Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 4

Me Ya Sa Muke Halartan Taron Tunawa da Mutuwar Yesu?

Me Ya Sa Muke Halartan Taron Tunawa da Mutuwar Yesu?

“Ku dinga yin haka don tunawa da ni.”​—LUK. 22:19.

WAƘA TA 20 Ka Ba da Ɗanka Mai Daraja

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1-2. (a) A wane lokaci ne wasu suka fi tunawa da ɗan’uwansu da ya mutu? (b) Mene ne Yesu ya kafa a dare na ƙarshe kafin ya mutu?

KO DA wani ɗan’uwanmu ya yi shekaru da yawa da mutuwa, mukan tuna da shi. Wasu sukan tuna da ɗan’uwansu da ya mutu idan ranar da ya mutu ta zagayo.

2 A kowace shekara, muna cikin miliyoyin mutane a faɗin duniya da suke halartan taron tunawa da mutuwar wanda muke ƙauna, wato Yesu Kristi. (1 Bit. 1:8) Muna halartan taron ne domin mu tuna da wanda ya ba da ransa domin ya cece mu daga zunubi da kuma mutuwa. (Mat. 20:28) Yesu yana so mabiyansa su tuna da mutuwarsa. A dare na ƙarshe kafin ya mutu, ya kafa jibin maraice kuma ya ce: “Ku dinga yin haka don tunawa da ni.”​—Luk. 22:19.

3. Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?

3 Mutane kaɗan ne a cikin waɗanda suke halartan taron Tunawa da Mutuwar Yesu suke da begen yin rayuwa a sama. Amma miliyoyin mutane da suke da begen yin rayuwa a aljanna a duniya ma, suna halartan wannan taron. A wannan talifin, za mu tattauna dalilai da suka sa waɗannan rukunonin mutane biyu suke marmarin halartan wannan taron a kowace shekara. Ƙari ga haka, za mu tattauna yadda muke amfana daga halartan taron. Bari mu soma da tattauna dalilan da suka sa shafaffun Kiristoci suke halarta.

DALILIN DA YA SA SHAFAFFU SUKE HALARTAN TARON

4. Me ya sa shafaffu suke cin burodi da kuma shan ruwan inabi a taron Tunawa da Mutuwar Yesu?

4 A kowace shekara, shafaffu suna marmarin halartan taron Tunawa da Mutuwar Yesu don su ci burodin kuma su sha ruwan inabin. Me ya sa suke yin hakan? Bari mu tattauna abin da ya faru a dare na ƙarshe da Yesu ya yi a duniya don mu amsa wannan tambayar. Bayan sun gama cin abincin Idin Ƙetarewa, Yesu ya kafa Jibin Maraice na Ubangiji. Ya miƙa wa manzaninsa guda 11 masu aminci burodi su ci da kuma ruwan inabi su sha. Yesu ya gaya musu game da sabon alkawari da kuma alkawarin Mulki. * (Luk. 22:​19, 20, 28-30) Wannan alkawarin ya ba wa manzannin Yesu da kuma wasu Kiristoci damar zama sarakuna da kuma firistoci a sama. (R. Yar. 5:10; 14:1) Sauran shafaffun da suka rage a duniya ne za su iya cin burodi kuma su sha ruwan inabi a taron Tunawa da Mutuwar Yesu, domin su ne aka yi wa alkawarin mulkin da kuma sabon alkawari.

5. Mene ne shafaffu suka sani game da begen da suke da shi?

5 Ga wani dalili kuma da ya sa shafaffu suke marmarin halartan taron Tunawa da Mutuwar Yesu. Wannan taron yana ba su damar yin tunani a kan begen da suke da shi. Jehobah ya ba su bege mai kyau, wato na yin rayuwa a sama da jikin da ba ya mutuwa kuma ba ya ruɓewa, don su yi mulki tare da Yesu da kuma sauran shafaffu 144,000, kuma za su kasance a gaban Jehobah! (1 Kor. 15:​51-53; 1 Yoh. 3:​2, Littafi Mai Tsarki) Shafaffu sun san cewa yin rayuwa a sama babban gata ne. Amma kafin hakan ya faru, suna bukatar su kasance da aminci har ƙarshe. (2 Tim. 4:​7, 8) Shafaffu suna farin cikin yin tunanin begen da suke da shi na yin rayuwa a sama. (Tit. 2:13) “Waɗansu tumaki” kuma fa? (Yoh. 10:16) Waɗanne dalilai ne suke da shi na halartan taron Tunawa da Mutuwar Yesu?

DALILIN DA YA SA WAƊANSU TUMAKI SUKE HALARTAN TARON

6. Me ya sa waɗansu tumaki suke murnar halartan taron Tunawa da Mutuwar Yesu a kowace shekara?

6 Waɗansu tumaki suna halartan taron ba don su ci burodin ko su sha ruwan inabin ba, amma don su shaida taron. A shekara ta 1938 ne lokaci na farko da aka gayyaci waɗansu tumaki zuwa taron Tunawa da Mutuwar Yesu. Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Maris, 1938, ta ce: “Ya dace [waɗansu tumaki] su halarci taron don su shaida yadda ake yin sa. . . . Kuma wannan lokaci ne da zai sa su ma su yi murna.” Kamar yadda waɗanda aka gayyata zuwa bikin aure suke murnar halarta, haka ma waɗansu tumaki suna farin cikin halartan taron Tunawa da Mutuwar Yesu.

7. Me ya sa waɗansu tumaki suke marmarin saurarar jawabin da ake yi a taron Tunawa da Mutuwar Yesu?

7 Waɗansu tumaki ma suna yin tunani a kan begen da suke da shi. Suna marmarin saurarar jawabin da za a bayar a taron. Yawancin abin da ake tattaunawa a taron shi ne abin da Yesu da kuma abokan sarautarsa 144,000 za su yi a Sarautar Yesu na Shekaru Dubu. A ƙarƙashin ja-gorancin Yesu Kristi, waɗannan sarakunan za su mai da duniya ta zama aljanna kuma za su taimaka wa ’yan Adam masu aminci su zama kamiltattu. Miliyoyin mutane da za su halarci taron za su yi farin cikin yin tunanin yadda alkawuran Allah za su cika, alal misali alkawuran da suke Ishaya 35:​5, 6; 65:​21-23 da kuma Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 21:​3, 4. Yin tunanin yadda su da kuma ’yan’uwansu za su kasance a sabuwar duniya zai ƙarfafa begensu kuma ya sa su ƙuduri niyya cewa ba za su daina bauta wa Jehobah ba.​—Mat. 24:13; Gal. 6:9.

8. Wane dalili ne kuma ya sa waɗansu tumaki suke halartan taron?

8 Ka yi la’akari da wani dalili kuma da ya sa waɗansu tumaki suke halartan taron Tunawa da Mutuwar Yesu. Suna so su nuna cewa suna ƙaunar shafaffu kuma suna goyon bayansu. Kalmar Allah ta annabta cewa shafaffu da waɗansu tumaki za su kasance da dangantaka mai kyau da juna. Ta yaya? Bari mu tattauna wasu misalai.

9. Mene ne annabcin da ke Zakariya 8:23 ya nuna game da dangantakar da ke tsakanin waɗansu tumaki da shafaffu?

9 Karanta Zakariya 8:23. Annabcin da ke wannan ayar ya bayyana a hanya mai kyau irin dangantakar da ke tsakani shafaffu da waɗansu tumaki. Furucin nan “mutumin Yahuda” da kuma “ku” suna nufin shafaffu da suka rage a duniya. (Rom. 2:​28, 29) Mutane goma da suka fito “daga kowane yare na kowace al’umma” suna wakiltar waɗansu tumaki. “Kama hannun rigar” yana nufin za su haɗa kai da shafaffu don yin bauta ta gaskiya. Saboda haka, kasancewa a wurin taron Tunawa da Mutuwar Yesu hanya ce da waɗansu tumaki suke nuna cewa suna da dangantaka mai kyau da shafaffu.

10. Mene ne Jehobah ya yi don annabcin da ke Ezekiyel 37:​15-19, 24, 25 ya cika?

10 Karanta Ezekiyel 37:​15-19, 24, 25. Don wannan annabcin ya cika, Jehobah ya sa shafaffu su kasance da dangantaka mai ƙarfi da waɗansu tumaki. A annabcin, an yi magana game da sanduna biyu. Waɗanda suke da begen zuwa sama suna kama da “sandan Yahuda” wato ƙabilar da ake zaɓan sarakuna a Isra’ila. Waɗanda suke da begen yin rayuwa a duniya kuma su ne sandan “Ifrayim.” * Jehobah zai sa waɗannan rukunoni biyu su kasance da haɗin kai don su zama “sanda ɗaya.” Hakan yana nufin suna hidima da haɗin kai a ƙarƙashin sarkinsu Yesu Kristi. A kowace shekara, shafaffu da waɗansu tumaki suna halartan taron Tunawa da Mutuwar Yesu a matsayin rukuni ɗaya, wato “garke ɗaya” ƙarƙashin “makiyayi ɗaya.”​—Yoh. 10:16.

11. Ta yaya ‘tumakin’ da aka ambata a Matiyu 25:​31-36, 40 suke nuna goyon bayansu ga ’yan’uwan Kristi?

11 Karanta Matiyu 25:​31-36, 40. ‘Tumakin’ da Yesu yake magana a kai suna wakiltar waɗanda suke da aminci a kwanakin ƙarshe kuma suke da begen yin rayuwa a duniya. Suna goyon bayan ’yan’uwan Yesu Kristi da suka rage don su yi aiki mai muhimmanci da aka ba su wato yin wa’azi a dukan duniya.​—Mat. 24:14; 28:​19, 20.

12-13. A waɗanne hanyoyi ne kuma waɗansu tumaki suke goyon bayan ’yan’uwan Yesu?

12 A kowace shekara kafin ranar taron Tunawa da Mutuwar Yesu, waɗansu tumaki suna nuna goyon bayansu ga ’yan’uwan Yesu ta wajen yin wa’azi da ƙwazo don su gayyaci mutane zuwa taron. (Ka duba akwatin nan “ Kana Yin Shiri don Ka Halarci Taron Tunawa da Mutuwar Yesu?”) Suna yin shirye-shirye don a iya yin taron Tunawa da Mutuwar Yesu a kowace ikilisiya a faɗin duniya, duk da cewa babu shafaffu a yawancin ikilisiyoyin. Waɗansu tumakin suna farin cikin goyon bayan ’yan’uwan Kristi ta waɗannan hanyoyin. Waɗannan tumakin sun san cewa Yesu yana ɗaukan abubuwan da suke yi don su goyi bayan ’yan’uwansa kamar suna yi masa ne.​—Mat. 25:​37-40.

13 Waɗanne dalilai ne kuma suke sa dukanmu halartan taron Tunawa da Mutuwar Yesu ko da muna da begen yin rayuwa a sama ko a duniya?

DALILIN DA YA SA DUKANMU MUKE HALARTAN TARON

14. Ta yaya Jehobah da Yesu suka nuna cewa suna ƙaunar mu?

14Muna farin ciki don ƙaunar da Jehobah da Yesu suke nuna mana. Jehobah ya nuna cewa yana ƙaunar mu a hanyoyi da yawa, amma akwai hanya ɗaya da ya nuna mana ƙauna fiye da sauran. Allah ya nuna cewa yana ƙaunar mu ta wajen turo Ɗansa da yake ƙauna don ya sha wahala kuma ya mutu a madadinmu. (Yoh. 3:16) Yesu ma ya nuna cewa yana ƙaunar mu ta wajen kasancewa a shirye don ya ba da ransa a madadinmu. (Yoh. 15:13) Ba za mu iya biyan Jehobah da Yesu don irin ƙauna da suka nuna mana ba. Amma za mu iya nuna godiyarmu ta yadda muke rayuwa. (Kol. 3:15) Saboda haka, muna halartan taron Tunawa da Mutuwar Yesu don mu tuna irin ƙaunar da suka nuna mana kuma mu nuna musu cewa mu ma muna ƙaunar su.

15. Me ya sa shafaffu da waɗansu tumaki suke daraja fansar da Yesu ya bayar?

15Muna godiya sosai saboda yadda Yesu ya fanshe mu. (Mat. 20:28) Shafaffu suna godiya domin fansar ta sa sun kasance da bege. Jehobah ya ɗauke su a matsayin masu adalci kuma ya mai da su ’ya’yansa, domin sun ba da gaskiya ga hadayar da Yesu ya yi. (Rom. 5:1; 8:​15-17, 23) Waɗansu tumaki ma suna godiya saboda hadayar da Yesu ya bayar. Da yake sun ba da gaskiya ga hadayar Yesu, suna da dangantaka mai kyau da Allah. Sun sami amincewar Allah, kuma za su iya bauta masa yadda yake so. Ƙari ga haka, suna da begen tsira daga “azaba mai zafi,” wato ƙunci mai girma. (R. Yar. 7:​13-15) Hanya ɗaya da shafaffu da kuma waɗansu tumaki suke nuna godiyarsu domin fansar da Yesu ya bayar ita ce ta wajen halartan taron a kowace shekara.

16. Wane dalili ne kuma ya sa muke halartan taron Tunawa da Mutuwar Yesu?

16 Wani dalili kuma da ya sa muke halartan taron Tunawa da Mutuwar Yesu shi ne domin muna so mu yi masa biyayya. Ko da muna da begen yin rayuwa a sama ko a duniya, zai dace mu bi umurnin Yesu a daren da ya kafa taron cewa: “Ku dinga yin haka don tunawa da ni.”​—1 Kor. 11:​23, 24.

YADDA MUKE AMFANA DAGA HALARTAN TARON

17. Ta yaya taron Tunawa da Mutuwar Yesu yake taimaka mana mu daɗa kusantar Jehobah?

17Muna ƙara kusantar Jehobah. (Yak. 4:8) Kamar yadda muka tattauna, taron Tunawa da Mutuwar Yesu yana ba mu damar yin tunani a kan begen da Jehobah ya ba mu, da kuma irin ƙaunar da ya nuna mana. (Irm. 29: 11; 1 Yoh. 4:​8-10) Idan muka yi tunanin abin da muke sa ran mora a nan gaba, za mu daɗa ƙaunar Jehobah, kuma mu daɗa kusantar sa.​—Rom. 8:​38, 39.

18. Mene ne yin tunani a kan misalin Yesu zai sa mu yi?

18Yana taimaka mana mu bi misalin Yesu. (1 Bit. 2:21) Kwanaki kaɗan kafin ranar taron, muna karanta Nassosin da suka yi magana game da makon Yesu na ƙarshe a duniya, da mutuwarsa da kuma tashinsa. A daren taron, jawabin yana tuna mana yadda Yesu yake ƙaunar mu. (Afis. 5:2; 1 Yoh. 3:16) Yayin da muke karanta irin sadaukarwar da Yesu ya yi kuma muke yin tunani a kai, hakan zai motsa mu mu yi ‘tafiya kamar yadda Yesu Almasihu ya yi.’​—1 Yoh. 2:6.

19. Ta yaya za mu ci gaba da kiyaye kanmu a cikin ƙaunar Allah?

19Muna daɗa ƙudura niyyar zama abokan Allah. (Yahu. 20, 21) Muna yin iya ƙoƙarinmu don mu kiyaye kanmu cikin ƙaunar Allah ta wajen yi masa biyayya da tsarkake sunansa, da kuma sa shi farin ciki. (K. Mag. 27:11; Mat. 6:9; 1 Yoh. 5:3) Halartan taron Tunawa da Mutuwar Yesu yana sa mu ƙuduri niyyar yin rayuwa a kowace rana a hanyar da za ta nuna wa Jehobah cewa muna so mu ci gaba da ‘kiyaye kanmu cikin ƙaunarsa’ har abada!

20. Waɗanne dalilai masu kyau ne muke da su na halartan taron Tunawa da Mutuwar Yesu?

20 Ko da muna da begen yin rayuwa a sama ko a duniya, muna da dalilai masu kyau da suka sa ya kamata mu halarci taron Tunawa da Mutuwar Yesu. A kowace shekara sa’ad da muka halarci taron, muna tuna mutuwar wanda muke ƙauna, wato Yesu Kristi. Amma abu mafi muhimmanci shi ne, muna tuna irin ƙaunar da Jehobah ya nuna mana ta wajen aiko Ɗansa don ya fanshe mu. A wannan shekarar, za a yi taron Tunawa da Mutuwar Yesu, da yamma ranar Jumma’a, 15 ga Afrilu, 2022. Muna ƙaunar Jehobah da Ɗansa. Saboda haka, babu abin da zai hana mu halartan taron Tunawa da Mutuwar Yesu, kome muhimmancin abin.

WAƘA TA 16 Mu Yabi Jehobah Domin Ɗansa

^ sakin layi na 5 Ko da muna da begen yin rayuwa a sama ko a duniya, dukanmu muna marmarin halartan taron Tunawa da Mutuwar Yesu a kowace shekara. A wannan talifin, za mu tattauna dalilai daga Littafi Mai Tsarki da suke sa mu halarci taron da kuma yadda hakan yake amfanar mu.

^ sakin layi na 4 Don samun ƙarin bayani game da sabon alkawari da kuma alkawarin Mulki, ka duba talifin nan “Za Ku Zama ‘Mulki na Firistoci’ ” a fitowar Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Oktoba, 2014, shafuffuka na 15-17.

^ sakin layi na 10 Don samun ƙarin bayani a kan annabcin sanduna biyu, ka duba “Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu,” a Hasumiyar Tsaro ta Yuli, 2016.