Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 19

Yadda Ake Nuna Kauna da Adalci Sa’ad da Aka Ci Zarafin Yara

Yadda Ake Nuna Kauna da Adalci Sa’ad da Aka Ci Zarafin Yara

“Kai ba Allah mai jin daɗin mugunta ba ne. Ba ka barin mugaye su kasance a gabanka.”​—ZAB. 5:4.

WAƘA TA 142 Mu Riƙe Begenmu da Ƙarfi

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1-3. (a) Kamar yadda aka nuna a Zabura 5:​4-6, yaya Jehobah yake ji game da mugunta? (b) Me ya sa cin zarafin yara ya saɓa wa dokar Kristi?

JEHOBAH ALLAH ya tsani kowace irin mugunta. (Karanta Zabura 5:​4-6.) Musamman ma ya tsani cin zarafin yara, domin hakan mugun zunubi ne sosai! Mu Shaidun Jehobah muna yin koyi da Jehobah, ba ma amincewa da cin zarafin yara kuma ba ma kāre waɗanda suke yin hakan a ikilisiyar Kirista.​—Rom. 12:9; Ibran. 12:​15, 16.

2 Cin zarafin yara ya saɓa wa dokar Kristi! (Gal. 6:2) Me ya sa muka ce hakan? Kamar yadda muka koya a talifin da ya gabata, dokar Kristi ta ƙunshi duk koyarwar Yesu da abubuwan da ya yi. Ƙauna ce ta sa Yesu ya koyar da mutane kuma koyarwar tana ƙarfafa yin adalci. Domin Kiristoci suna bin wannan dokar, suna bi da yara a yadda zai sa su kasance da kwanciyar rai kuma su ga cewa ana ƙaunar su sosai. Amma cin zarafinsu son kai ne da kuma zunubi. Ƙari ga haka, yana sa yara su ji babu wanda yake kāre su ko kuma ƙaunar su.

3 Abin baƙin ciki, cin zarafin yara ya zama ruwan dare gama gari, kuma matsala ce mai tsanani da ta shafi Kiristoci. Me ya sa? Domin “mugayen mutane da masu ruɗu” suna ƙaruwa, kuma wasu suna ƙoƙari su shigo cikin ikilisiya. (2 Tim. 3:13) Ƙari ga haka, wasu da suke da’awa su ’yan’uwa ne sun bi mugun sha’awoyinsu kuma suka ci zarafin yara. Za mu tattauna dalilin da ya sa cin zarafin yara zunubi ne mai tsanani. Sa’an nan za mu tattauna abin da dattawa za su yi sa’ad da wani ya yi zunubi mai tsanani, har da cin zarafin yara. Da kuma yadda iyaye za su kāre yaransu. *

ZUNUBI MAI TSANANI

4-5. Me ya sa cin zarafin yara zunubi ne ga yaran?

4 Cin zarafin yara yana shafan su na dogon lokaci. Yana shafan wanda aka ci zarafinsa da danginsa da kuma ’yan’uwa a ikilisiya. Cin zarafin yara zunubi ne mai tsanani sosai.

5 Zunubi ga wanda aka ci zarafinsa. * Sa wasu shan wahala zunubi ne. Kamar yadda za mu gani a talifi na gaba, mutumin da ya ci zarafin yara zai sa su shan wahala a hanyoyi da yawa. Ya ci amanar yaran, da yake yaron ko yarinyar ta amince da shi. Saboda haka, ya sa ta shaida abin da bai kamata ba. Dole ne mu kāre yara daga mutanen da ke son cin zarafinsu, kuma waɗanda aka ci zarafinsu suna bukatar ƙarfafawa da kuma taimako.​—1 Tas. 5:14.

6-7. Me ya sa cin zarafin yara zunubi ne ga ikilisiya da kuma hukuma?

6 Zunubi ne ga ikilisiya. Mai shela da ya ci zarafin yara ya ɓata sunan ikilisiyar. (Mat. 5:16; 1 Bit. 2:12) Hakan bai dace ba domin miliyoyin Kiristoci masu aminci sun dāge sosai don su ‘kiyaye bangaskiyarsu.’ (Yahu. 3) Ba ma barin mutane su kasance cikin ikilisiya idan sun yi mugayen abubuwa kuma sun ƙi tuba. Ƙari ga haka, ba ma amincewa da wanda ke ɓata sunan ikilisiya.

7 Zunubi ne ga hukumomi. Wajibi ne Kiristoci su “yi biyayya ga shugabanni.” (Rom. 13:1) Muna yin biyayya ta wajen bin dokokin ƙasarmu. Idan wani a ikilisiya ya taka wata dokar ƙasa, wataƙila ya ci zarafin yara, yana yin zunubi ne ga shugabanni. (Gwada Ayyukan Manzanni 25:8.) Dattawan ikilisiya ba su da ikon hukunta mutumin da ya taka dokar ƙasa, kuma ba sa kāre mutumin da ya ci zarafin yara daga hukuncin da gwamnati za ta yi masa. (Rom. 13:4) Mutumin da ya yi zunubin ne zai girbi abin da ya shuka.​—Gal. 6:7.

8. Ta yaya Jehobah yake ɗaukan zunubin da aka yi ga ’yan Adam?

8 Mafi tsanani, zunubi ne ga Allah. (Zab. 51:4) Idan mutum ya yi zunubi ga mutane, ya yi zunubi ma ga Jehobah. Ka yi la’akari da wani misali daga Dokar da Allah ya ba Isra’ila. A Dokar, an ce mutumin da ya zambaci maƙwabcinsa yana yin “rashin aminci” ne ga Jehobah. (L. Fir. 6:​2-4) Hakika, mai shela da ya ci zarafin yara yana nuna rashin aminci ga Allah. Ban da haka, mutumin yana ɓata sunan Jehobah. Saboda haka, cin zarafin yara zunubi ne mai tsanani ga Allah kuma wajibi ne mu tsani wannan zunubin sosai.

9. Wane bayani ne ƙungiyar Jehobah ta ba da game da cin zarafin yara, kuma me ya sa?

9 Ƙungiyar Jehobah ta wallafa abubuwa da yawa game da cin zarafin yara. Alal misali, talifofin Hasumiyar Tsaro da Awake! sun tattauna abin da waɗanda aka ci zarafinsu za su iya yi don baƙin cikin da suke fama da shi. Talifofin sun ambata yadda wasu za su iya taimaka musu, su ƙarfafa su, da kuma yadda iyaye za su kāre yaransu. Dattawa sun sami horarwa a kan matakin da za su ɗauka idan mai shela ya ci zarafin yara. Ƙungiyar Jehobah ta ci gaba da ba da ƙarin bayani game da yadda dattawa za su bi da zunubin cin zarafin yara. Me ya sa? Don a tabbatar da cewa yadda ake bi da batun ya jitu da dokar Kristi.

YADDA DATTAWA ZA SU BI DA ZUNUBI MAI TSANANI

10-12. (a) Me ya kamata dattawa su riƙa tunawa sa’ad da suke shari’ar da ta shafi zunubi mai tsanani, kuma mene ne suka fi damuwa da shi? (b) Kamar yadda aka nuna a littafin Yaƙub 5:​14, 15, me dattawa suke ƙoƙari su yi?

10 Sa’ad da dattawa suke yin shari’a a kan mutumin da ya yi zunubi mai tsanani, ya kamata su tuna cewa dokar Kristi tana bukatar su nuna ƙauna kuma su yi adalci. Saboda haka, ya kamata su yi la’akari da abubuwa da dama sa’ad da suka ji cewa wani ya yi zunubi mai tsanani. Abin da ya kamata ya fi muhimmanci ga dattawa shi ne su daraja Jehobah da kuma tsarkake sunansa. (L. Fir. 22:​31, 32; Mat. 6:9) Ban da haka, suna damuwa sosai game da dangantakar ’yan’uwansu da Jehobah, kuma suna so su taimaka ma waɗanda aka ci zarafinsu.

11 Ƙari ga haka, dattawan za su yi ƙoƙari su ga ko wanda ya yi zunubi ya tuba, idan ya yi hakan, za su taimaka masa ya gyara dangantakarsa da Jehobah. (Karanta Yaƙub 5:​14, 15.) Kirista da ya yi zunubi mai tsanani yana kamar mai rashin lafiya. Hakan yana nufin cewa ba shi da dangantaka mai kyau da Jehobah. * Muna iya kwatanta dattawa da likitoci. Suna ƙoƙari su sa “mai rashin lafiya [a wannan misalin, mai zunubin]” ya warke. Za su yi amfani da shawarar da ke cikin Littafi Mai Tsarki don su taimaka masa ya gyara dangantakarsa da Allah. Amma hakan zai yiwu ne idan ya tuba da gaske.​—A. M. 3:19; 2 Kor. 2:​5-10.

12 Hakika, dattawa suna da hakki mai muhimmanci. Suna kula da tumakin da Allah da ya ɗanka musu. (1 Bit. 5:​1-3) Dattawa suna so ’yan’uwa su kasance da kwanciyar rai a ikilisiya. Saboda haka, suna ɗaukan mataki nan da nan idan sun ji wani ya yi zunubi mai tsanani, har da cin zarafin yara. Ka yi la’akari da tambayoyin da aka yi a farkon  sakin layi na 13 da  15, da kuma  17.

13-14. Dattawa suna bin dokokin da suka bukaci a kai ƙarar wanda ya ci zarafin yara kuwa? Ka bayyana.

 13 Ya kamata dattawa su bi dokokin da suka ce a kai ƙarar mai cin zarafin yara wurin hukuma? E. Wasu ƙasashe suna da dokokin da suka bukaci mutane su gaya wa hukuma idan wani ya ci zarafin yara. Dattawa da suke waɗannan ƙasashen suna bin dokokin. (Rom. 13:1) Irin waɗannan dokokin ba su taka dokar Allah ba. (A. M. 5:​28, 29) Saboda haka, idan dattawa sun ji cewa wani ya ci zarafin yaro ko yarinya, suna gaya wa ofishinmu nan da nan don su san yadda za su bi da batun.

14 Dattawa suna gaya ma waɗanda aka ci zarafinsu da iyayensu ko kuma wanda ya san game da batun cewa suna iya kai ƙara wurin hukuma. Wane mataki ne za a ɗauka idan mai shela ne ya ci zarafin yara kuma mutanen unguwar sun san da batun? Bai kamata wanda ya kai ƙararsa ya ɗauka cewa ya ɓata sunan Allah ba. Mutumin da ya ci zarafin yaran ne ya ɓata sunan Allah.

15-16. (a) Kamar yadda aka nuna a 1 Timoti 5:​19, me ya sa ake bukatar shaidu biyu kafin dattawa su kafa kwamitin shari’a? (b) Wane mataki ne dattawa za su ɗauka sa’ad da suka ji cewa ana zargin wani mai shela da cin zarafin yara?

 15 Me ya sa dattawa suke bukatar aƙalla shaidu biyu don su tabbata cewa wani ya yi zunubi mai tsanani? Domin abin da Littafi Mai Tsarki ya ce a yi ke nan. Idan mutum ya ce bai yi laifi ba, wajibi ne a samo mutane biyu da suka shaida aukuwar kafin dattawa su kafa kwamitin shari’a. (M. Sha. 19:15; Mat. 18:16; karanta 1 Timoti 5:19.) Shin hakan yana nufin cewa sai an samo shaidu biyu kafin a kai ƙarar mai cin zarafin yara wurin hukuma? A’a. Wannan ƙa’idar Littafi Mai Tsarki ce. Hukuma ta bukaci a kai ƙarar mutumin da ake zarginsa da yin irin wannan laifin.

16 Idan dattawa sun ji cewa ana zargin wani mai shela da cin zarafin yara, za su yi ƙoƙari su bi dokokin da hukuma ta kafa game da kai ƙarar mutumin. Sa’an nan sai su yi bincike don su tabbatar da al’amarin. Idan mutumin ya ce bai yarda da zargin ba, dattawa za su so su ji daga bakin shaidun. Idan wanda ya kai ƙarar da kuma wani sun ce mutumin ya ci zarafin yarinyar ko kuma ya taɓa yi wa wani ko wata hakan, dattawa suna da ƙwaƙƙwarar dalilin kafa masa kwamitin shari’a. * Ko da babu shaida na biyu da ya ce mutumin ya yi zunubin, hakan ba ya nufin cewa wanda ya kai ƙararsa bai faɗi gaskiya ba. Idan babu shaidu biyu da za su tabbatar da cewa mutumin ya ci zarafin yara, dattawa sun san cewa mai yiwuwa mutumin ya yi wani mugun abu da ya ɓata wa mutane rai. Dattawa za su ci gaba da ƙarfafa waɗanda hakan ya sa su baƙin ciki kuma su taimaka musu. Ƙari ga haka, dattawa za su sa wa mutumin da ake zarginsa ido domin su kāre ikilisiyar daga gurɓatarwa.​—A. M. 20:28.

17-18. Ka bayyana aikin kwamitin shari’a.

 17 Wane mataki ne kwamitin shari’a za su ɗauka? Kalmar nan “shari’a” ba ta nufin cewa dattawa ne za su yanke shawara ko ya dace hukumomi su hukunta wanda ya ci zarafin yara ba. Dattawa ba sa hana hukuma yin shari’a a kan ɗan’uwa a ikilisiya da ya taka dokar ƙasa. (Rom. 13:​2-4; Tit. 3:1) Maimakon haka, suna tsai da shawara ko ɗan’uwan da ya yi zunubi zai ci gaba da kasancewa a cikin ikilisiya.

18 Dattawa suna shari’a a kan batutuwan da suka shafi dangantakar mai laifi da Allah da kuma ’yan’uwa a ikilisiya. Suna amfani da Littafi Mai Tsarki don su san ko mai laifin ya tuba da gaske ko a’a. Idan bai tuba ba, za a yi masa yankan zumunci kuma a sanar wa ikilisiya. (1 Kor. 5:​11-13) Idan ya tuba, ba za a yi masa yankan zumunci ba. Amma, dattawa za su gaya masa cewa wataƙila ba zai iya samun gata a ikilisiya ba. Ƙari ga haka, dattawa za su iya gargaɗi iyaye masu ƙananan yara a ikilisiyar cewa su yi hattara sosai sa’ad da yaransu suke sha’ani da mutumin. Sa’ad da dattawa suke hakan, su mai da hankali don kada su faɗi sunayen yaran da mutumin ya ci zarafinsu.

YADDA ZA KU KĀRE YARANKU

Iyaye suna kāre yaransu daga masu ɓata ƙananan yara ta wajen wayar musu da kai game da jima’i. Iyaye suna yin amfani da bayanan da ƙungiyar Jehobah ta tanadar wajen yin hakan. (Ka duba sakin layi na 19-22)

19-22. Mene ne iyaye za su yi don su kāre yaransu? (Ka duba hoton da ke bangon gaba.)

19 Wane ne yake da hakkin kāre yara? Iyaye ne. * Yaranku “gādo ne daga wurin” Jehobah. (Zab. 127:3) Jehobah ya ba ku hakkin kāre su. Mene ne za ku iya yi don kada a ci zarafin yaranku?

20 Na farko, ku yi bincike don ku san game da cin zarafin yara. Ku san irin mutane da suke cin zarafin yara da kuma irin dabarun da suke amfani da shi. Ku yi hattara don ku san yanayin da zai iya sa a ci zarafin yaranku ko kuma mutane da za su iya yin hakan. (K. Mag. 22:3; 24:3) Ku tuna cewa a yawancin lokaci, mai cin zarafin yara mutumi ne da yaron ko yarinyar ta sani kuma ta yarda da shi.

21 Na biyu, ku riƙa tattaunawa da yaranku sosai. (M. Sha. 6:​6, 7) Hakan ya ƙunshi saurarar yaranku da kyau. (Yaƙ. 1:19) Ku tuna cewa ba ya kasancewa da sauƙi yaran da aka ci zarafinsu su gaya ma wani abin da ya faru. Suna iya jin tsoron cewa ba za a gaskata da su ba, ko kuma mutumin da ya ci zarafinsu ya gaya musu zai yi musu wani mugun abu. Idan kuna ganin cewa wani abu ya faru da yaranku, ku yi musu tambayoyi a hankali kuma ku saurare su sa’ad da suke gaya muku abin da ya faru.

22 Na uku, ku koyar da yaranku. Ku gaya musu abin da ya kamata su sani game da jima’i daidai da shekarunsu. Ku koya musu abin da za su faɗa ko kuma abin da za su yi idan wani yana so ya taɓa su a wurin da bai kamata ba. Ku yi amfani da abubuwan da ƙungiyar Allah ta wallafa don ku kāre yaranku.​—Ka duba akwatin nan “ Ku Koyar da Kanku da Yaranku.”

23. Ta yaya muke ɗaukan cin zarafin yara, kuma wace tambaya ce za a amsa a talifi na gaba?

23 Shaidun Jehobah sun ɗauki cin zarafin yara a matsayin zunubi mai tsanani da mugun laifi. Da yake ikilisiyoyi suna bin dokar Kristi, ba sa kāre masu cin zarafin yara. Amma, mene ne za mu yi don mu taimaka ma waɗanda aka ci zarafinsu? Za a ba da amsar wannan tambayar a talifi na gaba.

WAƘA TA 103 Jehobah Ya Yi Tanadin Makiyaya

^ sakin layi na 5 A wannan talifin, za mu tattauna yadda za a kāre yara don kada a ci zarafinsu. Za mu koyi yadda dattawa za su kāre ikilisiya da kuma yadda iyaye za su kāre yaransu.

^ sakin layi na 3 MA’ANAR WASU KALMOMI: Cin zarafin yara shi ne sa’ad da wani babba ya yi amfani da yara don ya gamsar da sha’awarsa na yin jima’i. Hakan ya ƙunshi yin jima’i kai tsaye, ko yin jima’i ta baki ko ta dubura, ko tattaɓa al’aura ko mama ko kuma ɗuwawu da dai sauransu. Ko da yake an fi cin zarafin yara mata, amma ana cin zarafin yara maza da yawa ma. Maza sun fi cin zarafin yara, amma wasu mata ma suna cin zarafin yara.

^ sakin layi na 5 MA’ANAR WASU KALMOMI: A wannan talifin da kuma wanda zai biyo bayansa, kalmar nan “wanda aka ci zarafinsa” yana nufin yaro ko yarinyar da aka yi lalata da ita. Mun yi amfani da wannan kalmar ne don nuna cewa an ci zarafin yaron ko yarinyar ne kuma yaran ba su da laifi.

^ sakin layi na 11 Idan mutum ya yi zunubi mai tsanani domin dangantakarsa da Jehobah ba ta da ƙarfi, hakan ba zai hana shi ba da lissafin ayyukansa ga Jehobah ba kuma Allah zai hukunta shi.​—Rom. 14:12.

^ sakin layi na 16 Ba za a bukaci yarinyar ta kasance a wurin sa’ad da dattawa suke tuhumar wanda ake zarginsa da laifi. Iyaye ko kuma wani amini suna iya gaya wa dattawa game da batun ba tare da daɗa sa yarinyar baƙin ciki ba.

^ sakin layi na 19 Abin da aka faɗa a nan game da iyaye ya shafi waɗanda aka ba su riƙon yara ko kuma wanda yake renon yaran da ba na sa ba ne.