Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 16

Gaskiya Game da Mutuwa

Gaskiya Game da Mutuwa

Mun “san mutumin da yake da ruhun gaskiya da mutumin da yake da ruhun ƙarya.”​—1 YOH. 4:6.

WAƘA TA 73 Ka Ba Mu Ƙarfin Zuciya

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

Maimakon ka saka hannu a al’adun da ke ɓata wa Allah rai, ka ta’azantar da danginka don rasuwar da aka yi muku (Ka duba sakin layi na 1-2) *

1-2. (a) A waɗanne hanyoyi ne Shaiɗan ya yaudari mutane? (b) Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?

SHAIƊAN, wanda shi ne “uban ƙarya” ya soma yaudarar mutane tun zamanin Adamu da Hauwa’u. (Yoh. 8:44) Ɗaya cikin ƙaryace-ƙaryacen da yake tabkawa shi ne game da matattu da kuma abin da ke faruwa bayan mutuwa. Al’adu da koyarwa da yawa sun samo asali ne daga waɗannan koyarwar. A sakamakon haka, ’yan’uwanmu da yawa sun ‘dāge sosai su kiyaye bangaskiyarsu’ sa’ad da aka yi musu rasuwa.​—Yahu. 3.

2 Mene ne zai taimaka maka ka kasance da aminci idan kana fuskantar irin wannan jarrabawar? (Afis. 6:11) Ta yaya za ka iya taimaka wa wani ɗan’uwa da ake matsa masa ya saka hannu a al’adun da Allah ba ya so? A wannan talifin, za mu tattauna yadda Jehobah yake taimaka mana. Bari mu fara tattauna abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da mutuwa.

GASKIYA GAME DA YANAYIN MATATTU

3. Mene ne sakamakon ƙarya ta farko da Shaiɗan ya yi?

3 Allah bai so mutane su riƙa mutuwa ba. Amma Adamu da Hauwa’u suna bukatar su yi biyayya ga Jehobah don su rayu har abada. Jehobah ya umurce su cewa: “Daga itace mai kawo sanin nagarta da mugunta ba za ka ci ba, gama a ranar da ka ci daga itacen nan lallai za ka mutu.” (Far. 2:​16, 17) Bayan haka, sai Shaiɗan ya soma jawo matsaloli. Ya yi amfani da maciji wajen yi wa Hauwa’u magana cewa: “Ko kaɗan, ba za ku mutu ba.” Hauwa’u ta yarda da wannan ƙaryar kuma ta ci ’ya’yan itacen. Daga baya, mijinta ma ya ci ’ya’yan itacen. (Far. 3:​4, 6) Hakan ya sa mutane suka soma zunubi da kuma mutuwa.​—Rom. 5:12.

4-5. Ta yaya Shaiɗan ya ci gaba da yaudarar mutane?

4 Bayan da Adamu da Hauwa’u suka yi zunubi, sun mutu daidai yadda Allah ya ce. Amma Shaiɗan bai daina yin ƙarya game da yanayin matattu ba. Bayan wasu shekaru, ya soma tabka wasu ƙaryace-ƙaryace. Ɗaya cikinsu shi ne cewa sa’ad da mutum ya mutu, akwai wani abu da ke fitowa a cikinsa kuma ya ci gaba da rayuwa a lahira. Shaiɗan yana yaudarar mutane da yawa da wannan ƙaryar har yau.​—1 Tim. 4:1.

5 Me ya sa mutane da yawa suke yarda da wannan ƙaryar? Shaiɗan yana yin amfani da yadda muke ji sa’ad da aka yi mana rasuwa don ya ruɗe mu. Ya san cewa an halicce mu mu rayu har abada ba don mu mutu ba. (M. Wa. 3:11) Mutuwa maƙiyiya ce a gare mu.​—1 Kor. 15:26.

6-7. (a) Shaiɗan ya yi nasara wajen hana mutane sanin gaskiya game da mutuwa kuwa? Ka bayyana. (b) Ta yaya gaskiyar Littafi Mai Tsarki ta kāre mu daga jin tsoro?

6 Mun san gaskiya game da yanayin matattu duk da ƙoƙarin da Shaiɗan ya yi don ya ɓoye ta. A yau, mutane da yawa sun san gaskiya kuma suna koyar da abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da yanayin matattu da kuma begen da matattu suke da shi. (M. Wa. 9:​5, 10; A. M. 24:15) Wannan gaskiyar tana ta’azantar da mu kuma tana hana mu jin tsoro da kuma yin shakka. Alal misali, ba ma jin tsoron matattu ko kuma tsoron cewa wani mugun abu zai same su. Yanayinsu yana kamar mutumin da ke barci mai zurfi. (Yoh. 11:​11-14) Mun kuma san cewa matattu ba su san ko lokaci yana ƙurewa ba. Saboda haka, a lokacin da za a yi tashin matattu, mutanen da suka yi ɗarurruwan shekaru da mutuwa ba za su san cewa sun jima da mutuwa ba.

7 Babu shakka, gaskiya game da yanayin matattu ba shi da wuyar fahimta. Wannan gaskiyar ta yi dabam da ƙaryace-ƙaryacen Shaiɗan! Ƙaryarsa tana yaudarar mutane kuma tana ɓata sunan Mahaliccinmu. Tambayoyi na gaba za su taimaka mana mu san matsalolin da Shaiɗan ya jawo: Ta yaya ƙaryar Shaiɗan ta ɓata sunan Jehobah? Ta yaya ta hana mutane yin imani da hadayar da Yesu ya yi don ya fanshe mu? Ta yaya ta daɗa jefa mutane cikin baƙin ciki da wahala?

ƘARYACE-ƘARYACEN SHAIƊAN SUN JAWO MATSALOLI SOSAI

8. Kamar yadda Irmiya 19:5 ta nuna, ta yaya ƙaryace-ƙaryacen da Shaiɗan yake yi game da matattu suke ɓata sunan Jehobah?

8 Ƙaryace-ƙaryacen Shaiɗan game da mutuwa yana ɓata sunan Jehobah. Ɗaya daga cikin ƙaryace-ƙaryacen shi ne cewa matattu suna shan azaba a wutar jahannama. Wannan koyarwar tana ɓata sunan Allah! Ta yaya? Tana sa mutane su yi tunanin cewa Allah mai ƙauna yana da irin halayen Iblis. (1 Yoh. 4:8) Yaya hakan yake sa ka ji? Kuma yaya hakan yake sa Jehobah ya ji da yake ya tsani mugunta?​—Karanta Irmiya 19:5.

9. Kamar yadda aka kwatanta a Yohanna 3:16 da 15:​13, ta yaya ƙaryace-ƙaryacen Shaiɗan suka shafi hadaya da Yesu ya ba da?

9 Ƙaryace-ƙaryace Shaiɗan game da mutuwa suna sa mutane su ƙi yin imani cewa Yesu ya fanshe mu. (Mat. 20:28) Wata ƙarya da Shaiɗan yake yi kuma ita ce, mutane suna da kurwa marar mutuwa. Idan hakan gaskiya ne, kowa zai yi rayuwa har abada. Da Yesu bai ba da ransa domin ya fanshe mu mu sami rai na har abada ba. Ka tuna cewa hadayar da Kristi ya ba da ita ce hanya mafi muhimmanci da Allah ya nuna yana ƙaunar ’yan Adam. (Karanta Yohanna 3:16; 15:13.) Ka yi tunanin yadda Jehobah da Yesu suke ji game da koyarwar da ke sa mutane tunanin cewa wannan kyautar ba ta da muhimmanci!

10. Ta yaya ƙaryace-ƙaryacen Shaiɗan game da mutuwa suke daɗa sa mutane baƙin ciki da wahala?

10 Ƙaryace-ƙaryacen Shaiɗan suna daɗa sa mutane baƙin ciki da kuma wahala. Ana iya gaya wa iyayen da ɗansu ya rasu cewa wataƙila Allah ya kai shi sama domin ya zama mala’ika. Shin wannan ƙaryar za ta sa su daina baƙin ciki ne ko kuma za ta daɗa sa su baƙin ciki? Mutane suna yin amfani da koyarwar ƙarya na wutar jahannama don su nuna cewa ya dace a riƙa azabtar da wasu, har ma da ƙona mutanen da suka ƙi bin koyarwar coci a kan gungume. Akwai wani littafi da ya yi magana game da mutanen da aka azabtar da su domin sun ƙi koyarwar coci. Littafin ya ce ƙila wasu daga cikin waɗanda suke azabtar da mutanen sun gaskata cewa suna so mutanen “su ɗanɗana yadda wutar jahannama za ta kasance ne.” Suna so ne mutanen su tuba don kada su shiga wutar jahannama. A ƙasashe da yawa, mutane suna ganin cewa wajibi ne su bauta wa kakanninsu da suka mutu kuma su daraja su don su sami albarka. Wasu kuma suna son yin hakan ne don kada kakanninsu su azabtar da su. Abin takaici, yin imani da ƙaryace-ƙaryacen Shaiɗan ba ya ta’azantar da mutane. A maimakon haka, yana sa mutane damuwa ko kuma tsoro.

YADDA ZA MU GOYI BAYAN KOYARWAR LITTAFI MAI TSARKI

11. Ta yaya danginmu ko kuma abokanmu za su iya sa mu yi abin da bai jitu da koyarwar Littafi Mai Tsarki ba?

11 Ƙaunarmu ga Allah da kuma Kalmarsa na taimaka mana mu yi wa Jehobah biyayya. Ba ma saka hannu a al’adun da ke da alaƙa da matattu a duk lokacin da danginmu ko abokanmu suka ce mu yi hakan. Suna iya neman su kunyatar da mu, wataƙila su ce ba ma ƙaunar mamacin ko kuma daraja shi. Ko kuma suna iya cewa halinmu yana iya sa mamacin ya azabtar da waɗanda suke a raye. Ta yaya za mu goyi bayan koyarwar Littafi Mai Tsarki? Ka yi la’akari da yadda za ka iya yin amfani da waɗannan ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki.

12. Waɗanne al’adu game da matattu ne ba su jitu da koyarwar Littafi Mai Tsarki ba?

12 Ku ƙuduri niyyar “ware kanku” daga koyarwa da al’adun da ba su jitu da Littafi Mai Tsarki ba. (2 Kor. 6:17) A wani yankin da ke tsibirin Karibiya, mutane da yawa sun gaskata cewa idan mutum ya mutu, “fatalwarsa” tana azabtar da mutanen da suka wulaƙanta shi. Wani littafi ya ce: “Fatalwar” tana iya “jawo matsaloli sosai a yankin.” A wasu wurare a Afirka, al’adarsu ita ce a rufe madubin da ke gidan mamacin kuma a juya hotunansa. Me ya sa? Wasu sun ce bai kamata a bar mamacin ya ga kansa ba! A matsayinmu na bayin Jehobah, ba ma gaskata ko saka baki ko kuma hannu a al’adun da suke fifita ƙaryace-ƙaryacen Shaiɗan!​—1 Kor. 10:​21, 22.

Yin bincike sosai da kuma tattaunawa da danginka da ba sa bauta wa Jehobah zai iya taimaka maka ka magance matsaloli (Ka duba sakin layi na 13-14) *

13. Kamar yadda Yaƙub 1:5 ta nuna, mene ne za ka yi idan ba ka tabbata da wata al’ada ba?

13 Idan ba ka tabbata ko wata al’ada ko kuma batu ya jitu da koyarwar Littafi Mai Tsarki ba, ka yi addu’a ga Jehobah ya ba ka hikima. (Karanta Yaƙub 1:5.) Bayan haka, ka yi bincike a littattafanmu. Idan da bukata, kana iya tattaunawa da dattawan ikilisiyarku. Dattawan ba za su gaya maka abin da za ka yi ba, amma suna iya nuna maka ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki kamar waɗannan da aka tattauna a wannan talifin. Idan ka yi hakan, kana horar da kanka don ka “bambanta nagarta da mugunta.”​—Ibran. 5:14.

14. A waɗanne hanyoyi ne za mu iya guji sa wasu yin zunubi?

14 “Ku yi kome saboda ɗaukakar Allah. Kada ku zama dalilin yin zunubi” ga mutane. (1 Kor. 10:​31, 32) Sa’ad da muke tsai da shawara ko za mu bi wata al’ada, muna bukatar mu yi tunani a kan yadda yin hakan zai shafi lamirin wasu, musamman ma ’yan’uwanmu Kiristoci. Ba za mu so mu sa wasu yin tuntuɓe ba! (Mar. 9:42) Ban da haka, muna bukatar mu guji ɓata wa mutanen da ba sa bauta wa Jehobah rai. Domin muna ƙaunar su, za mu daraja su kuma hakan zai ɗaukaka Jehobah. Hakika, ba za mu yi faɗa da mutane ko kuma mu yi musu ba’a saboda al’adunsu ba. Muna bukatar mu tuna cewa ƙauna tana da iko! Idan muka nuna ƙauna a hanyar da ta dace kuma muka daraja mutane, hakan yana iya canja ra’ayin masu hamayya da mu.

15-16. (a) Me ya sa ya dace mu gaya wa mutane abin da muka yi imani da shi? Ka ba da misali. (b) Ta yaya kalaman Bulus a littafin Romawa 1:16 ta shafe mu?

15 Ka gaya wa mutanen yankinku cewa kai Mashaidin Jehobah ne. (Isha. 43:10) Idan wani a iyalinku ya rasu, danginku da kuma maƙwabta suna iya yin fushi in ka ƙi saka hannu a wasu al’adu. Amma yana iya kasancewa da sauƙi ka magance waɗannan matsalolin idan tun da farko ka bayyana musu abin da ka yi imani da shi. Wani ɗan’uwa mai suna Francisco da ke zama a ƙasar Mozambik ya ce: “A lokacin da ni da matata Carolina muka soma bauta wa Jehobah, mun gaya wa iyalinmu cewa ba za mu sake bauta wa matattu ba. Mun fuskanci jarrabawa sa’ad da ’yar’uwar Carolina ta rasu. A al’adarsu, ana yi wa gawa wanka. Bayan haka, dangin mamacin zai kwanta a wurin da aka zubar da ruwan wankar har dare uku. Ana yin hakan ne don a roƙi mamacin kada ya azabtar da mutane. Iyalin Carolina sun so ta saka hannu a wannan al’adar.”

16 Mene ne Francisco da matarsa suka yi? Francisco ya ce: “Da yake muna ƙaunar Jehobah kuma muna so mu yi abin da zai faranta masa rai, mun ƙi saka hannu a al’adar. Hakan ya ɓata wa iyalin Carolina rai sosai. Sun ce ba ma daraja matattu kuma suka ce ba wani a iyalin da zai sake kawo mana ziyara ko kuma ya taimaka mana. Da yake tun da farko mun bayyana musu abin da muka yi imani da shi, ba mu zauna mun tattauna da su sa’ad da suke fushi ba. Wasu daga cikin danginmu sun kāre mu kuma suka ce mun riga mun bayyana musu abin da muka yi imani da shi. Da shigewar lokaci, iyalin Carolina sun daina fushi kuma hakan ya ba mu damar sasantawa da su. Har ma wasu cikinsu sun zo gidanmu don mu ba su littattafanmu.” Kada mu ji kunyar yin tsayin daka a kan abin da Littafi Mai Tsarki yake koyarwa game da mutuwa.​—Karanta Romawa 1:16.

KU TA’AZANTAR DA MASU MAKOKI

Abokan kirki suna ta’azantar da waɗanda aka yi musu rasuwa kuma suna goyon bayansu (Ka duba sakin layi na 17-19) *

17. Mene ne zai taimaka mana mu zama abokan kirki ga ’yan’uwan da ke makoki?

17 Sa’ad da aka yi wa wani ɗan’uwa rasuwa, muna bukatar mu yi iya ƙoƙarinmu don mu zama abokai da kuma ɗan’uwa da aka haifa “domin taimako a kwanakin masifa.” (K. Mag. 17:17) Ta yaya za mu zama “abokin” kirki, musamman ma sa’ad da ake matsa wa ɗan’uwa ko ’yar’uwa ta saka hannu a al’adar da ba ta jitu da Littafi Mai Tsarki ba? Ka yi la’akari da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki guda biyu da za su taimaka mana mu ta’azantar da masu makoki.

18. Mene ne ya sa Yesu ya zub da hawaye, kuma me za mu iya koya daga misalinsa?

18 “Ku yi kuka tare da masu kuka.” (Rom. 12:15) Yana iya yi mana wuya mu san abin da za mu gaya wa mutumin da ke makoki. Amma a wasu lokuta, idan masu makoki suka ga muna kuka tare da su, hakan zai sa su san cewa mun damu da su. Sa’ad da Li’azaru abokin Yesu ya mutu, Maryamu da Marta da kuma wasu sun yi kuka domin mutuwar ɗan’uwansu da kuma abokinsu. Bayan kwana huɗu da Yesu ya zo, shi ma “ya yi hawaye,” duk da cewa ya san zai ta da Li’azaru daga mutuwa. (Yoh. 11:​17, 33-35) Hawayen da Yesu ya zub da ya nuna mana yadda Jehobah yake ji idan aka yi mana rasuwa. Sa’ad da iyalin suka ga yadda Yesu ya zub da hawaye, hakan ya nuna musu cewa ya damu da su sosai, kuma ya ta’azantar da Maryamu da Marta. Hakazalika, idan ’yan’uwa suka ga cewa mun damu da su, hakan zai taimaka musu su ga cewa ba su kaɗaita ba, amma suna da abokai da ke ƙaunar su da kuma goyon bayan su.

19. Sa’ad da muke ta’azantar da ɗan’uwan da ke makoki, ta yaya za mu iya bin abin da ke littafin Mai-Wa’azi 3:7?

19 “Akwai lokacin yin shiru, da lokacin yin magana.” (M. Wa. 3:7) Wata hanya kuma da za mu ta’azantar da ’yan’uwa masu makoki ita ce ta wajen saurarar su. Ka bar ɗan’uwanka ya faɗi abin da ke zuciyarsa, kada ‘maganarsa’ na rashin hankali ta ɓata maka rai. (Ayu. 6:​2, 3) Wataƙila yana fuskantar matsi daga danginsa da ba sa bauta wa Jehobah. Zai dace mu yi addu’a tare da shi, mu roƙi “mai jin addu’o’i” ya ba shi ƙarfi da kuma hikima. (Zab. 65:2) Idan zai yiwu, muna iya karanta Littafi Mai Tsarki tare. Ban da haka, muna iya karanta masa wani tarihi mai ban-ƙarfafa da ke littattafanmu.

20. Mene ne za mu tattauna a talifi na gaba?

20 Muna farin ciki sosai cewa mun san gaskiya game da mutuwa da kuma begen da matattu suke da shi! (Yoh. 5:​28, 29) Don haka, bari mu ci gaba da koyar da gaskiya game da mutuwa da gaba gaɗi a duk lokacin da muke da zarafin yin hakan. A talifi na gaba, za mu tattauna hanyar da Shaiɗan yake amfani da sihiri don ya hana mutane sanin gaskiya. Za mu ga dalilin da ya sa muke bukatar mu guji al’adu da kuma nishaɗin da ke da alaƙa da aljannu.

WAƘA TA 24 Ku Zo Tudun Jehobah

^ sakin layi na 5 Shaiɗan da aljanunsa sun daɗe suna yaudarar mutane game da yanayin matattu. Waɗannan ƙaryace-ƙaryace da suke koyarwa sun sa ana bin al’adu marasa kyau dabam-dabam. Wannan talifin zai taimaka maka ka kasance da aminci ga Jehobah sa’ad da wasu suka matsa maka ka bi waɗannan al’adun.

^ sakin layi na 55 BAYANI A KAN HOTO: Sa’ad da wata da ba ta bauta wa Jehobah take makoki, ’yan’uwanta Shaidu sun ta’azantar da ita.

^ sakin layi na 57 BAYANI A KAN HOTO: Bayan wani Mashaidi ya yi bincike a kan al’adun da ake bi kafin a binne mamaci, sai ya bayyana wa danginsa abin da ya yi imani da shi.

^ sakin layi na 59 BAYANI A KAN HOTO: Dattawan ikilisiya suna ta’azantar da wani ɗan’uwa da aka yi masa rasuwa kuma suna goyon bayan sa.