Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TARIHI

Jehobah Bai Taba Yasar da Ni Ba

Jehobah Bai Taba Yasar da Ni Ba

INA cikin yara huɗu da aka zaɓa su ba Adolf Hitler furanni bayan ya yi wani jawabi. Me ya sa aka zaɓe ni? A lokacin mahaifina yana goyon bayan ’yan Nazi sosai kuma shi direban wani shugabansu ne. Ƙari ga haka, mahaifiyata ’yar Katolika ce kuma tana son in je zama a gidan zuhudu. Duk da haka, ban zama ’yar Nazi ba kuma ban je zaman zuhudu ba. Bari in gaya muku dalilin.

AN HAIFE ni a birnin Graz da ke ƙasar Austriya. A lokacin da nake ’yar shekara bakwai, iyayena sun tura ni makarantar addini. Amma firistoci da kuma ’yan zaman zuhudu suna lalata sosai da juna. Hakan ya sa mahaifiyata ta cire ni daga makarantar kafin in yi shekara ɗaya a wurin.

Iyalinmu da mahaifina sanye da rigar soja

Bayan haka, sai aka tura ni makarantar kwana. Wata rana daddare, mahaifina ya zo don ya ɗauke ni da yake ana ruwan bama-bamai a birnin Graz. Mun je mun ɓoye a garin Schladming. Jim kaɗan bayan mun haye gada, sai bam ya sake tashi ya ragargaje gadar. Ban da haka, wata rana da ni da kakata muke cikin gida, sai sojoji a cikin jirgin sama suke ta harbin mu. Da aka daina yaƙin, mun ga cewa addini da gwamnati sun cuce mu.

YADDA NA KOYA GAME DA JEHOBAH

A 1950, wata Mashaidiyar Jehobah ta soma nazarin Littafi Mai Tsarki da mahaifiyata. Nakan saurari abin da suke tattaunawa, a wasu lokuta ma, ina bin mahaifiyata zuwa taronsu. Da yake mahaifiyata ta gaskata cewa Shaidun Jehobah ne suke koyar da gaskiya, sai ta yi baftisma a shekara ta 1952.

A lokacin, na ɗauka cewa ikilisiyar wurin taron mata tsofaffi ne. Amma da muka halarci taro a wata ikilisiya, na ga matasa da yawa kuma hakan ya sa na daina ɗaukar ikilisiya wurin taron mata tsofaffi. Da muka koma birnin Graz, sai na soma halartar duka taro. Bayan ɗan lokaci, sai na gaskata da abin da nake koya. Kuma hakan ya sa na tabbatar da cewa Jehobah, Allah ne da ke taimaka wa bayinsa. Yana yin hakan har a lokacin da suke fuskantar matsalolin da suke ganin babu mafita.​—Zab. 3:​5, 6.

Ina son yi wa mutane wa’azi kuma waɗanda na fara yi wa hakan su ne ’yan’uwana. Yayyena mata guda huɗu ba sa zama tare da mu don su malamai ne a wasu ƙauyuka. Amma nakan ziyarce su don in ƙarfafa su su yi nazarin Littafi Mai Tsarki. Daga baya, dukan yayyena biyar da ƙanwata guda sun soma bauta wa Jehobah.

A mako na biyu da na soma fita wa’azi, na haɗu da wata mata da ta ba shekara 30 baya, kuma muka soma nazarin Littafi Mai Tsarki. Ta sami ci gaba sosai a nazarinta. Daga baya, ita da mijinta da kuma yaranta biyu suka yi baftisma. Nazarin da na yi da matar ya ƙarfafa bangaskiyata sosai. Me ya sa? Dalilin shi ne, ba wanda ya taɓa yin nazarin Littafi Mai Tsarki da ni. Hakan ya sa ina yin shiri sosai kafin in yi nazari da ita, kamar dai ina koyar da kaina ne kafin in je in koyar da ita. Yin hakan ya sa na fahimci Littafi Mai Tsarki sosai kuma na yi baftisma a watan Afrilu na 1954.

AN TSANANTA MANA, AMMA BA A YASAR DA MU BA

Na halarci taron ƙasashe a Jamus da Faransa da kuma Ingila a 1955. A lokacin da nake Landan, na haɗu da Ɗan’uwa Albert Schroeder. Shi malami ne a Makarantar Gilead kuma daga baya ya zama memban Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu. A lokacin da muka je zagaya a ma’adanar kayayyakin tarihi na Biritaniya, Ɗan’uwa Schroeder ya nuna mana wasu littattafan Littafi Mai Tsarki na dā. Kuma littattafan suna ɗauke da sunan Allah a baƙaƙen Ibrananci. Bayan haka, ya bayyana mana muhimmancin sunan. Abin da ya faɗa ya sa na daɗa ƙaunar Jehobah da kuma gaskiyar da ke cikin Kalmarsa.

Ni da abokiyar wa’azina (dama), sa’ad da muke hidimar majagaba na musamman a garin Mistelbach a Austriya

Na soma yin hidimar majagaba na cikakken lokaci a ranar 1 ga Janairu, 1956. Bayan wata huɗu, sai aka tura ni yin hidimar majagaba na musamman a garin Mistelbach a ƙasar Austriya. A lokacin babu Shaidun Jehobah a garin. Na fuskanci wani ƙalubale mai wuya sosai. Ni da abokiyar wa’azina mun bambanta. Ni wajen ’yar shekara 19 ce a lokacin, kuma daga birni na fito, amma ita ’yar shekara 25 ce kuma daga ƙauye ta fito. Ba na tashi daga barci da wuri, amma ita tana tashi da asuba. Da daddare kuma ba na barci da wuri, amma ita tana barci da wuri. Amma duk da haka, mun bi ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki don mu magance matsalolinmu kuma mun ji daɗin hidimarmu tare.

Amma mun fuskanci matsalolin da suka fi waɗannan. Har ma an tsananta mana, amma Allah bai ‘yasar’ da mu ba. (2 Kor. 4:​7-9) Wata rana da muke wa’azi a wani ƙauye, sai mutanen suka cinna mana manyan karnuka. Karnukan suka kewaye ni da abokiyar wa’azina suna ta haushi kamar za su cije mu. Da muka ga haka, sai muka riƙe hannu, har na yi addu’a ga Jehobah cewa, “Jehobah ka taimake mu, idan suka haura mana mu mutu da sauri!” Sa’ad da karnukan suka zo kusa da mu, sai suka tsaya suna kaɗa wutsiyarsu kuma suka yi tafiyar su. Hakan ya sa mun tabbatar da cewa Jehobah ne ya kāre mu. Bayan haka, mun yi wa’azi a ƙauyen gabaki ɗaya kuma mun yi farin ciki cewa mutanen sun saurare mu sosai. Wataƙila don suna mamaki cewa ko da yake karnukan sun tsoratar da mu, mun ci gaba da yin wa’azi. Daga baya wasu cikin mutanen sun soma bauta wa Jehobah.

Mun fuskanci wata matsala kuma da ta tsoratar da mu. Wata rana, mutumin da muke haya a gidansa ya dawo gida a buge. Kuma ya ce zai kashe mu don muna damun mutane a unguwar. Matarsa ta yi ƙoƙarin hana shi amma bai yiwu ba. Mu kuma muna ɗakinmu muna jin su. Ba tare da ɓata lokaci ba, sai muka tāre ƙofar ɗakin da kujera kuma muka soma kwashe kayanmu. Da muka buɗe ƙofar, sai muka ga mutumin yana tsaye a kan matakala yana riƙe da babba wuƙa. Sai muka gudu da kayayyakinmu. Mun fita ta ƙofar baya kuma ba mu ƙara komawa ba.

Mun nemi wani masauki kuma mun zauna a wurin kusan shekara ɗaya. Hakan ya taimaka mana a hidimarmu sosai. Ta yaya? Masaukin yana cikin gari kuma wasu cikin ɗalibanmu suna son zuwa wurin don nazarin Littafi Mai Tsarki. Ba da daɗewa ba, sai muka soma rukunin nazari da kuma nazarin Hasumiyar Tsaro kowane mako a ɗakinmu, kuma wajen mutane 15 ne suke halarta.

Mun yi hidima a Mistelbach fiye da shekara ɗaya. Bayan haka, an tura ni yin hidima a garin Feldbach da ke kudu maso gabashin Graz. Kuma na sami wata abokiyar wa’azi, amma babu ikilisiya a garin ma. Mun zauna a wani ƙaramin ɗaki da ke ƙasan wani gidan bene na katako. Da yake akwai ramuka a ɗakin, iska tana shiga ciki sosai, sai muka yi amfani da jaridu don mu taushe ramukan. Ban da haka ma, a rijiya muke ɗiban ruwa, amma duk da haka, mun yi farin ciki don ba da daɗewa ba, an kafa rukuni a garin. Kuma mutane 30 a iyalin da muke nazari da su ne suka yi baftisma!

Irin labaran nan sun sa na ƙara godiya don yadda Jehobah yake taimaka wa mutanen da suka saka Mulkinsa a kan gaba a rayuwarsu. Kuma ko da mutane ba za su iya taimaka mana ba, Jehobah zai yi hakan ba fashi.​—Zab. 121:​1-3.

‘HANNUN DAMA NA ADALCIN’ ALLAH YA TAIMAKA MANA

Mun soma shirin yin taron ƙasashe a filin wasa na Yankee da na Polo da ke birnin New York a shekara ta 1958. Don haka, sai na rubuta wa ofishinmu da ke Austriya cewa ina so in halarci taron, amma aka tambaye ni ko zan so in halarci aji na 32 na Makarantar Littafi Mai Tsarki na Gilead. Halartan wannan makarantar gata ce babba. Saboda haka, nan da nan na ce “E!”

A aji, na zauna kusa da Ɗan’uwa Martin Poetzinger. Ya sha wahala sosai a sansanin aiki da ’yan Nazi suka tura shi. Kuma daga baya ya zama memban Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu. A wasu lokuta a aji, Martin yakan tambaye ni a kunne, “Erika mene ne wannan yake nufi a Jamusanci?”

Da muka yi wajen makonni 10 a makarantar, Ɗan’uwa Nathan Knorr ya gaya mana inda aka tura mu hidima. An tura ni hidima a ƙasar Paraguay. Amma da yake ni ƙarama ce sosai a lokacin, ina bukatar izinin mahaifina kafin in shiga ƙasar. Bayan haka, sai na je hidima a ƙasar Paraguay a watan Maris na 1959. An tura ni da sabuwar abokiyar wa’azi zama a gidan masu wa’azi a ƙasar waje da ke birnin Asunción.

Ba da daɗewa ba, sai na haɗu da Walter Bright, wani ɗan’uwa da ya halarci aji na 30 na makarantar Gilead kuma yana hidima a ƙasar waje. Daga baya, sai muka yi aure. Amma a duk lokacin da muka fuskanci matsala, muna karanta alkawarin da Jehobah ya yi a littafin Ishaya 41:10. Ayar ta ce: “Kada ka ji tsoro; gama ina tare da kai: kada ka yi fargaba; gama ni ne Allahnka: ni ƙarfafa ka.” Wannan ayar tana ƙarfafa mu sosai, don mun san cewa idan muka riƙe amincinmu kuma muka saka Mulkin Allah a kan gaba a rayuwarmu, Jehobah ba zai taɓa yasar da mu ba.

Da shigewar lokaci, an tura mu yin hidima a wani yankin da ke kusa da iyaka ƙasar Brazil. A wurin, limamai sun sa matasa su jefi gidanmu da duwatsu ko da yake gidan na bukatar gyara. Bayan haka, maigidana ya soma yin nazari da wani shugaban ’yan sanda. Wannan mutumin ya tabbatar da cewa ’yan sanda sun tsaya kusa da gidanmu har mako ɗaya, kuma hakan ya sa matasan suka daina damun mu. Jim kaɗan bayan haka, sai muka ƙaura zuwa wani gida mai kyau a ƙetaren iyakar Brazil. Hakan albarka ne sosai don muna iya yin taro a Paraguay da kuma Brazil. An kafa ikilisiyoyi biyu a wurin kafin mu bar yankin.

Ni da mijina Walter muna hidima a birnin Asunción a ƙasar Paraguay

JEHOBAH YA CI GABA DA KULA DA NI

Likitoci sun gaya mini cewa ba zan iya haihuwa ba. Amma a 1962, mun yi mamaki sosai da muka san cewa ina da juna biyu! A ƙarshe, mun koma zama kusa da iyalin maigidana a birnin Hollywood a jihar Florida. Ni da maigidana mun yi shekaru da yawa ba mu iya hidimar majagaba ba domin muna kula da iyalinmu. Amma duk da haka, Mulkin Allah ne abu na farko a rayuwarmu.​—Mat. 6:33.

Da muka zo jihar Florida a watan Nuwamba na 1962, mun yi mamaki da muka ga cewa baƙaƙen fata da turawa ba sa taro a wuri ɗaya. Ƙari ga haka, ba sa wa’azi a wuri ɗaya. Amma Jehobah ba ya son nuna bambanci. Ba da daɗewa ba, aka daina nuna bambanci a ikilisiya. Hakika, Jehobah ya goyi bayan wannan canjin, don yanzu akwai ikilisiyoyi da yawa a wurin.

Maigidana ya mutu a 2015 sanaddiyar ciwon kansa na ƙwaƙwalwa. Hakan ya sa ni baƙin ciki sosai. Mun yi shekara 55 da aure. Maigidana Walter miji ne nagari da yake ƙaunar Jehobah kuma ya taimaka wa ’yan’uwa da yawa. Ina ɗokin sake ganin sa da ƙoshin lafiya a ranar tashin matattu.​—A. M. 24:15.

Ina godiya don irin farin ciki da kuma albarkar da na samu fiye da shekara 40 da na yi ina hidima ta cikakken lokaci. Alal misali, ɗalibaina da na maigidana guda 136 sun yi baftisma. Hakika, mun fuskanci wasu matsaloli, amma ba mu bar hakan ya sa mu daina bauta wa Allahnmu ba. Maimakon haka, mun kusace shi kuma mun gaskata cewa zai magance matsalolin a lokacin da yake so kuma ya yi hakan!​—2 Tim. 4:​16, 17.

Ina kewar maigidana sosai, amma yin hidimar majagaba yana taimaka mini in daina damuwa. Ina jin daɗin koyar da wasu da kuma gaya musu game da begen tashin matattu. Babu shakka, ba zan iya ƙirga lokuta da Jehobah ya taimaka mini ba. Jehobah ya cika alkawarinsa ta wajen ƙarfafa ni da taimaka mini kuma ya ‘riƙe ni da hannun dama na adalcinsa.’​—Isha. 41:10.