Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Sarakuna da Ke Gāba da Juna a Kwanaki na Karshe

Sarakuna da Ke Gāba da Juna a Kwanaki na Karshe

Wasu cikin annabci da aka ambata a taswirar nan sun faru a lokaci ɗaya. Dukansu sun nuna cewa muna rayuwa a “kwanakin ƙarshe.”​—Dan. 12:4.

  • Nassosi R. Yar. 11:7; 12:​13, 17; 13:​1-8, 12

    Annabci “Dabbar” ta yi dubban shekaru tana mulki a kan mutane. A kwanaki na ƙarshe, an ji wa kai na bakwai na dabbar rauni. Daga baya, kan ya warke kuma “dukan duniya” ta soma bin dabbar. Shaiɗan ya yi amfani da ita don ya yaƙi “sauran zuriyar macen.”

    Yadda ya cika Bayan ambaliyar ruwa na zamanin Nuhu, gwamnatocin da ke gāba da Jehobah sun soma mulki. Bayan ƙarnuka da yawa, wato a lokacin Yaƙin Duniya na 1, ikon Birtaniya ya ragu sosai. Ta sake samun ƙarfi sa’ad da ta haɗa kai da Amirka. A kwanaki na ƙarshe, Shaiɗan yana amfani da dukan gwamnatoci don ya tsananta wa bayin Allah.

  • Nassosi Dan. 11:​25-45

    Annabci A kwanaki na ƙarshe, sarkin arewa da sarkin kudu za su yi jayayya da juna.

    Yadda ya cika Jamus ta yaƙi Amirka da Birtaniya. A shekara ta 1945, Tarayyar Soviet da magoya bayanta sun zama sarkin arewa. A 1991, Tarayyar Soviet ta wargaje, kuma daga baya, Rasha da magoya bayanta sun zama sarkin arewa.

  • Nassosi Isha. 61:1; Mal. 3:1; Luk. 4:18

    Annabci Jehobah ya tura mai idar da ‘saƙonsa’ don ya ‘shirya hanya’ kafin a kafa Mulkin Almasihu. Wannan mai idar da saƙon ya soma “shelar labari mai daɗi ga talakawa.”

    Yadda ya cika Daga shekara ta 1870, Ɗan’uwa C. T. Russell da abokansa sun yi aiki tuƙuru don su koya wa mutane gaskiya. A shekara ta 1881, sun soma nanata cewa bayin Allah suna bukatar yin wa’azi. Sun wallafa talifofin nan “Wanted 1,000 Preachers” (Ana Bukatar Masu Shela 1,000) da kuma “Anointed to Preach” (An Naɗa Masu Wa’azi.)

  • Nassosi Mat. 13:​24-30, 36-43

    Annabci Wani magabci ya shuka ciyawa a cikin gonar alkama kuma aka bar ta ta girma ta sha kan alkamar har lokacin girbi. A lokacin, za a ware ciyayin daga alkamar.

    Yadda ya cika Daga shekara ta 1870, ana iya ganin bambancin da ke tsakanin Kiristoci na ƙarya da Kiristoci na gaskiya. A kwanaki na ƙarshe, an tattare Kiristoci na gaskiya a cikin ikilisiyoyi kuma aka ware su daga Kiristoci na ƙarya.

  • Nassosi Dan. 2:​31-33, 41-43

    Annabci Wani gunki da aka ƙera da ƙarafuna dabam-dabam yana da ƙafafun baƙin ƙarfe gauraye da laka.

    Yadda ya cika Lakar tana wakiltar mutanen da Birtaniya da Amirka suke mulki a kansu da suka yi tawaye. Waɗannan mutanen suna hana waɗannan gwamnatoci yin amfani da ikonsu sosai..

  • Nassosi Mat. 13:30; 24:​14, 45; 28:​19, 20

    Annabci An tattara alkamar cikin ‘rumbu’ kuma an naɗa “bawan nan mai aminci, mai hikima” don ya kula da bayin maigidansa. An soma wa’azin “mulkin” ga “dukan al’umma.”

    Yadda ya cika A shekara ta 1919, an naɗa bawan nan mai aminci ya riƙa kula da mutanen Allah. Daga wannan lokacin ne Ɗaliban Littafi Mai Tsarki suka soma wa’azi sosai. A yau, Shaidun Jehobah suna wa’azi a ƙasashe fiye da 200 kuma suna wallafa littattafai a yaruka fiye da 1,000.

  • Nassosi Dan. 12:11; R. Yar. 13:​11, 14, 15

    Annabci Dabba mai ƙahoni biyu ta ce mutane su gina “siffa domin a girmama wannan dabbar” kuma “ta ba da numfashin rai ga wannan siffar.”

    Yadda ya cika Birtaniya da Amirka sun yi ja-goranci wajen kafa Tsohuwar Majalisar Ɗinkin Duniya. Wasu al’ummai suna goyon bayan wannan ƙungiyar. Daga baya, sarkin arewa ya goyi bayan wannan Majalisar daga shekara ta 1926 zuwa 1933. Kamar Tsohuwar Majalisar Ɗinkin Duniya, mutane suna ganin cewa Majalisar Ɗinkin Duniya za ta sa a yi zaman lafiya. Amma Mulkin Allah ne kaɗai zai yi hakan.

  • Nassosi Dan. 8:​23, 24

    Annabci Mugun sarki mai taurin fuska “zai kawo halakarwa mai ban tsoro.”

    Yadda ya cika Birtaniya da Amirka sun kashe mutane da yawa kuma sun yi ɓarna sosai. Alal misali, lokacin Yaƙin Duniya na 2, Amirka ta hallaka mutane da yawa sa’ad da ta jefa wa maƙiyinta bam-bamai guda biyu.

  • Nassosi Dan. 11:31; R. Yar. 17:​3, 7-11

    Annabci “Wata jar dabba” mai ƙahoni goma ta fito daga rami marar matuƙa kuma ita ce sarki na takwas. Littafin Daniyel ya kira wannan sarkin “abin ƙazanta mai kawo halakarwa.”

    Yadda ya cika Tsohuwar Majalisar Ɗinkin Duniya ta wargaje a lokacin Yaƙin Duniya na 2. Bayan yaƙin, an kafa Majalisar Ɗinkin Duniya. Kamar Tsohuwar Majalisar Ɗinkin Duniya, mutane suna ganin cewa Majalisar Ɗinkin Duniya za ta sa a sami zaman lafiya a duniya. Amma Majalisar Ɗinkin Duniya za ta kai wa addinai hari.

  • Nassosi 1 Tas. 5:3; R. Yar. 17:16

    Annabci Al’ummai sun yi shelar “zaman lafiya da salama,” kuma “ƙahoni goma” da “dabbar” sun kai wa ‘karuwar’ hari kuma sun hallaka ta. Bayan haka, za a hallaka al’umman.

    Yadda ya cika Al’ummai za su yi da’awar cewa sun kawo zaman lafiya da salama a duniya. Sa’an nan al’umman da ke goyon bayan Majalisar Ɗinkin Duniya za su hallaka ƙungiyoyin addinan ƙarya. Wannan zai zama somawar ƙunci mai girma. Za a daina ƙunci mai girma sa’ad da Yesu ya hallaka mugun zamanin Shaiɗan a yaƙin Armageddon.

  • Nassosi Ezek. 38:​11, 14-17; Mat. 24:31

    Annabci Gog zai kai wa mutanen Allah hari. Mala’iku za su tattara “waɗanda aka zaɓa.”

    Yadda ya cika Sarkin arewa da sauran sarakunan duniya za su kai wa mutanen Allah hari. Bayan sun soma kai wannan harin, za a tattara sauran shafaffu da suka rage zuwa sama.

  • Nassosi Ezek. 38:​18-23; Dan. 2:​34, 35, 44, 45; R. Yar. 6:2; 16:​14, 16; 17:14; 19:20

    Annabci Mahayin “farin doki” ya kammala “cin nasara” ta wajen hallaka Gog da sojojinsa. An jefa “dabbar” cikin “tafkin wuta mai ƙuna” kuma aka hallaka gunkin.

    Yadda ya cika Yesu wanda shi ne sarkin Mulkin Allah zai ceci bayin Allah. Yesu da mutane 144,000 da kuma mala’iku za su hallaka al’umman da suka kai wa mutanen Allah hari. Kuma hakan zai kawo ƙarshen mulkin Shaiɗan.