HASUMIYAR TSARO—NA NAZARI Mayu 2020

Wannan fitowar tana dauke da talifofin nazari da za a yi daga ranar 6 ga Yuli–2 ga Agusta, 2020.

“Sarkin Arewa” a Kwanaki na Karshe

Talifin nazari na 19: 6-12 ga Yuli, 2020. Muna ganin tabbaci cewa annabcin Daniyel game da “sarkin arewa” da “sarkin kudu” yana cika. Ta yaya muka sani? Me ya sa muke bukatar mu fahimci wannan annabcin dalla-dalla?

Sarakuna da Ke Gāba da Juna a Kwanaki na Karshe

Annabcin “sarkin arewa” da “sarkin kudu” ya faru a lokaci daya da wasu annabce-annabce. Ta yaya wadannan annabce-annabce suka nuna cewa karshen wannan zamanin ya kusa sosai?

Wane ne “Sarkin Arewa” a Yau?

Talifin nazari na 20: 13-19 ga Yuli, 2020. Waye ne ‘Sarkin arewa’ a yau, kuma yaya za a kawo karshensa? Sanin amsar za ta iya karfafa bangaskiyarmu kuma ta shirya mu don matsalolin da za mu fuskanta a nan gaba.

Kana Nuna Godiya Don Alherin Allah Kuwa?

Talifin nazari na 21: 20-26 ga Yuli, 2020. Wannan talifin zai sa mu daraja Jehobah da kuma wasu kyaututtukan da ya ba mu. Zai kuma taimaka mana mu iya tattaunawa da mutanen da ke shakkar wanzuwar Allah.

Ka Rika Nuna Godiya Don Abubuwan da Ba Ka Gani

Talifin nazari na 22: 27 ga Yuli–2 ga Agusta, 2020. A talifi na farko, muna tattauna abubuwa masu daraja da yawa da muke gani da ido. A wannan talifin, za a mai da hankali a kan abubuwa masu daraja da ba za mu iya gani da ido ba. Kuma za mu tattauna yadda za mu nuna godiya ga Jehobah don tanadodinsa masu daraja.