Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Wane ne Makiyinka?

Wane ne Makiyinka?

“Mun san dabarun [Shaiɗan] sarai.”​—2 KOR. 2:11.

WAƘOƘI: 150, 32

1. Mene ne Jehobah ya bayyana game da maƙiyinmu a lambun Adnin?

BABU SHAKKA, Adamu ya san cewa macizai ba sa magana. Saboda haka, wataƙila Adamu ya san cewa wani ruhu ne ya yi wa Hauwa’u magana ta yin amfani da maciji. (Far. 3:​1-6) Adamu da Hauwa’u ba su san wannan ruhun ba, amma Adamu ya goyi bayan wannan baƙon wajen yin tawaye da Allah. (1 Tim. 2:14) Nan da nan, Jehobah ya soma bayyana wasu abubuwa game da wannan maƙiyin da ya yaudari Adamu da Hauwa’u, kuma ya yi alkawari cewa zai halaka mugun. Amma, Jehobah ya ce wannan ruhun da ya yi magana ta wurin maciji zai tsananta wa dukan waɗanda suke ƙaunar Allah.​—Far. 3:15.

2, 3. Mene ne wataƙila ya sa ba a bayyana abubuwa da yawa game da Shaiɗan kafin Almasihu ya zo ba?

2 Jehobah bai gaya mana sunan mala’ikan da ya yi masa tawaye ba. * Sai bayan shekara 2,500 da aka yi wannan tawayen a lambun Adnin ne Allah ya faɗi sunan maƙiyin. (Ayu. 1:6) Ban da haka, littattafai guda uku ne kaɗai a Nassosin Ibrananci suka ambata Shaiɗan, wanda yake nufin “Mai tsayayya,” wato littafin 1 Tarihi da Ayuba da kuma Zakariya. Me ya sa ba a yi magana sosai game da wannan maƙiyin kafin Almasihu ya zo ba?

3 Jehobah bai yi bayani dalla-dalla game da Shaiɗan da ayyukansa a Nassosin Ibrananci ba. Wataƙila don ba ya son a ɗaukaka Shaiɗan fiye da kima. Ballantana ma, ainihin dalilin da ya sa aka wallafa Nassosin Ibrananci shi ne don a taimaka wa mutane su san Almasihu kuma su zama mabiyansa. (Luk. 24:44; Gal. 3:24) Sa’ad da Almasihu ya zo, Jehobah ya yi amfani da shi da almajiransa don ya bayyana abubuwa da yawa game da Shaiɗan da kuma mala’ikun da suka bi shi. * Hakan ya dace don Jehobah zai yi amfani da Yesu da shafaffu don ya halaka Shaiɗan da mabiyansa.​—Rom. 16:20; R. Yar. 17:14; 20:10.

4. Me ya sa bai kamata mu riƙa jin tsoron Iblis ba?

4 Manzo Bitrus ya ce Shaiɗan Iblis “yana ruri kamar zaki,” kuma Yohanna ya kira shi “maciji” da “dodo.” (1 Bit. 5:8; R. Yar. 12:9) Amma bai kamata mu riƙa jin tsoron Iblis ba domin ikonsa yana da iyaka. (Karanta Yaƙub 4:7.) Jehobah da Yesu da kuma mala’iku masu aminci suna goyon bayanmu kuma da taimakonsu za mu iya yin tsayayya da maƙiyinmu. Duk da haka, muna bukatar mu san amsoshin tambayoyi nan uku masu muhimmanci: Wane irin iko ne Shaiɗan yake da shi? Ta yaya yake yaudarar mutane? Waɗanne abubuwa ne ba zai iya yi ba? Sa’ad da muke tattauna waɗannan tambayoyin, za mu bincika darussan da za mu iya koya.

WANE IRIN IKO NE SHAIƊAN YAKE DA SHI?

5, 6. Me ya sa gwamnatocin ’yan Adam ba za su iya biyan bukatun mutane ba?

5 Mala’iku da yawa sun goyi bayan Shaiɗan wajen yin tawaye da Allah. Kafin ambaliyar ruwa da aka yi a zamanin Nuhu, Shaiɗan ya sa wasu mala’iku yin lalata da mata. Littafi Mai Tsarki ya kwatanta hakan a alamance sa’ad da ya ce dodon da ya faɗo daga sama ya ja kashi ɗaya bisa uku na taurari don ya fid da su daga sama. (Far. 6:​1-4; Yahu. 6; R. Yar. 12:​3, 4) Sa’ad da waɗannan mala’ikun suka fita daga iyalin Allah, sun goyi bayan Shaiɗan. Waɗannan ’yan tawayen ba kawai ’yan ta da zaune tsaye ba ne. Don Shaiɗan yana son ya yi koyi da Mulkin Allah, sai ya kafa gwamnatinsa wadda ba za mu iya gani da ido ba. Shi ne sarkin gwamnatin kuma ya sa aljanunsa su zama sarakunan duniya.​—Afis. 6:12.

6 Shaiɗan yana amfani da ƙungiyarsa don ya yi iko da dukan gwamnatocin ’yan Adam. Mun tabbata da hakan don sa’ad da Shaiɗan ya nuna wa Yesu “dukan mulkokin duniya,” ya ce: “Zan ba ka iko a kan dukan waɗannan da duk ɗaukakarsu, gama dukan waɗannan an ba ni su. Kuma zan iya ba duk wanda nake so in ba shi.” (Luk. 4:​5, 6) Duk da haka, gwamnatoci da yawa suna yi wa talakawansu abubuwa masu kyau, kuma wasu sarakuna suna son taimaka wa mutane. Amma, babu sarki ɗan Adam da zai iya biyan bukatun mutane.​—Zab. 146:​3, 4; R. Yar. 12:12.

7. Ta yaya Shaiɗan yake amfani da gwamnatoci da addinan ƙarya da kuma masu kasuwanci? (Ka duba hoton da ke shafi na 22.)

7 Ba gwamnatoci kaɗai Shaiɗan da aljanunsa suke amfani da su don su ruɗi ‘dukan duniya’ ba, amma suna yin amfani da addinan ƙarya da kuma masu kasuwanci. (R. Yar. 12:9) Yana kuma amfani da addinan ƙarya don ya yaɗa ƙaryace-ƙaryace game da Jehobah. Ƙari ga haka, ya ƙuduri niyyar sa mutane da yawa su manta da sunan Allah. (Irm. 23:​26, 27) Saboda haka, mutane masu zuciyar kirki suna bauta wa aljanu ko da yake suna ganin suna bauta wa Allah. (1 Kor. 10:20; 2 Kor. 11:​13-15) Ban da haka, Shaiɗan yana amfani da masu kasuwanci don yaɗa ƙaryace-ƙaryace. Alal misali, suna koya wa mutane cewa za su fi farin ciki idan suna neman kuɗi da kuma tara abin duniya. (K. Mag. 18:11) Waɗanda suka yarda da wannan ƙaryar suna bauta wa “kuɗi” maimakon Allah. (Mat. 6:24) A ƙarshe, son abin duniya zai iya sa su daina ƙaunar Allah.​—Mat. 13:22; 1 Yoh. 2:​15, 16.

8, 9. (a) Waɗanne darussa biyu ne za mu iya koya daga labarin Adamu da Hauwa’u da kuma mala’ikun da suka yi tawaye? (b) Me ya sa sanin cewa Shaiɗan ne yake mulkin duniya yake da kyau?

8 Misalan Adamu da Hauwa’u da kuma mala’ikun da suka yi tawaye sun koya mana darussa biyu masu muhimmanci. Na ɗaya, mun koyi cewa da akwai zaɓin da muke bukatar mu yi kuma wajibi ne mu zaɓi ɗaya. Ko mu yi biyayya ga Jehobah ko kuma mu yi biyayya ga Shaiɗan. (Mat. 7:13) Na biyu, waɗanda suka bi Shaiɗan ba za su amfana sosai ba. Adamu da Hauwa’u sun sami zarafin zaɓar wa kansu abin da ya dace da abin da bai dace ba. Kuma aljanu sun sami ikon mallakar gwamnatocin ’yan Adam. (Far. 3:22) Amma bin Shaiɗan yana kawo mugun sakamako a kowane lokaci, ba za mu amfana sosai ba.​—Ayu. 21:​7-17; Gal. 6:​7, 8.

9 Me ya sa yake da kyau mu san cewa Shaiɗan ne yake mulkin duniya? Domin hakan zai taimaka mana mu kasance da ra’ayin da ya dace game da gwamnatocin ’yan Adam kuma zai motsa mu mu riƙa yin wa’azi. Jehobah yana son mu riƙa girmama masu mulki. (1 Bit. 2:17) Kuma yana son mu bi dokokin gwamnatoci muddin ba su saɓa wa dokokin Allah ba. (Rom. 13:​1-4) Amma mun fahimci cewa wajibi ne mu ƙi saka hannu a siyasa, kuma ba za mu goyi bayan wani sarki ko rukunin siyasa ba. (Yoh. 17:​15, 16; 18:36) Domin mun fahimci cewa Shaiɗan yana ƙoƙari ya ɓata sunan Jehobah, za mu yi iya ƙoƙarinmu don mu koya wa mutane game da Allahnmu. Muna alfahari don ana kiran mu da sunan Jehobah kuma muna amfani da sunansa. A gare mu, yin ƙaunar Allah ta fi kuɗi ko abin duniya muhimmanci.​—Isha. 43:10; 1 Tim. 6:​6-10.

TA YAYA SHAIƊAN YAKE YAUDARAR MUTANE?

10-12. (a) Ta yaya Shaiɗan ya jawo hankalin wasu mala’iku? (b) Waɗanne darussa ne muka koya daga abin da ya faru da mala’iku da yawa?

10 Shaiɗan yana amfani da wasu dabaru don ya yaudari mutane. Alal misali, yana amfani da abubuwan da ke jawo hankalin mutane don ya sa su yin abubuwan da yake so. Ƙari ga haka, yana kawo musu hari don su yi masa biyayya.

11 Shaiɗan ya yi amfani da abin da ya jawo hankali mala’iku da yawa. Wataƙila ya lura da su sosai don ya san abin da zai jawo hankalinsu. Shaiɗan ya yi nasara sa’ad da wasu mala’iku suka yi lalata da mata kuma suka haifi ƙattai da suka zalunci mutane. (Far. 6:​1-4) Ƙari ga haka, mai yiwuwa Shaiɗan ya yi wa mala’ikun alkawari cewa za su mallaki ’yan Adam. Ta yin hakan, wataƙila yana ƙoƙari ya hana cikawar annabci game da ‘zuriyar macen.’ (Far. 3:15) Amma, Jehobah bai bar shi ya yi nasara ba, don ya sa aka yi ambaliyar ruwa kuma hakan ya ɓata duk dabarun Shaiɗan da aljanunsa a lokacin.

Shaidan yana kokarin jawo hankalin mutane ta wurin amfani da lalata fahariya da kuma sihiri (Ka duba sakin layi na 12, 13)

12 Mene ne muka koya daga wannan labarin? Shaiɗan yana nasara ta wurin yin amfani da fahariya da lalata don ya yaudari mutane. Mala’ikun da suka bi Shaiɗan sun yi shekaru da yawa a sama suna yi wa Allah hidima. Duk da haka, da yawa a cikin mala’iku sun bar sha’awoyin banza su yi jijiya a zuciyarsu. Hakazalika, ya kamata mu tuna cewa muna iya soma sha’awar banza ko da mun daɗe muna bauta wa Jehobah. (1 Kor. 10:12) Saboda haka, yana da muhimmanci mu riƙa bincika zuciyarmu a kowane lokaci don mu kawar da tunanin banza ko kuma fahariya!​—Gal. 5:26; karanta Kolosiyawa 3:5.

13. Mene ne kuma Shaiɗan yake amfani da shi don ya jawo hankalin mutane, kuma yaya za mu guje shi?

13 Wani abu kuma da Shaiɗan yake amfani da shi don ya yaudari mutane shi ne sihiri. A yau, yana sa mutane su soma sha’ani da aljanu ta wurin addinan ƙarya da kuma fina-finai. Fina-finai da wasannin bidiyo da kuma wasu kafofin yaɗa labarai suna sa mutane su soma sha’awar sihiri. Me zai taimaka mana don kada mu faɗa cikin wannan tarkon? Bai kamata mu riƙa tsammani cewa ƙungiyar Allah za ta lissafa mana nishaɗin da suka dace da waɗanda ba su dace ba. Wajibi ne mu horar da kanmu don mu yi zaɓin da suka yi daidai da ƙa’idodin Allah. (Ibran. 5:14) Amma, za mu yi zaɓin da ya dace idan muka bi shawarar manzo Bulus cewa mu bari ƙaunarmu ga Allah “ta zama ta gaskiya.” (Rom. 12:9) Muna iya yi wa kanmu wannan tambayar: ‘Shin nishaɗin da nake yi zai sa in zama munafuki? Idan waɗanda nake nazari da su suka ga nishaɗin da nake yi, shin za su ce ina yin abin da nake koya musu?’ Idan muka bi ƙa’idodin da muke koya ma wasu, zai yi mana sauƙi mu guji dabarun Shaiɗan.​—1 Yoh. 3:18.

Shaidan yana kai mana hari da wajen sa gwamnati su hana mu wa’azi da matsi daga wurin abokan makarantarmu da kuma tsanantawa daga ’yan iyalinmu (Ka duba sakin layi na 14)

14. Yaya Shaiɗan yake kawo mana hari, kuma me zai taimaka mana don kada mu faɗa cikin tarkonsa?

14 Ƙari ga haka, Shaiɗan yana ƙoƙari ya kawo mana hari don mu yi rashin aminci ga Jehobah. Alal misali, yana iya sa gwamnatoci su hana mu wa’azi. Ko kuma ya sa abokan aikinmu ko abokan makaranta su riƙa mana ba’a don muna bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki. (1 Bit. 4:4) Shaiɗan yana iya sa waɗanda ba sa bauta wa Allah a iyalinmu su hana mu halartan taro. (Mat. 10:36) Mene ne za mu yi? Bai kamata mu yi mamaki ba don Shaiɗan yana hamayya da mu. (R. Yar. 2:10; 12:17) Ƙari ga haka, wajibi ne mu tuna ainihin batun, wato Shaiɗan yana da’awa cewa muna bauta wa Jehobah kawai a lokacin da ba ma cikin matsala. Ya ce za mu ƙi Allah idan muna shan wahala. (Ayu. 1:​9-11; 2:​4, 5) Wajibi ne mu roƙi Jehobah ya taimaka mana don kada mu faɗa cikin tarkon Shaiɗan. Hakika, Jehobah ba zai taɓa yasar da mu ba.​—Ibran. 13:5.

ABUBUWAN DA SHAIƊAN BA ZAI IYA YI BA

15. Shaiɗan zai iya tilasta mana ne mu yi abin da ba ma so? Ka bayyana.

15 Shaiɗan ba zai iya tilasta wa mutane su yi abin da ba sa so ba. (Yaƙ. 1:14) Mutane da yawa a duniya ba su san cewa suna goyon bayan Shaiɗan ba. Amma bayan sun koya game da Jehobah, kowannensu zai zaɓi ko zai bauta wa Jehobah ko kuma zai goyi bayan Shaiɗan. (A. M. 3:17; 17:30) Shaiɗan ba zai iya tilasta mana mu yi rashin aminci ba idan muka ƙuduri niyyar riƙe amincinmu.​—Ayu. 2:3; 27:5.

16, 17. (a) Waɗanne abubuwa ne Shaiɗan da aljanu ba za su iya yi ba? (b) Me ya sa bai kamata mu ji tsoron yin addu’a da babbar murya ba?

16 Da akwai abubuwan da Shaiɗan da aljanu ba za su iya yi ba. Alal misali, Littafi Mai Tsarki bai ce za su iya sanin tunaninmu ba. Jehobah da Yesu ne kaɗai za su iya yin hakan. (1 Sam. 16:7; Mar. 2:8) Idan muna magana ko kuma yin addu’a kuma fa? Shin ya kamata mu ji tsoro cewa Iblis ko kuma aljanu za su ji addu’o’inmu kuma su yi mana illa? A’a. Me ya sa? Ba ma jin tsoron yin nagargarun ayyuka duk da yake Iblis yana iya ganin mu. Hakazalika, bai kamata mu ji tsoron yin addu’a da babbar murya ba duk da yake Iblis yana iya jin mu. Hakika, akwai misalan bayin Allah da yawa a cikin Littafi Mai Tsarki da suka yi addu’a da babbar murya. Ba a ce sun ji tsoron cewa Iblis zai ji su ba. (1 Sar. 8:​22, 23; Yoh. 11:​41, 42; A. M. 4:​23, 24) Idan muka yi iya ƙoƙarinmu don mu yi magana da kuma ayyukan da suka jitu da nufin Allah, muna da tabbaci cewa Jehobah zai sa mu sami rai na har abada ko da Iblis ya sa mun mutu.​—Karanta Zabura 34:7.

17 Muna bukatar mu san maƙiyinmu, amma bai kamata mu ji tsoron sa ba. Ko da mu ajizai ne, za mu iya yin tsayayya da Shaiɗan da taimakon Jehobah. (1 Yoh. 2:14) Shaiɗan zai guje mu idan muka yi tsayayya da shi. (Yaƙ. 4:7; 1 Bit. 5:9) A yau, kamar dai Shaiɗan ya fi rinjayar matasa. Amma me zai taimaka musu su yi tsayayya da Iblis? Za a tattauna wannan batun a talifi na gaba.

^ sakin layi na 2 Littafi Mai Tsarki ya ambata sunan wasu mala’iku. (Alƙa. 13:18; Dan. 8:16; Luk. 1:19; R. Yar. 12:7) Ya kuma ce Jehobah ya ba kowane tauraro suna. (Zab. 147:4) Saboda haka, ya dace mu yi tunani cewa ya ba dukan mala’ikunsa suna, har da wanda ya zama Shaiɗan.

^ sakin layi na 3 A Nassosin Ibrananci, an ambata “Shaiɗan” da sunan nan sau 18, a Nassosin Helenanci na Kirista kuma fiye da sau 30.