Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TARIHI

Na Ga Yadda Masu Bangaskiya Suka Yi Nasara

Na Ga Yadda Masu Bangaskiya Suka Yi Nasara

WATAƘILA za ka iya tuna wata tattaunawar da ka taɓa yi da ke da muhimmanci sosai a gare ka. Wanda na taɓa yi wajen shekaru 50 da suka shige, saꞌad da muke jin ɗumin wuta a ƙasar Kenya ce ta fi muhimmanci a gare ni. Mun yi watanni muna tafiya kuma mun yi baƙi. Mun zauna muna tattauna wani bidiyo da ya yi magana game da wani batu na addini, sai abokina ya ce, “abin da bidiyon ya faɗa bai jitu da Littafi Mai Tsarki ba.”

Na yi dariya, domin ban yi tunani cewa abokina mai bin addini ba ne. Sai na tambaye shi: “Me ka sani game da Littafi Mai Tsarki?” Bai yi saurin amsa min ba. A ƙarshe, ya gaya min cewa mamarsa Mashaidiyar Jehobah ce, kuma ya koyi wasu abubuwa daga wurin ta. Sai na soma marmarin koya game da hakan, kuma na yi masa tambayoyi.

Ranar mun yi dare muna tattaunawa. Abokina ya gaya min cewa Littafi Mai Tsarki ya ce Shaiɗan ne yake mulkin duniya. (Yoh. 14:30) Mai yiwuwa ka san da hakan tun da aka haife ka, amma a lokacin ne na fara sanin hakan kuma ya ban mamaki. Tun da nake, nakan ji cewa akwai Allah mai alheri da yake mulkin duniya. Amma hakan bai jitu da abubuwa da nake gani suna faruwa ba. Ko da yake shekaruna 26 ne kawai a lokacin, na ga abubuwa da yawa da suka dame ni sosai.

A lokacin, babana sojan sama ne na ƙasar Amirka. Don hakan, saꞌad da nake ƙarami, na san cewa za a iya yin yaƙin nukiliya, domin sojoji a shirye suke su harba bam na nukiliya. A Lokacin yaƙin Vietnam ne nake makarantar kwaleji a Kalifoniya. Ina cikin daliɓai da suka yi zanga-zanga. ꞌYan sanda sun bi mu da sanduna. Mun gudu muna numfashi da kyar, kuma da kyar muke gani saboda barkonon tsohuwa da suka fesa mana. An yi tashin hankali da kuma tawaye sosai a lokacin. An yi kashe-kashe da ke da alaƙa da siyasa, da zanga-zanga da kuma tashe-tashen hankula. Mutane sun yi ta bayyana raꞌayoyi dabam-dabam game da abin da ya kamata a yi. Abubuwan nan sun rikitar da ni.

Daga Landan zuwa Tsakiyar Afirka

A 1970, na soma aiki a arewacin gaɓar teku na Alaska, kuma na yi kuɗi sosai. Sai na tafi Landan ta jirgin sama, na sayi babur kuma na soma tafiya ta kudanci, ba tare da sanin inda za ni ba. Bayan wasu watanni, sai na isa Afirka. Saꞌad da nake hanyar tafiya, na haɗu da wasu mutane da suke sa ran cewa za su iya guje wa matsalolin da suke fuskanta.

Saboda abubuwan da na gani kuma na ji, na yarda da koyarwar Littafi Mai Tsarki cewa Shaiɗan ne yake iko da wannan duniyar. Amma idan ba Allah ne yake iko da wannan duniyar ba, mene ne yake yi? Na so in san amsar.

ꞌYan watanni bayan hakan, sai na sami amsar. Kuma da shigewar lokaci, na haɗu da maza da mata da suka riƙe amincinsu ga Allah na gaskiya duk da matsaloli dabam-dabam da suke fuskanta.

AREWACIN IRELAND, “ƘASAR BAMA-BAMAI DA HARSASAI”

Saꞌad da na koma Landan, na haɗu da mamar abokina kuma ta ba ni Littafi Mai Tsarki. Daga baya, saꞌad da na je Amsterdam na ƙasar Nedalan, wani Mashaidi ya gan ni ina karanta littafin a ƙarƙashin fitilar da ke bakin titi, sai ya taimaka min in ƙara fahimtar abin da nake karantawa. Bayan haka, na yi tafiya zuwa Dublin na ƙasar Ireland, kuma na ga reshen ofishin Shaidun Jehobah. Na kwankwasa kofar ofishin. A wurin, na haɗu da ɗanꞌuwa Arthur Matthews. Ɗanꞌuwan yana da ƙwarewa da kuma hikima sosai. Na gaya masa ya yi nazarin Littafi Mai Tsarki da ni, kuma ya yarda ya yi hakan.

Na soma yin nazari da ƙwazo sosai, kuma ina marmarin karanta littattafai da mujallun da Shaidun Jehobah suka wallafa. Ƙari ga haka, na karanta Littafi Mai Tsarki da kaina. Na ji daɗin yin hakan sosai! A taron Shaidun Jehobah, na lura cewa yara suna amsa tambayoyin da mutane masu ilimi sun yi ɗarurruwan shekaru suna neman amsoshin su. Kamar: ‘Me ya sa ake mugunta? Wane ne Allah? Me yake faruwa da mutane bayan sun mutu?’ Dukan abokaina Shaidun Jehobah ne. Hakan ya yi min sauƙi domin ban waye kowa ba a duk faɗin ƙasar. Sun taimaka min in ƙaunaci Jehobah kuma in soma yin nufinsa.

Nigel, Denis, da ni

Na yi baftisma a 1972. Bayan shekara ɗaya, na soma yin hidimar majagaba, kuma na soma halartan taro da wata ƙaramar ikilisiya a Newry da ke Arewacin Ireland. Na yi hayar wani ƙaramin gida da aka yi da dutse a kan tudu. Akwai shanaye kusa da wurin, kuma nakan shirya jawabina a gabansu. Kamar dai suna sauraran abin da nake cewa yayin da suke cin abinci. Ba sa iya ba ni shawara, amma sun taimaka min in san yadda zan yi magana a gaban jamaꞌa. A 1974, na zama majagaba na musamman, kuma mun yi hidima tare da ɗanꞌuwa Nigel Pitt, wanda ya zama abokina na kud-da-kud.

A lokacin, ana yawan tashe-tashen hankula a Arewacin Ireland. Wasu sukan kira Arewacin Ireland “ƙasar bama-bamai da harsasai.” Akan yi faɗa a titi, da harbe-harben bindiga, da kuma datsa bam a motoci. Yawancin matsalolin da aka fuskanta a lokacin suna da alaƙa da siyasa da kuma addini. ꞌYan darikar Katolika da ma waɗanda ba Katolika ba sun san cewa babu ruwan Shaidun Jehobah da harkokin siyasa. Don haka, mukan yi waꞌazi ba tare da takura ba. Magidanta sukan san wurare da kuma lokacin da za a yi tashin hankali, kuma sukan gaya mana tun da wuri don mu guji wuraren.

Amma duk da hakan, mun fuskanci wasu yanayoyi masu haɗari sosai. Wata rana, ni da wani majagaba mai suna Denis Carrigan muna waꞌazi a wani ƙaramin gari da babu Shaidun Jehobah, kuma sau ɗaya muka taɓa zuwa wurin. Sai wata mata ta zarge mu cewa mu ꞌyan leƙen asiri na sojojin Birtaniya ne. Me yiwuwa domin ba ma magana da harshen Ireland. Hakan ya tsorata mu. Yin faraꞌa da sojoji kawai zai iya sa a kashe ka, ko kuma a harbe ka a gwiwa. Yayin da muke tsaye a waje mu kaɗai kuma ana sanyi, mun ga wata mota ta tsaya kusa da wani shago inda matar ta zarge mu. Matar ta fito daga shagon kuma ta soma nuna mu yayin da take magana da mutanen da ke motar. Sai mutanen suka zo inda muke kuma suka yi mana tambayoyi game da motar da za ta ɗauke mu. Saꞌad da motar ta isa, sai suka yi magana da direban. Ba mu ji abin da suka faɗa ba, kuma babu fasinjoji a motar. Don haka, mun san cewa suna shirya yadda za su je su ci zalin mu a bayan gari ne. Da na shiga motar, sai na tambayi direban: “Mutanen nan suna tambaya game da mu ne?” Sai ya ce: “Na san ku, kuma na gaya masu game da ku. Kada ku damu. Ba abin da zai same ku.”

Ranar aurenmu a Maris, 1977

A taron gunduma a da aka yi a 1976 a Dublin, na haɗu da Pauline Lomax, wata majagaba na musamman da ta zo daga ƙasar Ingila. Ita mace ce mai bangaskiya da sauƙin kai kuma tana da hankali. Ita da ƙaninta Ray sun koyi gaskiya tun suna yara. Bayan shekara ɗaya, ni da Pauline mun yi aure kuma mun ci gaba da yin hidimar majagaba na musamman a Ballymena, na Arewacin Ireland.

Mun yi hidimar mai kula da daꞌira na ɗan lokaci a Belfast a Londonderry, da kuma wasu wurare da ke da haɗari sosai. Bangaskiyarmu ta daɗa ƙarfi yayin da muka ga yadda ꞌyanꞌuwanmu suka yi watsi da koyarwar ƙarya da suka koya, da nuna bambanci, da kuma ƙiyayya don su bauta wa Jehobah. Jehobah ya albarkace su kuma ya kāre su!

Na yi shekaru goma a Ireland. A 1981, an gayyace mu zuwa aji na 72 na makarantar Gilead. Bayan mun sauƙe karatu, an tura mu hidima a ƙasar Saliyo da ke Yammancin Afirka.

ꞌYANꞌUWA A SALIYO SUNA DA BANGASKIYA DUK DA TALAUCI

Mun zauna a wani gida da masu waꞌazi a ƙasar waje suke zama tare da wasu ꞌyanꞌuwa guda 11. Dukanmu muna amfani da kicin guda ɗaya, da wurin bayan gida guda uku, da wurin wanka biyu, da wayar tarho guda ɗaya, da injin wanki guda ɗaya, da kuma na busar da kaya guda ɗaya. Ana yawan ɗauke wuta ba zato. Ɓeraye sukan shiga rufin gidan, macizai kuma sukan shiga ɗakin da ke ƙarƙashin ƙasa.

Muna tsallake kogi don mu halarci taron yanki a ƙasar Guinea

Ko da yake akwai matsaloli a inda muke zama, mun ji daɗin yin waꞌazi sosai. Mutane suna daraja Littafi Mai Tsarki kuma sukan saurare mu da kyau. Mun yi nazari da mutane da yawa kuma sun zama Shaidun Jehobah. Mutanen garin sukan kira ni “Malam Robert.” Sukan kira Pauline “Malama Robert.” Amma daga baya, saꞌad da ayyuka daga ofishinmu suka soma ci min lokaci kuma ba na yawan zuwa waꞌazi, mutanen sun soma kiran Pauline “Malama Pauline.” Ni kuma sun soma kirana “Malam Pauline.” Pauline ta ji daɗin hakan!

Za mu waꞌazi a ƙasar Saliyo

Yawancin ꞌyanꞌuwan talakawa ne, amma a kullum Jehobah yana tanada musu abubuwan da suke bukata, wasu lokuta ma a hanya mai ban mamaki. (Mat. 6:33) Na tuna wata ꞌyarꞌuwa da kuɗin sayan abincin yini na ranar kawai take da shi, amma ta ba ma wani ɗanꞌuwa da ba shi da kuɗin sayan maganin zazzaɓin cizon sauro. A ranar, wata mata ta zo wurin ꞌyarꞌuwar ba zato kuma ta biya ta kuɗi don ta yi mata kitso. Akwai misalai da yawa kamar hakan.

NA KOYI SABUWAR ALꞌADA A NAJERIYA

Mun yi shekaru tara a Saliyo. Sai aka mai da mu Bethel da ke Najeriya kuma ofishi ne da ke da girma sosai. Na ci gaba da yin aiki a ofishi kamar yadda na yi a ƙasar Saliyo. Amma an canja wa Pauline aikin da take yi kuma hakan bai yi mata sauƙi ba. A dā takan yi awoyi 130 tana waꞌazi kowace wata kuma tana da ɗaliban Littafi Mai Tsarki da suke samun ci gaba. Amma ta gano cewa mutane suna farin ciki domin aikin da take yi kuma ta mai da hankali wajen yin amfani da zarafin da take da shi don ta ƙarfafa wasu ꞌyanꞌuwa da ke hidima a Bethel.

Ba mu saba da alꞌadun Najeriya ba. Saboda haka, akwai abubuwa da yawa da muke bukatar mu koya. Akwai lokacin da wani ɗanꞌuwa ya zo ofishina don ya gabatar da wata ꞌyarꞌuwa da ba ta jima da zuwa Bethel ba. Da na so in sha hannu da ita, sai ta rusuna a gabana. Na yi mamaki sosai! Nan da nan, sai na tuna da Nassosi guda biyu a Littafi Mai Tsarki, Ayyukan Manzanni 10:​25, 26 da Ruꞌuyar da Aka Yi wa Yohanna 19:10. Na yi tunani ko in gaya mata kada ta yi hakan. Amma sai na tuna cewa an gayyace ta Bethel, hakan yana nufin cewa ta san koyarwar Littafi Mai Tsarki.

Na ji kunya a tsawon lokacin da muka ɗauka muna tattaunawa. Amma daga baya, sai na yi bincike. Na gano cewa ꞌyarꞌuwar tana bin wata alꞌada ce da a lokacin ake bi a wasu sassan ƙasar. Maza ma sukan rusuna kamar yadda ta yi. Hanya ce da suke girmama mutane ba wai suna bauta musu ba ne. Littafi Mai Tsarki ya ba da misalai kamar haka. (1 Sam. 24:8) Na yi farin ciki cewa ban faɗi abin da zai kunyatar da ꞌyarꞌuwata a cikin rashin sani ba.

Mun haɗu da ꞌyanꞌuwa da yawa a Najeriya da suka yi shekaru suna nuna bangaskiya. Ka yi laꞌakari da labarin Isaiah Adagbona. b Ya koyi gaskiya saꞌad da yake matashi, amma daga baya sai ya kamu da ciwon kuturta. An kai shi asibitin kutare kuma shi kaɗai ne Mashaidin Jehobah a wurin. Duk da hamayya da aka nuna masa, ya taimaka wa kutare fiye da 30 su koya gaskiya kuma ya kafa ikilisiya a asibitin.

ꞌYANꞌUWA A KENYA SUN YI HAƘURI DA NI

Tare da marayan karkanda a Kenya

A 1996, an kai mu ofishinmu da ke Kenya. Wannan ne karo na farko da na sake koma ƙasar tun da na je ƙasar kamar yadda na ambata daga farko. Mun zauna a Bethel. Akwai biraye da yawa a ofishin. Sukan sace ꞌyaꞌyan itace daga wurin ꞌyanꞌuwa mata da ke ɗauke da su. Wata rana, wata ꞌyarꞌuwa a Bethel ta bar wundonta a buɗe. Da ta dawo, sai ta ga biri da yawa suna cin abincin da suka samu a ɗakinta. Sai ta yi ihu kuma ta fita da gudu. Birayen sun yi ihu kuma suka yi tsalle suka fita.

Ni da Pauline mun soma halartan taro a ikilisiyar da ake yaren Swahili. Jim kaɗan, sai aka naɗa ni mai Gudanar da Nazarin Littafi Na Ikilisiya, wanda yanzu ake kira Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya. Amma ban iya yaren sosai ba. Nakan yi nazarin littafin tun da wuri don in iya karanta tambayoyin. Amma idan ꞌyanꞌuwa suka ba da kalami dabam da abin da aka rubuta, ba na iya ganewa. Ban ji daɗin hakan ba kuma na tausaya ma ꞌyanꞌuwan. Yadda suka amince in ci gaba da gudanar da nazarin littafin ya burge ni sosai.

ꞌYANꞌUWA A AMIRKA SUNA NUNA BANGASKIYA DUK DA WADATARSU

Ba mu kai shekara ɗaya a Kenya ba. Sai aka gayyace mu zuwa Bethel na Brooklyn a Jihar New York, a 1997. A yanzu, muna ƙasar da mutane suke da wadata sosai kuma hakan ma yana jawo ƙalubale. (K. Mag. 30:​8, 9) Amma duk da hakan, ꞌyanꞌuwa a ƙasar suna da bangaskiya sosai. ꞌYanꞌuwan suna amfani da lokacinsu da kuma abubuwan da suke da shi ba don su tara wa kansu wadata ba amma don su goyi bayan aiki mai muhimmanci da ƙungiyar Jehobah take yi.

A waɗannan shekaru, mun ga yadda ꞌyanꞌuwanmu suka nuna bangaskiya a yanayoyi dabam-dabam da suka fuskanta. A ƙasar Ireland, ꞌyanꞌuwa sun nuna bangaskiya duk da tashe-tashen hankula. A Afirka, ꞌyanꞌuwa sun nuna bangaskiya duk da talauci da kuma zama a wuraren da babu Shaidu. A ƙasar Amirka, ꞌyanꞌuwa sun nuna bangaskiya duk da cewa suna da wadata. Babu shakka, Jehobah yana farin ciki yayin da yake ganin bayinsa suna nuna bangaskiya a yanayoyi dabam-dabam da suke fuskanta.

Tare da Pauline a Bethel da ke Warwick

Lokaci ya wuce da sauri “kamar zaren saƙa a hannun gwani.” (Ayu. 7:6) A yanzu muna aiki da ꞌyanꞌuwa a hedkwatarmu da ke Warwick na jihar New York kuma muna jin daɗin yin aiki da mutanen da suke ƙaunar juna. Muna farin ciki kuma mun gamsu da ɗan abin da muke yi don mu goyi bayan Sarkinmu Yesu Kristi, wanda nan ba da daɗewa ba zai albarkaci mutane masu bangaskiya.​—Mat. 25:34.

a A lokacin, ana kiran taron yanki taron gunduma.

b An wallafa labarin Isaiah Adagbona a Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Afrilu, 1998 shafuffuka na 22-27, a Turanci. Ya mutu a 2010.