Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 5

Ku Yi Amfani da Lokacinku da Kyau

Ku Yi Amfani da Lokacinku da Kyau

“Ku mai da hankali ƙwarai ga zamanku. Kada ku zama kamar wawaye, sai dai kamar masu hikima. Ku yi amfani da kowane zarafi na yin kirki.”​—AFIS. 5:​15, 16.

WAƘA TA 8 Jehobah Ne Mafakarmu

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1. Ta yaya za mu iya kasancewa tare da Jehobah?

MUNA jin daɗin kasancewa da mutanen da muke ƙauna. Ma’aurata suna jin daɗin kasancewa tare da juna. Matasa ma suna jin daɗin kasancewa tare da abokansu, kuma dukanmu muna jin daɗin kasancewa da ’yan’uwanmu masu bi. Amma dukanmu mun fi jin daɗin kasancewa tare da Ubanmu na sama Jehobah. Za mu iya yin hakan ta wajen yin addu’a gare shi, da karanta Kalmarsa Littafi Mai Tsarki da yin tunani a kan nufinsa da kuma halayensa masu kyau. Lokacin da muke amfani da shi don mu kasance tare da Jehobah yana da muhimmanci sosai!​—Zab. 139:17.

2. Waɗanne ƙalubale ne muke fuskanta?

2 Ko da yake muna jin daɗin yin addu’a da karanta Littafi Mai Tsarki, a wasu lokuta yin hakan zai yi mana wuya. Da yake muna da ayyukan yi da yawa, za mu iya rasa lokacin yin ayyukan ibada. Aikinmu da iyalinmu da kuma wasu ayyuka da muke bukatar mu yi, za su iya ɗaukan lokacinmu sosai, kuma su sa mu ji kamar ba mu da lokacin yin addu’a da nazari da kuma yin bimbini a kan abin da muka karanta.

3. Wane abu ne kuma zai iya cin lokacinmu?

3 Akwai wani abu kuma da zai iya cin lokacinmu. Idan ba mu yi hankali ba, za mu iya barin wasu ayyuka da yin su ba laifi ba ne su hana mu yin ayyukan ibada. Alal misali, yin nishaɗi yana da kyau. Amma idan muna ɓata lokaci da yawa a yin sa, za mu rasa lokacin yin ayyukan ibada. Muna bukatar mu riƙa tuna cewa nishaɗi ba shi ne abu mafi muhimmanci ba.​—K. Mag. 25:27; 1 Tim. 4:8.

4. Me za mu tattauna yanzu?

4 A wannan talifin, za mu tattauna dalilin da ya sa ya dace mu san abin da ya fi muhimmanci a rayuwarmu. Za mu kuma tattauna yadda za mu yi amfani da lokacinmu da kyau don ibada, da kuma yadda za mu amfana idan muka yi hakan.

KA YANKE SHAWARWARI MASU KYAU; KA SAN ABIN DA YA FI MUHIMMANCI

5. Ta yaya bincika gargaɗin da ke Afisawa 5:​15-17 zai taimaka wa matashi ya yi zaɓi mafi kyau?

5Ka zaɓi rayuwa mafi kyau. Matasa sukan damu a kan abin da za su yi da rayuwarsu. Malaman makarantarsu da iyalansu da ba Shaidu ba, za su iya matsa musu su je makarantar jami’a don su iya samun aikin da za a biya su albashi mai tsoka. Irin makarantar nan za ta ɗauki lokacinsu sosai. A wani ɓangaren kuma, iyaye da kuma abokan arziki a ikilisiya za su iya ƙarfafa matasa su yi amfani da rayuwarsu su bauta wa Jehobah. Me zai taimaka wa matashin da ke ƙaunar Jehobah ya yi zaɓin da ya fi dacewa? Karanta da kuma yin bimbini a kan Afisawa 5:​15-17 zai taimaka masa. (Karanta.) Bayan ya gama karanta nassin, matashin zai iya tambayar kansa: ‘Mene ne nufin Jehobah? Wace shawara ce za ta faranta masa rai? Wace shawara ce za ta sa in yi amfani da lokacina a hanyar da ta fi dacewa?’ Ka tuna cewa kwanakin da “muke ciki yanzu mugaye ne,” kuma nan ba da jimawa ba za a hallaka wannan duniyar da ke ƙarƙashin ikon Shaiɗan. Don haka, zai dace mu yi amfani da lokacinmu don mu yi abin da zai sa Jehobah farin ciki.

6. Wane zaɓi ne Maryamu ta yi kuma me ya sa zaɓin ya dace?

6Ka sa abin da ya fi muhimmanci farko a rayuwa. A wasu lokuta, za mu bukaci mu zaɓa tsakanin abubuwa biyu da yin su ba laifi ba ne. Abin da ya faru sa’ad da Yesu ya ziyarci Marta da Maryamu ya nuna hakan. Babu shakka, Marta ta yi farin ciki da Yesu ya ziyarci gidansu, shi ya sa ta shirya masa babban liyafa. Amma ’yar’uwarta Maryamu ta yi amfani da wannan damar ta zauna kusa da Yesu don ta saurari koyarwarsa. Abin da Marta ta yi ba laifi ba ne, amma Maryamu “ta zaɓi abu [mafi] kyau.” (Luk. 10:​38-42) Mai yiwuwa da shigewar lokaci, Maryamu ta manta da abincin da Marta ta dafa a ranar, amma mun tabbata cewa ba ta manta da abin da ta koya daga wurin Yesu ba. Kamar yadda Maryamu ta ɗauki lokacin da ta kasance da Yesu da muhimmanci, mu ma muna ɗaukan lokacin yin ibada da muhimmanci sosai. Ta yaya za mu iya amfani da lokacin da kyau?

KA MAI DA HANKALI YAYIN DA KAKE AYYUKAN IBADA

7. Me ya sa muke bukatar mu keɓe lokaci don yin addu’a da nazari da kuma bimbini?

7Ka san cewa yin addu’a da nazari da kuma bimbini a kan abin da muka karanta ibada ne. Idan muna yin addu’a, muna tattaunawa ne da Ubanmu na sama da ke ƙaunar mu sosai. (Zab. 5:7) A duk lokacin da muke nazari, muna ‘samun sanin Allah’ ne wanda shi ne mafi hikima. (K. Mag. 2:​1-5) Yayin da muke bimbini kuma, muna tunani ne a kan halayen Jehobah masu kyau, kuma muna tuna da abubuwa masu kyau da yake shirin yi mana da ’yan Adam. Babu shakka wannan ne hanya mafi kyau da za mu iya amfani da lokacinmu. Amma mene ne zai taimaka mana mu iya yin hakan?

Za ka iya neman wurin da babu surutu don ka yi nazari kai kaɗai? (Ka duba sakin layi na 8-9)

8. Wane darasi ne za mu iya koya game da yadda Yesu ya yi amfani da lokacinsa a cikin daji?

8Idan zai yiwu, ka nemi wurin da babu surutu. Ka yi la’akari da misalin Yesu. Kafin ya soma hidimarsa a duniya, Yesu ya yi kwanaki 40 a cikin daji. (Luk. 4:​1, 2) A wannan wurin da babu surutu, Yesu ya yi addu’a ga Jehobah kuma ya yi bimbini a kan abin da Jehobah yake so ya yi. Hakan ya taimaka wa Yesu ya shirya kansa don abubuwan da zai fuskanta a nan gaba. Ta yaya za ka yi koyi da misalin Yesu? Idan akwai mutane da yawa a cikin gidanku, wataƙila zai iya yi maka wuya ka sami wurin da babu surutu. Idan haka ne, ka nemi wurin da babu surutu a waje. Abin da wata ’yar’uwa mai suna Julie take yi ke nan a duk lokacin da take so ta yi addu’a ga Jehobah. Ita da mijinta suna zama a Faransa kuma ɗaki ɗaya kawai suke da shi, don haka samun wurin da babu surutu yakan yi mata wuya. Julie ta bayyana cewa: “Nakan je zagaya a wurin shaƙatawa kullum. A wurin, ina samun damar kasancewa ni kaɗai kuma in mai da hankali wajen tattaunawa da Jehobah.”

9. Duk da cewa Yesu yana da abubuwan yi da yawa, ta yaya ya nuna cewa yana ɗaukan dangantakarsa da Jehobah da muhimmanci?

9 A lokacin da Yesu yake duniya, yana da abubuwan yi da yawa. Mutane sukan bi shi duk inda ya je, kuma dukansu sun so ya ba su lokacinsa. Akwai wata rana da ‘dukan mutanen gari suka taru a ƙofar gidan’ da yake don su saurare shi. Duk da haka, Yesu ya keɓe lokaci don ya kasance tare da Jehobah. Da sassafe, Yesu ya nemi “wani wuri inda ba kowa” don ya yi magana da Ubansa.​—Mar. 1:​32-35.

10-11. Bisa ga Matiyu 26:​40, 41, wane gargaɗi mai kyau ne Yesu ya ba manzanninsa, amma mene ne ya faru?

10 A dare na ƙarshe kafin mutuwarsa, Yesu ya sake neman wani wuri inda babu kowa domin ya yi addu’a da kuma bimbini. Wurin da ya samu shi ne lambun Getsemani. (Mat. 26:36) A ranar, Yesu ya yi wa manzanninsa gargaɗi game da yin addu’a.

11 Ka yi la’akari da abin da ya faru. Da suka isa lambun Getsemani, dare ya riga ya yi, mai yiwuwa da tsakar dare suka isa. Yesu ya gaya wa manzanninsa cewa su yi ‘tsaro tare da shi,’ sai ya je shi kaɗai ya yi addu’a. (Mat. 26:​37-39) Amma sa’ad da yake addu’a, sai barci ya kama su. Da ya dawo ya same su suna barci, sai ya sake gaya musu cewa ‘su yi tsaro, su kuma yi addu’a.’ (Karanta Matiyu 26:​40, 41.) Yesu ya fahimci cewa sun damu sosai kuma sun gaji. Shi ya sa ya tausaya musu kuma ya ce “jikin ba ƙarfi.” Bayan haka, Yesu ya sake tafiya ya yi addu’a har sau biyu, kuma da ya dawo, ya sami manzanninsa suna barci maimakon su yi addu’a.​—Mat. 26:​42-45.

Za ka iya keɓe lokacin yin addu’a a lokacin da ba ka gaji sosai ba? (Ka duba sakin layi na 12)

12. Me za mu iya yi idan a wasu lokuta ba ma iya yin addu’a saboda damuwa ko kuma gajiya?

12Ka zaɓi lokacin da ya dace. A wasu lokuta mukan gaji sosai har mu ji kamar ba za mu iya yin addu’a ba. Idan hakan ya taɓa faruwa da kai, ka san cewa wasu ma sun taɓa fuskantar yanayin. Me za ka yi? Wasu ’yan’uwa da sun saba yin addu’a ga Jehobah da dare sun lura cewa ya fi musu sauƙi su yi addu’a da ɗan yamma domin a lokacin ba su gaji sosai ba. Wasu kuma sun lura cewa yadda suke yayin da suke yin addu’a yana taimaka musu, alal misali idan suna zaune ko kuma a tsugune. To me zai faru idan ka kasa yin addu’a saboda sanyin gwiwa ko kuma saboda yawan damuwa? Ka gaya wa Jehobah yadda kake ji. Ka tabbata cewa Jehobah Allahnmu mai jinƙai zai fahimci yanayinka.​—Zab. 139:4.

Ka yi ƙoƙari don kada ka amsa saƙonnin tes da imel yayin da kake taro (Ka duba sakin layi na 13-14)

13. Ta yaya na’urorinmu za su iya raba hankalinmu yayin da muke nazari ko addu’a ko kuma muke taro?

13Ka guji abubuwan da za su raba hankalinka yayin da kake yin nazari. Ba ta yin addu’a ne kaɗai za mu iya ƙarfafa dangantakarmu da Jehobah ba. Za mu iya yin hakan ta wajen yin nazarin Kalmar Allah da kuma halartan taro. Shin akwai abin da ya kamata ka yi don kada wani abu ya raba hankalinka yayin da kake nazari ko kuma kake taro? Ka yi wa kanka tambayoyin nan, ‘Wane abu ne yakan raba hankalina yayin da nake nazari ko kuma nake a taro?’ Shin saƙonnin da ake tura mini ta imel ko tes ko kuma kira suna raba hankalina? A yau, biliyoyin mutane suna da na’urori masu amfani, wasu masu bincike sun ce, idan muna so mu mai da hankali ga abin da muke yi, ganin waya kusa da mu kawai zai iya hana mu yin hakan. Wani ƙwararre ya ce, “Ba za ka iya mai da hankali ga abin da ake yi ba don hankalinka zai rabu.” Kafin taron yanki da taron da’ira, akan gaya mana mu saita wayarmu yadda ba za ta dami wasu ba. Zai yi kyau mu yi hakan ma yayin da muke nazari ko addu’a ko kuma muke taro, don kada na’urorinmu su dame mu ko su raba hankalinmu.

14. Kamar yadda Filibiyawa 4:​6, 7 suka nuna, ta yaya Jehobah zai taimaka mana mu tattara hankalinmu wuri ɗaya?

14Ka roƙi Jehobah ya taimaka maka ka tattara hankalinka wuri ɗaya. Idan ka lura cewa wasu abubuwa suna raba hankalinka yayin da kake nazari ko kuma kake taro, ka roƙi Jehobah ya taimaka maka. Idan kana cikin damuwa, zai iya yi maka wuya ka mai da hankali yayin da kake karanta Kalmar Allah. Amma yana da muhimmanci ka yi hakan. Ka roƙi Jehobah ya ba ka salamarsa don ta kāre ‘zuciyarka da tunaninka.’​—Karanta Filibiyawa 4:​6, 7.

YIN ADDU’A DA NAZARI DA KUMA HALARTAN TARO SUNA AMFANARMU

15. Mene ne amfanin yin addu’a da nazari da kuma halartan taro?

15 Idan ka ɗauki lokaci don ka tattauna da Jehobah, ka saurare shi, kuma ka yi tunani a kansa, za ka amfana sosai. Ta yaya? Da farko, za ka iya yanke shawarwari masu kyau. Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa “wanda ya yi tafiya tare da masu hikima zai kasance da hikima.” (K. Mag. 13:20) Don haka, yayin da kake kasancewa da Jehobah, wanda shi ne mafi hikima, kai ma za ka zama mai hikima. Za ka koyi yadda za ka faranta masa rai kuma ka guji ɓata masa rai.

16. Ta yaya yin addu’a da nazari da kuma halartan taro za su taimaka mana mu iya koyarwa da kyau?

16 Na biyu, za mu daɗa ƙwarewa a yadda muke wa’azi. Yayin da muke nazari da wani, ɗaya daga cikin maƙasudanmu shi ne mu taimaka masa ya yi kusa da Jehobah. Yayin da muke ci gaba da yin nazari da kuma addu’a ga Ubanmu na sama, dangantakarmu da shi za ta daɗa yin ƙarfi, kuma za mu ƙara koyan yadda za mu taimaka wa ɗalibanmu su ƙaunace shi. Abin da Yesu ya yi ke nan. Yadda ya bayyana Ubansa ga almajiransa, ya nuna musu cewa yana ƙaunar Ubansa kuma hakan ya taimaka musu su ma su ƙaunaci Jehobah.​—Yoh. 17:​25, 26.

17. Me ya sa yin addu’a da kuma nazari zai taimaka mana mu ƙarfafa bangaskiyarmu?

17 Na uku, bangaskiyarka za ta daɗa ƙarfi. Ka yi tunanin abin da ke faruwa a duk lokacin da ka roƙi Jehobah ya yi maka ja-goranci, ya ƙarfafa ka kuma ya taimaka maka. Yayin da kake ganin yadda Jehobah yake amsa addu’o’inka, bangaskiyarka za ta daɗa ƙaruwa. (1 Yoh. 5:15) Me kuma zai taimaka maka ka ƙarfafa bangaskiyarka? Yin nazari. Ka tuna cewa “akan ba da gaskiya ta wurin jin saƙon ne.” (Rom. 10:17) Amma idan muna so mu ƙarfafa bangaskiyarmu, ba nazari ne kawai za mu yi ba. Me kuma ya kamata mu yi?

18. Ka ba da misalin da ya nuna abin da ya sa ya dace mu riƙa tunanin abin da muka karanta.

18 Muna bukatar mu yi tunani a kan abin da muke koya. Ka yi la’akari da labarin marubucin Zabura ta 77. Ya damu sosai domin yana ganin shi da sauran ’yan’uwansa Isra’ilawa sun rasa amincewar Jehobah. Ya kasa barci da dare domin damuwar da yake ciki. (Ayoyi 2-8) Me ya yi? Ya gaya wa Jehobah cewa: “Zan yi ta tunani a kan dukan abubuwan da ka yi, zan dinga tunani a kan dukan ayyukanka.” (Aya ta 12) Hakika marubucin zaburar ya san abubuwan da Jehobah ya riga ya yi wa mutanensa a dā, duk da haka, ya yi wannan tunanin cewa: “Allah ya manta da yin jinƙai ne? Ko a cikin fushinsa ya janye tausayinsa?” (Aya ta 9) Sai marubucin zaburar ya yi tunani a kan abubuwan da Jehobah yake yi da kuma yadda Jehobah ya nuna musu jinƙai da tausayi a dā. (Aya ta 11) Mene ne sakamakon hakan? Marubucin zaburar ya tabbatar wa kansa cewa Jehobah ba zai taɓa yasar da mutanensa ba. (Aya ta 15) Haka ma bangaskiyarka za ta daɗa ƙarfi yayin da kake tunanin abin da Jehobah ya riga ya yi wa mutanensa da kuma abin da ya yi maka.

19. A wace hanya ce kuma za mu iya amfana daga yin nazari da addu’a da kuma halartan taro?

19 Na huɗu da kuma mafi muhimmanci, za ka daɗa ƙaunar Jehobah. Wannan ƙaunar ce za ta sa ka yi wa Jehobah biyayya, ka yi sadaukarwa don ka faranta masa rai kuma ka jimre duk matsalar da za ka fuskanta. (Mat. 22:​37-39; 1 Kor. 13:​4, 7; 1 Yoh. 5:3) Abin da zai fi muhimmanci a gare ka shi ne samun dangantaka mai kyau da Jehobah!​—Zab. 63:​1-8.

20. Me za ka yi don ka sami zarafin yin addu’a da nazari da kuma bimbini?

20 Ka tuna cewa yin addu’a da nazari da kuma bimbini suna cikin ayyukan ibadarmu. Kamar yadda Yesu ya yi, kai ma ka nemi wurin da babu surutu don ka riƙa yin addu’a da nazari da kuma bimbini. Kada ka bar wasu abubuwa su ɗauke hankalinka. Ka roƙi Jehobah ya taimaka maka ka tattara hankalinka wuri ɗaya yayin da kake yin ayyukan ibada. Idan ka yi amfani da lokacinka yadda ya kamata, Jehobah zai ba ka rai na har abada a cikin sabuwar duniyar da Allah zai kawo.​—Mar. 4:24.

WAƘA TA 28 Yadda Za Mu Zama Abokan Jehobah

^ sakin layi na 5 Jehobah ne babban abokinmu. Muna ɗaukan dangantakarmu da shi da daraja sosai, kuma muna so mu daɗa sanin sa da kyau. Zai iya ɗaukan lokaci kafin mu iya sanin wani da kyau. Haka ma yake idan muna so mu ci gaba da zama abokan Jehobah. Da yake muna da abubuwan yi da yawa a yau, ta yaya za mu keɓe lokacin kusantar Jehobah? Kuma ta yaya za mu amfana idan muka yi hakan?