Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 22

Ka Rika Nuna Godiya Don Abubuwan da Ba Ka Gani

Ka Rika Nuna Godiya Don Abubuwan da Ba Ka Gani

Ka riƙa mai da hankali ga “abubuwan da ba a gani. Gama abubuwan da ake gani suna saurin wucewa, amma abubuwan da ba a gani na har abada ne.”​—2 KOR. 4:18.

WAƘA TA 45 Abubuwan da Nake Tunani a Kai

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1. Mene ne Yesu ya ce game da tara dukiya a sama?

BA DUKAN abubuwan da ke da daraja ba ne muke gani ba. Akwai abubuwa mafi daraja da ba ma gani. A huɗubar da Yesu ya yi a kan dutse, ya ambata abubuwa masu daraja a sama da suka fi arziki. Sai ya daɗa cewa: “Inda dukiyarka take, a can zuciyarka take.” (Mat. 6:​19-21) Idan mun daraja abu, za mu yi ƙoƙari don mu same shi. Muna tara “dukiya a sama” ta wajen ƙulla dangantaka mai kyau da Allah. Yesu ya ce ba za a taɓa sace ko kuma hallaka wannan dukiyar ba.

2. (a) Kamar yadda yake a 2 Korintiyawa 4:​17, 18, mene ne Bulus ya ƙarfafa mu mu mai da wa hankali? (b) Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?

2 Manzo Bulus ya ƙarfafa mu mu mai da hankali ga “abubuwan da ba a gani.” (Karanta 2 Korintiyawa 4:​17, 18.) Waɗannan sun haɗa da abubuwan da za mu more a sabuwar duniya. A wannan talifin, za mu tattauna abubuwa huɗu da ba a iya gani da muke morewa a yanzu. Abubuwan nan su ne yin abota da Allah da yin addu’a da samun taimakon ruhun Allah da kuma yadda Jehobah da Yesu da kuma mala’iku suke taimaka mana a wa’azi. Ƙari ga haka, za mu koya yadda za mu riƙa nuna godiya don abubuwan nan da ba a gani.

YIN ABOTA DA JEHOBAH

3. Mene ne abu mafi daraja da ba a gani, me ya taimaka mana mu same shi?

3 Abu mafi daraja da ba a gani shi ne abotarmu da Jehobah. (Zab. 25:14) Ta yaya Allah yake abota da mutane ajizai kuma har ila yana da tsarki? Hakan ya yiwu ne domin mutuwar Yesu ta ɗauke “zunubin” mutane. (Yoh. 1:29) Kafin Yesu ya mutu, Jehobah ya san cewa zai kasance da aminci har mutuwa don ya ceci ’yan Adam. Hakan ya sa ya yiwu Allah ya iya ƙulla abota da ’yan Adam da suke raye kafin Kristi ya mutu.​—Rom. 3:25.

4. Ka ba da misalan maza masu aminci a dā da suka zama abokan Allah.

4 Ka yi la’akari da wasu maza da suka zama abokan Allah a zamanin dā. Ibrahim mutum ne mai bangaskiya sosai. Jehobah ya kira Ibrahim abokinsa bayan ya yi shekaru fiye da 1,000 da mutuwa. (Isha. 41:8) Saboda haka, mutuwa ma ba za ta iya hana mu zama abokai na kud da kud na Jehobah ba. Jehobah yana tunawa da Ibrahim. (Luk. 20:​37, 38) Wani misali kuma shi ne Ayuba. Sa’ad da mala’iku suka taru a sama, Jehobah ya nuna cewa ya amince da Ayuba. Jehobah ya kira Ayuba mutum “marar laifi . . . kuma mai gaskiya a zuci.” (Ayu. 1:​6-8) Yaya Jehobah ya ji game da Daniyel wanda ya bauta masa da aminci wajen shekara 80 a ƙasar da mutane ba sa bauta wa Jehobah? Sau uku mala’iku suka gaya masa cewa shi “mutum mai daraja ne sosai” a gaban Allah. (Dan. 9:23; 10:​11, 19) Muna da tabbaci cewa Jehobah yana ɗokin ranar da zai ta da abokansa daga mutuwa.​—Ayu. 14:15.

A waɗanne hanyoyi ne za mu nuna godiya don abubuwa masu daraja da ba a gani? (Ka duba sakin layi na 5) *

5. Mene ne muke bukatar mu yi don mu ƙulla dangantaka ta kud da kud da Jehobah?

5 A yau, miliyoyin mutane suna more dangantaka ta kud da kud da Jehobah. Mun san hakan domin maza da mata da kuma yara da yawa a duniya suna nuna su abokan Allah ne ta halayensu. Littafi Mai Tsarki ya ce Jehobah “yana amincewa da mai gaskiya a zuci.” (K. Mag. 3:32) Sun ƙulla wannan abota da Jehobah domin sun yi imani da hadayar da Yesu ya yi. Saboda haka, za mu iya zama abokan Jehobah, kuma mu yi alkawarin bauta masa da yin baftisma. Idan muka ɗauki waɗannan matakai masu muhimmanci, to, mun ƙulla abota da Jehobah kamar yadda miliyoyin mutane da suka yi alkawarin bauta masa suka yi.

6. Ta yaya za mu nuna godiya don abotarmu da Allah?

6 Ta yaya za mu nuna cewa muna daraja abotarmu da Allah? Kamar Ibrahim da Ayuba da suka kasance da aminci ga Allah fiye da shekara ɗari, wajibi ne mu kasance da aminci ko shekaru nawa ne muka yi muna bauta wa Jehobah. Kamar Daniyel, wajibi ne mu riƙa daraja abokantakarmu da Allah fiye da ranmu. (Dan. 6:​7, 10, 16, 22) Jehobah zai taimaka mana mu jimre duk jarrabawa da muke fuskanta domin mu ci gaba da zama abokansa.​—Filib. 4:13.

GATAR YIN ADDU’A

7. (a) Kamar yadda Karin Magana 15:8 ta nuna, yaya Jehobah yake ji game da addu’o’inmu? (b) Ta yaya Jehobah yake amsa addu’o’inmu?

7 Wani abu mai daraja kuma da ba a gani shi ne yin addu’a. Aminai suna gaya wa juna ra’ayinsu da kuma yadda suke ji. Shin haka ne abotarmu da Jehobah take? Ƙwarai kuwa! Jehobah yana mana magana ta wurin Kalmarsa, kuma ta hakan ne yake gaya mana ra’ayinsa. Muna magana da shi sa’ad da muke addu’a, a lokacin ne muke gaya masa ra’ayinmu da abin da ke zuciyarmu. Jehobah yana son jin addu’o’inmu. (Karanta Karin Magana 15:8.) Da yake Jehobah abokinmu ne, yana jin addu’o’inmu kuma yana amsa su. A wasu lokuta, yana amsawa da sauri. A wasu kuma za mu ci gaba da yin addu’a game da batun. Duk da haka, muna da tabbaci cewa zai amsa addu’ar a hanyar da ta dace da kuma lokacin da ya dace. Wataƙila Allah ba zai amsa yadda muke zato ba. Alal misali, a wasu lokuta ba ya cire jarrabawar, amma yana ba mu hikima da kuma ƙarfin “jimrewa.”​—1 Kor. 10:13.

(Ka duba sakin layi na 8) *

8. Ta yaya za mu riƙa nuna godiya don gatar yin addu’a?

8 Ta yaya za mu nuna godiya don wannan gata mai daraja na yin addu’a? Hanya ɗaya ita ce ta wajen bin shawarar da Jehobah ya ba da cewa mu riƙa “addu’a babu fasawa.” (1 Tas. 5:17) Jehobah ba ya tilasta mana mu yi addu’a. Maimakon haka, yana barin mu mu yi amfani da ’yancinmu kuma yana ƙarfafa mu mu “nace da addu’a.” (Rom. 12:​12, Littafi Mai Tsarki) Saboda haka, muna iya nuna godiya ta wurin yin addu’a a kai a kai kowace rana. Ya kamata mu riƙa gode wa Jehobah da kuma yaba masa a addu’o’inmu.​—Zab. 145:​2, 3.

9. Ta yaya wani ɗan’uwa yake ji game da yin addu’a, kuma yaya kake ji game da yin addu’a?

9 Idan mun daɗe muna bauta wa Jehobah kuma muka ga yadda ya amsa addu’o’inmu, hakan zai daɗa sa mu nuna godiya don gatar yin addu’a. Ka yi la’akari da wani ɗan’uwa mai suna Chris da ya yi shekara 47 yana hidimar majagaba. Ya ce: “Ina son tashiwa da sassafe don in yi addu’a ga Jehobah. Yin magana da Jehobah yayin da gari yake wayewa yana sa ni farin ciki sosai! Hakan yana sa in gode masa don duk abubuwan da ya ba ni, har da gatar yin addu’a. Sa’an nan daddare sa’ad da nake son in yi barci, ina yin addu’a kuma in yi barci hankali kwance.”

KYAUTAN RUHU MAI TSARKI

10. Me ya sa ya kamata mu riƙa daraja ruhun Allah?

10 Wani kyauta da ba a gani da ya kamata mu riƙa daraja shi ne ruhu mai tsarki. Yesu ya ƙarfafa mu mu riƙa yin addu’a don samun taimakon ruhu mai tsarki. (Luk. 11:​9, 13) Jehobah yana amfani da ruhu mai tsarki don ya ba mu “cikakken iko.” (2 Kor. 4:7; A. M. 1:8) Ruhun Allah zai iya taimaka mana mu jimre kowace jarrabawa.

(Ka duba sakin layi na 11) *

11. A wace hanya ce ruhu mai tsarki yake taimaka mana?

11 Ruhu mai tsarki yana taimaka mana mu yi ayyuka da aka ba mu a hidimar Jehobah. Ruhun Allah zai taimaka mana mu inganta baiwarmu da iyawarmu. Mun san cewa muna samun sakamako mai kyau a hidimarmu don taimakon ruhu mai tsarki.

12. Kamar yadda Zabura 139:​23, 24 suka nuna, mene ne za mu yi addu’a ruhu mai tsarki ya taimaka mana mu yi?

12 Wata hanya kuma da za mu nuna cewa muna daraja ruhun Allah ita ce ta yin addu’a ya taimaka mana mu gano duk wani mugun sha’awoyi ko tunani da ke zuciyarmu. (Karanta Zabura 139:​23, 24.) Idan muka yi hakan, Jehobah zai yi amfani da ruhunsa don ya taimaka mana mu gano duk wani mugun sha’awoyi da muke da shi. Idan muka ga cewa muna da irin wannan mugun sha’awoyi, ya kamata mu yi addu’a don ruhun Allah ya ba mu ƙarfin guje wa sha’awoyin. Idan muka yi hakan, Jehobah zai ga cewa ba ma son mu yi kome da zai sa ya daina taimaka mana da ruhunsa.​—Afis. 4:30.

13. Ta yaya za mu ƙara nuna godiya don ruhu mai tsarki?

13 Za mu fi nuna godiya don taimakon ruhu mai tsarki sa’ad da muka yi tunani a kan abin da yake yi a zamaninmu? Kafin Yesu ya je sama, ya gaya wa almajiransa cewa: “Za ku sami iko sa’ad da ruhu mai tsarki ya sauko muku, za ku zama shaiduna . . . har zuwa iyakar duniya.” (A. M. 1:8) Abin da yake faruwa a yau ke nan. Ruhu mai tsarki yana taimaka wa mutane fiye da miliyan takwas da dubu ɗari shida a dukan duniya su bauta wa Jehobah. Ƙari ga haka, a matsayinmu na bayin Allah, muna da haɗin kai a duniya domin ruhun Allah yana taimaka mana mu kasance da halaye masu kyau. Waɗannan halayen su ne ƙauna da farin ciki da salama da haƙuri da kirki da nagarta da aminci da tawali’u da kuma kamun kai. Waɗannan halayen su ne “halin da ruhun Allah yake haifar” da shi. (Gal. 5:​22, 23) Hakika, ruhu mai tsarki kyauta ne mai daraja sosai!

JEHOBAH DA YESU DA KUMA MALA’IKU SUNA TAIMAKA MANA A WA’AZI

14. Su waye ne suke taimaka mana sa’ad da muke wa’azi?

14 Muna da gatar yin ‘aiki tare’ da Jehobah da Yesu da kuma mala’iku. (2 Kor. 6:1) Muna yin hakan sa’ad da muke wa’azi. Bulus ya yi furucin nan game da kansa da kuma waɗanda suke wannan aikin: “Mu abokan aiki na Allah ne.” (1 Kor. 3:9) Mu abokan aiki da Yesu ne sa’ad da muka fita wa’azi. Ka tuna cewa bayan da Yesu ya umurci mabiyansa su sa mutane su ‘zama almajiransa,’ ya ce musu: “Ina tare da ku.” (Mat. 28:​19, 20) Mala’iku kuma fa? Muna godiya cewa mala’iku suna yi mana ja-goranci sa’ad da muke wa’azin “labari mai daɗi” ga mazaunan duniya.​—R. Yar. 14:6.

15. Ka ba da wani misali na Littafi Mai Tsarki da ya nuna yadda Jehobah yake taimaka mana a wa’azi.

15 Mene ne muke cim ma don wannan taimakon da ake ba mu? Yayin da muke wa’azi, wasu mutane suna saurarawa kuma su soma bauta wa Jehobah. (Mat. 13:​18, 23) Mene ne ke sa su soma yin hakan? Yesu ya bayyana cewa babu mutum da zai zama mabiyinsa sai “dai in Uba . . . ya jawo shi.” (Yoh. 6:44) Littafi Mai Tsarki ya ba da misalin hakan. Bulus ya yi wa wasu mata da ke kusa da birnin Filibi wa’azi. Ka yi la’akari da abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da ɗaya cikin su mai sun Lidiya. Ya ce: “Ubangiji ya buɗe zuciyarta, har ta sa hankali ta saurari abin da Bulus ya faɗa.” (A. M. 16:​13-15) Kamar Lidiya, mutane da yawa sun soma bauta wa Jehobah.

16. Wa ya kamata mu yaba wa idan mun samu sakamako mai kyau a wa’azi?

16 Wa ya kamata mu yaba wa idan mun samu sakamako mai kyau a wa’azi? Bulus ya amsa wannan tambayar a lokacin da ya rubuta wa ikilisiyar Korinti cewa: “Ni na shuka, Afollos ya yi ban ruwa, amma Allah ne ya sa shukar ta yi girma. Saboda haka da wanda ya shuka, da wanda ya yi ban ruwan ba a bakin kome suke ba, sai dai Allah kaɗai shi da ya sa shukar ta yi girma.” (1 Kor. 3:​6, 7) Kamar Bulus ya kamata mu yaba wa Jehobah don duk wani sakamako mai kyau da muka samu a wa’azi.

17. Ta yaya za mu nuna godiya don ‘yin aiki tare’ da Allah da Kristi da kuma mala’iku?

17 Ta yaya za mu nuna godiya don gatar ‘yin aiki tare’ da Allah da Kristi da kuma mala’iku? Za mu iya yin hakan ta wajen neman zarafin yi wa mutane wa’azi da ƙwazo. Da akwai hanyoyi da yawa na yin hakan, kamar yin wa’azi “a fili, da kuma gida-gida.” (A. M. 20:20) ’Yan’uwa da yawa suna jin daɗin yin wa’azi sa’ad da suke ayyukansu na yau da kullum. Idan suka haɗu da baƙo, suna gai da shi da fara’a kuma su yi iya ƙoƙarinsu don su soma tattaunawa da shi. Idan mutumin yana so ya tattauna da su, sai su yi masa wa’azi da dabara.

(Ka duba sakin layi na 18) *

18-19. (a) Ta yaya muke ban ruwa sa’ad da muka koya wa mutane gaskiya? (b) Ka ba da labarin da ya nuna yadda Jehobah ya taimaka ma wani ɗalibi.

18 Da yake “mu abokan aiki na Allah ne” ba shuka iri na gaskiya kaɗai za mu yi ba, amma za mu yi ban ruwa. Idan akwai wani da yake son saƙon, za mu yi iya ƙoƙarinmu mu ga cewa mun koma ziyara wajensa. Ko kuma mu gaya ma wani ya je ya soma nazarin Littafi Mai Tsarki da shi. Muna murna idan mun ga cewa Jehobah yana taimakon ɗalibin ya canja ra’ayinsa da tunaninsa.

19 Ka yi la’akari da misalin wani boka a Afirka ta Kudu mai suna Raphalalani. Ya so abin da ya koya a Littafi Mai Tsarki. Amma ya fuskanci ƙalubale sa’ad da ya karanta ayar da ta yi magana game da tattaunawa da kakaninsa da suka mutu. (M. Sha. 18:​10-12) A hankali, ya yarda Allah ya taimaka masa ya canja halayensa. Da shigewar lokaci, ya daina bokanci, duk da cewa da aikin ne yake ciyar da iyalinsa. Raphalalani wanda shekararsa 60 ne yanzu, ya ce: “Ina godiya ga Shaidun Jehobah don yadda suka taimaka mini a hanyoyi da yawa. Alal misali, sun nemo min aiki. Na fi gode wa Jehobah da ya taimaka min in yi canje-canje a rayuwata. Canje-canjen nan sun sa na yi baftisma kuma ina wa’azi.”

20. Mene ne ka ƙuduri niyyar yi?

20 A wannan talifin, mun tattauna abubuwa huɗu masu daraja da ba a gani. Mafi daraja a cikinsu shi ne gatar ƙulla abota da Jehobah. Hakan yana taimaka mana mu amfana daga sauran abubuwa masu daraja da ba ma gani. Abubuwan nan su ne yin addu’a da shaida taimakon ruhu mai tsarki da samun taimako daga Jehobah da Kristi da kuma mala’iku a hidimarmu. Bari mu ƙuduri niyyar nuna godiya don waɗannan abubuwa masu daraja da ba a gani. Kuma mu ci gaba da gode wa Jehobah don zama abokinmu na kud da kud.

WAƘA TA 145 Allah Ya Yi Mana Alkawarin Aljanna

^ sakin layi na 5 A talifin da ya gabata, mun tattauna abubuwa da yawa da Allah ya ba mu da ake gani. A wannan talifin, za mu mai da hankali ga abubuwan da ba a gani da yadda za mu iya nuna godiya dominsu. Hakan kuma zai sa mu ƙara nuna godiya ga Jehobah da ya tanada mana abubuwan nan.

^ sakin layi na 58 BAYANI A KAN HOTUNA: (1) Sa’ad da wata ’yar’uwa take kallon halittun Jehobah, ta yi bimbini a kan abotarta da Jehobah.

^ sakin layi na 60 BAYANI A KAN HOTUNA: (2) ’Yar’uwar kuma tana addu’a don Jehobah ya taimaka mata ta yi wa’azi.

^ sakin layi na 62 BAYANI A KAN HOTUNA: (3) Ruhu mai tsarki ya taimaka wa ’yar’uwa ta kasance da ƙarfin zuciyar yin wa’azi.

^ sakin layi na 64 BAYANI A KAN HOTUNA: (4) ’Yar’uwar tana nazari da wata da ta yi ma wa’azi sa’ad da take ayyukanta na yau da kullum. Mala’iku suna taimaka wa ’yar’uwar ta yi wa’azi.