Talifin Nazari na 12
A Wane Lokaci Ne Ya Dace Ka Yi Magana?
“Akwai lokacin yin shiru, da lokacin yin magana.”—M. WA. 3:1, 7.
WAƘA TA 124 Mu Kasance da Aminci
ABIN DA ZA A TATTAUNA *
1. Mene ne Mai-Wa’azi 3:1, 7 ya koya mana?
WASU cikinmu muna son yin magana sosai. Wasu kuma ba sa son yin magana. Kamar yadda littafin Mai-Wa’azi ya nuna, akwai lokacin yin magana da lokacin yin shiru. (Karanta Mai-Wa’azi 3:1, 7.) Duk da haka, muna iya so wasu cikin ʼyan’uwanmu su riƙa yin magana sosai. Wasu kuma su rage yin magana.
2. Wane ne ya kamata ya gaya mana lokacin da za mu yi shiru da kuma magana?
2 Furucinmu baiwa ne daga Jehobah. (Fit. 4:10, 11; R. Yar. 4:11) Jehobah ya gaya mana a Kalmarsa yadda za mu yi amfani da wannan baiwar. A wannan talifin, za mu tattauna wasu misalai na Littafi Mai Tsarki da za su taimaka mana mu san lokacin yin magana da kuma na yin shiru. Za mu kuma tattauna yadda Jehobah yake ji don abin da muke faɗa game da mutane. Bari mu fara tattauna lokacin da ya kamata mu yi magana.
A WANE LOKACI NE YA DACE MU YI MAGANA?
3. Kamar yadda Romawa 10:14 ta nuna, a wane lokaci ne ya kamata mu yi magana?
3 Ya kamata mu riƙa kasancewa a shirye mu yi magana game da Jehobah da Mulkinsa. (Mat. 24:14; karanta Romawa 10:14.) Idan mun yi hakan, muna yin koyi da Yesu. Ɗaya cikin dalilan da ya sa Yesu ya zo duniya shi ne don ya koya wa mutane gaskiya game da Ubansa. (Yoh. 18:37) Amma ya kamata mu tuna cewa yadda muke magana yana da muhimmanci. Saboda haka, sa’ad da muke tattaunawa da mutane game da Jehobah, wajibi ne mu yi hakan da “sauƙin kai da ban girma.” Kuma mu nuna cewa mun daraja ra’ayinsu da imaninsu. (1 Bit. 3:15) Idan muka yi hakan, ba tattaunawa da su kawai za mu yi ba, amma za mu koyar da su kuma mu ratsa zukatansu.
4. Kamar yadda Karin Magana 9:9 ta nuna, ta yaya furucinmu zai iya taimaka wa mutane?
4 Kada dattawa su yi jinkiri idan suka lura cewa wani ɗan’uwa ko ’yar’uwa tana bukatar shawara. Zai dace su yi hakan a lokacin da ba za su kunyatar da mutumin ba. Za su yi hakan a lokacin da babu kowa a wurin. Su yi musu magana a hanya mai ban-girma. Duk da haka, kada su yi jinkirin nuna musu ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki da za su taimaka musu su yi abin da ya dace. (Karanta Karin Magana 9:9.) Me ya sa yake da muhimmanci mu yi magana da ƙarfin zuciya a lokacin da ya dace? Bari mu tattauna misalai biyu. A misali na farko, mutumin ya bukaci ya yi wa yaransa gargaɗi, a na biyun kuma wata mata ta bukaci ta tattauna da wani da zai zama sarki.
5. A wane lokaci ne ya kamata Eli ya yi magana?
5 Eli Babban Firist yana da yara biyu da yake ƙauna sosai. Amma yaransa ba su daraja Jehobah ba. Su firistoci ne da ke hidima a mazauni. Amma sun yi ganganci da matsayin da Allah ya ba su. Ba su daraja hadayar da mutane suke miƙa wa Jehobah ba kuma suna yin lalata a mazaunin Jehobah. (1 Sam. 2:12-17, 22) Dokar da Allah ya ba Isra’ilawa ta nuna cewa yaran Eli suna bukatar su mutu, amma babansu ya ɗan yi musu gargaɗi kawai kuma ya ƙyale su su ci gaba da yin hidima a mazaunin. (M. Sha. 21:18-21) Yaya Jehobah ya ji don abin da Eli ya yi? Ya ce masa: “Kai Eli, don me kake girmama ’ya’yanka fiye da ni?”—1 Sam. 2:29, 34.
6. Me muka koya daga Eli?
6 Mun koyi darasi mai muhimmanci daga Eli. In mun lura cewa wani abokinmu ko danginmu ya ƙarya dokar Allah, dole ne mu gaya masa ƙa’idodin Jehobah. Bayan haka, ya wajaba mu tabbatar da cewa ya nemi taimako daga wurin dattawa. (Yaƙ. 5:14) Bai kamata mu zama kamar Eli, ta wajen daraja abokanmu ko danginmu fiye da Jehobah ba. Muna bukatar ƙarfin zuciya don mu gaya wa wani cewa ya yi laifi, amma hakan zai kawo sakamako mai kyau. Ku lura da bambanci da ke tsakanin Eli da wata Ba’isra’iliya mai suna Abigail.
7. Me ya sa Abigail ta tattauna da Dauda?
7 Abigail matar wani mai arziki ne da ke da filaye da yawa. Sunan mutumin Nabal ne. A lokacin da Dauda da mutanensa suka gudu don kada Sarki Saul ya kashe su, sun kasance tare da makiyayan Nabal kuma sun kāre su daga ɓarayi. Shin Nabal ya nuna godiya kuwa? A’a. A lokacin da Dauda da mutanensa suka roƙi Nabal ya ɗan ba su ruwa da abinci, Nabal ya yi fushi kuma ya zazzage su. (1 Sam. 25:5-8, 10-12, 14) A sakamakon haka, Dauda ya so ya kashe dukan mazaje a gidan Nabal. (1 Sam. 25:13, 22) Sa’ad da Abigail ta lura da hakan, sai ta ga cewa ya dace ta yi magana. Ta yanke shawarar tattaunawa da Dauda da mutanensa 400.
8. Wane darasi ne muka koya daga Abigail?
8 A lokacin da Abigail ta haɗu da Dauda, ta yi masa magana da ƙarfin zuciya da ban-girma kuma ta ratsa zuciyarsa. Ko da yake Abigail ba ta yi wani laifi ba, ta ba Dauda haƙuri. Ta ce ta san cewa Dauda mutumin kirki ne kuma ta dogara ga Jehobah. (1 Sam. 25:24, 26, 28, 33, 34) Kamar Abigail, idan mun lura cewa wani yana so ya yi abin da zai jawo masa lahani, ya kamata mu faɗakar da shi. (Zab. 141:5) Kada mu rena shi amma mu kasance da ƙarfin zuciya. Idan mun yi wa mutane gargaɗi a lokacin da hakan ya dace, za mu nuna cewa mu aminansu ne.—K. Mag. 27:17.
9-10. Mene ne ya kamata dattawa su tuna sa’ad da suke wa wani gargaɗi?
9 Yana da muhimmanci dattawa su kasance da ƙarfin zuciyar yin gargaɗi ga mutumin da ya yi laifi a ikilisiya. (Gal. ) Dattawa sun san cewa su ma ajizai ne kuma za su bukaci gargaɗi idan sun yi laifi. Amma duk da haka, ba sa jinkirin gargaɗar da mutumin da ya yi laifi. ( 6:12 Tim. 4:2; Tit. 1:9) A lokacin da suke yin gargaɗi, suna yin amfani da furucinsu wajen koyar da mutumin. Suna ƙaunar ʼyan’uwansu, kuma ƙaunar tana motsa su su ɗauki mataki. (K. Mag. 13:24) Amma abin da ya fi muhimmanci a gare su shi ne su bi ƙa’idodin Jehobah kuma su kāre ikilisiyar daga gurɓatawa.—A. M. 20:28.
10 Daga sakin layi na uku zuwa wannan sakin layin, mun tattauna lokacin da ya dace mu yi magana. Amma akwai lokacin da ya kamata mu yi shiru. Waɗanne ƙalubale ne za mu iya fuskanta a waɗannan lokuta?
A WANE LOKACI NE YA DACE MU YI SHIRU?
11. Wane misali ne Yaƙub ya yi amfani da shi, kuma me ya sa ya dace?
11 Yana da wuya mu kame bakinmu. Manzo Yaƙub ya yi amfani da wani misali don ya bayyana hakan. Ya ce: “Idan kuwa wani ba ya kuskure a maganarsa, to, lallai shi cikakke ne, mai iya lura da jikinsa gaba ɗaya. Mukan sa wa doki linzami a baki domin ya yi biyayya da mu. Ta haka mukan iya bi da shi zuwa inda muke so.” (Yaƙ. 3:2, 3) Ana saka linzami a kan doki da kuma bakinsa. Idan mahayin ya ja linzamin, zai iya yi wa dokin ja-goranci ko ya tsayar da shi. Idan linzamin ya fice daga hannun mahayin, dokin zai iya yin gudu yadda ya ga dama kuma ya ji wa kansa da mahayin rauni. Hakazalika, idan ba mu iya kame bakinmu ba, za mu jawo matsaloli da yawa. Bari mu tattauna wasu lokuta da za mu bukaci yin shiru.
12. A wane lokaci ne ya dace mu yi shiru?
12 Idan wani ɗan’uwa ya san wani batun da sirri ne, kana tilasta masa ya gaya maka ne? Alal misali, idan ka haɗu da wani ɗan’uwa da ya fito daga ƙasar da aka saka wa aikinmu takunkumi, kana tambayarsa yadda muke gudanar da ayyukanmu a ƙasar ne? Muna ƙaunar ʼyan’uwanmu kuma muna so mu san abin da ke faruwa da su. Kuma a lokacin da muke addu’a a madadinsu, muna ambata matsalolin da suke fuskanta. Amma, wannan lokaci ne na yin shiru. Idan muka tilasta wa ʼyan’uwanmu su gaya mana batun da sirri ne, hakan rashin ƙauna ne ga ɗan’uwan da kuma sauran ʼyan’uwa da suke da tabbaci cewa ɗan’uwan ba zai fallasa sirrin ba. Hakika, babu kowannenmu da zai so ya daɗa tsananta yanayin ʼyan’uwanmu da ke ƙasashen da aka saka wa aikinmu takunkumi. Hakazalika, babu ɗan’uwa da ke ƙasashen nan da zai so ya fallasa yadda suke wa’azi da kuma taron ikilisiya.
13. Kamar yadda Karin Magana 11:13 ta nuna, me ya wajaba dattijo ya yi kuma me ya sa?
13 Wajibi ne dattawa su bi ƙa’idar Littafi Mai Tsarki da ke Karin Magana 11:13 a batun sirri. (Karanta.) Yin hakan zai iya kasancewa da wuya musamman idan dattijon yana da aure. Ma’aurata suna tattaunawa da juna a kowane lokaci game da batutuwan sirri da dai sauransu. Amma ya kamata dattijo ya san cewa ba zai dace ya fallasa sirrin wani a ikilisiya ba. Idan ya yi hakan, zai zubar da mutuncinsa. ʼYan’uwan da aka ba su gata a cikin ikilisiya “ba masu baki biyu a magana ba” ne. (1 Tim. 3:8) Wato, ba za su ruɗi mutane ba kuma ba za su riƙa gulma ba. Idan dattijo yana ƙaunar matarsa, ba zai gaya mata batun da ba ta bukatar ta sani ba.
14. Ta yaya matar dattijo za ta iya taimaka masa kada ya zubar da mutuncinsa?
14 Matar dattijo za ta iya taimaka masa ya riƙe sirri idan ba ta tilasa masa ya gaya mata batutuwan sirri. Idan matar dattijo ta bi wannan shawarar, za ta nuna cewa tana goyon bayan mijinta kuma tana daraja mutanen da suka gaya masa sirri. Kuma mafi muhimmanci, za ta sa Jehobah farin ciki domin tana sa zaman lafiya da haɗin kai ya kasance a ikilisiya.—Rom. 14:19.
YAYA JEHOBAH YAKE ƊAUKAN FURUCINMU?
15. Yaya Jehobah ya ji don abin da abokan Ayuba suka yi, kuma me ya sa?
15 Za mu iya koyan darussa game da lokacin yin magana da na yin shiru a littafin Ayuba. Bayan Ayuba ya fuskanci matsaloli dabam-dabam, sai maza huɗu suka zo ƙarfafa shi da kuma yi masa gargaɗi. Mazajen sun yi kwanaki da yawa ba su ce ko uffan ba. Amma furucin da Elifaz da Bildad da kuma Zofar suka yi daga baya ya nuna cewa ba zama suka yi suna tunani a kan yadda za su taimaka wa Ayuba ba. Maimakon hakan, suna tunani ne a kan yadda za su nuna wa Ayuba cewa ya yi wani laifi. Ko da yake wasu cikin abubuwan da suka faɗa gaskiya ne, amma yawanci abubuwa da suka ce game da Ayuba da kuma Jehobah ba gaskiya ba ne. Sun ce Ayuba mugu ne. (Ayu. 32:1-3) Yaya Jehobah ya ji? Ya yi fushi sosai da mazajen nan uku. Ya ce su wawaye ne kuma ya ce su roƙi Ayuba ya yi addu’a a madadinsu.—Ayu. 42:7-9.
16. Wane darasi ne za mu iya koya daga Elifaz da Bildad da kuma Zofar?
16 Mun koyi darussa da dama daga misalai Mat. 7:1-5) Maimakon haka, mu saurare su sosai kafin mu yi magana. Hakan zai taimaka mana mu fahimci yanayinsu. (1 Bit. 3:8) Na biyu, idan mun yi magana, mu tabbata cewa ba baƙar magana ba ce kuma gaskiya muka faɗa. (Afis. 4:25) Kuma na uku, Jehobah yana saurarar furucin da muke yi wa juna.
marasa kyau na Elifaz da Bildad da kuma Zofar. Na ɗaya, bai kamata mu shari’anta ʼyan’uwanmu ba. (17. Wane darasi ne za mu iya koya daga misalin Elihu?
17 Mutum na huɗu da ya ziyarci Ayuba shi ne wani dangin Ibrahim mai suna Elihu. Ya saurara yayin da Ayuba da maza ukun suke magana. Babu shakka, ya saurari furucinsu sosai shi ya sa ya iya yi wa Ayuba gargaɗin da ya taimaka masa. (Ayu. 33:1, 6, 17) Abin da ya fi muhimmanci ga Elihu shi ne ya ɗaukaka Jehobah, ba kansa ko wani mutum ba. (Ayu. 32:21, 22; 37:23, 24) Misalin Elihu ya koya mana cewa akwai lokacin yin shiru da na yin magana. (Yaƙ. 1:19) Mun kuma koya cewa a duk lokacin da muka yi wa wani gargaɗi, muna so ne mu ɗaukaka Jehobah ba kanmu ba.
18. Ta yaya za mu nuna cewa muna daraja baiwar yin magana da Allah ya ba mu?
18 Za mu iya nuna cewa muna daraja baiwar yin magana da Jehobah ya ba mu ta wajen bin shawarar Littafi Mai Tsarki game da lokacin yin magana da kuma na yin shiru. Allah ya hure Sarki Sulemanu ya ce: “Maganar da ta fito daidai take, kamar adon zinariyar da aka yi a kan azurfa.” (K. Mag. 25:11) Idan muna saurarawa sosai sa’ad da mutane suke magana kuma muna yin tunani kafin mu yi magana, furucinmu zai iya zama kamar wannan adon zinariya. Hakan zai sa furucinmu ya riƙa ƙarfafa mutane kuma zai sa Jehobah farin ciki ko da mu masu yin magana ne sosai ko a’a. (K. Mag. 23:15; Afis. 4:29) Wannan ne hanya mafi kyau da za mu nuna godiya ga Allah don kyautar da ya ba mu!
WAƘA TA 82 ‘Mu Bari Haskenmu Ya Haskaka’
^ sakin layi na 5 Kalmar Allah tana ɗauke da ƙa’idodin da za su taimaka mana mu san lokacin da ya kamata mu yi magana da kuma yin shiru. Idan muka san abin da Littafi Mai Tsarki ya ce kuma muna yin sa, za mu riƙa yabon Jehobah da furucinmu.
^ sakin layi na 62 BAYANI A KAN HOTO: Wata ’yar’uwa ta ga cewa ya dace ta ba wata shawara.
^ sakin layi na 64 BAYANI A KAN HOTO: Wani ɗan’uwa yana ba wani shawara game da tsabta.
^ sakin layi na 66 BAYANI A KAN HOTO: Abigail ta tattauna da Dauda a lokacin da ya dace kuma hakan ya kawo sakamako mai kyau.
^ sakin layi na 68 BAYANI A KAN HOTO: Wasu ma’aurata sun ƙi faɗin yadda ake gudanar da ayyukanmu a ƙasar da aka saka takunkumi.
^ sakin layi na 70 BAYANI A KAN HOTO: Wani dattijo ya tabbata cewa babu wani da ke jin batun sirri na ikilisiya da suke tattaunawa.