TALIFIN NAZARI NA 1
“Masu Neman Sanin Jehobah Ba Za Su Rasa Abu Mai Kyau Ba”
JIGON SHEKARA NA 2022: Masu neman sanin Jehobah ba za su rasa abu mai kyau ba.—ZAB. 34:10.
WAƘA TA 4 “Jehobah Makiyayina Ne”
ABIN DA ZA A TATTAUNA *
1. A wane mawuyacin yanayi ne Dauda ya sami kansa?
DAUDA ya yi gudun hijira domin Shawulu sarkin Isra’ila ya so ya kashe shi. Sa’ad da Dauda yake tafiya kuma ya bukaci abinci, ya tsaya a birnin Nob, kuma ya roƙa a ba shi dunƙulen burodi guda biyar. (1 Sam. 21:1, 3) Bayan haka, shi da mutanensa sun ɓoye a wani kogon dutse. (1 Sam. 22:1) Ta yaya Dauda ya sami kansa a wannan yanayin?
2. Ta yaya Shawulu ya sa kansa a yanayi mai wuya? (1 Sama’ila 23:16, 17)
2 Shawulu ya yi kishin Dauda domin mutane suna ƙaunar Dauda kuma suna yabon shi saboda nasarori da ya samu a yaƙe-yaƙe da ya yi. Shawulu ya san cewa Jehobah ya ƙi shi a matsayin sarkin Isra’ila saboda rashin biyayyarsa, kuma ya zaɓi Dauda ya zama sarki a madadinsa. (Karanta 1 Sama’ila 23:16, 17.) Duk da haka, Shawulu sarki ne, akwai mutane da yawa da suke goyon bayansa kuma yana da sojoji da yawa, hakan ya sa Dauda ya yi gudun hijira. Shin Shawulu ya ɗauka cewa zai iya hana Allah ba Dauda sarautar? (Isha. 55:11) Littafi Mai Tsarki bai faɗa ko Shawulu ya yi wannan tunanin ba. Amma mun san cewa Shawulu ya sa kansa a yanayi mai wuya, domin duk masu yin gāba da Allah ba sa yin nasara!
3. Yaya Dauda ya ji duk da yanayin da yake ciki?
3 Dauda mutum ne mai sauƙin kai. Ba shi ya zaɓa ya zama sarkin Isra’ila ba. Jehobah ne ya zaɓe shi. (1 Sam. 16:1, 12, 13) Hakan ya sa Shawulu ya tsani Dauda sosai. Amma Dauda bai ɗora wa Jehobah laifi domin yanayin da ya shiga ba. Kuma bai yi gunaguni domin ya rasa isasshen abinci da kuma wurin kwana ba. A maimakon haka, wataƙila sa’ad da yake kogon dutsen ne ya rubuta waƙar yabon nan da ta ƙunshi jigonmu na shekara ta 2022 wato: “Masu neman sanin Jehobah ba za su rasa abu mai kyau ba.”—Zab. 34:10.
4. Waɗanne tambayoyi ne za mu tattauna, kuma me ya sa suke da muhimmanci?
4 A zamaninmu, musamman ma a lokacin annobar korona, bayin Jehobah da yawa suna fama da rashin isasshen abinci da kuma wasu abubuwan biyan bukata. * Kuma abubuwa za su daɗa wuya yayin da muke kusantar “azaba mai zafi” ko kuma ƙunci mai girma. (Mat. 24:21) Don haka, bari mu amsa tambayoyi huɗun nan: A wace hanya ce Dauda bai “rasa abu mai kyau” ba? Me ya sa muke bukatar mu gamsu da abin da muke da shi? Me ya sa ya kamata mu tabbata cewa Jehobah zai kula da mu? Kuma ta yaya za mu shirya kanmu don abin da zai faru a nan gaba?
“BA ZAN RASA KOME BA”
5-6. Ta yaya Zabura ta 23:1-6 sun taimaka mana mu fahimci abin da Dauda yake nufi sa’ad da ya ce bayin Allah ba za su “rasa abu mai kyau” ba?
5 Mene ne Dauda yake nufi sa’ad da ya ce bayin Jehobah ba za su “rasa abu mai kyau” ba? Sa’ad da Dauda yake rubuta Zabura ta 23, ya yi amfani da furuci makamancin wannan. Don haka, wannan zaburar za ta iya taimaka mana mu san abin da Dauda yake nufi. (Karanta Zabura 23:1-6.) Dauda ya soma zaburar da waɗannan kalaman: ‘Yahweh shi ne makiyayina, ba zan rasa kome ba.’ A sauran ayoyin, Dauda ya ambata wasu abubuwan da suke da muhimmanci sosai, kamar abubuwa masu kyau da yake mora don ya amince Jehobah ya zama makiyayinsa. Jehobah ya bi da shi ta “hanyar adalci” kuma ya taimake shi a lokacin da yake cikin matsaloli. Dauda ya san cewa yin rayuwa a “wuraren kiwo masu ɗanyar ciyawa” da Jehobah ya kai shi ba ya nufin cewa ba zai fuskanci matsaloli ba. A wasu lokuta, yakan yi sanyin gwiwa. Ya kwatanta hakan da yin tafiya a “ramin duhun mutuwa” kuma ya ce zai sami maƙiya. Amma da yake Jehobah ne makiyayinsa, Dauda bai ji “tsoron kome ba.”
6 Yanzu, bari mu amsa tambayar nan: A wace hanya ce Dauda bai “rasa abu mai kyau” ba? Dauda bai rasa wani abin da zai taimaka masa ya kasance kusa da Jehobah ba. Dauda ya gamsu da abin da Jehobah ya tanadar masa. Abin da ya fi muhimmanci a gare shi shi ne yadda Jehobah ya kāre shi da kuma yi masa albarka.
7. Kamar yadda Luka 21:20-24 suka nuna, wane ƙalubale ne Kiristoci a ƙarni na farko da suke zama a Yahudiya suka fuskanta?
7 Daga furucin Dauda, mun fahimci cewa bai kamata mu sa abin duniya ya zama farko a rayuwarmu ba. Za mu iya moran abubuwan da muke da su. Amma kada mu ɗauke su da muhimmanci fiye da kome a rayuwarmu. Abin da Kiristoci a ƙarni na farko da suke zama a Yahudiya suka bukaci su fahimta ke nan. (Karanta Luka 21:20-24.) Yesu ya gargaɗe su cewa lokaci yana zuwa da sojoji za su “kewaye Urushalima.” Sa’ad da hakan ya faru, za su bukaci su “gudu zuwa cikin tuddai.” Idan suka bar birnin, za su tsira, amma za su rasa dukiyoyinsu. Ga yadda wata Hasumiyar Tsaro a shekarun baya ta bayyana yanayin, ta ce: “Sun bar gonakinsu da gidajensu har ma da dukiyoyinsu. Sun tabbata cewa Jehobah zai kula da su kuma zai kāre su. Saboda haka, sun sa bautarsa abu na farko a rayuwarsu.”
8. Wane darasi mai muhimmanci ne muka koya daga Kiristoci a ƙarni na farko da suke zama a Yahudiya?
8 Wane darasi mai muhimmanci ne za mu iya koya daga Kiristoci a ƙarni na farko da suke zama a Yahudiya? Hasumiyar Tsaro da aka ambata ɗazu ta ce: “A nan gaba, za mu fuskanci jarrabobi da za su nuna ko muna ɗaukan dukiya da muhimmanci fiye da kome, ko kuma kasancewa da aminci don mu sami ceto ne ya fi muhimmanci a gare mu. Sa’ad da ƙarshe ya zo, za mu bukaci mu jimre matsaloli kuma mu yi sadaukarwa da yawa. Za mu bukaci mu kasance a shirye kuma mu ɗauki matakan da suka dace, kamar yadda Kiristocin da suka bar Yahudiya suka yi.”
9. Ta yaya shawarar Bulus ga Yahudawa ya ƙarfafa ka?
9 Ka yi tunanin yadda ya yi wa Kiristocin nan wuya su bar kome kuma su soma rayuwa a sabon wuri. Sun bukaci bangaskiya don su dogara ga Jehobah ya biya bukatunsu. Amma akwai wani abin da ya taimaka musu. Shekaru biyar kafin sojojin Roma su kewaye Urushalima, manzo Bulus ya gaya wa Kiristocin cewa: “Ku yi nesa da halin son kuɗi, ku kuma kasance da kwanciyar rai [“ku gamsu,” NW] da abin da kuke da shi. Ga shi kuwa Allah ya ce, ‘Har abada ba zan bar ka ba, sam sam ba zan yar da kai ba.’ Shi ya sa, ba tare da shakka ba, muna iya cewa, ‘Ubangiji mai taimakona ne, ba zan ji tsoro ba. Me ɗan Adam zai iya yi mini?’ ” (Ibran. 13:5, 6) Hakika waɗanda suka bi shawarar Bulus kafin sojojin Roma su kawo musu hari, sun yi saurin sabawa da wurin da suka koma. Sun kasance da tabbaci cewa Jehobah zai kula da su. Abin da Bulus ya faɗa ya tabbatar mana cewa mu ma Jehobah zai kula da mu.
“DA SU ZA MU YI WADAR ZUCI”
10. Mene ne Bulus ya gaya mana?
10 Irin shawarar da Bulus ya ba wa Timoti 1 Tim. 6:8, Tsohuwar Hausa a Sauƙaƙe) Hakan yana nufin cewa ba za mu iya sayan abinci mai tsada, ko mu zauna a gida mai kyau, ko kuma mu sayi sabbin riguna ba ne? Ba abin da Bulus yake nufi ba ke nan. Bulus yana nufin cewa ya kamata mu gamsu da dukan abin da muke da shi. (Filib. 4:12) Darasin da Bulus ya koya ke nan. Abu mafi daraja a gare mu shi ne dangantakarmu da Allah, ba dukiya ba.—Hab. 3:17, 18.
ke nan, kuma ta shafe mu a yau. Ya ce: “Amma da yake muna da abinci da sutura, da su za mu yi wadar zuci.” (11. Wane darasi game da gamsuwa ne muka koya daga abin da Musa ya gaya wa Isra’ilawa?
11 Wataƙila abin da muke tunanin cewa muna bukata, ba shi ne Jehobah yake ganin muna bukata ba. Ka yi la’akari da abin da Musa ya gaya wa Isra’ilawa bayan sun yi shekaru 40 a daji. Ya ce: ‘Gama Yahweh Allahnku ya yi muku albarka cikin dukan ayyukan hannuwanku. Ya san da tafiye-tafiyenku a cikin dajin nan. Yahweh Allahnku ya kasance tare da ku a cikin shekaru arba’in ɗin nan, ba ku rasa kome ba.’ (M. Sha. 2:7) A cikin shekaru 40 da suka yi a cikin daji, Jehobah ya yi wa Isra’ilawa tanadin manna. Rigunan da suka bar Masar da su, ko koɗewa ba su yi ba. (M. Sha. 8:3, 4) Ko da yake wasu a cikinsu sun ɗauka cewa abubuwan da Jehobah yake yi musu tanadi ba su ishe su ba, Musa ya tuna wa Isra’ilawan cewa suna da dukan abin da suke bukata. Idan muka gamsu da abubuwan da Jehobah yake yi mana tanadinsu, hakan zai sa shi farin ciki. Yana so mu nuna godiya ko da abu kaɗan ne muka samu, kuma mu tuna cewa kyauta ce daga gare shi.
KA KASANCE DA TABBACI CEWA JEHOBAH ZAI KULA DA KAI
12. Mene ne ya nuna cewa Dauda ya dogara ga Jehobah ba kansa ba?
12 Dauda ya san cewa Jehobah yana da aminci kuma yana kula sosai da waɗanda suke ƙaunar shi. Sa’ad da Dauda yake rubuta Zabura ta 34, bangaskiya ta sa shi ya ce mala’ikan Allah ya kafa “sansaninsa kewaye” da shi. (Zab. 34:7) Wataƙila Dauda yana kwatanta mala’ikan Jehobah da sojan da ya kafa tanti a inda ake yaƙi yana gādi don ya ga ko maƙiya suna zuwa. Dauda jarumi ne, kuma Jehobah ya yi masa alkawari cewa zai zama sarki. Duk da haka, bai dogara ga dabararsa ta harba majajjawa ko kuma yin amfani da takobi don ya yi nasara a kan maƙiyansa ba. (1 Sam. 16:13; 24:12) Dauda ya dogara ga Allah kuma ya kasance da tabbaci cewa mala’ikan Jehobah zai kuɓutar da waɗanda suke tsoron Allah. Hakika, ba ma sa rai cewa Jehobah zai yi mu’ujiza don ya kāre mu a yau. Amma mun tabbata cewa dukan waɗanda suka dogara ga Jehobah za su sami rai na har abada ko da sun mutu.
13. Sa’ad da Gog na Magog ya kawo mana hari, me ya sa za mu kasance kamar ba mu da kāriya, amma me ya sa ba za mu ji tsoro ba? (Ka duba hoton da ke shafin farko.)
13 A nan gaba, za mu fuskanci jarrabawa da zai nuna ko mun yi imani cewa Jehobah zai iya kāre mu. Za mu iya ɗauka cewa rayuwarmu za ta shiga haɗari a lokacin da Gog na Magog, wato ƙasashen da suka haɗa kai za su kawo mana hari. Dole ne mu gaskata cewa Jehobah zai iya kāre mu, kuma yana da niyyar yin hakan. Ƙasashen za su iya ɗauka cewa muna kama da tumakin da ba su da wanda zai iya kāre su. (Ezek. 38:10-12) Ba za mu kasance da makamai ko dabarun yaƙi ba. Ƙasashen za su yi mana kallon kiyashi da za su iya murkushewa cikin sauƙi. Ba su san cewa mala’ikun Jehobah suna shirye don su kāre mu ba. Amma mun san hakan domin muna da bangaskiya sosai. Ƙasashen ba su gaskata da Allah ba. Za su yi mamaki sa’ad da mala’iku suka yi faɗa a madadinmu!—R. Yar. 19:11, 14, 15.
KA YI SHIRI YANZU DON RAYUWA A NAN GABA
14. Ta yaya za mu yi shiri yanzu don nan gaba?
14 Ta yaya za mu yi shiri yanzu don nan gaba? Da farko, kada mu ɗauka cewa abin duniya yana da muhimmanci domin wata rana za mu rabu da su. Ƙari ga haka, muna bukatar mu gamsu da abubuwan da muke da su kuma mu riƙa farin ciki domin dangantakarmu da Jehobah. Idan muka kusaci Allah sosai, za mu kasance da tabbaci cewa zai kāre mu sa’ad da Gog na Magog ya kawo mana hari.
15. Waɗanne abubuwa ne suka faru da Dauda da suka sa ya gaskata cewa Jehobah ba zai bar shi ba?
15 Yin la’akari da abin da ya taimaka wa Dauda zai iya taimaka mana mu yi shiri don jarrabawa da za mu iya fuskanta. Dauda ya ce: “Ku ɗanɗana ku ga Yahweh mai alheri ne, mai albarka ne wanda ya sami wurin ɓuya a cikinsa.” (Zab. 34:8) Waɗannan kalmomin sun bayyana abin da ya sa Dauda ya dogara ga Jehobah. Dauda ya dogara ga Jehobah kuma Jehobah bai kunyatar da shi ko sau ɗaya ba. A lokacin da Dauda yake matashi, ya yi faɗa da wani katon jarumi Bafilisti mai suna Goliyat. Dauda ya gaya masa cewa: “Yau ɗin nan Yahweh zai ba da kai a hannuna.” (1 Sam. 17:46) Bayan haka, Dauda ya soma yi wa Sarki Shawulu hidima, kuma sau da yawa Shawulu ya so ya kashe shi. Amma “Yahweh yana tare da” Dauda. (1 Sam. 18:12) Dauda ya san cewa Jehobah zai taimaka masa ya shawo kan matsalar da yake fuskanta, domin Jehobah ya riga ya taimaka masa a dā.
16. Ta waɗanne hanyoyi ne za mu iya “ɗanɗana” alherin Jehobah?
16 Yayin da muke daɗa dogara ga Jehobah yanzu, za mu daɗa kasancewa da tabbaci cewa zai cece mu a nan gaba. Muna bukatar mu halarci taron da’ira da taron yanki da dukan taron ikilisiya kuma mu fita yin wa’azi. Sai ta wurin bangaskiya da kuma dogara ga Jehobah ne za mu iya tambayar shugaban wurin aikinmu ya ba mu lokaci don yin abubuwan nan. Idan shugaban wurin aikinmu ya ƙi kuma ya kore mu daga aiki fa? Shin muna da bangaskiya cewa Jehobah ba zai bar mu ba kuma zai ci gaba da biyan bukatunmu? (Ibran. 13:5) ’Yan’uwa da yawa da suke hidima ta cikakken lokaci za su iya ba da labarin yadda Jehobah ya taimaka musu a lokacin da suke bukatar taimako. Jehobah mai aminci ne.
17. Mene ne jigon shekara na 2022, kuma me ya sa ya dace?
17 Da yake Jehobah yana tare da mu, bai kamata mu ji tsoron abin da zai faru a nan gaba ba. Allahnmu ba zai taɓa yasar da mu ba, muddin mun ci gaba da saka mulkinsa farko a rayuwarmu. Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu ta zaɓi Zabura 34:10 a matsayin jigon shekara na 2022. Wannan ayar za ta riƙa tuna mana amfanin shirya kanmu yanzu domin wahaloli da za mu fuskanta a nan gaba, kuma mu dogara ga Jehobah cewa ba zai yasar da mu ba. Jigon shi ne: “Masu neman sanin Jehobah ba za su rasa abu mai kyau ba.”
WAƘA TA 38 Zai Ƙarfafa Ka
^ sakin layi na 5 An ɗauko jigon shekara ta 2022 daga Zabura 34:10 da ta ce: “Masu neman sanin Jehobah ba za su rasa abu mai kyau ba.” Bayin Jehobah da yawa talakawa ne. To me ya sa Littafi Mai Tsarki ya ce ba sa “rasa abu mai kyau”? Ta yaya fahimtar wannan ayar za ta taimaka mana mu yi shiri don mawuyacin lokaci da za mu fuskanta a nan gaba?
^ sakin layi na 4 Ka duba “Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu” a Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Satumba, 2014.
^ sakin layi na 53 BAYANI A KAN HOTO: Har ma a lokacin da Dauda yake ɓoyewa a kogon dutse don Sarki Shawulu, ya nuna godiya domin abubuwan da Jehobah ya yi masa tanadinsu.
^ sakin layi na 55 BAYANI A KAN HOTO: Bayan Isra’ilawa sun bar Masar Jehobah ya ba su manna su ci kuma rigunan da suka bar Masar da su ba su koɗe ba.