Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Tawali’u​—Yaya Yake Amfanar Mu?

Tawali’u​—Yaya Yake Amfanar Mu?

Wata mai suna Sara * ta ce: “Ni mai jin kunya ce sosai, kuma ba ni da ƙarfin zuciya. Saboda haka, ba na sake jiki sa’ad da nake tare da mutane da suke ji da kansu da kuma masu saurin fushi. Amma nakan saki ji da mutum mai tawali’u da sauƙin kai. Zan iya gaya wa mutumin abin da ke zuciyata da kuma matsalolina. Abokaina na kud da kud masu tawali’u da sauƙin kai ne.”

Abin da Sara ta ce ya nuna cewa idan muna da tawali’u, mutane za su kusace mu. Ban da haka, Jehobah yana ƙaunar masu tawali’u. Kalmarsa ta ce: Ku riƙa “nuna tawali’u.” (Kol. 3:12) Mene ne tawali’u? Ta yaya Yesu ya nuna tawali’u? Kuma ta yaya zama masu tawali’u zai sa mu farin ciki?

MENE NE TAWALI’U?

Tawali’u hali ne da za ka kasance da shi idan kai mai son zaman lafiya ne. Mai tawali’u yakan bi da mutane a hankali kuma yana kame kansa sa’ad da aka ɓata masa rai.

Tawali’u hali ne da ke nuna cewa mutum yana da ƙarfin hali. A Girkanci, ana yin amfani da kalmar nan “tawali’u” don kwatanta dokin da aka sa ya riƙa yin biyayya. Har ila, dokin yana da ƙarfi, amma an horar da shi ya riƙa kame kansa. Hakazalika, idan muka nuna tawali’u, za mu kame kanmu kuma mu riƙa zaman lafiya da mutane.

Muna iya tunani cewa ‘ni ba mai tawali’u ba ne.’ A yau mutane da yawa suna saurin fushi, kuma ba su da haƙuri. Hakan yana iya sa ya yi mana wuya mu zama masu tawali’u. (Rom. 7:19) Saboda haka, muna bukatar mu ƙoƙarta sosai don mu zama masu tawali’u. Amma ruhun Jehobah zai taimaka mana mu ci gaba da ƙoƙartawa. (Gal. 5:​22, 23) Me ya sa ya kamata mu yi ƙoƙari mu zama masu tawali’u?

Tawali’u hali ne da ke sa mutane su kusace mu. Kamar Sara, muna so mu zama masu tawali’u. Yesu ne ya fi kafa misali mai kyau a nuna tawali’u da kuma alheri. (2 Kor. 10:1) Hakan ya sa yara da ba su san shi ba, sun so su zama abokansa.​—Mar. 10:​13-16.

Idan muna da tawali’u, hakan zai taimaka wa mu da sauran mutane. Tawali’u zai hana mu saurin fushi. (K. Mag. 16:32) Zuciyarmu ba za ta riƙa damun mu ba domin ba za mu ɓata wa mutane rai ba, musamman abokanmu. Ƙari ga haka, mutane za su amfana domin tawali’u zai sa mu riƙa kame kanmu kuma mu guji halaye da kuma abubuwa da za su ɓata musu rai.

MISALI MAFI KYAU NA NUNA TAWALI’U

Yesu ya shagala da aiki sosai kuma ba shi da lokaci, amma duk da haka, ya kasance da tawali’u. Mutane da yawa a zamaninsa suna shan wahala, kuma suna bukatar samun wartsakewa. Sun samu ƙarfafa sosai sa’ad da Yesu ya ce: “Ku zo gare ni, . . . domin ni mai tawali’u ne, mai sauƙin kai.”​—Mat. 11:​28, 29.

Ta yaya za mu koyi nuna tawali’u kamar Yesu? Mu riƙa nazarin Kalmar Allah don mu koyi yadda Yesu ya yi sha’ani da mutane da kuma abin da ya yi a mawuyacin yanayi. Hakan zai taimaka mana mu nuna tawali’u kamar Yesu sa’ad da muka fuskanci mawuyacin yanayi. (1 Bit. 2:21) Ka yi la’akari da abubuwa uku da suka taimaka wa Yesu ya nuna tawali’u.

Yesu mai sauƙin kai ne sosai. Ya ce shi “mai tawali’u ne” da kuma “mai sauƙin kai.” (Mat. 11:29) Littafi Mai Tsarki ya ambata waɗannan halaye biyu tare domin tawali’u yana da alaƙa da sauƙin kai.​—Afis. 4:​1-3.

Sauƙin kai yana taimaka mana mu guji yin fushi sa’ad da mutane suka ɓata sunanmu. Mene ne Yesu ya yi sa’ad da mutane suka ce shi “mai yawan ci da sha” ne? Ya nuna cewa hakan ba gaskiya ba ne, kuma domin shi mai tawali’u ne sai ya ce “ana gane hikimar Allah a ayyukanta.”​—Mat. 11:19.

Idan wani ya faɗi abin da bai kamata ba game da launin fatarka da jinsinka ko kuma yadda aka rena ka. Kana iya nuna tawali’u ta wajen ƙin yin baƙar magana. Wani dattijo mai suna Peter a ƙasar Afirka ta Kudu ya ce: “Idan wani ya faɗi abin da ya ɓata min rai, nakan tambayi kaina, ‘Da a ce Yesu ne, me zai yi a wannan yanayin?’ ” Ya ƙara da cewa: “Na koyi kada in bar abin da mutane suka faɗa ya riƙa damuna.”

Yesu ya san cewa ’yan Adam ajizai ne. Almajiran Yesu suna son yin abin da ya dace, amma a wasu lokuta ba sa yin hakan domin ajizancinsu. Alal misali, a dare na ƙarshe kafin Yesu ya mutu, Bitrus da Yakubu da Yohanna ba su kasance a faɗake kamar yadda Yesu ya umurce su ba. Yesu ya fahimci yanayinsu kuma ya ce: “Lallai ruhu ya yarda, amma jikin ba ƙarfi.” (Mat. 26:​40, 41) Yesu bai yi fushi da manzanninsa ba domin ya san cewa su ajizai ne.

Wata ’yar’uwa mai suna Mandy tana yawan sūkar mutane, amma yanzu tana ƙoƙarin yin koyi da Yesu ta wajen zama mai tawali’u. Ta ce: “Ina ƙoƙari kada in riƙa mai da hankali ga ajizancin mutane amma kamar Jehobah zan riƙa mai da hankali ga halayensu masu kyau.” Ya kamata halin Yesu na jin tausayin mutane ya taimaka mana mu riƙa nuna tawali’u sa’ad da muke sha’ani da mutane.

Yesu ya dogara ga Allah. Yesu ya jimre da wulaƙanci sa’ad da yake duniya. Mutane ba su fahimce shi ba, sun rena shi da kuma gana masa azaba. Duk da haka, ya ci gaba da zama mai tawali’u domin “ya dogara ga Allah wanda yake yin shari’ar gaskiya.” (1 Bit. 2:23) Yesu ya san cewa Jehobah zai taimaka masa ya jimre kuma a lokacin da ya dace zai hukunta waɗanda suka nuna masa rashin adalci.

Idan aka yi mana rashin adalci kuma muka yi fushi, hakan yana iya sa yanayin ya daɗa muni. Shi ya sa Littafi Mai Tsarki ya ce: “Fushin mutum ba ya kai shi ga aikata adalcin Allah.” (Yaƙ. 1:20) Ko da muna da dalilin yin fushi, ajizancinmu yana iya sa mu ɗauki matakin da bai dace ba.

Akwai wata ’yar’uwa a Jamus mai suna Cathy da a dā take ganin cewa ‘Idan ba ka kāre kanka ba, ba wanda zai taimaka maka.’ Amma halinta ya canja sa’ad da ta soma dogara ga Jehobah sosai. Ta ce: “A yanzu ba na yawan son kāre kaina, amma ina nuna tawali’u don na san cewa Jehobah zai magance dukan rashin adalci a duniya.” Idan an taɓa yi maka rashin adalci, yin koyi da Yesu ta wajen dogara ga Allah zai taimaka maka ka kasance da tawali’u.

“MASU TAWALI’U SUNA FARIN CIKI”

Ta yaya tawali’u zai taimaka mana a mawuyacin yanayi

Yesu ya nuna cewa zama mai tawali’u yana sa mutum farin ciki. Ya ce. “Masu tawali’u suna farin ciki.” (Mat. 5:​5, New World Translation.) Ka yi la’akari da yadda zama mai tawali’u zai taimaka maka.

Tawali’u yana taimaka wa ma’aurata sa’ad da suka samu saɓani. Wani ɗan’uwa mai suna Robert daga Ostareliya ya ce: “Ko da yake ba na son ɓata wa matata rai, na yi baƙar magana da ya ɓata mata rai sosai. Gaskiyar ita ce, ba za mu iya janye baƙar magana da muka yi ba. Na yi da-na-sani da na ga cewa abin da na faɗa ya ɓata mata rai.”

“Dukanmu mukan yi kuskure da yawa” sa’ad da muke magana kuma hakan yana iya jawo matsala a aurenmu. (Yaƙ. 3:2) A irin wannan yanayin, kasancewa da tawali’u zai taimaka mana mu kame kanmu sa’ad da muke magana.​—K. Mag. 17:27.

Robert ya ƙoƙarta sosai don ya riƙa kame kansa. Mene ne sakamakon? Ya ce: “A yanzu, sa’ad da ni da matata muka sami saɓani, nakan ƙoƙarta in saurare ta sosai, in guji yin magana da garaje da kuma yin fushi. Hakan ya kyautata dangantakarmu.”

Tawali’u yana taimaka mana mu zauna lafiya da mutane. Mutanen da suke saurin fushi ba sa samun abokai da yawa. Amma kasancewa da tawali’u yana taimaka mana mu zauna lafiya kuma mu kasance da haɗin kai. (Afis. 4:​2, 3) Cathy da aka ambata ɗazu ta ce: “Kasancewa da tawali’u yana taimaka min in more cuɗanya da mutane, ko da yake yana da wuya a yi cuɗanya da wasu.”

Tawali’u yana taimaka mana mu kasance da kwanciyar rai. Littafi Mai Tsarki ya ce “hikimar da take daga Allah,” tana sa mutum ya kasance da tawali’u da kuma kwanciyar rai. (Yaƙ. 3:​13, 17) Mai tawali’u yana da “kwanciyar zuciya.” (K. Mag. 14:30) Wani ɗan’uwa mai suna Martin da ya yi ƙoƙari ya zama mai tawali’u ya ce: “Yanzu ba na nacewa mutane su bi ra’ayina, kuma ina farin ciki da kwanciyar hankali.”

Hakika, muna bukatar mu ƙoƙarta don mu zama masu tawali’u. Wani ɗan’uwa ya ce: “A gaskiya, har yau nakan yi fushi sosai a wasu lokuta.” Amma, Jehobah da ke ƙarfafa mu mu zama masu tawali’u, zai taimaka mana mu kasance da wannan halin. (Isha. 41:10; 1 Tim. 6:11) Zai ‘mai da mu cikakku’ kuma zai ‘ƙarfafa mu.’ (1 Bit. 5:10) Da shigewar lokaci, kamar manzo Bulus za mu iya yin koyi da “tawali’u da sauƙin kai na Almasihu.”​—2 Kor. 10:1.

^ sakin layi na 2 An canja wasu sunaye.