Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DAGA TARIHINMU

“Wanda Aka Danka wa Aikin”

“Wanda Aka Danka wa Aikin”

AN YI kwanaki ana ruwa da iska a Cedar Point, a jihar Ohio na ƙasar Amirka, amma a ranar Litinin ta 1 ga Satumba, ta shekara ta 1919, sai rana ta fito. A wannan ranar ce mutane ƙasa da 1,000 suka halarci wani babban taron Shaidun Jehobah a wani babban ɗakin taro mai ɗaukan mutane 2,500. A ranar da yamma, mutane 2,000 sun zo ta jirgin ruwa da mota da kuma jirgin ƙasa don su halarci taron. A ranar Talata, ƙarin mutane sun hallara har ɗakin ya kasa ɗaukansu. Saboda haka, aka gudanar da sauran shiryen-shiryen taron a waje a ƙarƙashin itatuwa.

Rana tana haska itatuwan kuma hakan ya sa ana ganin inuwar ganyayen a jikin tufafin mazan. Iska mai daɗi daga tafkin Erie tana busa adon gashin tsuntsu da ke hulunan matan. Wani ɗan’uwa ya ce, “Mahallin yana da ban sha’awa kuma ’yan’uwa suna tare cikin kwanciyar hankali, nesa daga duniyar nan, kamar suna aljanna.”

Duk da cewa yanayin wurin yana da kyau, fara’ar mutanen ne aka fi gani. Wata jarida a yankin ta ba da rahoto cewa: “Dukan mutanen da ke wajen masu ibada ne amma suna farin ciki kuma suna fara’a sosai. Waɗannan ɗaliban Littafi Mai Tsarki suna jin daɗin taron nan musamman ma don wahalar da suka sha a cikin ’yan shekarun da suka shige. Hakan ya haɗa da tsanantawa da suka fuskanta a lokacin yaƙi da rashin jituwa a cikin ikilisiyoyi da rufewar Bethel da ke Brooklyn. Ƙari ga haka, an yi wa ’yan’uwa guda takwas da suke ja-gora hukuncin ɗaurin shekara 20 a cikin kurkuku. *

Wasu ɗaliban Littafi Mai Tsarki sun yi sanyin gwiwa kuma sun rasa abin yi a waɗannan shekarun gwaji. Saboda haka, suka daina yin wa’azi. Amma wasu sun yi iya ƙoƙarinsu kuma suka ci gaba da yin wa’azi duk da cewa hukuma ta yi ƙoƙarin hana aikin. Wani mai bincike ya ba da rahoto cewa duk da gargaɗi da aka yi musu, ɗaliban Littafi Mai Tsarki za su “ci gaba da yin wa’azin bishara har zuwa ƙarshe.”

A wannan lokacin gwaji, amintattun ɗaliban Littafi Mai Tsarki sun “mai da hankali ga ja-gorar Ubangiji, . . . suna yin addu’a a kowane lokaci don Allah ya ja-gorance su.” Yanzu sun sake haɗuwa a wannan babban taro a Cedar Point suna farin ciki. Wata ’yar’uwa ta yi tunani kuma ta ce yaushe za su “soma yin hidima gadan-gadan?” Furucinta ya jitu da ra’ayin ’yan’uwa da yawa don sun ƙosa su soma yin wa’azi!

WANI SABON KAYAN AIKI!

A cikin makon, mahalartan sun yi mamakin ko mene ne ma’anar harufan nan “GA” da aka buga a tsarin ayyuka na taron da katin gaisuwa da kuma wurare dabam-dabam a filin taron. A ranar Jumma’a Ɗan’uwa Joseph F. Rutherford ya bayyana ma’anar waɗannan harufa da mutane 6,000 da suka halarta suke mamakinsa. “GA” yana nufin The Golden Age, wata sabuwar mujalla da aka fitar don wa’azi. *

Ɗan’uwa Rutherford ya yi magana game da ’yan’uwansa shafaffun Kirista, ya ce: “Da yake suna da bangaskiya, suna ganin wannan lokaci ne mai muhimmanci (Golden Age) na sarautar Almasihu. . . . Sun ɗauki hakkin yin shelar zuwan wannan lokaci. Hakkin nan ya ƙunshi aikin da Allah ya ba su na yin wa’azi.”

An rubuta a bangon cewa wannan mujallar The Golden Age, mujalla ce na “Gaskiya da Bege da kuma Tabbaci.” Za a yi amfani da ita wajen sanar da gaskiya a wata sabuwar hanya kuma za a riƙa zuwa gida-gida don gaya wa mutane cewa za mu riƙa kawo musu mujallar kowane wata. Sa’ad da aka yi tambaya ko mutane nawa ne za su so su soma wannan aikin, kowa ya tashi tsaye. Bayan haka, suka soma waƙar nan: “Send out thy light and truth, O Lord” (Ka aika haskenka da gaskiyarka, Ya Ubangiji). Wani Ɗan’uwa mai suna J. M. Norris ya ce suna waƙa da murya sosai “har kamar itatuwan suna rawa.”

Bayan sashen taron, mutane sun shiga layi don su kasance a cikin mutane na farko da za a riƙa aika musu mujallun kowane wata. Wata ’yar’uwa mai suna Mabel Philbrick ta ce: “Na yi farin ciki cewa mun sake kasancewa da aikin yi!” Haka ma sauran ’yan’uwan suka ji.

“WANDA AKA DANƘA WA AIKIN”

Ɗaliban Littafi Mai Tsarki wajen 7,000 ne suka yi shiri don yin wannan aiki. An ba da ƙarin bayani a fallen takardar nan Organization Method da kuma ƙasidar nan To Whom The Work Is Entrusted (Wanda Aka Danƙa wa Aikin) cewa: Wani sabon Sashen Hidima a hedkwata ne zai ja-goranci aikin. Za a naɗa Kwamitin Hidima a cikin Ikilisiya da kuma mai ja-gora don ya riƙa ba da umurni. Kowane yanki zai kasance da gidaje 150 zuwa 200. Kuma za a riƙa yin Taron Hidima kowace ranar Alhamis da yamma don ’yan’uwa su ba da labarai game da aikin kuma don a tattara rahotanni.

’Yar’uwa Herman Philbrick ta ce: “Sa’ad da muka koma gidajenmu, sai muka soma kamfen na sanar da mutane game da mujallar.” Mutane a ko’ina sun saurare su. Wata ’yar’uwa mai suna Beulah Covey ta ce: “Kamar dai bayan yaƙin da kuma baƙin cikin da mutane suka fuskanta, kowa ya yi farin cikin jin labarin lokacin da za a magance dukan matsaloli kuma kowa zai yi rayuwa cikin salama.” Wani ɗan’uwa mai suna Arthur Claus ya rubuta cewa: “Dukan ’yan’uwa a ikilisiyar sun yi mamakin yawan mutane da suka amince a riƙa aika musu mujallar a kowane wata.” A cikin watanni biyu, an rarraba fitowar mujallar ta farko kusan dubu ɗari biyar, kuma mutane 50,000 ne suka ce a riƙa aika musu kowane wata.

An wallafa wani talifi a cikin Hasumiyar Tsaro na 1 ga Yuli, 1920, da jigon nan, “Gospel of the Kingdom” (Bisharar Mulki). Game da wannan talifin, ɗan’uwa A. H. Macmillan ya ce wannan shi ne “lokaci na farko da ƙungiyar Jehobah ta ƙarfafa dukan ’yan’uwa maza da mata a faɗin duniya cewa su yi wa’azi game da Mulkin Allah.” Talifin ya ƙarfafa dukan shafaffun Kiristoci cewa su “shaida wa dukan duniya cewa mulkin sama ya kusa.” A yau, ’yan’uwan Kristi, wato, ‘waɗanda aka danƙa wa aikin’ tare da miliyoyin sauran Shaidun Jehobah suna yin wa’azin bishara da ƙwazo yayin da suke jiran lokacin da Mulkin Almasihu na shekara dubu zai magance dukan matsalolin ’yan’ Adam.

^ sakin layi na 5 Ka duba jigon nan “Lokacin Gwaji,” da ke babi na 2 na Mulkin Allah Yana Sarauta!, shafuffuka na 22 zuwa 25.

^ sakin layi na 9 An canja sunan mujallar daga The Golden Age zuwa Consolation a shekara ta 1937, kuma a shekara ta 1946, aka canja sunan zuwa Awake!