Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Baftisma Tana da Muhimmanci ga Kiristoci

Baftisma Tana da Muhimmanci ga Kiristoci

“Baftisma ke cetonku yanzu.”​—1 BIT. 3:21.

WAƘOƘI: 52, 41

1, 2. (a) Yaya wasu iyaye suke ji sa’ad da yaransu za su yi baftisma? (b) Me ya sa ake tambayar mutanen da za su yi baftisma ko sun yi alkawarin bauta wa Jehobah? (Ka duba hoton da ke shafin nan.)

IYAYEN wata yarinya mai suna Maria sun ga ’yarsu ta tashi tsaye tare da sauran mutanen da suke so su yi baftisma. Sai mai jawabin ya yi musu tambayoyi biyu kuma Maria ta amsa da babbar murya. Bayan haka, aka yi mata baftisma.

2 Iyayen Maria sun yi alfahari sosai da ’yarsu domin ta yanke shawarar bauta wa Jehobah muddar ranta kuma ta yi baftisma. Amma kafin ta yi haka, mahaifiyarta ta ɗan damu. Ta yi wa kanta waɗannan tambayoyin: ‘Maria ta isa yin baftisma kuwa? Ta san muhimmancin yin hakan? Zai fi dacewa ta ɗan jira kaɗan kafin ta yi baftisma ne?’ Iyaye da yawa suna yin waɗannan tambayoyin sa’ad da yaransu suke so su yi baftisma. (M. Wa. 5:5) Suna yin hakan domin sun san cewa baftisma shawara ce babba da Kirista yake yankewa.​—Ka duba akwatin nan “ Ka Yi Alkawarin Bauta wa Jehobah Kuwa?

3, 4. (a) Ta yaya manzo Bitrus ya kwatanta muhimmancin yin baftisma? (b) Me ya sa Bitrus ya ce baftisma tana kamar jirgin Nuhu?

3 Sa’ad da manzo Bitrus yake magana game da baftisma, ya ambata jirgin da Nuhu ya gina. Ya ce: “Bisa ga wannan misali, baftisma ke cetonku yanzu.” (Karanta 1 Bitrus 3:​20, 21.) Jirgin da Nuhu ya gina ya nuna cewa yana so ya yi nufin Allah. Nuhu ya yi aikin da Allah ya ba shi. Bangaskiyarsa ta sa ambaliyar ba ta halaka shi da iyalinsa ba. Mene ne wannan kwatancin ya koya mana?

4 Jirgin ya nuna cewa Nuhu yana da bangaskiya. Hakazalika, yin baftisma a gaban jama’a shaida ce babba. Wace shaida ke nan? Tana nuna cewa Kirista ya yi alkawarin bauta wa Jehobah domin ya yi imani ga hadayar Kristi. Kiristocin da suka yi hakan suna kamar Nuhu domin suna yin ayyukan da Allah ya ce su yi. Jehobah zai kāre su sa’ad da ya halaka mugaye a yaƙin Armageddon, yadda ya kāre Nuhu sa’ad da aka yi ambaliyar ruwa a zamaninsa. (Mar. 13:10; R. Yoh. 7:​9, 10) Shi ya sa yin alkawarin bauta wa Jehobah da kuma baftisma suke da muhimmanci sosai. Mutumin da ke jinkirin yin baftisma ba gaira ba dalili, zai iya rasa gatan yin rayuwa har abada a aljanna.

5. Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?

5 Da yake mun san cewa baftisma na da muhimmanci sosai, zai dace mu tattauna tambayoyin nan uku. Mene ne Littafi Mai Tsarki ya ce game da baftisma? Waɗanne matakai ne mutum ke bukatar ya ɗauka kafin ya yi baftisma? Me ya sa ya kamata mu riƙa tunawa da muhimmancin baftisma sa’ad da muke nazari da yaranmu ko ɗalibanmu?

BAFTISMA DA AKA AMBATA A LITTAFI MAI TSARKI

6, 7. (a) Mece ce baftismar da Yohanna ya yi take wakilta? (b) Wace baftisma ta musamman ce Yohanna ya yi?

6 Yohanna Mai Baftisma ne aka fara ambatawa a cikin Littafi Mai Tsarki cewa ya yi wa mutane baftisma. (Mat. 3:​1-6) Mutanen da Yohanna ya yi wa baftisma sun yi hakan ne domin sun amince cewa sun karya dokar da aka bayar ta hannun Musa kuma sun tuba. Amma baftisma mafi muhimmanci da Yohanna ya yi tana da manufa dabam. Yohanna ya sami gatan yi wa Yesu, Ɗan Allah baftisma. (Mat. 3:​13-17) Yesu bai taɓa yin zunubi ba, saboda haka, ba ya bukatar ya tuba. (1 Bit. 2:22) Baftismar da ya yi tana nuna cewa yana a shirye ya yi nufin Allah.​—Ibran. 10:7.

7 Da Yesu ya soma hidima a duniya, almajiransa sun yi wa mutane baftisma. (Yoh. 3:22; 4:​1, 2) Mutanen sun yi baftisma domin sun karya dokar da aka bayar ta hannun Musa kuma sun tuba. Amma bayan Yesu ya mutu kuma ya tashi daga matattu, mutanen da ke so su yi baftisma za su yi hakan domin wani dalili dabam.

8. (a) Wane umurni ne Yesu ya ba mabiyansa bayan ya tashi daga matattu? (b) Me ya sa baftisma take da muhimmanci?

8 Jim kaɗan bayan Yesu ya tashi daga mutuwa a shekara ta 33, ya bayyana ga maza da mata da kuma wataƙila ƙananan yara fiye da 500. Mai yiwuwa a wannan lokacin ne ya umurce su cewa: “Ku tafi fa, ku almajirtar da dukan al’ummai, kuna yi musu baftisma zuwa cikin sunan Uba da na Ɗa da na Ruhu Mai-tsarki: kuna koya musu su kiyaye dukan iyakar abin da na umurce ku.” (Mat. 28:​19, 20; 1 Kor. 15:6) Wataƙila Yesu ya ba da wannan umurnin ne ga ɗarurruwan almajiransa. Furucin nan ya nuna cewa wajibi ne duk wanda ke so ya ɗauki ‘karkiyar’ Yesu ko kuma ya zama almajirinsa ya yi baftisma. (Mat. 11:​29, 30) Duk mutumin da ke so ya faranta wa Allah rai yana bukatar ya amince cewa Allah yana amfani da Yesu wajen cim ma nufinsa. Bayan haka, sai mutumin ya yi baftisma. Irin wannan baftismar ce kaɗai Allah yake amincewa da ita. Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa almajiran Yesu a ƙarni na farko sun san muhimmancin yin baftisma. Ƙari ga haka, ba su yi jinkirin yin hakan ba gaira ba dalili ba.​—A. M. 2:41; 9:18; 16:​14, 15, 32, 33.

KADA KA ƁATA LOKACI

9, 10. Wane darasi ne za mu iya koya game da baftisma daga wajen wani Bahabashe da kuma manzo Bulus?

9 Karanta Ayyukan Manzanni 8:​35, 36. Da akwai wata rana da wani Bahabashe da ya soma bin addinin Yahudawa yake dawowa gida daga Urushalima. Sai mala’ikan Jehobah ya tura Filibus ya yi masa wa’azi game da “Yesu.” Wane mataki ne Bahabashen ya ɗauka? Abin da ya yi ya nuna cewa ya daraja gaskiyar da ya koya sosai. Bahabashen ya yi baftisma nan da nan domin yana so ya yi nufin Allah.

10 Misali na biyu shi ne na wani Bayahude da ke tsananta wa Kiristoci. Sunan Bayahuden Shawulu. An haife shi cikin al’ummar da Allah ya zaɓa. Amma, Yahudawa sun rasa wannan gata na musamman domin sun karya dokar Allah. Shawulu ya yi zato cewa har ila, Allah yana goyon bayan Yahudawa. Saboda haka, ya soma tsananta wa Kiristoci. Amma wata rana, sai Yesu wanda ya riga ya tashi daga mutuwa ya yi masa magana daga sama. Mene ne Shawulu ya yi? Ya amince wani Kirista mai suna Hananiya ya taimaka masa. Littafi Mai Tsarki ya ce Shawulu “ya tashi, aka yi masa baftisma.” (A. M. 9:​17, 18; Gal. 1:14) Daga baya, an canja sunansa zuwa manzo Bulus. Ka lura cewa Bulus ya yi baftisma da zarar ya san cewa Allah yana amfani da Yesu ne wajen cika nufinsa.​—Karanta Ayyukan Manzanni 22:​12-16.

11. (a) Mene ne ke motsa ɗalibanmu a yau su yi baftisma? (b) Yaya muke ji sa’ad da sababbi suka yi baftisma?

11 Haka ma yake da ɗaliban da muke nazarin Littafi Mai Tsarki da su a yau ko da su yara ne ko manya. Waɗanda suke da bangaskiya kuma suke son abin da suka koya suna ɗokin yi wa Allah alkawari cewa za su bauta masa kuma su yi baftisma. Hakika, jawabin baftisma da ake yi a taron yanki da na da’ira, lokaci ne na musamman a taron. Shaidun Jehobah suna farin ciki sosai sa’ad da ɗalibansu suka san gaskiya kuma suka yi baftisma. Babu shakka, iyaye Kiristoci suna murna matuƙa sa’ad da suka ga yaransu za su yi baftisma. Alal misali, a shekara ta 2017, mutane 284,000 ne suka yi baftisma don su nuna cewa sun yi alkawarin bauta wa Allah muddar ransu. (A. M. 13:48) A bayyane yake cewa mutanen sun san cewa Kiristoci suna bukatar yin baftisma. Amma mene ne suka yi don su cancanci yin hakan?

12. Waɗanne matakai ne ya wajaba ɗalibinmu ya ɗauka kafin ya yi baftisma?

12 Kafin mutum ya yi baftisma, wajibi ne ya san gaskiya game da Allah da nufinsa ga mutane da duniya da kuma yadda ya tanadar mana da fansa. (1 Tim. 2:​3-6) Yana kuma bukatar ya kasance da bangaskiya domin za ta taimaka masa ya riƙa bin dokokin Jehobah kuma ya daina yin abin da Jehobah ba ya so. (A. M. 3:19) Hakan yana da muhimmanci domin Allah ba zai amince da alkawarin da mutum ya yi masa ba idan ya ci gaba da yin abubuwan da Jehobah ba ya so. (1 Kor. 6:​9, 10) Amma yana bukatar ya ƙara yin wasu abubuwa. Wanda ya yi alkawarin bauta wa Allah zai riƙa halartan taro, ya yi wa’azi kuma ya koyar da wasu. Yesu ya ce almajiransa na gaske za su riƙa yin wannan aikin. (A. M. 1:8) Wajibi ne ɗalibin ya yi waɗannan abubuwan kafin ya yi alkawari cewa zai bauta wa Jehobah muddar ransa. Bayan hakan, sai ya yi baftisma.

MAƘASUDAN DA ƊALIBAI ZA SU KAFA

Kana taimaka wa ɗalibinka ya san muhimmancin baftisma sa’ad da kuke nazari? (Ka duba sakin layi na 13)

13. Me ya sa ya kamata waɗanda suke nazari da ɗalibai su riƙa tuna cewa yin baftisma na da muhimmanci?

13 Yayin da muke taimaka wa yaranmu da ɗalibanmu su ɗauki waɗannan matakan, ya kamata mu tuna cewa waɗanda suke so su zama mabiyan Yesu za su yi baftisma. Hakan zai taimaka mana mu gaya musu cewa yin baftisma yana da muhimmanci sosai. Kuma za mu yi hakan a lokacin da ya dace. Hakika, muna son yaranmu da ɗalibanmu su cancanci yin baftisma!

14. Me ya sa bai kamata mu matsa wa ɗalibi ya yi baftisma ba?

14 Amma bai kamata iyaye ko mai nazari da mutum ko kuma wani a ikilisiya ya matsa wa ɗalibi ya yi baftisma ba. Jehobah ma ba ya yin hakan. (1 Yoh. 4:8) A maimakon haka, yayin da muke nazari da su, mu taimaka musu su san muhimmancin ƙulla dangantaka na kud da kud da Allah. Idan ɗalibin ya daraja gaskiyar da ya koya, kuma yana son ya zama Kirista, hakan zai sa ya so yin baftisma.​—2 Kor. 5:​14, 15.

15, 16. (a) Shin akwai shekarar da mutum zai kai kafin ya yi baftisma? Ka bayyana. (b) Me ya sa ya dace mutum ya yi baftisma ko da ya yi hakan sa’ad da yake bin wani addini?

15 Ba a faɗi shekarar da mutum zai kai kafin ya yi baftisma ba. Mutane sun bambanta, kuma wasu ɗalibai sukan cancanci yin baftisma da sauri fiye da wasu. Mutane da yawa sun yi baftisma sa’ad da suke yara kuma sun ci gaba da riƙe amincinsu ga Jehobah. Wasu kuma sun riga sun tsufa kafin su koyi gaskiya kuma su yi baftisma. Wasu ma sun fi shekara 100 kafin su yi hakan.

16 Wata tsohuwa ta tambayi wadda take nazari da ita cewa ko ya dace ta sake yin baftisma. Ta yi wannan tambayar don ta yi baftisma a addinai dabam-dabam da take a dā. Amma mai nazari da ita ta nuna mata wasu Nassosi da suka amsa tambayarta. Ɗalibar ta fahimci cewa ya kamata ta yi baftisma kuma ta yi hakan ba da daɗewa ba. Ko da yake ta kusan shekara 80, ta fahimci cewa ya dace ta yi baftisma. Hakan ya koya mana cewa Jehobah zai amince da baftismarmu idan mun san gaskiya sosai. Saboda haka, wajibi ne sababbi su yi baftisma ko da sun yi hakan a wani addini.​—Karanta Ayyukan Manzanni 19:​3-5.

17. Mene ne ya kamata mutum ya yi tunani a kai a ranar da yake baftisma?

17 Mutane suna farin ciki sosai a ranar da suka yi baftisma. Ƙari ga haka, baftisma lokaci ne na yin tunani sosai a kan abin da yin hakan yake nufi. Yin duk abubuwan da ake bukatar Kirista ya yi ba shi da sauƙi. Ya kamata almajiran Yesu su daina ‘rayuwa don kansu, amma ga wanda ya mutu ya kuwa tashi sabili da su.’​—2 Kor. 5:15; Mat. 16:24.

18. Waɗanne tambayoyi ne za mu tattauna a talifi na gaba?

18 Mahaifiyar Maria ta yi irin wannan tunanin sa’ad da ta yi tambayoyin da aka ambata a sakin layi na biyu. Idan kana da yara, kana iya tambayar kanka: ‘Ɗana yana a shirye ya yi baftisma? Shin ya san Jehobah sosai da zai sa ya yi alkawarin bauta masa? Ya kamata ne ya yi makaranta sosai kuma ya sami aiki mai kyau kafin ya yi baftisma? Idan ya yi zunubi mai tsanani bayan ya yi baftisma kuma fa?’ Za mu tattauna waɗannan batutuwan da kuma yadda iyaye za su kasance da ra’ayin da ya dace game da baftisma a talifi na gaba.