Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 3

Darussan da Za Mu Iya Koya Daga Hawayen Yesu

Darussan da Za Mu Iya Koya Daga Hawayen Yesu

“Yesu ya yi hawaye.”​—YOH. 11:35.

WAƘA TA 17 “Na Yarda”

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1-3. Waɗanne abubuwa ne za su iya sa bayin Jehobah su zub da hawaye?

KA TUNA lokaci na ƙarshe da ka zub da hawaye? A wasu lokuta, mukan zub da hawaye saboda murna. Amma a yawancin lokaci mukan yi kuka saboda baƙin ciki. Alal misali, mukan yi kuka sa’ad da aka yi mana rasuwa. Wata ’yar’uwa mai suna Lorilei da ke zama a ƙasar Amirka ta ce: “Akwai lokutan da na yi baƙin ciki sosai saboda mutuwar ’yata, har na ji kamar ba zan daina baƙin ciki ba, kuma na ɗauka cewa ba zan iya jimre yanayin ba.” *

2 Akwai wasu abubuwa kuma da za su iya sa mu zub da hawaye. Wata ’yar’uwa mai suna Hiromi da ke hidimar majagaba a Jafan ta ce: “Nakan yi sanyin gwiwa domin yadda mutane sukan nuna mini halin ko-in-kula a wa’azi. A wasu lokuta, nakan zub da hawaye ina roƙon Jehobah ya taimaka mini in haɗu da mutumin da zai saurari wa’azina.”

3 Shin a wasu lokuta kai ma kakan ji kamar ’yan’uwan nan? Yawancinmu mukan ji hakan. (1 Bit. 5:9) Muna so mu ci gaba da yi wa Jehobah “hidima da murna!” Amma a wasu lokuta mukan yi kuka don an yi mana rasuwa, ko don muna baƙin ciki, ko kuma domin muna fuskantar matsaloli da suke jarraba amincinmu ga Jehobah. (Zab. 6:6; 100:2) Me za mu iya yi don mu iya jimrewa?

4. Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?

4 Za mu iya koyan darussa daga wurin Yesu. Akwai lokutan da shi ma ya yi baƙin ciki sosai har ‘ya zub da hawaye.’ (Yoh. 11:35; Luk. 19:41; 22:44; Ibran. 5:7) Bari mu tattauna hakan. Yayin da muke tattaunawa, za mu ga darussan da za mu iya koya. Za mu kuma tattauna abubuwan da za mu iya yi don mu jimre yanayoyin da za su sa mu zub da hawaye.

YESU YA YI KUKA DON ABOKANSA

Ka taimaki waɗanda suke makoki kamar yadda Yesu ya yi (Ka duba sakin layi na 5-9) *

5. Bisa ga abin da ke Yohanna 11:​32-36, mene ne muka koya daga abin da Yesu ya yi?

5 A lokacin ɗari na shekara ta 32, abokin Yesu Li’azaru ya yi rashin lafiya kuma ya mutu. (Yoh. 11:​3, 14) Li’azaru yana da ’yan’uwa mata guda biyu, wato Maryamu da kuma Marta, kuma Yesu yana ƙaunar wannan iyalin sosai. Matan nan sun yi baƙin ciki sosai domin rasuwar ɗan’uwansu. Bayan Li’azaru ya rasu, Yesu ya yi tafiya zuwa ƙauyen Betani inda Marta da Maryamu suke zama. Da Marta ta ji cewa Yesu yana zuwa, sai ta fita a guje don ta marabce shi. Ka yi tunanin yadda take baƙin ciki yayin da take cewa: “Ubangiji, ai, da kana nan da ɗan’uwana bai mutu ba.” (Yoh. 11:21) Jim kaɗan bayan haka, sa’ad da Yesu ya ga Maryamu da sauran mutane suna kuka, sai shi ma “ya yi hawaye.”​—Karanta Yohanna 11:​32-36.

6. Me ya sa Yesu ya yi kuka a wannan lokacin?

6 Me ya sa Yesu ya zub da hawaye a wannan lokacin? Littafin nan Insight on the Scriptures ya ba da amsar. Ya ce: “Mutuwar Li’azaru da kuma baƙin cikin da ’yan’uwan Li’azaru suka yi sun dami Yesu a zuciya kuma sun sa ‘ya yi hawaye.’ ” * Mai yiwuwa Yesu ya yi tunani a kan zafin da Li’azaru ya ji sa’ad da yake rashin lafiya, da kuma irin baƙin cikin da mutumin ya yi sa’ad da ya ga cewa ba zai rayu ba. Wani abu kuma da ya sa Yesu zub da hawaye shi ne yadda ya ga Maryamu da Marta suke baƙin ciki domin mutuwar ɗan’uwansu. Idan abokinka ko wani a iyalinku ya rasu, ba shakka kai ma ka yi baƙin ciki kamar haka. Ka lura da darussa guda uku da za ka iya koya daga wannan labarin.

7. Mene ne muka koya game da Jehobah daga yadda Yesu ya zub da hawaye?

7Jehobah ya san yadda kake ji. Yesu shi ne “ainihin kamannin Allah.” (Ibran. 1:3) Sa’ad da Yesu ya yi hawaye, ya nuna yadda Ubansa yake ji ne. (Yoh. 14:9) Idan kana baƙin ciki don wani ya rasu, ka tabbata cewa Jehobah ya san yadda kake ji kuma ya damu da kai sosai. Yana so ya yi maka ta’aziyya kuma ya ƙarfafa ka.​—Zab. 34:18; 147:3.

8. Me ya sa za mu iya kasancewa da tabbaci cewa Yesu zai iya tā da ’yan’uwanmu da suka rasu?

8Yesu yana marmarin tā da ƙaunatattunka da suka rasu. Jim kaɗan kafin Yesu ya zub da hawaye, ya tabbatar wa Marta cewa: “Ɗan’uwanki zai tashi.” Marta ta gaskata da abin da Yesu ya faɗa. (Yoh. 11:​23-27) Da yake Marta tana bauta ma Jehobah da aminci, ba mamaki ta san yadda Iliya da Elisha suka tā da mutane daga mutuwa shekaru da yawa kafin a haife ta. (1 Sar. 17:​17-24; 2 Sar. 4:​32-37) Kuma babu mamaki ta ji labarin mutanen da Yesu ya tā da su daga mutuwa. (Luk. 7:​11-15; 8:​41, 42, 49-56) Kai ma za ka iya kasancewa da tabbaci cewa za ka ga ’yan’uwanka da suka rasu. Yadda Yesu ya zub da hawaye yayin da yake ta’azantar da abokansa, ya nuna mana cewa yana marmarin tā da abokansa da suka mutu!

9. Ta yaya za ka taimaka ma waɗanda ke baƙin ciki kamar yadda Yesu ya yi? Ka ba da misali.

9Za ka iya taimaka ma waɗanda suke baƙin ciki. Yesu bai yi kuka kawai tare da Marta da Maryamu ba, amma ya saurare su kuma ya ƙarfafa su. Mu ma za mu iya yin hakan ga waɗanda suke baƙin ciki. Wani dattijo mai suna Dan a Ostareliya ya ce: “Bayan rasuwar matata, na bukaci taimako sosai. ’Yan’uwa ma’aurata da yawa sun kasance tare da ni dare da rana don su saurare ni. Sun bar ni in faɗi yadda nake ji kuma ba su ji kunya sa’ad da nake kuka ba. Sun kuma taimaka mini a hanyoyi dabam-dabam, kamar taya ni wanke motata da taya ni cefane, da kuma dafa abinci a lokutan da na kasa yin hakan. Ƙari ga haka, sukan yi addu’a tare da ni. Sun nuna mini cewa su abokaina ne na ƙwarai, da ’yan’uwa da ke ba da ‘taimako a kwanakin masifa.’ ”​—K. Mag. 17:17.

YESU YA ZUB DA HAWAYE DON MAƘWABTANSA

10. Ka bayyana labarin da ke Luka 19:​36-40.

10 Yesu ya isa Urushalima a ranar 9 ga Nisan na shekara ta 33. Yayin da yake kusa da birnin, mutane da yawa sun taru kuma suka shimfiɗa rigunansu don ya yi tafiya a kai domin su nuna cewa sun amince da shi a matsayin sarkinsu. Babu shakka wannan ranar murna ce. (Karanta Luka 19:​36-40.) Don haka, manzanninsa ba su yi zaton abin da ya faru bayan hakan ba. “Da [Yesu] ya zo kurkusa, ya ga birnin Urushalima, sai ya yi mata kuka.” Yesu ya yi hawaye sa’ad da yake annabta masifar da za ta auko ma Urushalima.​—Luk. 19:​41-44.

11. Me ya sa Yesu ya yi hawaye domin mazaunan Urushalima?

11 Yesu ya yi baƙin ciki sosai domin duk da cewa mutane sun marabce shi da kyau, ya san cewa mafi yawan Yahudawa za su ƙi amincewa da saƙon Mulkin Allah. Hakan zai sa a hallaka Urushalima, kuma duk wani Bayahuden da ba a kashe shi a lokacin ba, za a kai shi bauta. (Luk. 21:​20-24) Abin baƙin ciki ne cewa mutane da yawa sun ƙi Yesu kamar yadda ya faɗa cewa za a ƙi shi. Mene ne yawancin mutane suke yi a yankinku yayin da kuke yi musu wa’azi? Idan mutane kaɗan ne suke saurarar wa’azinku, mene ne za ku iya koya daga hawaye da Yesu ya yi? Ku yi la’akari da darussa guda uku da za mu tattauna yanzu.

12. Me za mu iya koya game da Jehobah daga yadda Yesu ya yi hawaye domin mutane?

12Jehobah ya damu da mutane. Yadda Yesu ya yi hawaye ya nuna mana yadda Jehobah yake damuwa da mutane. “Ba ya so wani ya halaka, sai dai kowa ya zo ya tuba.” (2 Bit. 3:9) A yau, za mu iya nuna cewa muna ƙaunar mutanen da muke yi musu wa’azi ta wajen yin iya ƙoƙarinmu don mu koya musu saƙon Mulkin Allah.​—Mat. 22:39. *

Ka ziyarci mutane a lokacin da za ka same su kamar yadda Yesu ya yi (Ka duba sakin layi na 13-14) *

13-14. Ta yaya Yesu ya ji tausayin mutane, kuma ta yaya mu ma za mu iya yin hakan?

13Yesu ya yi wa’azi da ƙwazo sosai. Ya nuna wa mutane ƙauna ta wajen koyar da su a duk lokacin da ya sami zarafi. (Luk. 19:​47, 48) Me ya sa Yesu ya yi hakan? Ya yi hakan ne domin ya ji tausayin su. Akwai lokutan da mutane da yawa suka taru don Yesu ya koyar da su, “har shi da almajiransa ba su iya cin abinci ba.” (Mar. 3:20) Ya ma yarda ya koyar da wani ɗalibinsa da dare, domin lokacin da ya fi dacewa da ɗalibin ke nan. (Yoh. 3:​1, 2) Yawancin mutane da suka saurari Yesu da farko ba su zama almajiransa ba. Amma ya koyar da dukan waɗanda suka saurare shi da kyau. A yau, mu ma muna so mu ba wa kowa zarafin koya game da Jehobah. (A. M. 10:42) Mai yiwuwa za mu bukaci mu canja yadda muke yin wa’azi don mu iya yin hakan.

14Ka kasance a shirye don yin wasu canje-canje. Idan ba ma zuwa wa’azi a lokuta dabam-dabam, mai yiwuwa ba za mu sami waɗanda za su so su saurari wa’azinmu ba. Wata ’yar’uwa mai suna Matilda ta ce: “Ni da maigidana mukan je wa’azi a lokuta dabam-dabam. Da safe mukan yi wa’azi a wuraren kasuwanci, da rana kuma mukan yi wa’azi da amalanke domin a lokacin ne mutane da yawa suke wucewa. Da yamma kuma mukan sami mutane sosai a gida.” A maimakon mu nace da zuwa wa’azi a lokacin da muka fi so, zai dace mu canja lokutan da muke zuwa wa’azi don mu iya samun mutane. Idan mun yi hakan, za mu iya tabbata cewa Jehobah zai yi farin ciki da mu.

YESU YA ZUB DA HAWAYE DOMIN SUNAN UBANSA

Ka yi addu’a ga Jehobah a lokacin da kake cikin damuwa kamar yadda Yesu ya yi (Ka duba sakin layi na 15-17) *

15. Bisa ga Luka 22:​39-44, mene ne ya faru a dare na ƙarshe kafin Yesu ya mutu?

15 A daren 14 ga Nisan na shekara ta 33, Yesu ya je lambun Getsemani. A wurin, ya yi addu’a ga Jehobah da dukan zuciyarsa. (Karanta Luka 22:​39-44.) A wannan lokacin ne “ya miƙa addu’o’i . . . tare da kuka mai tsanani da hawaye.” (Ibran. 5:7) A kan me Yesu ya yi addu’a a dare na ƙarshe kafin mutuwarsa? Ya roƙi Jehobah ya ƙarfafa shi domin ya iya riƙe amincinsa kuma ya yi nufin Allah. Jehobah ya ji addu’ar Ɗansa, kuma ya aiki mala’ikansa ya ƙarfafa shi.

16. Me ya sa Yesu ya yi baƙin ciki sosai sa’ad da yake addu’a a lambun Getsemani?

16 Yesu ya yi kuka a lambun Getsemani sa’ad da yake addu’a domin yana baƙin ciki cewa mutane za su ɗauke shi a matsayin mai saɓo. Ya kuma san cewa yana da muhimmanci ya riƙe amincinsa don ya wanke sunan Ubansa daga zargi. Idan kana fuskantar yanayi da ke gwada amincinka, wane darasi ne za ka iya koya daga yadda Yesu ya zub da hawaye? Ka yi la’akari da darussa uku da za mu koya yanzu.

17. Me za mu iya koya game da Jehobah daga yadda ya amsa addu’ar Yesu?

17Jehobah yana jin addu’o’inka. Jehobah ya ji addu’ar Yesu. Me ya sa? Domin abin da Yesu ya mai da hankali a kai shi ne yadda zai kasance da aminci ga Jehobah kuma ya wanke sunansa daga zargi. Idan mun fi mai da hankali ga yadda za mu kasance da aminci ga Jehobah kuma mu wanke sunansa daga zargi, Jehobah zai amsa addu’armu.​—Zab. 145:​18, 19.

18. A wace hanya ce Yesu yake kamar abokin kirki da ya san yanayinmu?

18Yesu ya san yadda muke ji. Za mu yi farin ciki idan muna da abokin da ya san yadda muke ji, musamman ma wanda ya taba shiga irin yanayin da muke ciki. Yesu yana kamar wannan abokin. Shi ma akwai lokacin da ya yi baƙin ciki kuma ya bukaci taimako. Ya san yanayinmu, kuma zai yi ƙoƙari ya ga cewa mun sami taimakon da muke bukata a lokacin da ya dace. (Ibran. 4:​15, 16) Kamar yadda Yesu ya yarda mala’ika ya taimaka masa a lambun Getsemani, mu ma ya kamata mu karɓi taimakon da Jehobah yake yi mana, ko da ya yi hakan ta wajen littattafanmu ne ko bidiyo ko jawabi ko kuma ziyarar ƙarfafa daga wani dattijo ko kuma wani ɗan’uwa da ya manyanta.

19. Ta yaya za ka sami ƙarfafa idan ka shiga yanayin da ke jarraba amincinka ga Jehobah? Ka ba da misali.

19Jehobah zai ba mu salamarsa. Ta yaya Jehobah zai ƙarfafa mu? Idan muka yi addu’a, za mu sami salamar Allah “wadda ta wuce dukan ganewar ɗan Adam.” (Filib. 4:​6, 7) Salamar Allah za ta taimaka mana mu natsu, kuma mu yi tunani da kyau. Ka yi la’akari da yadda salamar Allah ta taimaka ma wata ’yar’uwa mai suna Luz. Ta ce: “Na yi fama da kaɗaici. A wasu lokuta hakan yana sa in ji kamar Jehobah ba ya ƙauna ta. Amma a duk lokacin da na ji hakan, sai in gaya wa Jehobah yadda nake ji nan da nan. Yin addu’a yana sa in sami sauƙi.” Kamar yadda labarinta ya nuna, za mu iya samun salama ta wurin yin addu’a.

20. Waɗanne darussa ne muka koya daga yadda Yesu ya zub da hawaye?

20 Hakika mun koyi darussa masu ban ƙarfafa daga yadda Yesu ya zub da hawaye! An tuna mana cewa mu riƙa ƙarfafa ’yan’uwanmu da suke makoki, kuma mu tabbata cewa Jehobah da Yesu za su taimaka mana idan wani namu ya rasu. An ƙarfafa mu cewa mu riƙa tausaya wa mutane yayin da muke yi musu wa’azi da kuma koyar da su, domin Jehobah da Yesu ma suna nuna wannan hali mai kyau. Sanin cewa Jehobah da Ɗansa sun san yadda muke ji, suna tausaya mana saboda baƙin cikin da muke yi, kuma suna taimaka mana mu jimre yana ƙarfafa mu. Bari dukanmu mu ci gaba da yin abubuwan da muka koya, har sai lokacin da Jehobah ya cika alkawarin da ya yi cewa zai share ‘hawaye daga idanunmu’!​—R. Yar. 21:4.

WAƘA TA 120 Mu Koyi Nuna Sauƙin Kai Kamar Yesu

^ sakin layi na 5 Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa akwai wasu lokuta da Yesu ya zub da hawaye. A wannan talifin, za mu tattauna lokuta uku da Yesu ya zub da hawaye da kuma darussan da za mu iya koya daga hakan.

^ sakin layi na 1 An canja wasu sunayen.

^ sakin layi na 12 A yaren Helenanci, kalmar nan ‘maƙwabcinka’ da ke Matiyu 22:39 ba ta nufin mutane da suke zama kusa da mu kawai. Amma tana nufin duk wani da muka sani.

^ sakin layi na 58 BAYANI A KAN HOTO: Tausayi ya sa Yesu ya ta’azantar da Maryamu da Marta. Mu ma za mu iya ta’azantar da ’yan’uwanmu da suke makoki.

^ sakin layi na 60 BAYANI A KAN HOTO: Da son ran Yesu ya koyar da Nikodimus da dare. Mu yi nazari da mutane a lokacin da suka fi so.

^ sakin layi na 62 BAYANI A KAN HOTO: Yesu ya roƙi Jehobah ya taimaka masa ya riƙe amincinsa. Abin da ya kamata mu ma mu yi ke nan idan ana jarraba mu.