Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Yara da Matasa, Ta Yaya Za Ku Yi Shirin Yin Baftisma?

Yara da Matasa, Ta Yaya Za Ku Yi Shirin Yin Baftisma?

“Murna nake yi in yi nufinka, ya Allahna.”—ZABURA 40:8.

WAƘOƘI: 51, 58

1, 2. (a) Ka bayyana abin da ya sa baftisma ba abin wasa ba ne. (b) Me ya kamata mutumin da yake so ya yi baftisma ya tabbata da shi kafin ya yi hakan kuma me ya sa?

SHIN kai yaro ne ko kuma matashi da ya kai yin baftisma, kuma za ka so ka yi hakan? Idan haka ne, wannan babban gatan ne a gare ka. A talifi na farko, an tattauna cewa baftisma mataki ne mai muhimmanci sosai. Yana nuna wa mutane cewa ka keɓe kanka ga Jehobah wato ka yi masa alkawari cewa za ka bauta masa har abada. Ƙari ga haka, yin nufinsa ne abu mafi muhimmanci a rayuwarka. Wannan alkawarin da ka yi wa Allah yana da muhimmanci sosai. Shi ya sa kake bukatar ka manyanta sosai kuma ya kasance kai ne ka tsai da shawarar yin baftisma da kanka. Ƙari ga haka, ka fahimci abin da keɓe kai ga Allah yake nufi.

2 Amma, wataƙila kana ganin kamar ba ka yi shirin yin baftisma ba. Ko kuma kana ganin ka shirya amma iyayenka sun ce ka jira har sai ka girma kuma ka yi wayo. Shin me ya kamata ka yi? Kada ka karaya. A maimakon haka, ka yi amfani da wannan lokacin ka inganta ƙudurinka don ka zama wanda ya cancanta ya yi baftisma nan ba da daɗewa ba. Zai dace ka yi la’akari da abubuwa guda uku don ka cim ma hakan: (1) bangaskiyarka, (2) ayyukanka (3) nuna godiya ga Allah.

ABIN DA KA YI IMANI DA SHI

3, 4. Wane darasi ne yara da matasa za su iya koya daga misalin Timotawus?

3 Ka yi tunanin yadda za ka amsa waɗannan tambayoyin: Me ya sa na gaskata cewa akwai Allah? Me ya sa nake da tabbacin cewa Littafi Mai Tsarki littafi ne daga Allah? Me ya sa nake yin biyayya ga umurnin Allah maimakon na yi koyi da abubuwan da mutanen duniya suke yi? Waɗannan tambayoyin za su taimaka maka ka bi shawarar da manzo Bulus ya bayar cewa: ‘Ku tabbatar da abin da Allah ke so, wato nufinsa kyakkyawa, abin karɓa, cikakke kuma.’ (Romawa 12:⁠2) Me ya sa ya kamata ka yi hakan?

Timotawus ya amince da abin da ya koya don ya yi tunani da kuma tabbatar da hakan

4 Misalin da Timotawus ya kafa zai iya taimaka maka. Mahaifiyarsa da kuma kakarsa sun koya masa game da Jehobah. Hakan ya sa ya san Nassosi sosai. Amma Bulus ya gaya wa Timotawus cewa: ‘Ka lizima kai a cikin al’amuran da ka koya, waɗanda ka tabbata da su.’ (2 Timotawus 3:​14, 15) Wannan kalmar “tabbata” tana nufin amincewa da “gaskiyar wani batu.” Saboda haka, Timotawus ya tabbata cewa abubuwan da yake koya gaskiya ne kuma suna cikin Nassosi. Ya amince da hakan ne don ya yi tunani da kuma tabbatar da abin da ya koya ba don mahaifiyarsa da kuma kakarsa sun gaya masa ya gaskata da hakan ba.​—Karanta Romawa 12:⁠1.

5, 6. Me ya sa yake da muhimmanci ku koyi yadda za ku yi amfani da “hankalinku” tun da wuri?

5 Kai kuma fa? Wataƙila ka daɗe kana koya game da Jehobah. Idan haka ne, ka yi tunani sosai a kan dalilan da suka sa ka amince da gaskiyar da koya. Hakan zai taimaka maka ka ƙarfafa bangaskiyarka. Ƙari ga haka, zai sa ka guji yin shawarwarin da ba su dace ba saboda matsi daga tsaranka, ko ra’ayin mutanen duniya ko kuma ra’ayinka.

6 Idan ka koya yin amfani da hankalinka sa’ad da kake yaro ko kuma matashi, za ka iya amsa tambayoyin da tsaranka za su yi maka kamar: ‘Wane tabbaci kake da shi cewa Allah ya wanzu? Idan Allah yana ƙaunarmu, me ya sa ya bar mugayen abubuwan suna faruwa? Idan Allah ya halicci kome, wane ne ya halicci Allah?’ Sa’ad da ka soma yin nazarin Littafi Mai Tsarki cikin natsuwa, irin waɗannan tambayoyin ba za su sa ka fara yin shakka a zuciyarka ba. A maimakon haka, za su motsa ka ka ƙarfafa bangaskiyarka.

7-9. Ka kwatanta yadda wannan jerin umurni don nazari na “Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?” da ke dandalinmu zai taimaka maka ka tabbata da abin da ka yi imani da shi.

7 Idan kana mai da hankali wajen yin nazarin Littafi Mai Tsarki sosai, hakan zai taimaka maka ka iya amsa wasu tambayoyi. Ƙari ga haka, zai taimake ka ka daina shakka kuma zai sa ka kasance da tabbaci game da abin da ka yi imani da shi. (Ayyukan Manzanni 17:11) Akwai littattafai da yawa da za su taimaka maka ka yi hakan. Mutane da yawa sun yi nazarin ƙasidar nan The Origin of Life—Five Questions Worth Asking da littafin nan Is There a Creator Who Cares About You? kuma ya taimaka musu sosai. Ƙari ga haka, matasa da yawa sun amfana sosai daga jerin “Menene Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?” da yake a dandalinmu na jw.org/ha. Za ka iya samunsa a ƙarƙashin KOYARWAR LITTAFI MAI TSARKI. An tsara kowane umurni don nazari a wannan jerin don ya taimaka maka ka ƙarfafa imaninka game da wani batu da aka tattauna a cikin Littafi Mai Tsarki.

8 Da yake kana nazarin Littafi Mai Tsarki, wataƙila ka san amsoshin wasu tambayoyin da ke cikin waɗannan umurni don nazari. Amma ka tabbata da amsoshin kuwa? Wannan umurni don nazari zai taimaka maka ka yi tunani sosai game da nassosi dabam-dabam na Littafi Mai Tsarki kuma zai motsa ka ka rubuta dalilin da ya sa ka gaskata da abin da ka yi imani da shi. Hakan zai taimaka maka ka san yadda za ka bayyana wa mutane abin da ka yi imani da shi. Idan kana iya shiga dandalin jw.org/⁠ha, ka nemi jerin “Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?” za ka iya amfani da shi a nazarin Littafi Mai Tsarki don ya taimaka maka ka tabbata da abin da ka yi imani da shi.

9 Kana bukatar ka tabbatar wa kanka cewa abin da kake koya gaskiya ne. Hakan zai taimaka maka ka yi shiri da kyau don yin baftisma. Wata ‘yar’uwa matashiya ta ce: “Kafin na yanke shawarar yin baftisma, na yi nazarin Littafi Mai Tsarki kuma na kasance da tabbacin cewa wannan shi ne addini na gaskiya. A kowace rana, na ci gaba da ƙarfafa wannan tabbacin.”

AYYUKANKA

10. Me ya sa ya kamata Kirista da ya yi baftisma ya riƙa yin ayyukan da suka jitu da imaninsa?

10 Littafi Mai Tsarki ya ce: “Hakanan kuwa bangaskiya, in ba ta da ayyuka ba, matacciya ce cikin kanta.” (Yaƙub 2:17) Idan ka tabbata da abin da ka yi imani da shi sosai, za ka nuna hakan ta ayyukanka. Za ka kasance da abin da Littafi Mai Tsarki ya kira “tasarrufi mai-tsarki da ibada kuma.”​—Karanta 2 Bitrus 3:⁠11.

11. Ka bayyana abin da wannan kalmar “tasarrufi mai-tsarki” take nufi.

11 Mene ne ake nufin da “tasarrufi mai-tsarki”? Za ka iya kasancewa da ɗabi’u masu kyau idan ayyukanka masu tsarki ne. Alal misali, ka yi tunanin wata shida da suka wuce. Shin ka yi tunani sosai game da nagarta da mugunta sa’ad da ka fuskanci gwajin yin abin da bai da kyau? (Ibraniyawa 5:14) Shin ka tuna da wasu lokatai da ka guje wa gwaji ko kuma ka ƙi yin abin da tsaranka suka ce ka yi? Shin kana nuna halaye masu kyau a makaranta kuwa? Kana kasancewa da aminci ga Jehobah ne ko kuma kana ƙoƙarin ka zama kamar ‘yan ajinka don kada su yi maka ba’a? (1 Bitrus 4:​3, 4) Hakika dukan mu ajizai ne. A wani lokaci, waɗanda suka daɗe suna bauta wa Jehobah suna iya jin kunyar yi wa mutane wa’azi. Amma wanda ya keɓe kansa ga Jehobah yana alfahari cewa shi Mashaidin Jehobah ne kuma saboda haka, zai nuna halaye masu kyau.

12. Mene ne ayyukan ibada suka ƙunsa kuma yaya ya kamata mu ɗauki waɗannan ayyuka?

12 Mene ne ayyukan “ibada” suka ƙunsa? Sun ƙunshi ayyukan da kake yi a ikilisiya kamar zuwa taro da kuma wa’azi. Ƙari ga haka, sun ƙunshi abubuwan da mutane ba za su iya gani ba kamar addu’arka ga Jehobah da kuma nazarin Littafi Mai Tsarki da kake yi. Wanda ya keɓe kansa ga Jehobah ba zai riƙa ganin waɗannan abubuwan kamar kaya mai nauyi a gare shi ba. Amma zai jin kamar yadda Sarki Dauda ya ce: “Murna na ke yi in yi nufinka, ya Allahna, Hakika, shari’arka tana cikin zuciyata.”​—⁠Zabura 40:8.

13, 14. Mene ne zai taimaka maka ka yi ayyukan “ibada,” kuma ta yaya wasu matasa suka amfana daga yin haka?

13 Idan kana so ka cim ma maƙasudanka, kana bukata ka yi wa kanka wasu tambayoyi kamar: “Shin ina ambata wasu abubuwa na musamman a addu’o’ina, kuma hakan ya nuna cewa ina ƙaunar Jehobah da gaske?” “Waɗanne abubuwa ne nake nazarin Littafi Mai Tsarki a kai?” “Ina zuwa wa’azi ko da iyayena ba su je ba?” Kana iya rubuta amsoshinka ga waɗannan tambayoyin. Ƙari ga haka, za ka iya rubuta maƙasudan da kake so ka cim ma game da addu’arka da nazarin Littafi Mai Tsarki da kuma wa’azi.

Shin kana ambata wasu abubuwa na musamman a addu’o’inka, kuma hakan ya nuna cewa kana ƙaunar Jehobah da gaske?

14 Matasa da yara da yawa da suke so su yi baftisma sun amfana sa’ad da suka rubuta maƙasudansu. Wata ‘yar’uwa matashiya mai suna Tilda ta ce takan rubuta maƙasudanta kuma ta hakan, ta cim ma waɗannan maƙasudan da ta kafa ɗaya bayan ɗaya. Bayan wajen shekara ɗaya, ta cancanci ta yi baftisma. Wani ɗan’uwa matashi mai suna Patrick ya ce: “Na san maƙasudaina amma rubuta su ya taimaka min in yi aiki tuƙuru don na cim ma waɗannan maƙasudan.”

Shin za ka bauta wa Jehobah ko da iyayenka sun daina yin hakan? (Ka duba sakin layin na 15)

15. Mene ne ya sa ya kamata ka yanke shawarar yin baftisma da kanka?

15 Ɗaya daga cikin tambayoyin da ke shafin rubutun shi ne: “Shin za ka bauta wa Jehobah ko da iyayenka da kuma abokanka sun daina yin hakan?” Sa’ad da ka keɓe kanka ga Jehobah kuma ka yi baftisma, za ka kasance da dangantaka ta kud da kud da shi. Saboda haka, kada ka dogara ga iyayenka ko kuma wani a bautarka ga Jehobah. Kasancewa da halaye masu kyau da ibada da kuma yin ayyuka da suka shafi ibada za su nuna ka tabbata cewa abin da ka koya gaskiya ne kuma kana so ka bi waɗannan ƙa’idodin. Waɗannan abubuwa za su sa ka zama wanda ya cancanta ya yi baftisma nan ba da daɗewa ba.

NUNA GODIYA GA ALLAH

16, 17. (a) Mene ne ya kamata ya motsa mutum ya zama Kirista? (b) Ta yaya za a iya kwatanta nuna godiya saboda fansar?

16 Wani masanin Attaura ya tambayi Yesu: “Malam, wace ce babbar doka a cikin Attaurat?” Yesu ce masa: “Ka yi ƙaunar Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka, da dukan ranka, da dukan azancinka.” (Matta 22:​35-37) Yesu ya bayyana cewa yadda mutum yake ƙaunar Jehobah ne zai sa shi ya yi baftisma kuma ya zama Kirista. Za ku iya daɗa ƙaunar Jehobah ta yin bimbini a kan yadda Jehobah ya ba da ɗansa don ya fanshe mu daga zunubi da mutuwa. Wannan ita ce kyauta mafi tamani da Allah ya ba wa ‘yan Adam. (Karanta 2 Korintiyawa 5:​14, 15; 1 Yohanna 4:​9, 19.) Idan kuka yi hakan, za ku so ku nuna godiyarku don wannan kyauta mai muhimmanci.

17 Za a iya kwatanta godiyarku don wannan fansa a wannan hanyar: A ce kana nitsewa a cikin ruwa, sai wani ya zo ya cece ka. Shin za ka tashi ka tafi gida ne kuma ka manta da abin da wannan mutumin ya yi maka? A’a! A kowane lokaci, za ka riƙa nuna masa godiya don ya cece ka! Hakazalika, ya kamata mu riƙa gode wa Jehobah da kuma Yesu saboda wannan kyautar fansa. Sun cece mu daga zunubi da kuma mutuwa. Yanzu muna da begen yin rayuwa har abada a aljanna don suna ƙaunarmu!

18, 19. (a) Me ya sa bai kamata ka ji tsoron bauta wa Jehobah ba? (b) Ta yaya bauta wa Jehobah zai sa rayuwarka ta kasance da ma’ana?

18 Shin kana gode wa Jehobah saboda abin da ya yi maka? Idan haka ne, ya dace ka keɓe kanka ga Jehobah kuma ka yi baftisma. Ka yi wa Jehobah alkawari sa’ad da kake keɓe kanka cewa za ka yi nufinsa har abada. Ya kamata ka ji tsoron yin wannan alkawarin ne? A’a! Jehobah yana so ka ji daɗin rayuwa kuma zai albarkaci duk waɗanda suke yin nufinsa. (Ibraniyawa 11:⁠6) Sa’ad da ka keɓe kanka ga Jehobah kuma ka yi baftisma, rayuwarka za ta kasance da ma’ana! Wani ɗan’uwa mai shekara 24 da ya yi baftisma kafin ya zama matashi ya ce, “Da a ce na jira har sai na girma da wataƙila na fahimci wasu abubuwa amma shawarar da na yanke na keɓe kaina ga Jehobah ya kāre ni daga biɗan abin duniya.”

19 Jehobah yana so ka yi farin ciki a rayuwarka sosai. Amma Shaiɗan mugu ne kuma ba ya ƙaunar ka. Ba shi da wani abu mai kyau da zai ba ka idan ka bi shi. Ba shi da wani albishiri mai kyau kuma ba shi da begen yin rayuwa a nan gaba. Bin Shaiɗan zai kai ga hallaka don shi ma za a hallaka shi!​—⁠Ru’ya ta Yohanna 20:⁠10.

Shaiɗan mugu ne kuma ba ya ƙaunar ka

20. Mene ne yara da kuma matasa za su yi don su samu ci gaba har su keɓe kansu ga Jehobah kuma su yi baftisma? (Ka duba akwatin nan “Abin da Zai Taimaka Maka Ka Sami Ci Gaba.”)

20 Shawara mafi kyau da za ka yi ita ce keɓe kanka ga Jehobah. Shin ka shirya? Idan amsarka e ce, kada ka ji tsoron keɓe kanka ga Jehobah. Amma idan kana ganin cewa ba ka shirya ba, ka yi amfani da shawarwarin da ke cikin wannan talifin don ka sami ci gaba. Bulus ya gaya wa ‘yan’uwan da ke Filibbiyawa cewa su riƙa ci gaba a bautar su ga Jehobah. (Filibbiyawa 3:16) Idan ka bi wannan shawarar, ba da daɗewa ba za ka keɓe kanka ga Jehobah kuma ka yi baftisma.