Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Farin Cikin da Karban Baki Ke Kawowa!

Farin Cikin da Karban Baki Ke Kawowa!

“Ku dinga karɓar juna a cikin gidajenku, ba tare da gunaguni ba.”​—1 BIT. 4:​9, Juyi Mai Fitar da Ma’ana.

WAƘOƘI: 100, 87

1. Wace wahala ce Kiristoci a ƙarni na farko suka sha?

A TSAKANIN shekara ta 62 da 64, manzo Bitrus ya rubuta wasiƙa zuwa ga “zaɓaɓɓun Allah da ke bare, a warwatse a Fantas, da Galatiya, da Kafadokiya, da Asiya, da kuma Bitiniya.” (1 Bit. 1:​1, Littafi Mai Tsarki) ’Yan’uwa da ke cikin waɗannan ikilisiyoyi na Asiya Ƙarama sun fito daga wurare dabam-dabam, kuma suna shan matsananciyar wahala. Ban da haka, ana tsananta musu kuma ana tuhumarsu. Saboda haka, suna bukatar a ƙarfafa su da kuma yi musu ja-goranci. Bitrus ya ce: “Ƙarshen dukan abubuwa ya gabato.” Hakika, za a halaka Urushalima kafin shekara goma. Mene ne zai iya taimaka wa Kiristoci a ko’ina su jimre da wannan mawuyacin lokaci?​—1 Bit. 4:​4, 7, 12.

2, 3. Me ya sa Bitrus ya ƙarfafa ’yan’uwa su riƙa nuna karimci? (Ka duba hoton da ke shafin nan.)

2 Bitrus ya gaya wa ’yan’uwa su ‘dinga karɓar juna a cikin gidajensu.’ (1 Bit. 4:​9, Juyi Mai Fitar da Ma’ana) Kalmar nan “karɓar juna” a Helenanci tana nufin “son baƙi ko kuma yi musu alheri.” Amma Bitrus ya ƙarfafa ’yan’uwa su riƙa nuna wa “juna” karimci, duk da cewa sun san juna kuma suna yin abubuwan tare. Ta yaya yin hakan zai taimake su?

3 Zai sa su kasance da haɗin kai. Kai kuma fa? Ka tuna yadda ka ji daɗin yin cuɗanya da wani ɗan’uwa sa’ad da ya gayyace ka gidansa? Ka yi farin cikin sanin ’yan’uwanka sosai sa’ad da ka gayyace su zuwa gidanka? Hanya mafi kyau na sanin ’yan’uwanmu sosai ita ce ta wurin nuna musu karimci. Kiristoci da ke zamanin Bitrus suna bukatar su kusaci juna yayin da matsaloli suke ƙaruwa. Mu ma muna bukatar mu yi hakan a wannan “kwanaki na ƙarshe.”​—2 Tim. 3:1.

4. Waɗanne tambayoyi ne za mu tattauna a wannan talifin?

4 Wane zarafi ne muke da shi na nuna wa “juna” karimci? Ta yaya za mu ƙi barin kome ya hana mu karɓan baƙi? Mene ne zai taimaka mana mu zama masu karɓan baƙi sosai?

ZARAFOFIN NUNA KARIMCI GA BAƘI

5. Ta yaya za mu riƙa karɓan baƙi a taro?

5 A taro: Jehobah da ƙungiyarsa ne suka gayyace mu zuwa taro. Don haka, muna son dukan waɗanda suka halarci taron su ji daɗin taron kuma su saki jiki. (Rom. 15:7) Sababbi ma baƙin Jehobah ne. Saboda haka, muna bukatar mu marabce su sosai ko da adonsu bai da kyau. (Yaƙ. 2:​1-4) Idan ka lura cewa ba wanda yake kula da wani baƙo, kana iya gaya masa ya zauna tare da kai. Zai yi farin ciki idan ka taimaka masa ya fahimci abin da ake tattaunawa ko kuma buɗe nassosi da ake karantawa. Hakan hanya ce mai kyau na nuna karimci.​—Rom. 12:13.

6. Wane ne ya kamata mu fi nuna wa karimci?

6 Don cin abinci tare: A lokacin da ake rubuta Littafi Mai Tsarki, mutane sukan nuna karimci ta wurin gayyatar baƙi zuwa gidansu don su ci abinci. (Far. 18:​1-8; Alƙa. 13:15; Luk. 24:​28-30) Yin hakan yana nuna cewa masu karɓar baƙi suna son su zama abokan baƙin kuma su zauna lafiya. Su wane ne ainihi ya kamata mu fi nuna wa karimci? ’Yan’uwan da ke cikin ikilisiyarmu ne. Ya kamata mu riƙa taimaka wa juna yayin da wannan zamanin yake taɓarɓarewa. Ƙari ga haka, ya kamata mu zama aminansu. Shi ya sa a 2011, Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu ta canja lokacin da iyalin Bethel ke Nazarin Hasumiyar Tsaro a Amirka. An canja lokacin nazarin daga ƙarfe 7 sauran minti 15 zuwa 6 da minti 15. Me ya sa? A sanarwar an ce, idan an tashi taron da wuri, hakan zai sa masu hidima a Bethel su riƙa nuna wa juna karimci. Wasu ofisoshi da ke kula da ayyukanmu sun yi hakan. Hakan ya sa waɗanda suke hidima a Bethel su kusaci juna sosai.

7, 8. Ta yaya za mu nuna karimci ga ’yan’uwan da suka zo yin jawabi a ikilisiyoyinmu?

7 Za mu iya nuna karimci ga ’yan’uwan da suka zo yin jawabi daga wasu ikilisiyoyi da masu kula da da’ira da kuma baƙin da ke zuwa yin jawabi daga Bethel a wasu lokuta. (Karanta 3 Yohanna 5-8.) Cin abinci tare hanya ce mai kyau na yin hakan. Za ka iya nuna musu karimci kuwa?

8 Wata ’yar’uwa a Amirka ta ce: “Ni da maigidana mun sami zarafin gayyatar masu jawabi da yawa da matansu zuwa gidanmu don nuna musu karimci. Kuma kowace gayyata da muka yi ta ƙarfafa bangaskiyarmu kuma ta sa mu farin ciki sosai. Ba mu taɓa yin da-na-sani don yin hakan ba.”

9, 10. (a) Su waye ne za su bukaci masauki na dogon lokaci? (b) Me waɗanda ba su da babban gida za su iya yi? Ka ba da kwatanci.

9 Baƙin da za su yi kwan-biyu: A zamanin dā, mutane sukan ba da masauki ga baƙi. (Ayu. 31:32; Fil. 22) Muna bukatar mu yi hakan a yau. Alal misali, ’yan’uwa ne suke ba masu kula da da’ira masauki. Kuma ɗaliban makarantunmu da kuma masu aikin gine-gine sukan bukaci masauki. Ƙari ga haka, bala’i yakan sa wasu iyalai su rasa gidansu. Don haka, za su bukaci masauki kafin masu ba da kayan agaji su gyara musu gidansu. Bai kamata mu sa rai cewa waɗanda ke da babban gida ne kaɗai za su iya taimaka musu ba. Wataƙila masu babban gida sun sha taimaka ma waɗanda bala’i ya same su. Zai dace mu ba wani baƙo masauki a gidanmu ko da gidanmu bai da girma.

10 Wani ɗan’uwa a Koriya ta Kudu da ke ba ɗalibai masauki a gidansa ya ce: “Da farko na yi jinkirin yin hakan domin ba mu daɗe da aure ba kuma gidanmu bai da girma. Amma mun yi farin ciki sosai a lokacin da ɗaliban suka zauna da mu. Ko da ba mu daɗe da aure ba, mun ga yadda ma’aurata suke farin ciki idan suka bauta wa Jehobah tare kuma suka biɗi maƙasudai a hidimarsa.”

11. Me ya sa kuke bukatar ku nuna karimci ga waɗanda suka ƙauro ikilisiyarku?

11 Sababbi a cikin ikilisiya: Wataƙila wasu ’yan’uwa da iyalai sukan ƙauro yankinku don yin hidima a inda ake bukatar masu shela. Ko kuma an turo majagaba su zo su taimaka muku a ikilisiyarku. Zai yi musu wuya su saba da yanayin wurin, kuma wataƙila za su koyi sabon yare ko kuma wata al’ada. Gayyatar su cin abinci tare da iyalinka ko kuma fita yawo tare zai taimaka musu su sami abokai kuma su saba da yankinku.

12. Wane labari ne ya nuna cewa ba ma bukatar abinci mai yawa kafin mu nuna karimci?

12 Ba ka bukatar ka ba da abinci mai yawa idan za ka nuna karimci. (Karanta Luka 10:​41, 42.) Wani ɗan’uwa ya tuna abin da ya faru sa’ad da shi da matarsa suka soma hidima a ƙasar waje. Ya ce: “Mu matasa ne, ba mu taɓa yin hidima a wata ƙasa ba kuma muna kewar gida sosai. Wata rana, na yi ƙoƙari in taimaka wa matata da take kewar gida sosai, amma ban yi nasara ba. Sa’an nan, da misalin ƙarfe bakwai da rabi na dare, sai wata ta ƙwanƙwasa ƙofarmu. Wata ɗalibarmu ce ta kawo mana lemu guda uku. Ta zo ne ta yi mana maraba. Sai muka ba ta ruwan sha kuma muka yi mata shayi da cakuleti. Ba mu iya yaren Swahili ba, ita kuma ba ta iya Turanci ba. Amma, wannan ya taimaka mana mu soma abokantaka da ’yan’uwa a yankin kuma ya sa mu farin ciki sosai.”

KADA KOME YA HANA KA NUNA KARIMCI GA BAƘI

13. Mene ne amfanin nuna karimci?

13 Ka taɓa jinkirin karɓan baƙi ne? Idan haka ne, ka yi rashin zarafin shaƙatawa da kuma samun abokai na dindindin. Karɓan baƙi hanya ce mafi kyau na daina jin kaɗaici. Amma, kana iya yin tunani, ‘Me zai hana mutum nuna karimci?’ Ga wasu dalilai.

14. Mene ne za mu iya yi idan ba mu da lokaci da ƙarfin karɓan baƙi ko kuma amincewa da gayyata?

14 Lokaci da kuzari: Bayin Jehobah sun shagala da ayyuka da yawa. Don haka, wasu suna ganin ba su da lokaci da kuma ƙarfin nuna karimci. Idan kana jin haka, wataƙila kana bukatar ka sake bincika ayyukanka. Shin za ka iya yin wasu canje-canje don ka sami lokaci da ƙarfin nuna karimci ko kuma zuwa wurin wani da ya gayyace ka gidansa? Littafi Mai Tsarki ya ce Kiristoci su riƙa karɓan baƙi. (Ibran. 13:2) Saboda haka, zai dace ka riƙa yi hakan. Amma, kana bukatar ka rage yin ayyuka da ba su da muhimmanci sosai don ka sami lokacin karɓan baƙi.

15. Mene ne zai iya hana wasu nuna karimci?

15 Yadda kake ji game da kanka: Ka taɓa so nuna karimci amma ka ji cewa ba za ka iya yin hakan ba? Wasu suna jin kunya kuma suna ganin cewa ba za su iya yin taɗi da baƙin ba kuma hakan zai hana su jin daɗin ziyarar. Wasu kuma ba su da kuɗi. Saboda haka, sun damu cewa ba za su iya ba baƙin abin da wasu ’yan’uwa a cikin ikilisiya suke bayarwa ba. Amma ka tuna cewa, ba sai gidanka yana da kyau sosai ba ne za ka iya karɓan baƙi. Baƙi za su fi farin ciki idan gidanka yana da tsabta, kuma ka shirya shi sosai.

16, 17. Me zai iya taimaka maka ka daina tsoron karɓan baƙi?

16 Idan kana tsoro a duk lokacin da kake da baƙi, ka san cewa hakan na faruwa da kowa. Wani dattijo a Biritaniya ya ce: “Yin shiri a duk sa’ad da muke so mu yi baƙi na iya sa mu tsoro sosai. Amma da yake hakan na da alaƙa da ibadarmu, muna samun sakamako masu kyau sosai fiye da ƙalubalen da hakan zai kawo. Ina jin daɗin shan shayi tare da mutanen da suka ziyarce mu.” Ya kamata mu riƙa nuna cewa mun damu da su. (Filib. 2:4) Kusan kowa na jin daɗin faɗin labarinsa. Kuma hanya ɗaya da za mu iya yin hakan ita ce sa’ad da muke liyafa. Wani dattijo kuma ya ce: “Gayyatar ’yan’uwa a ikilisiyarmu zuwa gidanmu na taimaka mini in san su sosai kuma in san yadda suka koyi gaskiya.” Idan muka nuna cewa muna ƙaunar mutanen da muka gayyata zuwa gidanmu, hakan zai sa kowa ya ji daɗin ziyarar.

17 Wata majagaba wadda ɗaliban da suka zo makarantu na ƙungiyar Jehobah suke yawan zama a gidanta ta ce: “Da farko ina tsoro domin babu kayan ado a ɗakina kuma kujerun da ke ciki tsofaffi ne. Amma matar wani ɗan’uwa da ke koyarwa a makarantan ta kwantar mini da hankali. Ta ce sa’ad da ita da maigidanta suke kula da da’ira, sun fi jin daɗin zama da ’yan’uwan da ke da irin maƙasudansu a bautar Jehobah. Wato, ’yan’uwan da ke bauta wa Jehobah kuma suke sauƙaƙa rayuwarsu. Hakan ya sa na tuna abin da mahaifiyarmu take gaya mana sa’ad da muke ƙanana: ‘Gwamma a ci abinci na ganye wurin da ƙauna take.’ ” (Mis. 15:17) Bai kamata mu riƙa damuwa ba, domin abu mafi muhimmanci shi ne nuna ƙauna ga mutanen da muka gayyace su.

18, 19. Ta yaya nuna karimci zai taimaka mana mu canja yadda muke ji game da wasu?

18 Yadda kake ji game da wasu: Shin da akwai wani a ikilisiyarku da ba ka son halinsa? Idan ba ka ɗauki mataki nan da nan don ka canja yadda kake ji ba, matsalar za ta ci gaba. Idan ba ka son halin wani, ba za ka so ka gayyato shi gidanka ba. Ko kuma wataƙila da akwai wani da ya taɓa ɓata maka rai, da har yanzu ba ka manta ba.

19 Littafi Mai Tsarki ya ce mu riƙa yin alheri idan muna so mu kyautata dangantakarmu da mutane har da maƙiyanmu. (Karanta Misalai 25:​21, 22.) Idan ka gayyaci mutum zuwa gidanka, hakan zai sa ka canja ra’ayinka game da shi. Ƙari ga haka, zai taimaka maka ka ga wasu halayensa masu kyau, wato halayen da suka sa Jehobah ya jawo sa cikin ƙungiyarsa. (Yoh. 6:44) Idan ƙauna ta motsa ka ka gayyaci mutumin da bai yi zaton za ka yi hakan ba, dangantakarka da shi za ta gyaru sosai. Mene ne za ka yi don ka nuna cewa ƙauna ce ta motsa ka ka gayyaci mutane zuwa gidanka? Hanya ɗaya ita ce ta bin abin da ke Filibiyawa 2:3 da ta ce: “A cikin tawali’u kowa ya mai da wani ya fi kansa.” Muna bukatar mu nemi sanin hanyoyin da ’yan’uwanmu suka fi mu. Wataƙila sun fi mu bangaskiya ko jimrewa ko ba sa jin tsoro ko kuma suna da wasu halaye masu kyau na Kirista. Idan muka san hakan, zai taimaka mana mu ƙara ƙaunar su kuma mu ci gaba da nuna musu karimci.

KA ZAMA BAƘO NA ƘWARAI

Mutane suna shiri sosai sa’ad da za su yi baƙi (Ka duba sakin layi na 20)

20. Me ya sa ya kamata mu cika alkawarin da muka yi kuma ta yaya za mu yi hakan?

20 Dauda marubucin zabura ya ce: “Ya Ubangiji, wa za ya sauka cikin tenti naka?” (Zab. 15:1) Bayan haka, sai ya tattauna halayen da Jehobah yake so baƙi su kasance da shi. Ɗaya cikin halayen shi ne cika alkawari: “Kullum yana cika alkawuran da ya yi ko ta halin ƙaƙa.” (Zab. 15:​4, LMT) Idan wani ya gayyace mu gidansa kuma mun yarda, kada mu ƙi zuwa ba tare da ƙwaƙƙwaran dalili ba. Babu shakka, mutumin da ya kira mu gidansa ya riga ya yi shirye-shirye sosai. Idan ba mu je ba, dukan shirye-shiryen da ya yi za su bi iska. (Mat. 5:37) Wasu suna saɓa alkawarin da suka yi domin suna so su je wurin wani da suke gani za su fi jin daɗi. Yin haka na nuna cewa muna daraja ’yan’uwanmu kuma muna ƙaunarsu kuwa? Ya kamata mu gamsu da duk abin da wani da ya kira mu gidansa ya ba mu. (Luk. 10:7) Idan wani abu ya faru da ya sa ya zama wajibi mu fasa zuwa wurinsa, zai dace mu gaya masa tun da wuri.

21. Ta yaya bin al’adar mutanen yankin da muke zai sa mu faranta ran wanda ya kira mu gidansa?

21 Ya kuma kamata mu daraja al’adar mutanen yankin da muke. A wasu al’adu, ana marabtar baƙon da ya zo ba tare da an gayyace shi ba. A wasu kuma, sai da gayyata ake zuwa wurin mutum. A wasu wurare, ana ba baƙi abinci mafi kyau, sai mutanen gidan su ci wani abu dabam. Amma a wasu wurare, baƙon da mutanen gidan suna cin abincin tare. A wasu wurare, baƙon yana tahowa da abinci ko abin sha. A wasu kuma maigidan ne ke ciyar da kowa. A wasu al’ada kuma, baƙo ba ya yarda ya zo gidan wani a ƙaro na farko ko na biyu da aka gayyace shi. A wasu kuma, yin hakan rashin kunya ne. Ya kamata mu tabbatar da cewa mun sa duk mutumin da ya kira mu gidansa farin ciki.

22. Me ya sa yake da muhimmanci mu “dinga karɓar juna”?

22 Manzo Bitrus ya ce: “Matuƙar dukan abu ta kusa.” (1 Bit. 4:7) A yau, ƙarshen ya fi kusa sosai. Nan ba da daɗewa ba, za mu fuskanci ƙunci mafi tsanani a tarihin ’yan Adam. Yayin da zamanin nan yake daɗa lalacewa, ya kamata mu sa ƙaunarmu ga ’yan’uwanmu ta daɗa ƙarfi sosai. Shawarar manzo Bitrus ta fi muhimmanci a yau. Ta ce: “Ku dinga karɓar juna a cikin gidajenku.” Babu shakka, karɓan baƙi hali ne mai kyau da zai ci gaba har abada.​—1 Bit. 4:​9, Juyi Mai Fitar da Ma’ana.