Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 4

Jehobah Yana Mana Albarka don Muna Halartan Taron Tunawa da Mutuwar Yesu

Jehobah Yana Mana Albarka don Muna Halartan Taron Tunawa da Mutuwar Yesu

“Ku dinga yin haka don tunawa da ni.”​—LUK. 22:19.

WAƘA TA 19 Jibin Maraice na Ubangiji

ABIN DA ZA A TATTAUNA a

1-2. Me ya sa muke halartan Taron Tunawa da Mutuwar Yesu a kowace shekara?

 KUSAN shekaru 2000 da suka shige, Yesu ya ba da ransa a madadinmu kuma hakan ya buɗe mana hanyar samun rai na har abada. A dare na ƙarshe kafin Yesu ya mutu, ya umurci almajiransa su ci gaba da tunawa da mutuwarsa ta wajen yin biki mai sauƙi da ya ƙunshi burodi da kuma ruwan inabi.​—1 Kor. 11:​23-26.

2 Muna yin biyayya ga umurnin Yesu domin muna ƙaunar sa sosai. (Yoh. 14:15) Kowace shekara, a lokacin Tunawa da Mutuwar Yesu, mukan nuna godiyarmu ta wajen ɗaukan lokaci mu yi adduꞌa da kuma bimbini a kan maꞌanar mutuwar sa. Ƙari ga haka, muna farin cikin daɗa ƙwazo a waꞌazi don mu gayyaci mutane da yawa su zo su yi taron tare da mu. Kuma mukan tabbata cewa babu wani abu da zai hana mu halartan taron.

3. Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?

3 A wannan talifin, za mu tattauna hanyoyi uku da Shaidun Jehobah suka yi ƙoƙari sosai don su yi Taron Tunawa da Mutuwar Yesu: (1) ta wajen bin tsarin da Yesu ya kafa, (2) ta wajen gayyatar mutane zuwa taron, (3) ta wajen yin taron duk da matsalolin da muke fuskanta.

BIN TSARIN DA YESU YA KAFA

4. Waɗanne muhimman gaskiya ne muke koya a Taron Tunawa da Mutuwar Yesu kowace shekara, kuma me ya sa bai kamata mu yi wasa da su ba? (Luka 22:​19, 20)

4 A kowace shekara a taron, mukan saurari jawabi daga Littafi Mai Tsarki da ke ba da amsoshi masu gamsarwa ga tambayoyi da yawa. Mukan koyi dalilin da ya sa ꞌyan Adam suke bukatar fansa, da kuma yadda mutuwar mutum ɗaya ta wanke zunuban mutane da yawa. Akan tuna mana abin da burodin da ruwan inabin suke nufi, da kuma waɗanda ya dace su ci. (Karanta Luka 22:​19, 20.) Kuma mukan yi bimbini a kan albarku da waɗanda za su yi rayuwa a duniya za su mora. (Isha. 35:​5, 6; 65:​17, 21-23) Bai kamata mu yi wasa da waɗannan muhimman gaskiya ba. Biliyoyin mutane ba su san gaskiyar nan ba, kuma ba su san yadda fansar Yesu take da daraja ba. Ƙari ga haka, ba sa yin taron yadda Yesu ya tsara shi. Me ya sa?

5. Bayan yawancin manzannin Yesu sun mutu, mene ne ya faru da tsarin da Yesu ya kafa?

5 Jim kaɗan bayan yawancin manzannin Yesu suka mutu, sai Kiristocin ƙarya suka shiga cikin ikilisiya. (Mat. 13:​24-27, 37-39) Sun “yi maganganun ƙarya, domin su jawo masu bi zuwa gefensu.” (A. M. 20:​29, 30) Ɗaya daga cikin “maganganun ƙarya” da Kiristocin ƙarya suka fara koyarwa shi ne cewa Yesu bai mutu “sau ɗaya domin ya ɗauki zunuban mutane da yawa” kamar yadda Littafi Mai Tsarki ya faɗa ba. Amma cewa ana bukatar a riƙa maimaita hadayar da ya yi a kai a kai. (Ibran. 9:​27, 28) A yau, mutane da yawa sun gaskata da wannan koyarwar ƙarya. Sukan je coci a kowane mako wasu lokuta ma a kullum don su gudanar da hadayar da Yesu ya yi wanda a cocin Katolika ana kira “the Sacrifice of the Mass.” b Wasu cocin kuma, ba a kowane lokaci ne suke tuna hadayar da Yesu ya yi ba, amma yawancin mambobinsu ba su fahimci abin da hadayar Yesu take nufi ba. Sukan ce, ‘Anya mutuwar Yesu zai sa a gafarta min zunubaina?’ Me ya sa sukan yi tambayar nan? Domin mutanen da ba su gaskata cewa mutuwar Yesu za ta iya sa a gafarta mana zunubanmu ba sun cusa musu raꞌayinsu. Ta yaya mabiyan Yesu sun taimaka wa mutane su fahimci abin da hadayar Yesu ta ƙunsa, da kuma yadda ya dace a gudanar da Taron Tunawa da Mutuwar Yesu?

6. Wane abu ne ɗaliban Littafi Mai Tsarki suka gano daga Littafi Mai Tsarki a 1872?

6 A ƙarshen ƙarni na 19, wani rukunin ɗalibai da Charles Taze Russell yake yi musu ja-goranci sun soma yin nazari mai zurfi na Littafi Mai Tsarki. Suna so su san abin da hadayar Yesu take nufi da kuma yadda ya dace a yi Taron Tunawa da Mutuwarsa. A 1872, sun gano daga Littafi Mai Tsarki cewa Yesu ya tanadar da fansa ga dukan ꞌyan Adam. Ba su ɓoye abin da suka gano ba. A maimakon haka, sun sanar da hakan ta wajen littattafai da mujallu da kuma jaridu. Kuma jim kaɗan bayan hakan, sun soma yin koyi da Kiristocin ƙarni na farko ta wajen yin Taron Tunawa da Mutuwar Yesu sau ɗaya a shekara.

7. Ta yaya muke amfana daga nazari mai zurfi da ɗaliban Littafi Mai Tsarki a dā suka yi?

7 A yau, muna amfana daga nazari mai zurfi da mutanen nan suka yi shekaru da yawa da suka shige. Ta yaya? Jehobah ya taimaka mana mu fahimci abin da fansar Yesu take nufi, da kuma abin da fansar za ta yi wa dukan ꞌyan Adam. (1 Yoh. 2:​1, 2) Mun kuma koyi cewa Littafi Mai Tsarki ya yi alkawarin rai marar mutuwa ga wasu mutane a sama da kuma rai na har abada ga miliyoyin mutane a nan duniya. Mukan yi kusa da Jehobah yayin da muke tattauna yadda ya nuna mana ƙauna da kuma yadda kowannenmu ya amfana daga mutuwar Yesu Kristi. (1 Bit. 3:18; 1 Yoh. 4:9) Don haka, muna yin koyi da ꞌyanꞌuwanmu Kiristoci na dā ta wajen gayyatar mutane zuwa Taron Tunawa da Mutuwar Yesu yadda Yesu ya tsara.

GAYYATAR MUTANE ZUWA TARON TUNAWA DA MUTUWAR YESU

Mene ne za ka iya yi don ka daɗa ƙwazo a yin ayyukan ibada a lokacin Taron Tunawa da Mutuwar Yesu? (Ka duba sakin layi na 8-10) e

8. Wane abu ne Shaidun Jehobah suka yi don su gayyaci mutane zuwa Taron Tunawa da Mutuwar Yesu? (Ka duba hoton.)

8 Shaidun Jehobah sun daɗe suna gayyatar mutane zuwa taron. A 1881, an gayyaci ꞌyanꞌuwa maza da mata a Amirka su halarci taron a wani gida da ke Allegheny, a Pennsylvania. Daga baya, kowace ikilisiya ta soma yin nata taron. A watan Maris na 1940, an gaya wa masu shela cewa za su iya gayyatar kowa a yankinsu zuwa taron. A 1960, Bethel ta soma ba da takardar gayyata ga ikilisiyoyi. Tun daga lokacin, ana rarraba biliyoyin takardun gayyatar. Me ya sa muke yin aiki tukuru don mu gayyaci mutane zuwa taron?

9-10. Su waye ne suke amfana daga ƙoƙarin da muke yi don mu gayyaci mutane zuwa Taron Tunawa da Mutuwar Yesu? (Yohanna 3:16)

9 Ɗaya daga cikin dalilan da suka sa muke gayyatar mutane zuwa Taron Tunawa da Mutuwar Yesu shi ne, muna so waɗanda suka halarci taron a karo na farko su koyi abin da Jehobah da kuma Yesu suka yi wa dukanmu. (Karanta Yohanna 3:16.) Muna sa rai cewa abubuwan da suka gani kuma suka ji a taron zai sa su su daɗa koya game da Jehobah kuma su zama bayinsa. Amma akwai wasu ma da suke amfana daga taron.

10 Muna kuma gayyatar waɗanda suka daina bauta ma Jehobah. Muna yin hakan ne don mu tuna musu cewa har yanzu Jehobah yana ƙaunar su. Da yawa sukan amince da gayyatar mu kuma mukan yi farin ciki idan muka gan su. Halartan taron yana tuna musu da yadda suka ji daɗin bauta ma Jehobah a dā. Ka yi laꞌakari da misalin wata mai suna Monica. c An sake mai da ita mai shela a lokacin annobar korona. Bayan ta halarci taron a shekara ta 2021, ta ce: “Wannan taron yana da muhimmanci sosai a gare ni. Wannan ne karo na farko bayan shekaru 20 da na yi waꞌazi ga mutane kuma na gayyace su zuwa Taron Tunawa da Mutuwar Yesu. Na yi iyakacin ƙoƙarina in gayyaci mutane domin ina farin ciki sosai don abin da Jehobah da Yesu suka yi mini.” (Zab. 103:​1-4) Ko da mutane sun amince da gayyatarmu ko ba su amince ba, muna gayyatar mutane da ƙwazo zuwa taron domin mun san cewa Jehobah yana farin ciki domin ƙoƙarin da muke yi.

11. Ta yaya Jehobah yake albarkaci ƙoƙarin da muke yi don mu gayyaci mutane zuwa Taron Tunawa da Mutuwar Yesu? (Haggai 2:7)

11 Jehobah ya albarkaci ƙoƙarin da muke yi don mu gayyaci mutane zuwa taron. A 2021, duk da cewa annobar korona ta taƙaita yadda muke waꞌazi, mutane 21,367,603 ne suka halarci taron. Hakan ya ninka adadin Shaidun Jehobah a duk faɗin duniya sau biyu da raɓi! Amma Jehobah ba ya mai da hankali a kan adadin mutane kawai. Yana fi mai da hankali ga kowannenmu ne. (Luk. 15:7; 1 Tim. 2:​3, 4) Muna da tabbaci cewa Jehobah yana amfani da gayyatar da muke yi wajen samo mutane masu zuciyar kirki.​—Karanta Haggai 2:7.

YIN TARON TUNAWA DA MUTUWAR YESU DUK DA MATSALOLI

Jehobah yana albarkaci ƙoƙarin da muke yi don mu halarci Taron Tunawa da Mutuwar Yesu (Ka duba sakin layi na 12) f

12. Waɗanne yanayoyi ne za su iya sa ya yi mana wuya mu halarci Taron Tunawa da Mutuwar Yesu? (Ka duba hoton.)

12 Yesu ya annabta cewa a kwanakin ƙarshe za mu fuskanci matsaloli dabam-dabam, kamar hamayya daga mambobin iyalinmu da tsanantawa da yaƙe-yaƙe da cututtuka da dai sauransu. (Mat. 10:36; Mar. 13:9; Luk. 21:​10, 11) A wasu lokuta, irin matsalolin nan suna sa ya yi mana wuya mu halarci Taron Tunawa da Mutuwar Yesu. Mene ne ꞌyanꞌuwanmu maza da mata suka yi don su shawo kan matsalolin nan, kuma ta yaya Jehobah ya taimaka musu?

13. Ta yaya Jehobah ya albarkaci Artem domin ƙarfin zuciyarsa da kuma yadda ya ƙudiri niyyar yin Taron Tunawa da Mutuwar Yesu?

13 Kurkuku. ꞌYanꞌuwanmu da suke kurkuku sukan yi iya ƙoƙarinsu don su yi Taron Tunawa da Mutuwar Yesu. Ka yi laꞌakari da misalin Artem. A lokacin Taron Tunawa da Mutuwar Yesu na 2020, an tsare shi a kurkuku da ke da girman kafa 183, kuma mutane huɗu ko biyar ne suke zama a ciki. Duk da cewa an tsare shi a kurkuku, ya iya ya samo abubuwan da yake bukata don ya iya gudanar da taron kuma ya shirya yadda zai ba da jawabin da kansa. Amma sauran mutanen da ke kurkukun tare da shi suna shan taba sosai, kuma suna yawan yin maganganun banza. Mene ne ya yi? Ya tambaye su ko za su iya guji yin maganganun banza da kuma shan taba na awa ɗaya. Artem ya yi mamaki da suka yarda cewa ba za su yi maganganun banza ko kuma su sha taba a lokacin taron ba. Artem ya ce, “Na yi ƙoƙari in gaya musu game da taron.” Ko da yake sun ce ba sa so su ji game da taron, da suka ji da kuma ga yadda Artem ya yi taron, sai suka yi masa tambayoyi game da taron.

14. Wane ƙoƙari ne ꞌyanꞌuwa suka yi don su halarci Taron Tunawa da Mutuwar Yesu duk da annobar korona?

14 Annobar korona. Saꞌad da aka soma annobar korona, Shaidun Jehobah sun kasa yin taron a zahiri kamar yadda suka saba yi. Amma hakan bai hana su yin taron ba. d Ikilisiyoyin da suke iya shigan intane sun yi taron ta bidiyo. Amma ta yaya miliyoyin ꞌyanꞌuwa da ba sa iya shiga intane suka yi taron? A wasu ƙasashe, an shirya yadda za a yaɗa taron a tashoshin talabijin ko kuma na rediyo. Ƙari ga haka, ofisoshinmu a faɗin duniya sun yi rikodin na taron a yaruka sama da 500 don waɗanda suke ƙauyuka ma su iya yin taron. Kuma wasu ꞌyanꞌuwa masu aminci sun shirya yadda za a iya kai wa ꞌyanꞌuwan rikodin na taron.

15. Wane darasi ne ka koya daga misalin wata ɗalibar Littafi Mai Tsarki mai suna Sue?

15 Hamayya daga mambobin iyalinmu. Hamayya daga mambobin iyalinmu ne matsala mafi girma da wasu suke fuskanta yayin da suke so su halarci Taron Tunawa da Mutuwar Yesu. Ka yi laꞌakari da misalin wata ɗalibar Littafi Mai Tsarki mai suna Sue. Ana gobe za a yi Taron Tunawa da Mutuwar Yesu na 2021, sai Sue ta gaya wa ꞌyarꞌuwa da ke nazari da ita cewa ba za ta iya halarci taron ba saboda hamayya daga iyalinta. ꞌYarꞌuwar ta karanta Luka 22:44. Sai ta bayyana mata cewa a duk lokacin da muke fuskantar matsaloli, zai dace mu yi koyi da misalin Yesu ta wajen yin adduꞌa ga Jehobah kuma mu dogara gare shi da dukan zuciyarmu. Washegari sai Sue ta shirya burodin da kuma ruwan inabin. Ƙari ga haka, ta kalli ibadar safiya ta musamman da aka nuna a jw.org. Da yammar saꞌad da take ɗaki ita kaɗai, ta kalli taron ta wayarta. Bayan haka, Sue ta aika wasiƙa ga ꞌyarꞌuwar cewa: “Kin ƙarfafa ni sosai jiya. Na yi iyakacin ƙoƙarina don in halarci taron kuma Jehobah ya taimaka mini. Ba zan iya bayyana irin farin cikin da nake yi ba!” Kana ganin Jehobah zai iya taimaka maka idan ka fuskanci irin yanayin nan?

16. Me ya sa muke da tabbaci cewa Jehobah zai albarkaci ƙoƙarin da muke yi don mu halarci Taron Tunawa da Mutuwar Yesu? (Romawa 8:​31, 32.)

16 Jehobah yana farin ciki sosai don ƙoƙarin da muke yi don mu halarci Taron Tunawa da Mutuwar Yesu. Za mu iya kasancewa da tabbaci cewa zai albarkace mu don yadda muke nuna godiya don abin da ya yi mana. (Karanta Romawa 8:​31, 32.) Bari mu ƙudiri niyyar halartan taron a wannan shekarar, kuma mu yi iya ƙoƙarinmu don mu daɗa ƙwazo a yin ayyukan ibada a lokacin taron.

WAƘA TA 18 Muna Godiya Domin Mutuwar Yesu

a A ranar Talata, 4 ga Afrilu, 2023, miliyoyin mutane a faɗin duniya za su halarci Taron Tunawa da Mutuwar Yesu. Mutane da yawa za su halarci taron a karo na farko. Wasu da Shaidun Jehobah ne a dā za su halarci taron a karo na farko bayan shekaru da yawa. Wasu kuma za su shawo kan matsaloli da dama don su iya halartan taron. Ko da yaya yanayinka yake, ka kasance da tabbaci cewa Jehobah zai yi farin ciki domin ƙoƙarin da ka yi don ka halarci taron.

b Masu yin wannan ibadar sun gaskata cewa a duk lokacin da suke yin hakan, burodin da kuma ruwan inabin sukan juya su zama jinin Yesu da kuma namarsa. A ganinsu, suna yin hadaya da jinin Yesu da kuma namarsa a duk lokacin da suke yin wannan ibadar.

c An canja wasu sunayen.

d Ka kuma duba talifin nan “2021 Memorial Commemoration” a jw.org.

e BAYANI A KAN HOTUNA: Tun daga 1960, an ci gaba da daɗa yawan takardun gayyata da ake bugawa na Taron Tunawa da Mutuwar Yesu kuma yanzu ana iya samun su a intane.

f BAYANI A KAN HOTUNA: Kwaikwayo da ke nuna yadda ꞌyanꞌuwa suka yi Taron Tunawa da Mutuwar Yesu a lokacin da ake tashin hankali.