Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 22

Ka Inganta Yadda Kake Nazari!

Ka Inganta Yadda Kake Nazari!

Ku zaɓi “abin da ya fi kyau.”​—FILIB. 1:10.

WAƘA TA 35 Mu Riƙa Yin “Abin da Ya Fi Kyau”

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1. Me ya sa yin nazari yake wa wasu wuya?

A YAU mutane suna aiki tuƙuru don su biya bukatunsu. ’Yan’uwanmu da yawa suna aiki na tsawon lokaci don su yi wa iyalansu tanadin abubuwan biyan bukata. Ƙari ga haka, da yawa suna ɗaukan sa’o’i kowace rana don su yi tafiya mai nisa zuwa wurin aikinsu da kuma komawa gidajensu. Wasu kuma suna yin aiki mai wuya don su biya bukatunsu. A ƙarshe, waɗannan ’yan’uwan sukan gaji sosai, kuma hakan yana iya sa ya yi musu wuya su yi nazari.

2. A wane lokaci ne kake yin nazari?

2 Gaskiyar ita ce, wajibi ne mu nemi lokaci don yin nazarin Kalmar Allah da kuma littattafanmu. Yin hakan yana da muhimmanci idan muna so mu ƙulla dangantaka mai kyau da Jehobah kuma mu yi rayuwa har abada. (1 Tim. 4:15) Wasu suna yin nazari da sassafe sa’ad da mutane ba su tashi ba tukun kuma za su iya yin tunani sosai da yake ba su daɗe da tashi ba. Wasu kuma suna ɗaukan ’yan mintoci daddare don yin nazari da kuma bimbini.

3-4. Waɗanne canje-canje ne ƙungiyar Jehobah ta yi game da abubuwan da ake wallafawa, kuma me ya sa?

3 Hakika, za ka yarda cewa yana da muhimmanci mu nemi lokacin yin nazari. Amma mene ne za mu yi nazari a kai? Kana iya cewa, ‘Da akwai abubuwa da yawa da zan iya karanta. Don haka, yana yi mini wuya in karanta duka.’ Wasu suna iya karanta dukan littattafanmu kuma su kalli dukan bidiyoyin da ƙungiyar Jehobah ta fitar, amma hakan yana yi wa ’yan’uwanmu da yawa wuya. Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu ta san da hakan. Shi ya sa aka yanke shawarar rage yawan abubuwan da ƙungiyar Jehobah take bugawa da kuma waɗanda ake wallafawa a Intane.

4 Alal misali, mun daina wallafa littafin nan Yearbook of Jehovah’s Witnesses, da yake da akwai labarai masu ban-ƙarfafa da yawa a jw.org® da kuma waɗanda ake wallafa kowace wata a Tashar JW. Yanzu, sau uku a shekara ake wallafa mujallun Hasumiyar Tsaro na wa’azi da kuma Awake! An yi waɗannan canje-canjen don mu sami damar mai da hankali ga “abin da ya fi kyau,” ba don yin abubuwan da ba su shafi bautarmu ga Jehobah ba. (Filib. 1:10) Bari mu tattauna yadda za ka sa abubuwa masu muhimmanci a kan gaba da kuma yadda za ka amfana daga yin nazari.

KA SA ABUBUWA MASU MUHIMMANCI A KAN GABA

5-6. Waɗanne littattafai ne muke bukatar mu yi nazarin su sosai?

5 Mene ne muke bukatar mu fara yin nazari a kai? Muna bukatar mu keɓe lokaci don mu riƙa yin nazarin Kalmar Allah kowace rana. An rage yawan surorin da muke karantawa a taron tsakiyar mako don mu sami damar yin bimbini a kan abin da muka karanta kuma mu sami lokacin yin bincike sosai. Maƙasudinmu ba kawai mu karanta surorin da za a tattauna a makon ba ne, amma mu bar abin da muka karanta ya ratsa zuciyarmu kuma ya sa mu kusaci Jehobah.​—Zab. 19:14.

6 Mene ne kuma muke bukatar mu yi nazarinsa sosai? Hakika, muna bukatar mu shirya taron Hasumiyar Tsaro da Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya da kuma abubuwan da za a yi nazarinsu a taron tsakiyar mako. Ƙari ga haka, ya kamata mu riƙa karanta kowace Hasumiyar Tsaro da kuma Awake!

7. Ya kamata mu yi sanyin gwiwa domin ba mu iya karanta da kuma kallon dukan abubuwan da ke dandalinmu da kuma Tashar JW ne?

7 Kana iya cewa, ‘Hakan gaskiya ne, amma sauran talifofin da suke fitowa a dandalin jw.org da kuma abubuwan da ake nunawa a Tashar JW kuma fa? Suna da yawa sosai!’ Ka yi la’akari da wannan misalin: Da akwai abubuwa da yawa a kasuwa. Amma mutum ba zai sayi dukan abin da aka yi masa talla ba. A maimakon haka, zai sayi abin da yake bukata. Don haka, idan ba za ka iya karanta dukan abubuwan da ƙungiyar Jehobah take wallafawa a Intane ba, kada ka yi sanyin gwiwa. Ka karanta kuma ka kalli abubuwan da za ka iya. Yanzu, bari mu tattauna abubuwan da yin nazari ya ƙunsa da kuma yadda za mu amfana daga yin hakan.

YIN NAZARI AIKI NE!

8. Waɗanne abubuwan ne muke bukatar mu yi yayin da muke nazarin Hasumiyar Tsaro, kuma ta yaya za ka amfana daga yin hakan?

8 Sa’ad da kake yin nazari, ya kamata ka mai da hankali sosai ga abin da kake karantawa don ka koyi wani abu mai muhimmanci. Yin nazari ba kawai yin karatu da sauri da kuma jan layi a amsoshin ba ne. Alal misali, sa’ad da kake shirya Hasumiyar Tsaro da za a yi nazarinsa, da farko ka karanta sashen abin da za a tattauna da ke farkon talifin. Bayan haka, ka karanta kuma ka yi tunani a kan jigon talifin da ƙanana jigo da kuma tambayoyin bita. Sai ka karanta dukan talifin da kyau a hankali. Ka mai da hankali ga kalmomin da suke nuna abin da sakin layin yake magana a kai. Irin waɗannan kalmomin za su taimaka maka ka san abin da sakin layin ke bayyanawa. Yayin da kake karanta talifin, ka mai da hankali ga yadda kowanne sakin layi yake da alaƙa da jigon talifin da kuma ƙanana jigo. Ka rubuta dukan kalmomi da kuma darussan da a dā ba ka sani ba amma za ka so ka ƙara yin bincike a kansu.

9. (a) Me ya sa muke bukatar mu mai da hankali ga nassosi sa’ad da muke nazarin Hasumiyar Tsaro kuma ta yaya za mu yi hakan? (b) Kamar yadda Yoshuwa 1:8 ta nuna, mene ne muke bukatar mu yi bayan mun karanta nassosi?

9 Yin nazarin Hasumiyar Tsaro a taro yana taimaka mana mu fahimci Littafi Mai Tsarki. Saboda haka, ka mai da hankali ga nassosin da ke talifin, musamman ma waɗanda za a karanta sa’ad da ake yin nazarin. Ka mai da hankali sosai ga yadda kalmomin da ke nassosin suke goyon bayan abin da ake tattaunawa a sakin layin. Ban da haka, sa’ad da ka karanta nassosin, ka yi bimbini sosai a kansu kuma ka yi tunanin yadda za ka yi amfani da su a rayuwarka.​—Karanta Yoshuwa 1:8.

Iyaye, ku koya wa yaranku yadda za su riƙa yin nazari (Ka duba sakin layi na 10) *

10. Kamar yadda Ibraniyawa 5:14 ta nuna, me ya sa iyaye suke bukatar su keɓe lokaci sa’ad da suke Ibada ta Iyali don su koya wa yaransu yadda za su riƙa yin nazari da bincike?

10 Gaskiya ne cewa iyaye suna son yaransu su ji daɗin Ibada ta Iyali a kowane mako. Ko da yake ya dace iyaye su shirya abin da za su tattauna a Ibada ta Iyali, ba dole ne sai sun shirya abubuwa na musamman da za a yi a lokacin ba. Sa’ad da ake yin Ibada ta Iyali, ana iya yin amfani da lokacin don kallon shirye-shiryen Tashar JW ko kuma yin wasu ayyuka kamar gina irin jirgin ruwan Nuhu, amma ƙarami. Ƙari ga haka, yana da muhimmanci iyaye su koya wa yaransu yadda za su riƙa yin nazari. Suna bukatar su koyi yadda za su riƙa shirya taro. Alal misali, ya kamata su koyi yadda za su yi bincike a kan wani batun da ya taso a makaranta. (Karanta Ibraniyawa 5:14.) Idan suka keɓe lokaci suna yin nazari a gida, hakan zai taimaka musu su riƙa saurarawa sosai sa’ad da suka halarci taron ikilisiya ko na da’ira ko kuma na yanki. Ba a kowane lokaci ne za a nuna bidiyoyi a taro ba. Hakika, iyaye ne za su yanke shawarar sa’o’in da za su keɓe don yin nazari da yaransu dangane da shekarunsu da kuma halinsu.

11. Me ya sa yake da muhimmanci mu koya wa ɗalibanmu yadda za su yi nazari da kansu?

11 Ɗalibanmu ma suna bukatar su koyi yadda za su riƙa yin nazari. Sa’ad da muka soma yin nazari da su, muna farin cikin idan mun ga sun ja layi a amsoshi da ke littafin da suke nazari da shi ko kuma idan suna shirya taro. Amma muna bukatar mu koya wa ɗalibanmu yadda za su riƙa yin bincike da kuma yadda za su yi nazari. Idan muka koya musu yin hakan, za su yi bincike a littattafanmu su san irin shawarar da ya kamata su yanke sa’ad da suka fuskanci matsala. Ba za su yi saurin neman taimako daga ’yan’uwa a ikilisiya ba.

KA YI NAZARI DA MANUFAR CIM MA WANI ABU

12. Waɗanne maƙasudai ne ya kamata mu kafa sa’ad da muke yin nazari?

12 Idan ba ka son yin nazari, kana iya tunanin cewa ba zai yiwu ka soma jin daɗin yin hakan ba. Amma za ka iya soma jin daɗin yin nazari. Kana iya somawa ta wajen yin nazarin na ɗan lokaci, a sannu-a-hankali sai ka ƙara lokacin da kake yin nazarin. Zai dace ka kafa maƙasudi. Babu shakka, burinmu na yin nazari shi ne mu kusaci Jehobah. Amma wani abu da za mu iya cim ma nan da nan shi ne amsa tambayar da wani ya yi ko kuma yin bincike a kan wata matsala da muke fuskanta.

13. (a) Ka bayyana matakan da matashi zai iya ɗauka don ya kāre imaninsa a makaranta. (b) Ta yaya za ka yi amfani da shawarar da ke Kolosiyawa 4:6?

13 Alal misali, kai matashi ne da ke makaranta? Wataƙila dukan ’yan ajinku suna yin bikin tuna da ranar haihuwarsu. Za ka so ka yi amfani da Littafi Mai Tsarki don ka nuna musu dalilin da ya sa ba ka yin bikin, amma ƙila kana ganin ba za ka iya ba. Hakan yana nufin cewa kana bukatar ka yi nazari! A nazarin, kana da manufa biyu: (1) ka tabbatar wa kanka dalilin da ya sa Allah ya tsani bikin tuna da ranar haihuwa kuma (2) ka inganta yadda kake bayyana wa mutane gaskiyar da ke Kalmar Allah. (Rom. 1:20; 1 Bit. 3:15) Da farko, kana bukatar ka tambayi kanka, ‘Waɗanne dalilai ne ’yan ajinmu suka ce ya sa suke yin bikin tuna da ranar haihuwarsu?’ Bayan haka, ka yi amfani da littattafanmu don ka yi bincike sosai. Bayyana abin da ka yi imani da shi yana iya kasance maka da sauƙi fiye da yadda ka yi zato. Mutane da yawa suna yin bikin tunawa da ranar haihuwarsu ne domin suna ganin kowa yana yin hakan. Idan ka ba da amsa ɗaya ko biyu, hakan zai iya taimaka ma wani da yake so ya san gaskiya.​—Karanta Kolosiyawa 4:6.

KA INGANTA MARMARIN KOYAN ABUBUWA

14-16. (a) Mene ne za ka yi don ka san game da wani littafi a Littafi Mai Tsarki da ba ka sani sosai ba? (b) Ka yi amfani da nassosin da aka rubuta don ka bayyana littafin Amos. (Ka duba akwatin nan “ Ka San Marubutan Littafi Mai Tsarki da Kyau!”)

14 A ce abin da ake so a karanta da kuma tattauna a taron ikilisiya shi ne littafi ɗaya daga cikin littattafan Hosiya zuwa Malakai. Wataƙila ba ka san annabin da ya rubuta littafin da za a yi nazarinsa ba sosai. Abu na farko da za ka yi shi ne soma yin sha’awar sanin abin da annabin ya rubuta. Ta yaya za ka yi hakan?

15 Da farko, ka tambayi kanka: ‘Me na sani game da marubucin? Wane ne shi, a ina ya zauna, kuma wane irin aiki ya yi?’ Yadda aka yi renon marubucin yana iya nuna mana dalilin da ya sa ya yi amfani da wasu kalmomi da kuma misalai. Yayin da kake karanta Littafi Mai Tsarki, ka nemi kalmomin da ke nuna halayen marubucin.

16 Bayan haka, wani abu kuma da zai taimaka maka shi ne sanin lokacin da aka rubuta littafin. Kana iya sanin lokacin da aka rubuta littafin ta wajen duba “Table of the Books of the Bible” a bayan juyin New World Translation of the Holy Scriptures. Ƙari ga haka, kana iya yin nazarin taswirar da ke ƙasidar nan Taimako don Nazarin Kalmar Allah, shafuffuka na 14-17. Idan littafin da kake yin nazarinsa na annabci ne, zai dace ka san abubuwan da suka faru a lokacin da aka rubuta littafin. Waɗanne mugayen abubuwa ne mutanen suke yi da ya sa aka tura annabin ya taimaka musu su tuba? Waɗanne annabawa ne suka yi rayuwa a lokaci ɗaya da annabin da ya rubuta littafin? Don ka sami cikakken bayani game da abubuwan da suka faru a lokacin, wataƙila za ka bukaci karanta wasu littattafan Littafi Mai Tsarki. Alal misali, don ka fahimci abin da ya faru a lokacin da annabi Amos yake raye, za ka amfana idan ka karanta wasu ayoyi daga littafin 2 Sarakuna da kuma 2 Tarihi, waɗanda ke ƙarin bayani a Amos 1:1. Ƙari ga haka, kana iya bincika littafin Hosiya wanda wataƙila sun yi rayuwa a lokaci ɗaya da Amos. Idan ka bincika waɗannan littattafan, za ka fahimci yadda rayuwa take a lokacin da Amos yake raye.​—2 Sar. 14:​25-28; 2 Tar. 26:​1-15; Hos. 1:​1-11; Amos 1:1.

KA MAI DA HANKALI GA WASU BAYANAI

17-18. Ka yi amfani da misalan da ke sakin layin nan ko kuma wani misali don ka bayyana yadda mai da hankali a kan ƙanana batutuwa zai sa mu ji daɗin nazari.

17 Idan muna karanta Littafi Mai Tsarki, zai dace mu yi sha’awar koyan sabbin abubuwa. Alal misali, a ce kana karanta sura ta 12 a littafin Zakariya da ya yi annabci game da mutuwar Almasihu. (Zak. 12:10) Sa’ad da ka kai aya ta 12, sai ka karanta cewa “iyalin gidan Natan” za su yi kuka da kuma baƙin ciki sosai saboda mutuwar Almasihu. Maimakon ka wuce wannan furucin, sai ka ɗan dakata kuma ka tambayi kanka: ‘Mece ce dangantakar Almasihu da iyalin Natan? Zan iya samun ƙarin bayani kuwa?’ Sai ka yi bincike. Kuma ka karanta 2 Sama’ila 5:​13, 14, a wurin ka fahimci cewa Natan ɗan Sarki Dauda ne. Sai bincikenka ya sake kai ka Luka 3:​23, 31, a wurin an bayyana cewa Yesu ya fito ne daga zuriyar Natan ta wajen Maryamu. (Ka duba Hasumiyar Tsaro ta Agusta 2017, shafi na 32, sakin layi na 4.) Sai ka ga kana marmarin ci gaba da nazarin! Ka san an yi annabci cewa Yesu zai fito daga zuriyar Dauda. (Mat. 22:42) Amma, Dauda yana da yara maza fiye da 20. Babu shakka, ya dace da Zakariya ya ambata sunan iyalin Natan cewa za su yi kuka saboda mutuwar Yesu.

18 Ga wani misali kuma. A sura ta farko na littafin Luka, wurin ya ce mala’ika Jibra’ilu ya ziyarci Maryamu kuma ya gaya mata game da yaron da za ta haifa. Ya ce: ‘Zai zama babban mutum, kuma za a ce da shi Ɗan Mafi Ɗaukaka. Ubangiji Allah zai ba shi kujerar mulkin kakansa Dawuda. Zai yi mulkin gidan Yakub har abada.’ (Luk. 1:​32, 33) Wataƙila muna iya mai da hankali kawai ga wurin da Jibra’ilu ya ce za a kira Yesu, “Ɗan Mafi Ɗaukaka.” Amma Jibra’ilu ya yi annabci cewa Yesu ‘zai yi mulki.’ Muna iya tunanin abin da Maryamu take ganin Jibra’ilu yake nufi. Shin ta yi tunani cewa mala’ikan yana nufin Yesu zai sauya Sarki Hiridus ko kuma wani da zai gāje shi a matsayin sarkin Isra’ila ne? Idan Yesu ya zama sarki, Maryamu za ta zama magajiya, hakan yana nufin cewa iyalinta za su koma fādar sarki da zama. Amma Littafi Mai Tsarki bai faɗa cewa Maryamu ta gaya wa Jibra’ilu wannan batun ba. Ƙari ga haka, babu inda aka nuna cewa Maryamu ta ce a ba ta matsayi a Mulkin Allah, kamar yadda mabiyan Yesu biyu suka yi. (Mat. 20:​20-23) Wannan bayanin ya nuna mana cewa Maryamu tana da tawali’u sosai!

19-20. Kamar yadda Yaƙub 1:​22-25 da kuma 4:8 suka nuna, me muke son mu cim ma sa’ad da muke nazari?

19 Ya kamata mu tuna cewa dalilin da ya sa muke yin nazarin Littafi Mai Tsarki da kuma littattafanmu shi ne don mu kusaci Jehobah. Muna son mu san halayenmu da kuma canje-canjen da muke bukatar yi don mu faranta wa Allah rai. (Karanta Yaƙub 1:​22-25; 4:8.) A duk lokacin da muka soma nazari, mu roƙi Jehobah ya ba mu ruhu mai tsarki, ya taimaka mana mu amfana daga nazarin kuma mu yi canje-canje a rayuwarmu.

20 Bari dukanmu mu zama kamar bawan Allah da wani marubucin zabura ya yi magana a kai cewa: ‘Yana jin daɗin kiyaye koyarwar Yahweh, yana tunanin Koyarwar dare da rana. . . . A kome kuwa zai yi nasara.’​—Zab. 1:​2, 3.

WAƘA TA 88 Ka Koya Mini Hanyoyinka

^ sakin layi na 5 Jehobah ya yi mana tanadin abubuwan da za mu kalla, mu karanta da kuma nazarta. Wannan talifin zai taimaka maka ka zaɓi abin da za ka riƙa yin nazari da shi, kuma an ba da shawarwarin da za su taimaka maka ka amfana daga nazarin da kake yi.

^ sakin layi na 61 BAYANI A KAN HOTO: Wasu iyaye suna nuna wa yaransu yadda za su shirya Hasumiyar Tsaron da za a nazarta.

^ sakin layi na 63 BAYANI A KAN HOTO: Wani ɗan’uwa yana bincike a kan marubucin littafin Amos. Sauran hotunan suna nuna abubuwan da ɗan’uwan yake tunaninsa sa’ad yake karanta Littafi Mai Tsarki kuma yake yin bimbini.