Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 15

Ka Yi Koyi da Yesu Don Ka Kasance da Kwanciyar Rai

Ka Yi Koyi da Yesu Don Ka Kasance da Kwanciyar Rai

“Allah zai ba ku salama iri wadda ta wuce dukan ganewar ɗan Adam.”​—FILIB. 4:7.

WAƘA TA 113 Salama da Muke Morewa

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1-2. Me ya sa Yesu ya damu a daren da mutu?

YESU ya damu sosai a daren da ya mutu domin mutane masu zunubi za su kashe shi. Amma ba mutuwar kaɗai ba ce take damunsa don yana ƙaunar Ubansa kuma yana so ya faranta masa rai. Yesu ya san cewa za a ɗaukaka sunan Jehobah idan ya kasance da aminci a wannan lokacin. Ƙari ga haka, yana ƙaunar mutane kuma ya san za mu sami begen yin rayuwa har abada idan ya kasance da aminci har mutuwa.

2 Yesu ya natsu ko da yana cikin matsi sosai. Ya gaya wa manzanninsa: “Salamata nake ba ku.” (Yoh. 14:27) Yesu yana da “salama” da Allah yake bayarwa, wato kasancewa da kwanciyar rai don ƙulla dangantaka na kud da kud da Jehobah. Wannan salama ce ta sa Yesu ya kasance da kwanciyar rai ko da yana cikin matsi sosai.​—Filib. 4:​6, 7.

3. Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?

3 Babu wani a cikinmu da zai fuskanci irin matsi da Yesu ya jimre, amma dukan mabiyan Yesu za su fuskanci jarrabawa. (Mat. 16:​24, 25; Yoh. 15:20) Kuma kamar Yesu mukan damu a wasu lokuta. Mene ne za mu iya yi don kada mu riƙa damuwa ainun kuma mu kasance da kwanciyar rai? Bari mu bincika abubuwa uku da Yesu ya yi sa’ad da yake hidima a duniya kuma mu ga yadda za mu iya yin koyi da shi sa’ad da muke cikin matsala.

YESU YA YI ADDU’A A KAI A KAI

Za mu kasance da kwanciyar rai ta wajen yin addu’a (Ka duba sakin layi na 4-7)

4. Bisa abin da ke littafin 1 Tasalonikawa 5:​17, ka ba da wasu misalan da suka nuna cewa Yesu ya yi addu’a sau da yawa a daren da ya mutu.

4 Karanta 1 Tasalonikawa 5:17. Yesu ya yi addu’a sau da yawa a daren da ya mutu. Ya yi hakan sa’ad da zai miƙa wa almajiransa gurasa da kuma ruwan inabi a lokacin da ya nuna musu yadda za su riƙa tuna da mutuwarsa. (1 Kor. 11:​23-25) Yesu ya yi addu’a da almajiransa kafin ya bar wurin da suka yi Idin Ƙetarewa. (Yoh. 17:​1-26) Ƙari ga haka, ya yi addu’a a kai a kai sa’ad da shi da almajiransa suka kai Getsemani a daren da ya rasu. (Mat. 26:​36-39, 42, 44) Kuma furuci na ƙarshe da Yesu ya yi kafin ya mutu addu’a ce. (Luk. 23:46) Yesu ya yi addu’a ga Jehobah game da dukan abubuwa na musamman da suka faru a daren.

5. Me ya sa manzannin Yesu ba su kasance da ƙarfin zuciya ba?

5 Abin da ya taimaka wa Yesu ya jimre da jarrabawar da ya fuskanta shi ne cewa ya dogara ga Jehobah kuma ya yi addu’a a kai a kai. Amma manzanninsa ba su iya jimrewa ba domin ba su nace da yin addu’a da kasancewa a faɗake a wannan daren ba. A sakamakon haka, ba su kasance da ƙarfin zuciya ba sa’ad da suka fuskanci jarrabawa. (Mat. 26:​40, 41, 43, 45, 56) Za mu kasance da aminci idan muka bi misalin Yesu kuma muka yi “addu’a” a kai a kai sa’ad da muke cikin matsaloli. Mene ne za mu iya yin addu’a a kai?

6. Ta yaya kasancewa da bangaskiya zai taimaka mana mu kasance da kwanciyar rai?

6 Muna iya yin addu’a ga Jehobah cewa ya “ƙara mana bangaskiya.” (Luk. 17:5; Yoh. 14:1) Muna bukatar kasancewa da bangaskiya domin Shaiɗan zai jarraba dukan mabiyan Yesu. (Luk. 22:31) Ta yaya bangaskiya za ta taimaka mana mu kasance da kwanciyar rai a lokacin da muke fuskantar matsaloli? Idan muka yi iya ƙoƙarinmu don mu magance wata matsala, kasancewa da bangaskiya cewa Jehobah zai taimaka mana zai sa mu daina damuwa ainun. Za mu yi hakan don mun san cewa Jehobah zai magance matsalar a lokacin da ya dace. Ƙari ga haka, za mu kasance da kwanciyar rai don mun san cewa Jehobah ya san matakin da zai ɗauka.​—1 Bit. 5:​6, 7.

7. Wane darasi ne ka koya daga furucin Robert?

7 Yin addu’a zai taimaka mana mu kasance da kwanciyar rai a duk lokacin da muke fuskantar jarrabawa. Alal misali, Robert ɗan shekara 80 ne kuma dattijo ne mai aminci. Ya ce: “Shawarar da ke littafin Filibiyawa 4:​6, 7 ta taimaka mini in jimre da matsaloli da yawa a rayuwata. Akwai lokacin da aka sauke ni daga dattijo kuma ina fama da rashin kuɗi.” Mene ne ya taimaka wa Robert ya natsu? Ya ce: “Nakan yi addu’a da zarar na soma damuwa, kuma na ga cewa yin addu’a a kai a kai ya taimaka mini in kasance da kwanciyar rai.”

YESU YA YI WA’AZI DA ƘWAZO

Za mu kasance da kwanciyar rai ta yin wa’azi (Ka duba sakin layi na 8-10)

8. Kamar yadda yake a Yohanna 8:​29, wane abu ne kuma ya sa Yesu kasancewa da kwanciyar rai?

8 Karanta Yohanna 8:29. Yesu ya kasance da kwanciyar rai a lokacin da ake tsananta masa domin ya san yana faranta ran Jehobah. Ya ci gaba da yin biyayya a lokacin da yin hakan ya yi masa wuya. Ƙari ga haka, ya ƙaunaci Jehobah kuma bauta masa ne ya fi muhimmanci a gare shi. Alal misali, kafin Yesu ya zo duniya, shi ne gwani mai aiki tare da Allah. (K. Mag. 8:30) Kuma sa’ad da yake duniya, ya yi ƙwazo wajen koya wa mutane game da Jehobah. (Mat. 6:9; Yoh. 5:17) Yin wannan aikin ya sa Yesu farin ciki sosai.​—Yoh. 4:​34-36.

9. Me ya sa muke da kwanciyar rai sa’ad da muka shagala a yin wa’azi?

9 Za mu yi koyi da Yesu idan muka yi biyayya ga Jehobah kuma muka “yalwata cikin aikin Ubangiji” kullum. (1 Kor. 15:58) Idan muka ‘ba da dukan lokacinmu’ ga yin wa’azi, za mu kasance da ra’ayin da ya dace game da matsalolinmu. (A. M. 18:5) Alal misali, waɗanda muke haɗuwa da su a wa’azi sun fi mu fuskantar matsaloli. Amma, sukan inganta rayuwarsu kuma su soma farin ciki sa’ad da suka koya game da Jehobah kuma suka bi shawararsa. A duk lokacin da muka ga hakan ya faru, mukan kasance da tabbaci cewa Jehobah zai kula da mu. Kuma wannan tabbacin zai taimaka mana mu kasance da kwanciyar rai. Wata ’yar’uwa da ta daɗe tana tunanin cewa ba ta da amfani ta fahimci cewa shagala a yin wa’azi na taimaka mana. Ta ce: “Ba na yawan tunanin matsalolina kuma ina farin ciki sa’ad da na fita yin wa’azi. Sa’ad da nake wa’azi, nakan kusaci Jehobah sosai.”

10. Mene ne ka koya daga furucin Brenda?

10 Ka yi la’akari da wata ’yar’uwa mai suna Brenda wadda ita da ’yarta suke rashin lafiya mai tsanani. Brenda tana amfani da keken guragu kuma ba ta da ƙarfi. A wasu lokuta tana wa’azi gida-gida, amma ta fi yin wa’azi ta wajen rubuta wasiƙu. Ta ce: “Sa’ad da na fahimci cewa ba zan taɓa warkewa ba, sai na mai da hankali ga hidimata. Yin wa’azi ya sa ba na yawan tunani game da matsalolina. Amma, ina mai da hankali wajen taimaka wa mutanen da na yi musu wa’azi. Kuma yin hakan yana tuna mini game da begen da nake da shi.”

YESU YA YARDA ABOKANSA SU TAIMAKA MASA

Za mu kasance da kwanciyar rai ta wurin yin cuɗanya da abokan kirki (Ka duba sakin layi na 11-15)

11-13. (a) Ta yaya manzanni da kuma wasu suka zama abokan kirki ga Yesu? (b) Ta yaya abokan Yesu suka taimaka masa?

11 A lokacin da Yesu yake wa’azi, manzanninsa sun zama abokan kirki a gare shi. Su irin abokai ne da Littafi Mai Tsarki ya ambata cewa: “Akwai irin abokin da ya fi ɗan’uwa aminci.” (K. Mag. 18:24) Yesu ya daraja irin waɗannan abokai. Babu wani cikin ’yan’uwansa da suka ba da gaskiya gare shi sa’ad da yake hidima a duniya. (Yoh. 7:​3-5) Akwai lokacin da danginsa suke ganin ya haukace. (Mar. 3:21) Amma a daren da Yesu ya mutu, ya yi furuci game da manzanninsa masu aminci cewa: “Ku ne kuka tsaya da aminci tare da ni a duk gwaje-gwajen da na sha.”​—Luk. 22:28.

12 Akwai wasu lokutan da manzannin Yesu suka sa shi baƙin ciki, amma bai mai da hankali ga kurakurensu ba. Maimakon haka, ya lura cewa sun ba da gaskiya a gare shi. (Mat. 26:40; Mar. 10:​13, 14; Yoh. 6:​66-69) A daren da Yesu ya mutu, ya ce ma waɗannan maza masu aminci: “Ina ce da ku abokai gama na gaya muku dukan abin da na ji daga wurin Ubana.” (Yoh. 15:15) Babu shakka, abokan Yesu sun ƙarfafa shi sosai. Yadda suka taimaka masa a hidimarsa ya sa shi farin ciki ainun.​—Luk. 10:​17, 21.

13 Ban da manzaninsa, Yesu yana da wasu abokai maza da mata da suka taimaka masa a wa’azi da kuma wasu hidimomi. Wasu sun gayyace shi zuwa gidajensu don ya ci abinci. (Luk. 10:​38-42; Yoh. 12:​1, 2) Wasu kuma sun yi tafiya da shi kuma suka yi masa hidima daga cikin dukiyarsu. (Luk. 8:3) Yesu yana da abokan kirki domin shi ma abokin kirki ne a gare su. Ya yi musu alheri kuma ba ya bukatar su yi abin da ya fi ƙarfinsu. Duk da cewa Yesu kamiltacce ne, ya nuna godiya ga yadda abokansa ajizai suka tallafa masa. Babu shakka, sun taimaka masa ya kasance da kwanciyar rai.

14-15. Ta yaya za mu samu abokan kirki, kuma yaya za su iya taimaka mana?

14 Abokan kirki za su taimaka mana mu kasance da aminci ga Jehobah. Za mu samu abokan kirki idan mu ma muka zama abokin kirki. (Mat. 7:12) Alal misali, Littafi Mai Tsarki ya ƙarfafa mu mu yi amfani da lokacinmu da kuzarinmu don mu taimaka wa mutane, musamman “waɗanda” suke da bukata. (Afis. 4:28) Ka san wani a cikin ikilisiyarku da za ka iya taimaka masa? Za ka iya taimaka wa wani da ya tsufa ko yake rashin lafiya yin cefane? Za ka iya sayan abinci ka ba wasu da ke fama da rashin kuɗi? Idan ka san yadda ake amfani da dandalin jw.org® da kuma manhaja JW Library® shin za ka iya taimaka ma wasu a ikilisiyarku don su iya yin amfani da su? Za mu yi farin ciki idan muka mai da hankali ga taimaka wa mutane.​—A. M. 20:35.

15 Abokanmu za su tallafa mana sa’ad da muke fuskantar matsaloli kuma su taimaka mana mu kasance da kwanciyar rai. Kamar yadda Elihu ya saurari Ayuba sa’ad da yake magana game da gwaje-gwajensa, abokanmu suna taimaka mana sa’ad da suka saurare mu yayin da muke gaya musu matsalolinmu. (Ayu. 32:4) Bai kamata mu sa rai cewa abokanmu za su gaya mana abin da za mu yi ba, amma za mu yi nasara idan muka saurari shawararsu daga Littafi Mai Tsarki. (K. Mag. 15:22) Ƙari ga haka, kamar yadda Sarki Dauda ya amince da taimakon abokansa, ya kamata mu kasance da tawali’u mu amince da taimakon abokanmu a lokacin da muke cikin matsala. (2 Sam. 17:​27-29) Hakika, irin waɗannan abokan kirki kyauta ce daga wurin Jehobah.​—Yaƙ. 1:17.

YADDA ZA MU SAMU KWANCIYAR RAI

16. Kamar yadda aka ambata a littafin Filibiyawa 4:​6, 7, ta wace hanya ce kaɗai za mu kasance da kwanciyar rai? Ka bayyana.

16 Karanta Filibiyawa 4:​6, 7Me ya sa Jehobah ya ce za mu iya samun salamar da yake ba mu ta wurin “Yesu” kaɗai? Domin za mu sami kwanciyar rai na dindindin idan muka fahimci kuma muka ba da gaskiya cewa Jehobah zai cika nufinsa ta wurin Yesu. Alal misali, ta wurin hadayar da Yesu ya ba da ne za a iya gafarta mana dukan zunubanmu. (1 Yoh. 2:12) Sanin hakan yana sa mu kasance da kwanciyar hankali! A matsayinsa na Sarkin Mulkin Allah, Yesu zai kawar da dukan wahalolin da Shaiɗan da mutanensa suka jawo mana. (Isha. 65:17; 1 Yoh. 3:8; R. Yar. 21:​3, 4) Muna ɗokin hakan ya faru a nan gaba! Kuma duk da cewa aikin da Yesu ya ba mu yana da wuya, yana tare da mu kuma yana tallafa mana a wannan kwanaki na ƙarshe. (Mat. 28:​19, 20) Hakan ya sa mu kasance da ƙarfin zuciya! Hakika, muna bukatar kasancewa da bege da ƙarfin zuciya domin mu kasance da kwanciyar rai.

17. (a) Ta yaya Kirista zai ci gaba da kasancewa da kwanciyar rai? (b) Kamar yadda aka yi mana alkawari a littafin Yohanna 16:​33, mene ne za mu iya yi?

17 Ta yaya za ka kasance da kwanciyar rai sa’ad da kake fuskantar matsaloli masu wuya? Za ka iya yin hakan ta wajen yin abubuwan da Yesu ya yi. Na farko, ka riƙa yin addu’a a kai a kai. Na biyu, ka yi biyayya ga Jehobah kuma ka riƙa wa’azi da ƙwazo, har a lokacin da yin hakan yake da wuya. Kuma na uku, ka nemi taimakon abokan kirki sa’ad da kake cikin matsala. Idan ka yi hakan, kwanciyar rai da Allah yake bayarwa zai tsare zuciyarka da tunaninka. Kuma kamar Yesu, za ka yi nasara a duk jarrabawar da kake fuskanta.​—Karanta Yohanna 16:33.

WAƘA TA 41 Allah Ka Ji Roƙona

^ sakin layi na 5 Dukanmu muna fuskantar matsalolin da za su iya sa ya yi wuya mu kasance da kwanciyar rai. A wannan talifin, za a tattauna abubuwa uku da Yesu ya yi don ya kasance da kwanciyar rai da kuma yadda za mu bi misalinsa a lokacin da muke fuskantar matsaloli masu tsanani.