Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 21

Kada Ka Bar ‘Hikimar Wannan Duniyar’ ta Yaudare Ka

Kada Ka Bar ‘Hikimar Wannan Duniyar’ ta Yaudare Ka

“Hikimar wannan duniya wawanci ne a wurin Allah.” ​—1 KOR. 3:19.

WAƘA TA 98 Nassosi Hurarre Ne Daga Allah

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1. Mene ne Kalmar Allah ta koya mana?

ZA MU iya magance duk wata matsala da muke fuskanta domin Jehobah ne Babban Malaminmu. (Isha. 30:​20, 21) Kalmarsa ta ba mu dukan abin da muke bukata don mu zama ‘cikakku’ kuma mu “kasance a shirye . . . domin kowane irin kyakkyawan aiki.” (2 Tim. 3:17) Idan muka bi koyarwar Littafi Mai Tsarki, za mu zama masu hikima fiye da waɗanda suke ɗaukaka “hikimar wannan duniya.”​—1 Kor. 3:19; Zab. 119:​97-100.

2. Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?

2 Kamar yadda za mu koya, hikimar duniya tana yawan ƙarfafa mu mu riƙa bin sha’awoyinmu. Saboda haka, yana iya yi mana wuya mu ƙi bin ra’ayi mutanen duniya da kuma abubuwan da suke yi. Shi ya sa Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ku lura fa, kada wani ya kama hankalinku ta wurin ilimin duniyar nan da kuma ilimin ruɗu na banza, waɗanda suka fito daga wurin al’adar ’yan Adam.” (Kol. 2:8) A wannan talifin za mu ga yadda mutane suka soma amincewa da ƙaryace-ƙaryace biyu da Shaiɗan yake yaɗawa. A kowannensu, za mu ga yadda hikimar da ke cikin Kalmar Allah ta fi hikimar duniya.

RA’AYIN MUTANE GAME DA JIMA’I YA CANJA

3-4. Yaya ra’ayin mutane game da jima’i ya canja a Amirka a ƙarni na 20?

3 Ra’ayin mutane game da jima’i ya canja sosai a Amirka a somawar ƙarni na 20. A dā, mutane da yawa sun gaskata cewa ma’aurata ne kaɗai ya kamata su yi jima’i kuma bai kamata a riƙa tattauna batun a gaban jama’a ba. Amma mutane sun daina kasancewa da wannan ra’ayin kuma suna yin abin da suka ga dama.

4 Hali da kuma ra’ayin mutane game da jima’i sun canja sosai ne bayan Yaƙin Duniya ta Ɗaya. Wata mai aikin bincike ta ce: “Fina-finai da wasanni da waƙoƙi da littattafai da kuma masu talla sun soma nuna abubuwan da ke ƙarfafa yin lalata.” A wannan lokacin, mutane sun soma irin rawa da ke ta da sha’awar yin jima’i kuma sun soma saka tufafi da ba su dace ba. Kamar yadda Littafi Mai Tsarki ya ce zai faru a kwanaki na ƙarshe, mutane sun zama “masu son jin daɗin kansu.”​—2 Tim. 3:4.

Bayin Jehobah ba sa bin ra’ayin mutanen duniya game da ɗabi’a (Ka duba sakin layi na 5) *

5. Mene ne ra’ayin mutane game da ɗabi’a bayan shekara ta 1960?

5 Bayan 1960, zaman dadiro da daudanci da kuma kashe aure sun zama ruwan dare gama gari. Abubuwan da mutane suke karantawa da kuma kallo sun soma nuna yin lalata sosai. Mene ne mugun sakamakon waɗannan abubuwan? Wata mawallafiya ta ce mutane sukan sha wahala sosai idan suka daina yin abin da ya dace. Alal misali, miji da mata suna rabuwa da juna, ko kuma miji ko mata suna barin iyalin. Ƙari ga haka, mutane suna fuskantar matsaloli ko kuma su shaƙu da kallon hotunan batsa. Wani sakamako shi ne cututtuka da ake yaɗawa ta lalata, kamar cutar kanjamau. Dukan waɗannan abubuwan sun nuna cewa hikimar duniya wawanci ne.​—2 Bit. 2:19.

6. Ta yaya ra’ayin mutanen duniya game da jima’i yake ɗaukaka abin da Shaiɗan yake so?

6 Shaiɗan yana son ra’ayin mutanen duniya game da jima’i. Babu shakka, yana farin cikin ganin yadda mutane suke taka dokar Allah game da jima’i da kuma rena gamin aure da Allah ya shirya wa ’yan Adam. (Afis. 2:2) Idan mutane suna lalata, suna nuna cewa ba sa daraja baiwar haifan yara da Jehobah ya ba ’yan Adam. Kuma yin hakan yana iya hana su samun rai na har abada.​—1 Kor. 6:​9, 10.

RA’AYIN ALLAH GAME DA LALATA

7-8. Me ya sa ra’ayin Allah game da jima’i ya fi na duniyar Shaiɗan?

7 Mutane da suke bin hikimar wannan duniya sun rena dokokin Allah game da ɗabi’a, suna da’awa cewa dokokin ba su dace ba. Wasu mutane suna iya tambaya, ‘Me ya sa Allah zai halicce mu da sha’awar yin jima’i kuma ya hana mu yin hakan?’ Suna yin wannan tambayar domin suna ganin cewa ya kamata mutane su yi abin da suke so. Amma Littafi Mai Tsarki bai amince da wannan ra’ayin ba. Ya koya mana cewa bai kamata mu gamsar da dukan sha’awoyinmu ba, kuma muna iya ƙin yin abin da bai dace ba. (Kol. 3:5) Ƙari ga haka, Jehobah ya shirya aure don mu iya gamsar da sha’awoyinmu na yin jima’i a hanyar da ta dace. (1 Kor. 7:​8, 9) Ta wannan hanyar, mata da miji suna iya jin daɗin yin jima’i ba tare da yin da-na-sani da kuma damuwa don sakamakon da yin lalata ke jawowa ba.

8 Hikimar da ke Littafi Mai Tsarki ta bambanta da ta wannan duniya. Littafi Mai Tsarki ya koya mana ra’ayin da ya dace game da jima’i da ba za ta cutar da mu ba. Ya ce jima’i yana iya sa mutum farin ciki. (K. Mag. 5:​18, 19) Kuma Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kowa ya san yadda zai bi da jikinsa cikin tsarki da mutunci, ba ta muguwar sha’awa ba yadda waɗanda ba Yahudawa ba suke yi, waɗanda ba su san Allah ba.”​—1 Tas. 4:​4, 5.

9. (a) Ta yaya aka ƙarfafa mutanen Jehobah su bi hikimar da ke cikin Kalmar Allah a farkon ƙarni na 20? (b) Wace shawara ce ke littafin 1 Yohanna 2:​15, 16? (c) Kamar yadda aka lissafa a Romawa 1:​24-27, waɗanne ayyukan lalata ne ya kamata mu guji?

9 Kusan shekara 100 da suka shige, mutanen Jehobah ba su bi ra’ayin mutane masu “rashin kunya” ba. (Afis. 4:19) Sun yi ƙoƙari su bi ƙa’idodin Jehobah sosai. Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Mayu, 1926, ta ce “ya kamata namiji ko tamace ta kasance da tsarki a tunaninta da ayyukanta, musamman a batun da ya shafi wani jinsi.” Bayin Jehobah suna bin hikimar da ke cikin Kalmar Allah ko da mene ne mutanen duniya suke yi. (Karanta 1 Yohanna 2:​15, 16.) Muna godiya cewa muna da Kalmar Allah! Ƙari ga haka, muna godiya cewa Jehobah yana koyar da mu a lokacin da ya dace don ya taimaka mana mu guji bin ra’ayin mutanen duniya a batun ɗabi’a. *​—Karanta Romawa 1:​24-27.

MUTANE SUN SOMA SON KANSU FIYE DA KIMA

10-11. Mene ne Littafi Mai Tsarki ya ce zai faru a kwanaki na ƙarshe?

10 Littafi Mai Tsarki ya ce a kwanaki na ƙarshe, “mutane za su zama masu son kansu.” (2 Tim. 3:​1, 2) Saboda haka, ba ma mamaki cewa mutane suna ɗaukaka wannan halin son kai. Wani littafi ya ce bayan shekara ta 1970, an “wallafa wasu littattafan da suke ba mutum shawara a yadda zai yi nasara a rayuwa.” Wasu littattafai sun ce “bai kamata mutum ya canja kome game da kansa ba ko kuma ya riƙa ganin cewa yadda yake yin abubuwa bai dace ba.” Alal misali, ka yi la’akari da abin da aka ƙara faɗa a irin wannan littafin: “Ka ƙaunaci kanka domin ka fi kowa kyau kuma babu mutum irin ka da ya taɓa wanzuwa.” Littafin ya ce, “ya kamata mutum ya tsai da shawarar yadda zai riƙa yin abubuwa, kuma ya yi duk wani abin da yake ganin ya dace.”

11 Ka taɓa jin irin wannan ra’ayin? Abin da Shaiɗan ya ƙarfafa Hauwa’u ta yi ke nan. Ya ce mata za ta iya ‘zama kamar Allah, mai sanin nagarta da mugunta.’ (Far. 3:5) A yau, mutane da yawa suna ji da kansu kuma suna ganin ba wanda ya isa ya gaya musu abin da za su yi, har da Allah ma. Alal misali, ana ganin wannan ra’ayin musamman a yadda mutane suke ɗaukan aure.

Kirista yana saka bukatun wasu a gaba, musamman na matarsa ko na mijinta (Ka duba sakin layi na 12) *

12. Wane ra’ayi ne game da aure mutanen duniya suke bi?

12 Littafi Mai Tsarki ya umurci ma’aurata su riƙa daraja juna kuma su cika alkawarin da suka yi sa’ad da suka yi aure. Ya ƙarfafa su su ƙuduri niyyar kasancewa tare, ya ce: “Mutum zai bar babansa da mamarsa ya manne wa matarsa, biyun su zama ɗaya.” (Far. 2:24) Amma waɗanda suke bin ra’ayin mutanen duniya suna ɗaukaka wani ra’ayi dabam, sun ce ya kamata kowa ya mai da hankali ga biyan bukatunsa. Wani littafi game da kashe aure ya ce: “A wasu ƙasashe, idan mata da miji suka yi aure, suna yin alkawari a gaban mutane cewa za su kasance tare muddar ransu. Amma mutane da yawa sun canja kalamin wannan alkawarin cewa za su kasance tare muddin suna son juna.” Da yake mutane ba sa daraja aure, iyalai da yawa sun rabu kuma hakan ya jawo wa mutane da yawa matsaloli. Hakika, a bayyane yake cewa ra’ayin mutanen duniya game da aure wawanci ne.

13. Me ya sa Jehobah ya tsani masu girman kai?

13 Littafi Mai Tsarki ya ce: “Kowane mai girman kai, abin ƙyama ne ga Yahweh.” (K. Mag. 16:5) Me ya sa Jehobah ya tsani masu girman kai? Dalili ɗaya shi ne cewa waɗanda suke son kansu fiye da kima kuma suke ɗaukaka wannan ra’ayin suna yin koyi da Shaiɗan. Ka yi tunanin wannan, Shaiɗan ya gaskata cewa Yesu wanda Allah ya yi amfani da shi wajen halittar dukan abubuwa zai bauta masa! (Mat. 4:​8, 9; Kol. 1:​15, 16) Mutanen da ke da wannan ra’ayin sun sa mu kasance da tabbaci cewa hikimar duniya wawanci ne a wurin Allah.

RA’AYIN ALLAH GAME DA JI DA KAI

14. Ta yaya littafin Romawa 12:3 ya taimaka mana mu kasance da ra’ayin da ya ce game da kanmu?

14 Littafi Mai Tsarki ya taimaka mana mu kasance da ra’ayin da ya dace game da kanmu. Ya ce ya kamata mutum ya so kansa yadda ya dace. Yesu ya ce: Ka “ƙaunaci maƙwabcinka kamar yadda kake ƙaunar kanka,” hakan ya nuna cewa ya kamata mu ɗan mai da hankali ga biyan bukatunmu. (Mat. 19:19) Amma, Littafi Mai Tsarki ya ce bai kamata mu riƙa ganin mun fi wasu muhimmanci ba. Maimakon haka, ya ce: “Kada ku yi kome da sonkai ko girman kai, sai dai da sauƙin kai. Amma cikin sauƙin kai kuma bari kowa ya ɗauka ɗan’uwansa da muhimmanci fiye da kansa.”​—Filib. 2:3; karanta Romawa 12:3.

15. Me ya sa kake ganin cewa bin shawarar Littafi Mai Tsarki game da yadda muke ɗaukan kanmu tana da amfani?

15 A yau, mutane da yawa da ake ganin suna da wayo sun ce bin shawarar Littafi Mai Tsarki game da son kanmu wawanci ne. Sun ce mutane za su rena ka kuma su cuce ka idan kana ɗaukansu da muhimmanci fiye da kanka. Amma, mene ne sakamakon ra’ayin da duniyar Shaiɗan take ɗaukakawa? Mene ne ka lura da shi? Mutane masu son kansu suna farin ciki ne? Iyalansu suna farin ciki ne? Suna da abokai na ƙwarai? Shin suna da dangantaka na kud da kud da Allah? Mene ne ka gani da ya tabbatar maka da cewa bin shawarar Littafi Mai Tsarki game da yadda muke ɗaukan kanmu tana da amfani?

16-17. Waɗanne abubuwa ne ya kamata su sa mu yin godiya, kuma me ya sa?

16 Bin shawarar mutanen da ake ganin suna da hikima na kamar baƙon da ke neman kwatancen hanya daga wurin wani baƙo. Babu shakka, dukansu za su ɓata. Yesu ya ce mutanen da suke ganin suna da hikima a zamaninsa “makafi ne masu yi wa makafi ja-gora. Idan kuwa makaho ya yi wa wani makaho ja-gora, ai, dukansu za su fāɗi cikin rami.” (Mat. 15:14) Hakika, hikimar wannan duniya wawanci ne a wurin Allah.

Bayin Allah suna farin cikin tuna yadda bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki ya amfane su (Ka duba sakin layi na 17) *

17 Shawarar Littafi Mai Tsarki tana “da amfani wajen koyarwa, da tsawatarwa, da gyaran hali, da kuma horarwa cikin adalci.” (2 Tim. 3:16) Muna godiya sosai cewa Jehobah yana yin amfani da ƙungiyarsa wajen kāre mu daga hikimar wannan duniyar! (Afis. 4:14) Abubuwan da ya yi tanadinsu suna ƙarfafa mu mu bi ƙa’idodin da ke cikin Kalmarsa. Abin ban al’ajabi ne cewa Jehobah yana yi mana ja-goranci ta wurin ƙa’idodin da ke cikin Littafi Mai Tsarki!

WAƘA TA 54 ‘Wannan Ita Ce Hanyar Rai’

^ sakin layi na 5 Wannan talifin zai sa mu ƙara kasancewa da tabbaci cewa Jehobah ne kaɗai zai yi mana ja-goranci mai kyau. Ƙari ga haka, zai nuna mana cewa bin hikimar duniya zai jawo mugun sakamako, amma bin hikimar da ke cikin Kalmar Allah zai amfane mu.

^ sakin layi na 9 Alal misali, ka duba littafin nan Questions Young People Ask​—Answers That Work, Littafi na 1, babi na 24-26, da Littafi na 2, babi na 4-5 da kuma Amsoshi ga Tambayoyi 10 da Matasa Suke Yi, tambaya ta 7, shafuffuka na 21-23.

^ sakin layi na 50 BAYANI A KAN HOTA: Mun ga abubuwa da wasu ma’aurata suka shaida tun suna matasa har suka tsufa. Ɗan’uwan da ’yar’uwar suna wa’azi a shekara ta 1967 zuwa 1969.

^ sakin layi na 52 BAYANI A KAN HOTA: A shekara ta 1980 zuwa 1989, mijin yana kula da matarsa sa’ad da take rashin lafiya kuma ’yarsu tana ganin yadda babanta yake kula da mamarta.

^ sakin layi na 54 BAYANI A KAN HOTA: A yanzu, ma’auratan suna farin cikin ba da labarin yadda bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki ya amfane su. Kuma ’yarsu da iyalinta suna taya su murna.