Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Wajibi ne Kiristoci su yi amfani da lamirinsu da suka horar bisa koyarwar Littafi Mai Tsarki sa’ad da suke sha’ani da ma’aikatan gwamnati

Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu

Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu

Mene ne zai taimaka wa Kiristoci su san ko ya dace su ba da kyautar kuɗi ko kuma wani abu ga ma’aikatan gwamnati?

Akwai abubuwa da dama da ya kamata mu yi la’akari da su. Wajibi ne Kiristoci su zama masu faɗan gaskiya. Ya kamata su riƙa bin dokar ƙasar da ba ta saɓa wa dokar Jehobah ba. (Mat. 22:21; Rom. 13:1, 2; Ibran. 13:18) Ƙari ga haka, suna yin la’akari da al’adu da kuma ra’ayin mutanen ƙasar kuma su ‘ƙaunaci maƙwabcinsu kamar ransu.’ (Mat. 22:39; Rom. 12:17, 18; 1 Tas. 4:11, 12) Bin irin waɗannan ƙa’idodin zai shafi yadda Kiristoci da ke zama a ɓangarori dabam-dabam na duniya za su ɗauki ba da kyautar kuɗi ko kuma wani abu.

A wurare da yawa, ba dole ba ne mutum da yake zama a wani yanki ya ba ma’aikatan gwamnati kuɗin goro saboda wata hidima da aka yi masa ba. Gwamnati tana biyansu don hidimomin da suke yi, saboda haka ba sa ce a ba su kuɗi kuma ba sa zato cewa za a ba su da yake ana biyansu albashi. A ƙasashe da yawa, idan ma’aikatan gwamnati suka karɓi kuɗi don aikinsu da suke yi, sun taka doka ko da suna yin aikin da aka bukace su su yi. Yin hakan cin ha’inci ne, ko idan kyautar ba ta shafi hidimar da ma’aikacin ya yi ba. A irin wannan yanayin, Kirista ba zai ba ma’aikatan gwamnati kuɗi ba domin hakan bai dace ba.

Amma, a ƙasashen da babu irin waɗannan dokoki ko kuma ba a bin su, ma’aikatan gwamnati suna ganin cewa karɓan kyautar kuɗi ba laifi ba ne. Har ma a wasu ƙasashe, ma’aikatan gwamnati suna yin amfani da matsayinsu don su karɓi kuɗi ko kuma wani abu daga wurin mutane kafin su yi musu hidimomi, kuma ba za su yi hidimar ba idan ba a ba su kyautar kuɗi ba. Saboda haka, ma’aikatan gwamnati da ke rajistan aure da karɓan haraji da kuma ba da takardan izinin gina gida da dai sauransu, sukan ce a ba su kyautar kuɗi kafin su yi waɗannan hidimomin. Ƙari ga haka, idan mutane ba su ba da kyautar kuɗi ba, ma’aikatan za su yi jinkirin yin waɗannan hidimomin ko kuma su ƙi yin hakan gabaki ɗaya. An ba da rahoto cewa a wata ƙasa mutane masu kashe gobara ba za su yarda su kashe gobara ba sai an ba su kuɗin goro.

A wasu lokatai, ba laifi ba ne Kirista ya ba da kyauta don wasu hidimomi da aka yi masa

A ƙasashen da abubuwan da aka ambata a nan ya zama gama gari, wasu suna ganin ba zai yiwu ba a guji ba da kyauta. A irin wannan yanayin, Kirista yana iya lissafin kuɗin goron a cikin kuɗin da yake bukata ya biya don a yi masa wasu hidimomi. Amma, a wurin da cin hanci da rashawa ya zama gama gari, Kirista yana bukatar ya mai da hankali don kada ya yi abin da Allah ya haramta. Ba da kyautar kuɗi wa ma’aikacin gwamnati don ya yi abin da aka bukace shi ya yi ya bambanta da ba da cin hanci don yin wani abin da doka ta hana. A wurin da cin hanci ya zama gama gari, wasu mutane suna ba ma’aikacin gwamnati kyautar kuɗi don a yi musu wata hidima da bai kamata a yi musu ba ko kuma su ba ɗan sanda ko kuma ma’aikacin gwamnati “kyautar kuɗi” don kada su biya wata diyya. Hakika, ba zai dace ba mu ba da “cin hanci” ko kuma mu karɓi cin hanci ba. Yin hakan rashin adalci ne.—Fit. 23:8; K. Sha. 16:19; Mis. 17:23.

Kiristoci sun horar da lamirinsu bisa ga koyarwar Littafi Mai Tsarki. Saboda haka, yawancin Kiristoci da suka manyanta ba sa son ba da kyautar kuɗi ga ma’aikatan gwamnati da suka bukaci hakan. Suna ganin cewa idan suka yi hakan suna goyon bayan cin hanci da rashawa. Saboda haka, ba sa ba da kuɗin goro kuma ba sa karɓa.

Kiristoci da suka manyanta suna ganin cewa ba da kuɗin goro don a yi musu wasu hidimomi da doka ta hana zai iya zama cin hanci. Amma, suna ganin cewa suna iya ba da kuɗin goro don a yi musu wasu hidimomi ko kuma kada a ɓata lokacin su. A wani yanayi, bayan an yi wa wasu Kiristoci jinya a asibiti, sukan ba wa likitoci da nas-nas kyauta don nuna godiya saboda jinya da aka yi musu. A wannan yanayin ba za a ce kyautar cin hanci ne ba don sun yi hakan ne bayan jinyar da aka yi musu.

Ba zai yiwu mu tattauna dukan yanayin da za a iya fuskanta a kowace ƙasa ba. Saboda haka, ko da yaya yanayin ƙasarsu yake, ya kamata Kiristoci su yi abin da ya dace da zai sa su kasance da lamiri mai kyau. (Rom. 14:1-6) Wajibi ne su guji yin abubuwan da suka saɓa wa doka. (Rom. 13:1-7) Za su guji yin abin da zai sa a zargi sunan Jehobah ko kuma da zai sa mutane su yi tuntuɓe. (Mat. 6:9; 1 Kor. 10:32) Ƙari ga haka, ya kamata shawarwarin da suke yi su nuna cewa suna ƙaunar maƙwabtansu.—Mar. 12:31.

Ta yaya ’yan’uwa a ikilisiya za su iya nuna farin ciki sa’ad da aka sanar cewa an dawo da wani da aka yi masa yankan zumunci?

A littafin Luka sura 15, Yesu ya ba da kwatancin wani mutum da yake da tumaki ɗari. Sa’ad da ɗaya cikin tumakin ya ɓata, sai mutumin ya bar tumaki casa’in da tara a cikin jeji kuma ya je neman tunkiyar da ta ɓata har ‘ya same’ ta. Yesu ya ci gaba da cewa: “Sa’anda ya same ta, ya ɗibiya ta bisa kafaɗunsa, yana murna. Sa’anda ya isa gida, ya kirawo abokansa da maƙwabtansa, ya tara su, ya ce musu, Ku yi murna tare da ni, gama na sami tunkiyata wadda ta ɓace.” A ƙarshe, Yesu ya ce: ‘Ina ce muku, Hakanan kuma za a yi murna cikin sama bisa mai zunubi guda ɗaya wanda ya tuba, ta fi ta bisa mutum casa’in da tara masu-adalci waɗanda ba su da bukatar tuba ba.’—Luk. 15:4-7.

Mahallin ya nuna cewa Yesu ya ba da wannan kwatancin ne domin ya daidaita ra’ayin marubuta da Farisawa da suke zargin sa cewa yana tarayya da masu karɓan haraji da kuma masu zunubi. (Luk. 15:1-3) Yesu ya nuna cewa ana farin ciki sosai a sama sa’ad da mai zunubi ya tuba. Saboda haka, za mu iya yin wannan tambayar, ‘Tun da ana farin ciki a sama, shin bai dace a yi murna a duniya sa’ad da wani ya tuba kuma ya gyara halayensa ba?’—Ibran. 12:13.

Muna da dalilin yin farin ciki sosai, sa’ad da aka dawo da wani da aka yi masa yankan zumunci a ikilisiya. Mutumin zai ci gaba da nuna aminci ga Allah, amma wajibi ne ya tuba kafin a dawo da shi cikin ikilisiya kuma muna farin ciki cewa ya yi hakan. Saboda haka, zai dace ’yan’uwa su yi tafi kuma su yi hakan da daraja kuma a lokaci ɗaya sa’ad da aka yi sanarwa cewa an dawo da mutumin da aka yi masa yankan zumunci.

Mene ne ya sa ruwan tafkin Baitasda yake “motsi”?

Wasu mazaunan Urushalima a zamanin Yesu sun gaskata cewa tafkin Baitasda yana iya warkar da mutum sa’ad da ruwan yake “motsi.” (Yoh. 5:​1-7) Saboda haka, marasa lafiya sukan taru a wurin.

Yahudawa suna da wata al’ada na zuwa yin wanka a wannan tafkin. Ana zuba ruwa a wannan tafkin daga wani tafkin da ke kusa da wurin. Bayan an yi wani bincike a wurin, an gano cewa wani dam ne ya raba waɗannan tafkuna biyu. Ana buɗe wata hanyar ruwa da ke wannan dam don ruwa ya zubo daga wannan tafkin zuwa tafkin Baitasda. Babu shakka, a irin wannan lokacin da ruwan yake zubowa ne tafkin yake motsi sosai.

A littafin Yohanna 5:​4, wasu juyin Littafi Mai Tsarki sun ce mala’ika ne ya sa ruwan Baitasda yake motsi, amma wannan ayar ba ta cikin sanannun rubuce-rubucen Helenanci na dā ­kamar Codex Sinaiticus na ƙarni na huɗu. A tafkin Baitasda, Yesu ya warkar da wani mutum da yi shekara 38 yana rashin lafiya. Mutumin ya warke nan take ba tare da ya shiga cikin tafkin ba.