Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 8

“Ku Yi Hankali, . . . Ku Yi Zaman Tsaro”

“Ku Yi Hankali, . . . Ku Yi Zaman Tsaro”

“Ku yi hankali, . . . ku yi zaman tsaro.”​—1 BIT. 5:​8, Tsohuwar Hausa a Sauƙaƙe.

WAƘA TA 144 Mu Riƙa Ɗokin Samun Ladan!

ABIN DA ZA A TATTAUNA a

1. Mene ne Yesu ya gaya wa almajiransa game da ƙarshen zamani, kuma wane gargaɗi ne ya yi musu?

 ꞌYAN kwanaki kafin Yesu ya mutu, huɗu daga cikin almajiransa sun tambaye shi cewa: “Mece ce alamar . . . ƙarshen zamani?” (Mat. 24:3) Da alama, mabiyan Yesu suna tunanin yadda za su san lokacin da za a halaka Urushalima da kuma haikalinta. Saꞌad da yake ba su amsa, Yesu bai gaya musu lokacin da za a halaka Urushalima da haikalinta kawai ba, amma ya gaya musu alamun “ƙarshen zamani” da muke ciki a yau. Game da lokacin da ƙarshen zai zo, Yesu ya ce: “Ba wanda ya san ranar, ko a ƙarfe nawa ne wannan zai faru, ko malaꞌikun da suke sama, ko Ɗan, sai dai Uban kaɗai.” Bayan haka, ya gargaɗi dukan mabiyansa su “zauna da shiri.”​—Mar. 13:​32-37.

2. Me ya sa yake da muhimmanci Yahudawa a ƙarni na farko su zauna da shiri?

2 Kiristoci Yahudawa a ƙarni na farko suna bukatar su zauna da shiri domin su iya kāre rayukansu. Yesu ya gaya wa mabiyansa abubuwan da za su iya lura da su don su san lokacin da za a halaka Urushalima da kuma haikalinta. Ya ce: “Saꞌad da kuka ga sojoji sun kewaye Urushalima, za ku sani cewa an yi kusa a rushe ta.” A wannan lokacin, suna bukatar su bi gargaɗin da Yesu ya yi musu cewa “su gudu zuwa cikin tuddai.” (Luk. 21:​20, 21) Waɗanda suka bi gargaɗin Yesu sun tsira saꞌad da Romawa suka halaka Urushalima.

3. Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?

3 A yau, muna rayuwa a kwanakin ƙarshe. Mu ma muna bukatar mu lura kuma mu zauna da shiri. A wannan talifin, za mu tattauna yadda za mu kasance da raꞌayin da ya dace yayin da muke lura da abubuwan da suke faruwa a duniya da yadda za mu lura da kanmu da kuma yadda za mu yi amfani da lokacin da ya rage mana da kyau.

MU KASANCE DA RAꞌAYIN DA YA DACE GAME DA ABUBUWAN DA SUKE FARUWA

4. Me ya sa zai dace mu mai da hankali ga yadda abubuwan da suke faruwa a yau suke cika annabcin Littafi Mai Tsarki?

4 Muna da dalilai masu kyau na mai da hankali a kan yadda abubuwan da suke faruwa suke cika annabcin Littafi Mai Tsarki. Alal misali, Yesu ya gaya mana jerin abubuwan da za su faru da za su nuna mana cewa ƙarshen zamani ya yi kusa. (Mat. 24:​3-14) Manzo Bitrus ya ƙarfafa mu mu mai da hankali ga yadda annabce-annabcen Littafi Mai Tsarki suke cika don bangaskiyarmu ta yi ƙarfi. (2 Bit. 1:​19-21) Littafi na ƙarshe na Littafi Mai Tsarki ya soma da kalmomin nan: “Ruꞌuyar Yesu Almasihu wanda Allah ya ba shi domin ya nuna wa bayinsa abin da zai faru ba da daɗewa ba.” (R. Yar. 1:1) Don haka, muna lura da abubuwan da suke faruwa a duniya a yau da ganin yadda suke cika annabcin Littafi Mai Tsarki. Kuma mukan yi marmarin tattauna abubuwan da suke faruwa da junanmu.

Mene ne ya kamata mu guji yi yayin da muke tattauna annabcin Littafi Mai Tsarki? (Ka duba sakin layi na 5) c

5. Me muke bukatar mu guje wa, amma me muke bukatar mu yi? (Ka kuma duba hoton.)

5 Amma saꞌad da muke tattauna annabcin Littafi Mai Tsarki, zai dace mu guji faɗan abubuwan da ba mu da tabbaci a kai. Me ya sa? Domin ba ma so mu faɗi abubuwan da za su raba kan ikilisiya. Alal misali, za mu iya jin shugabannin duniya suna magana game da yadda za su kawo salama da kuma tsaro a dukan duniya. Maimakon mu soma cewa abin da shugabannin suka faɗa yana cika annabcin da ke 1 Tasalonikawa 5:​3, zai dace mu mai da hankali ga yadda littattafanmu suka bayyana wannan batun a kwana-kwanan nan. Idan abubuwan da muke tattaunawa sun jitu da abubuwan da ƙungiyar Jehobah ta koya mana, za mu sa ikilisiya ta zauna da “nufi ɗaya” da kuma tunani ɗaya.​—1 Kor. 1:10; 4:6.

6. Waɗanne darussa ne za mu iya koya daga 2 Bitrus 3:​11-13?

6 Karanta 2 Bitrus 3:​11-13. Manzo Bitrus ya taimaka mana mu kasance da raꞌayin da ya dace yayin da muke bincika annabcin Littafi Mai Tsarki. Ya ƙarfafa mu mu yi “marmarin zuwan Ranar Allah.” Me ya sa? Ba don muna so mu san “ranar” da Jehobah zai soma yaƙin Armageddon ba ne, amma domin muna so mu yi amfani da lokacin da ya rage mana mu “yi rayuwa mai tsarki, mai hali iri na Allah.” (Mat. 24:36; Luk. 12:40) Wato muna so mu yi abubuwan da suka dace, kuma mu tabbata cewa duk wani abin da muke yi wa Jehobah, muna yin shi ne domin muna ƙaunar sa sosai. Don mu ci gaba da yin hakan, muna bukatar mu lura da kanmu.

ME AKE NUFI DA MU KULA DA KANMU?

7. Ta yaya za mu nuna cewa muna kula da kanmu? (Luka 21:34)

7 Yesu bai gaya wa almajiransa su mai da hankali ga abubuwan da ke faruwa a duniya kawai ba. Ya kuma gaya musu su mai da hankali ga kansu. Ya yi wannan gargaɗin dalla-dalla a Luka 21:34. ‘(Karanta. b)’ Ku lura cewa Yesu ya ce: ‘Ku kula da kanku fa.’ Mutumin da yake kula da kansa yakan mai da hankali ga abubuwan da za su raunana bangaskiyarsa ga Jehobah kuma yakan ɗau mataki domin ya guje su. Ta yin haka, zai ci gaba da kasancewa a cikin ƙaunar Allah.​—K. Mag. 22:3; Yahu. 20, 21.

8. Wane gargaɗi ne manzo Bulus ya ba wa Kiristoci?

8 Manzo Bulus ya ƙarfafa Kiristoci su kula da kansu. Alal misali, ya gaya wa Kiristocin da ke Afisa: “Ku mai da hankali ƙwarai ga zamanku. Kada ku zama kamar wawaye, sai dai kamar masu hikima.” (Afis. 5:​15, 16) A kullum, Shaiɗan yana ƙoƙarin raunana dangantakarmu da Jehobah, shi ya sa Littafi Mai Tsarki ya gargaɗe mu cewa mu “fahimci ko mene ne nufin Ubangiji” don mu iya kāre kanmu daga duk wani harin da Shaiɗan zai kawo mana.​—Afis. 5:17.

9. Ta yaya za mu iya sanin nufin Jehobah?

9 Littafi Mai Tsarki bai gaya mana dukan abubuwan da za su iya ɓata dangantakarmu da Jehobah ba. A kullum, muna bukatar mu yanke shawarwarin da ba a bayyana su a cikin Littafi Mai Tsarki ba. Don mu yanke shawarar da ta dace, muna bukatar mu fahimci “ko mene ne nufin Ubangiji.” Za mu iya yin hakan idan a kullum muna karanta Kalmar Allah kuma muna yin bimbini a kai. Idan muka ci gaba da fahimtar nufin Allah kuma muka kasance da ‘tunanin Almasihu,’ za mu zama masu hikima ko a yanayin da ba a ba da takamammen doka game da shi ba. (1 Kor. 2:​14-16) A wasu lokuta, yana yi mana sauƙi mu san abubuwan da muke bukatar mu guje musu, a wasu lokuta kuma ba ya mana sauƙi.

10. Waɗanne abubuwa ne muke bukatar mu guje musu?

10 Wasu daga cikin abubuwan da muke bukatar mu guje musu su ne kwarkwasa da yawan ci da sha da zage-zage da kallon fina-finan da ake faɗa a ciki ko batsa. (Zab. 101:3) A kullum, maƙiyinmu Shaiɗan yana neman hanyar da zai lalata dangantakarmu da Jehobah. (1 Bit. 5:8) Idan ba mu lura ba, Shaiɗan zai sa mu soma ƙishi da rashin gaskiya da haɗama da ƙiyayya da girman kai da kuma riƙe ꞌyanꞌuwanmu a zuci. (Gal. 5:​19-21) Da farko, za mu iya yin tunani cewa waɗannan halayen ba su da haɗari. Amma idan ba mu ɗauki mataki kuma mun kawar da su daga zuciyarmu ba, za su ci gaba da yin girma kuma su jawo mana matsala.​—Yak. 1:​14, 15.

11. Wane abu mai haɗari ne muke bukatar mu guje wa, kuma me ya sa?

11 Wani abu da muke bukatar mu guje wa shi ne abokan banza. Ka yi laꞌakari da wannan misalin. A ce kana aiki kullum da wani da ba Mashaidin Jehobah ba ne. Kana taimaka masa da kuma yi masa alheri domin kana so ya kasance da raꞌayi mai kyau game da Shaidun Jehobah. Kana zuwa cin abincin rana da shi loto-loto. Kafin ka ankara, sai ka soma yin hakan a kullum. A wasu lokuta, mutumin yakan yi maganganun lalata, amma ba ka jin daɗin hakan da farko. A kwana a tashi, ka fara saba da irin maganganun nan har ma ba sa damin ka. Sai wata rana mutumin ya ce ka zo ku je ku ɗan shaƙata bayan an tashi aiki kuma ka yarda da hakan. A ƙarshe, sai ka soma tunani kamar mutumin. Ba da jimawa ba, za ka soma yin abubuwa kamar mutumin. Hakika, yana da kyau mu daraja mutane kuma mu yi musu alheri, amma zai dace mu tuna cewa waɗanda muke yawan kasancewa tare da su za su iya shafan halayenmu. (1 Kor. 15:33) Idan muna kula da kanmu kamar yadda Yesu ya umurce mu mu yi, za mu guji ƙulla dangantaka da waɗanda ba sa bin ƙaꞌidodin Jehobah. (2 Kor. 6:15) Za mu ga haɗarin da ke tattare da hakan kuma mu guje masa.

KA YI AMFANI DA LOKACINKA DA KYAU

12. Mene ne mabiyan Yesu za su yi yayin da suke jiran ƙarshen zamani?

12 Ba wai mabiyan Yesu za su yi zaman kashe wando suna jiran ƙarshen zamani ya zo ba ne. Yesu ya ba su aikin yi. Ya umarce su su yi waꞌazi a “Urushalima, da cikin dukan yankin Yahudiya, da Samariya, har zuwa iyakar duniya.” (A. M. 1:​6-8) Wannan gagarumin aiki ne da Yesu ya ba wa almajiransa! Za su yi amfani da lokacinsu a hanyar da ta dace idan suna mai da hankali ga yin aikin nan.

13. Me ya sa muke bukatar mu yi amfani da lokacin da muke da shi da kyau? (Kolosiyawa 4:5)

13 Karanta Kolosiyawa 4:5. Don mu kula da kanmu, muna bukatar mu mai da hankali ga yadda muke amfani da lokacinmu. “Saꞌa, da tsautsayi” za su iya shafan kowannenmu. (M. Wa. 9:​11, MMA) Za mu iya mutuwa babu zato.

Ta yaya za mu yi amfani da lokacinmu da kyau? (Ka duba sakin layi na 14-15)

14-15. Ta yaya za mu yi amfani da lokacinmu da kyau? (Ibraniyawa 6:​11, 12) (Ka kuma duba hoton.)

14 Kyautata dangantakarmu da Jehobah da kuma yin nufinsa hanya ɗaya ce da za mu iya amfani da lokacinmu da kyau. (Yoh. 14:21) Muna bukatar mu ‘tsaya daram mu kafu, kullum muna yalwata cikin aikin Ubangiji.’ (1 Kor. 15:58) Idan muka yi haka, saꞌad da ƙarshen rayuwarmu ko ƙarshen wannan zamanin ya zo, ba za mu yi da-na-sani ba.​—Mat. 24:13; Rom. 14:8.

15 A yau, Yesu yana yi wa mabiyansa ja-goranci yayin da suke yin waꞌazin Mulkin Allah a dukan duniya. Ya cika alkawarin da ya yi. Ta ƙungiyar Jehobah, Yesu yana koyar da mu yadda za mu yi waꞌazi, kuma yana tanada mana abubuwan da muke bukata don mu yi hakan. (Mat. 28:​18-20) Yayin da muke jiran lokacin da Jehobah zai kawo ƙarshen wannan zamanin, muna bin umurnin Yesu ta wajen yin iya ƙoƙarinmu don mu yi waꞌazi da koyar da mutane da kuma zama da shiri. Idan muna yin abin da ke Ibraniyawa 6:​11, 12, hakan zai taimaka mana mu riƙe begenmu “har zuwa ƙarshe.”​—Karanta.

16. Wane abu ne muka ƙudiri niyyar yi?

16 Jehobah ya shirya rana da kuma saꞌa da zai kawo ƙarshen wannan zamanin. Saꞌad da ranar ta zo, ba abin da zai hana Jehobah cika alkawuran da ya yi a cikin Kalmarsa game da sabuwar duniya. A wasu lokuta, za mu iya gani kamar ƙarshen zamanin yana jinkirin zuwa. Amma ranar Jehobah “ba za ta yi latti ba.” (Hab. 2:3) Don haka, bari mu ƙudiri niyyar ci gaba da “zuba ido ga Yahweh,” muna ‘jiran Allah mai cetonmu.’​—Mik. 7:7.

WAƘA TA 139 Rayuwa a Cikin Aljanna

a Wannan talifin zai tattauna yadda za mu yi hankali yayin da muke lura da abubuwan da suke faruwa a duniya. Ƙari ga haka, za mu ga yadda za mu mai da hankali ga kanmu da kuma yadda za mu yi amfani da lokacinmu da kyau.

b Luka 21:34 (Mai Makamantu Ayoyi): “Ku kula da kanku fa, kada zuciyarku ta zarme da yawan shaye-shaye da buguwa, da kuma taraddadin wannan duniya, har ba labari ranan nan ta mamaye ku kamar tarko.”

c BAYANI A KAN HOTUNA: (Sama) Wasu maꞌaurata suna kallon labarai a talabijin. Daga baya, suna gaya wa ꞌyanꞌuwa raꞌayinsu game da maꞌanar abubuwan da ke faruwa bayan an tashi taro. (Ƙasa) Wasu maꞌaurata suna kallon ƙarin bayani daga Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu don su san yadda bawan nan mai aminci yake bayyana maꞌanar annabcin Littafi Mai Tsarki. Suna ba wa mutane littattafan da bawan nan mai aminci ya tanadar.