali, sukan ja-goranci masu fita wa’azi. Masu wa’azi a ƙasar waje sukan yi ja-gora a cikin ikilisiya har sai ‘yan’uwa da ke yankin sun ƙware. Idan kai ɗan’uwa ne da ya yi baftisma, shin kana “biɗan 1 Timotawus 3:1.
aiki,” ma’ana, kana ba da kanka don ka yi wa ‘yan’uwa maza da mata da ke ikilisiyarku hidima a matsayin bawa mai hidima ko kuma dattijo?—KA RIƘA ƘARFAFA ‘YAN’UWANKA
Za mu iya taimakawa a ikilisiyarmu a wasu hanyoyi dabam. Dukanmu, yara da manya, maza da mata za mu iya ƙarfafa ‘yan’uwa da suke bukatar hakan.—Kolosiyawa 4:11.
Idan muna so mu taimaka wa ‘yan’uwanmu maza da mata, muna bukata mu san su sosai. Littafi Mai Tsarki ya ƙarfafa mu mu “lura da juna,” wato mu yi la’akari da bukatun ‘yan’uwanmu maza da mata sa’ad da muka haɗu da su. (Ibraniyawa 10:24) Ba wai za mu riƙa sa ido a abubuwan suke yi da ba su shafe mu ba. Amma hakan yana nufin cewa mu yi ƙoƙarin sanin ‘yan’uwanmu maza da mata da kuma abubuwan da suke bukata. Za mu iya taimaka musu ta wajen ba su abin biyan bukata ko ta ziyararsu ko kuma ta ƙarafa su daga Littafi Mai Tsarki. Ko da yake, a wani yanayi, dattawa ne kawai za su iya taimaka musu. (Galatiyawa 6:1) Amma dukanmu za mu iya taimaka wa ‘yan’uwa maza da mata da suka tsufa, ko iyalai da suke fuskantar matsaloli.
Irin taimakon da aka yi wa Salvatore ke nan. Ya sami koma baya sosai a kasuwancinsa. Saboda haka, ya sayar da sa’anarsa da gidansa da wasu abubuwa da dama da iyalin suka mallaka. Hakan ya sa shi damuwa sosai game da iyalinsa. Sa’ad da wani ɗan’uwa da iyalinsa suka lura cewa iyalin Salvatore suna bukatar taimako, sai suka ba su kuɗi kuma suka taimaka wa matarsa ta sami aikin yi. Ƙari ga haka, sun riƙa ziyarar iyalin kowace yamma don su ƙarfafa su. Hakan ya sa sun zama abokai na kud da kud. Yanzu iyalan biyu ba sa manta da yadda suka shaƙu a wannan mawuyacin lokaci.
Kiristoci na gaskiya ba sa jinkirin gawa wa mutane abin da suka yi imani da shi. Wajibi ne mu yi koyi da Yesu kuma mu sanar da kowa game da alkawuran da Allah ya yi. Ko da za mu iya ƙaura ko a’a, dukanmu za mu iya yin ƙoƙarinmu mu taimaka wa wasu a cikin ikilisiyarmu. (Galatiyawa 6:10) Yayin da muke taimaka wa wasu, za mu yi farin ciki kuma za mu “ba da ‘ya’ya cikin kowane kyakkyawan aiki.”—Kolosiyawa 1:10; Ayyukan Manzanni 20:35.