Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 19

“Sarkin Arewa” a Kwanaki na Karshe

“Sarkin Arewa” a Kwanaki na Karshe

“A kwanakin ƙarshe, sarkin kudu zai kai wa sarkin arewa yaƙi.”​—DAN. 11:40.

WAƘA TA 150 Mu Bi Allah Don Mu Sami Ceto

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1. Mene ne annabcin da ke Littafi Mai Tsarki ya taimaka mana mu sani?

MENE NE zai faru da mutanen Jehobah nan ba da daɗewa ba? Za mu iya sanin amsar domin Littafi Mai Tsarki ya nuna abubuwa masu muhimmanci da za su shafi dukanmu nan ba da daɗewa ba. Akwai annabcin da ya nuna abubuwan da gwamnatoci masu iko za su yi a duniya. Wannan annabci da aka rubuta a littafin Daniyel sura 11, ya yi magana game da sarkuna biyu da suke yaƙi da juna, kuma ana kiran su sarkin arewa da sarkin kudu. Yawancin annabcin nan sun cika kuma hakan ya sa mu kasance da tabbaci cewa sauran annabcin za su cika.

2. Kamar yadda Farawa 3:15 da Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 11:7 da kuma 12:17 suka nuna, me muke bukatar mu tuna sa’ad da muke nazarin annabcin Daniyel?

2 Don mu fahimci annabcin da ke littafin Daniyel sura 11, muna bukatar mu tuna cewa annabcin ya yi magana ne game da sarakuna da kuma gwamnatoci waɗanda sarautarsu ta shafi mutanen Allah. Mutanen Allah ba su da yawa a duniya, amma me ya sa gwamnatoci suke gāba da su? Domin ainihi burin Shaiɗan da mutanensa shi ne su hallaka abokan Jehobah da Yesu. (Karanta Farawa 3:15 da kuma Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 11:7; 12:17.) Ƙari ga haka, wajibi ne annabcin da ke littafin Daniyel ya jitu da sauran annabcin da ke Kalmar Allah. Babu shakka, idan muna so mu fahimci annabcin Daniyel, wajibi ne mu fahimci sauran annabci da ke Littafi Mai Tsarki.

3. Me za mu tattauna a wannan talifin da kuma na gaba?

3 A yanzu, za mu tattauna littafin Daniyel 11:​25-39. Za mu san ko su waye ne sarkin arewa da kuma sarkin kudu daga shekara ta 1870 zuwa 1991. Kuma za mu ga dalilin da ya sa ya dace mu yi gyara ga yadda muka fahimci wani sashen annabcin. A talifi na gaba, za mu tattauna littafin Daniyel 11:40–12:​1, kuma za mu bayyana abin da sashen annabcin nan ya nuna game da shekara ta 1991 zuwa lokacin yaƙin Armageddon. Yayin da kake nazarin waɗannan talifofi biyu, zai dace ka duba taswirar nan “Sarakuna da Ke Gāba da Juna a Kwanaki na Ƙarshe.” Da farko, muna bukatar mu san ko su waye ne sarakuna biyu da aka ambata a annabcin.

SU WAYE NE SARKIN AREWA DA SARKIN KUDU?

4. Waɗanne abubuwa uku ne za su taimaka mana mu san ko su waye ne sarkin arewa da kuma sarkin kudu?

4 Sarakunan da ke arewaci da kuma kudancin Isra’ila ne aka fara kira da wannan laƙabi “sarkin arewa” da kuma “sarkin kudu.” Me ya sa muka ce hakan? Ka yi la’akari da abin da mala’ikan da ya idar da wannan saƙon ya gaya wa Daniyel. Ya ce: ‘Na zo domin in sa ka gane abin da zai faru da mutanenka nan gaba a ƙarshen kwanaki.’ (Dan. 10:14) Jehobah ya daina amfani da al’ummar Isra’ila a lokacin Fentakos na shekara ta 33. Tun daga lokacin, Jehobah ya nuna cewa mabiyan Yesu masu aminci ne mutanensa. Saboda haka, yawancin annabcin da ke littafin Daniyel sura 11, ya shafi mabiyan Yesu ne ba al’ummar Isra’ila ba. (A. M. 2:​1-4; Rom. 9:​6-8; Gal. 6:​15, 16) Kuma sarakuna dabam-dabam sun zama sarkin arewa da kuma sarkin kudu. Amma akwai alaƙa tsakanin waɗannan sarakuna. Na farko, sarakunan sun sarauci ƙasashen da mutanen Allah suke zama ko kuma sun tsananta musu. Na biyu, yadda suka bi da mutanen Allah ya nuna cewa sun tsani Jehobah. Na uku, sarakunan suna jayayya da juna a kan wanda ya fi iko.

5. Shin akwai sarkin arewa da sarkin kudu a tsakanin shekara ta 100 da kuma 1870? Ka bayyana.

5 A ƙarni na biyu bayan haihuwar Yesu, Kiristoci na ƙarya sun soma gurɓata bauta ta gaskiya. Sun koyar da ƙarairayi kuma sun hana mutane sanin gaskiyar da ke Kalmar Allah. Tun daga wannan lokacin har zuwa wajen ƙarshen ƙarni na 19, Allah ba shi da ƙungiya a duniya. Kiristoci na ƙarya sun yaɗu kamar ciyayi kuma hakan ya sa ya yi wuya mutane su gane Kiristoci na gaskiya. (Mat. 13:​36-43) Me ya sa sanin wannan yake da muhimmanci? Domin hakan ya nuna cewa sarakuna da suka yi mulki a tsakanin shekara ta 100 zuwa shekara ta 1870 ba su ne sarkin arewa da sarkin kudu ba. A lokacin, Allah ba shi da ƙungiya a duniya waɗanda sarakunan nan za su kai wa hari. * Amma jim kaɗan bayan shekara ta 1870, sarkin arewa da sarkin kudu sun sake kunno kai. Ta yaya muka san da hakan?

6. Yaushe ne mutanen Jehobah suka sake soma ayyukansu? Ka bayyana.

6 Daga shekara ta 1870 ne mutanen Jehobah suka sake soma ayyukansu. A wannan shekarar ce Ɗan’uwa Charles T. Russell da abokansa suka kafa rukunin nazarin Littafi Mai Tsarki. Ɗan’uwa Russell da abokansa ne masu idar da saƙo da aka annabta cewa za su ‘shirya hanya’ kafin a kafa Mulkin Allah. (Mal. 3:1) An sake kafa ƙungiyar da ke bauta wa Jehobah a hanyar da ta dace! Shin da akwai gwamnatoci a lokacin waɗanda mulkinsu zai shafi mutanen Allah? Ka yi la’akari da wannan.

WANE NE SARKIN KUDU?

7. Wane ne sarkin kudu har lokacin Yaƙin Duniya na Ɗaya?

7 A shekara ta 1870, Birtaniya ce take mulki a kan ƙasashe da yawa a duniya, kuma tana da sojoji da suka fi na kowace ƙasa ƙarfi. A annabcin Daniyel, an ambata ɗan ƙaramin ƙaho da ya tumɓuke ƙahoni uku. Wannan ɗan ƙaho yana wakiltar daular Birtaniya, kuma ƙahoni ukun su ne ƙasar Faransa da Sifen da kuma Holan. (Dan. 7:​7, 8) Birtaniya ita ce sarkin kudu har lokacin Yaƙin Duniya na Ɗaya. A wannan lokaci ne Amirka ta zama ƙasa mafi arziki kuma ta soma haɗa kai da Birtaniya.

8. Wane ne sarkin kudu a wannan kwanaki na ƙarshe?

8 A lokacin Yaƙin Duniya na Ɗaya, Amirka da Birtaniya sun yaƙi wasu ƙasashe tare kuma hakan ya sa suka zama ƙasashe masu iko sosai. A wannan lokacin ne Birtaniya da Amirka suka ƙulla kawance kuma suka zama al’umma mafi iko a duniya. Kamar yadda Daniyel ya faɗa, wannan sarkin ya tattara “babbar ƙungiyar sojoji mai ƙarfi sosai.” (Dan. 11:25) A wannan kwanaki na ƙarshe, Amirka da Birtaniya ne sarkin kudu. * Amma wane ne sarkin arewa?

SARKIN AREWA YA SAKE KUNNO KAI

9. A wane lokaci ne sarkin arewa ya sake kunno kai, kuma ta yaya Daniyel 11:25 ya cika?

9 A shekarar da Russell da abokansa suka kafa rukunin nazarin Littafi Mai Tsarki, wato a shekara ta 1871 ne sarkin arewa ya sake kunno kai. A wannan shekarar ne Otto von Bismarck ya kafa ƙasar Jamus. Sarkin jihar Prussia mai suna Wilhelm na Ɗaya ne ya zama sarkin Jamus na farko kuma ya zaɓi Bismarck ya zama kansala. * Da shigewar lokaci, Jamus ta mallaki wasu ƙasashe da yawa a Afirka da Tekun Fasifik, kuma ta soma jayayya da Birtaniya. (Karanta Daniyel 11:25.) Jamus ta sami sojoji masu ƙarfi sosai da suka yi kusan na Birtaniya. Kuma ta yi amfani da sojojin don ta yaƙi abokan gābanta a lokacin yaƙin duniya na ɗaya.

10. Ta yaya Daniyel 11:25b, 26 ya cika?

10 Daniyel ya annabta abin da zai faru da mulkin Jamus da kuma sojojinta. Ya annabta cewa sarkin arewa “ba zai iya tsayawa ba.” Me ya sa? Domin ‘za a yi masa ƙulle-ƙulle. Waɗanda suke ci da sha tare da sarkin, su ne za su nemi su halakar da shi.’ (Dan. 11:25b, 26a) A zamanin Daniyel, waɗanda suke cin abincin sarki sun ƙunshi masu yi wa “sarki hidima.” (Dan. 1:5) Su waye ne wannan annabcin yake magana a kai? Annabcin yana magana ne game da manya-manyan ma’aikatan gwamnatin Jamus, wato su janarori da sojoji da suke aiki tare da sarkin. Abin da waɗannan mutanen suka yi ya sa aka yi wa sarkin juyin mulki kuma aka kafa sabuwar gwamnati a Jamus. * Ban da haka a annabcin, an bayyana sakamakon yaƙin da za a yi da sarkin kudu. Kuma an yi bayanin nan game da sarkin arewa cewa: “Za a halakar da ƙungiyar sojojinsa kamar yadda ambaliyar ruwa take yi, kuma sojojin da yawa za su mutu.” (Dan. 11:26b) Kamar yadda aka annabta, sojojin Jamus da yawa sun “mutu” a yaƙin duniya na ɗaya. A yaƙin ne aka fi kashe mutane a wannan lokacin.

11. Mene ne sarkin arewa da sarkin kudu suka yi?

11 Sa’ad da ake bayyana abin da zai faru kafin Yaƙin Duniya na Ɗaya, Daniyel 11:​27, 28 sun ce sarkin arewa da sarkin kudu “za su zauna a tebur guda suna ta yi wa juna ƙarya.” Ayoyin sun kuma ce sarkin arewa zai tattara “dukiya mai ɗumbun yawa.” Kuma abin da ya faru ke nan. Jamus da Birtaniya sun gaya wa juna cewa suna son zaman lafiya, amma sa’ad da suka soma yaƙan juna a shekara ta 1914, hakan ya nuna cewa ƙarya suka tabka wa juna. Shekaru da yawa kafin shekara ta 1914, Jamus ta zama ƙasa ta biyu mai arziki sosai a duniya. Annabcin da ke Daniyel 11:29 da kuma sashen farko na aya ta 30 ya cika sa’ad da Jamus ta yaƙi sarkin kudu kuma aka ci nasara a kan Jamus.

SARAKUNAN SUN YAƘI MUTANEN ALLAH

12. Mene ne sarkin arewa da sarkin kudu suka yi a lokacin Yaƙin Duniya na Ɗaya?

12 Tun daga shekara ta 1914, sarakunan sun ci gaba da yaƙan juna da kuma mutanen Allah. Alal misali, a Yaƙin Duniya na Ɗaya, gwamnatin Jamus da kuma Birtaniya sun tsananta wa bayin Allah domin sun ƙi saka hannu a yaƙi. Ban da haka, gwamnatin Amirka ta jefa ’yan’uwa da ke ja-goranci a ƙungiyar Jehobah cikin kurkuku. Wannan tsanantawar ta cika annabcin da ke Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 11:​7-10.

13. Mene ne sarkin arewa ya yi daga shekara ta 1933 da kuma musamman a lokacin yaƙin duniya na biyu?

13 Daga shekara ta 1933 da kuma musamman a lokacin yaƙin duniya na biyu, sarkin arewa ya kai wa mutanen Allah hari mai tsanani. Sa’ad da jam’iyyar Nazi ta soma mulki a Jamus, Hitler da mabiyansa sun saka wa aikinmu taƙunƙumi. Sarkin arewa ya kashe ɗarurruwan Shaidun Jehobah kuma ya saka dubbai a kurkuku. Daniyel ya annabta waɗannan abubuwan. Sarkin arewa ya ɓata “Wuri Mai Tsarki” kuma ya “hana yin hadayu na yau da kullum” sa’ad da ya hana bayin Jehobah yin wa’azi. (Dan. 11:30b, 31a) Shugaban ƙasar Jamus mai suna Hitler ya rantse cewa zai hallaka dukan bayin Jehobah a Jamus.

SABON SARKIN AREWA YA TASO

14. Waye ne ya zama sarkin arewa bayan yaƙin duniya na biyu? Ka bayyana.

14 Bayan yaƙin duniya na biyu, Tarayyar Soviet ta zama sarkin arewa kuma ta soma mulki a kan ƙasashen da ta ƙwace daga hannun ƙasar Jamus. Kamar gwamnatin Nazi da ta taƙura wa mutane, gwamnatocin Tarayyar Soviet sun tsananta wa mutanen da suka saka ibada ga Jehobah farko a rayuwarsu.

15. Mene ne sarkin arewa ya yi bayan da aka daina Yaƙin Duniya na Biyu?

15 Jim kaɗan bayan Yaƙin Duniya na Biyu, sabon sarkin arewa, wato Tarayyar Soviet da magoya bayanta sun kai wa mutanen Allah hari. Kamar yadda annabcin da ke Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 12:​15-17 ya nuna, wannan sarkin ya saka wa aikinmu taƙunƙumi, kuma ya jefa dubban Shaidun Jehobah cikin kurkuku a Siberiya, inda ake mugun sanyi. Hakika a waɗannan kwanaki na ƙarshe, sarkin arewa ya tsananta wa bayin Allah sosai domin yana so su daina bauta wa Jehobah. *

16. Ta yaya Tarayyar Soviet ta cika abin da ke Daniyel 11:​37-39?

16 Karanta Daniyel 11:​37-39. Don a cika wannan annabcin, sarkin arewa ya nuna bai damu da “gumakan kakanninsa ba.” Ta yaya? Tarayyar Soviet tana so ta kawar da addinai, saboda haka, ta yi ƙoƙarin ƙwace ikonsu. Don ta cim ma hakan, tun daga shekara ta 1918, gwamnatin Tarayyar Soviet ta ba da umurni da ya sa aka soma koyarwa a makarantu cewa Allah ba ya wanzuwa. Ta yaya wannan sarkin arewa ya “girmama allahn wurare masu katanga”? Tarayyar Soviet ta kashe kuɗaɗe sosai don ta horar da sojojinta da kuma gina dubban makaman nukiliya domin ta sami iko sosai. A ƙarshe, sarakunan nan biyu suna da makamai masu ɗimbin yawa da za su iya amfani da su wajen kashe biliyoyin mutane!

SARAKUNAN SUN YI AIKI TARE

17. Mene ne “abin ƙazanta mai kawo halakarwa”?

17 Sarkin arewa da sarkin kudu sun yi aiki tare don “su kafa abin ƙazanta mai kawo halakarwa.” (Dan. 11:31) Wannan “abin ƙazanta” shi ne Majalisar Ɗinkin Duniya.

18. Me ya sa aka kira Majalisar Ɗinkin Duniya “abin ƙazanta”?

18 An kira Majalisar Ɗinkin Duniya “abin ƙazanta” domin tana da’awa cewa za ta kawo zaman lafiya a duniya, amma Mulkin Allah ne kaɗai zai iya cim ma hakan. Kuma a annabcin, an ce abin ƙazantar yana “kawo halakarwa” domin Majalisar Ɗinkin Duniya ce za ta hallaka addinan ƙarya.​—Ka duba taswirar nan “Sarakuna da Ke Gāba da Juna a Kwanaki na Ƙarshe.”

ME YA SA MUKE BUKATAR MU SAN WANNAN BATUN?

19-20. (a) Me ya sa muke bukatar mu san wannan labarin? (b) Wace tambaya ce za a amsa a talifi na gaba?

19 Muna bukatar mu san wannan labarin domin daga shekara ta 1870 zuwa 1991, annabcin da Daniyel ya yi game da sarkin arewa da sarkin kudu ya cika. Hakan ya tabbatar mana da cewa sauran annabcin da ke Littafi Mai Tsarki za su cika.

20 A shekara ta 1991, Tarayyar Soviet ta rugurguje. Saboda haka, wane ne sarkin arewa a yau? Za a amsa wannan tambayar a talifi na gaba.

WAƘA TA 128 Mu Jimre Har Ƙarshe

^ sakin layi na 5 Akwai abubuwa da yawa a yau da suka nuna cewa annabcin Daniyel game da “sarkin arewa” da kuma “sarkin kudu” yana cika. Me ya tabbatar mana da hakan? Kuma me ya sa muke bukatar mu fahimci wannan annabcin sosai?

^ sakin layi na 5 Domin dalilin da aka ba da a nan, ba zai dace ba a ce Sarkin Roma mai suna Aurelian ne “sarkin arewa” (270-275 B.H.Y.) ko kuma a ce Sarauniya Zenobia (267-272 B.H.Y.) ce “sarkin kudu.” Wannan ƙarin hasken ya sauya abin da aka wallafa a littafin nan Pay Attention to Daniel’s Prophecy!, babi na 13 da 14.

^ sakin layi na 9 A shekara ta 1890, Kaiser Wilhelm na Biyu ya yi wa Bismarck juyin mulki.

^ sakin layi na 10 Sun yi abubuwa da yawa da suka sa ya kasance da sauƙi a yi nasara a kan sarkin. Alal misali, sun daina taimaka wa sarkin, sun fallasa asiri game da yaƙin, kuma suka tilasta masa ya yi murabus.

^ sakin layi na 15 Kamar yadda aka annabta a Daniyel 11:​34, an rage tsananta wa Kiristocin da suke zama a ƙasashen da sarkin arewa yake mulki. Alal misali, hakan ya faru a shekara ta 1991 sa’ad da Tarayyar Soviet ta rugurguje.