Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Shawara A Kan Yin Nazari

Shawara A Kan Yin Nazari

Kana jin daɗin karanta labaran ꞌyanꞌuwanmu maza da mata?

Wasu maꞌaurata da suke karanta labari ɗaya kowane safe sun ce: “Karanta labaran nan yana ƙarfafa mu kuma yana sa mu farin ciki! Suna tuna mana cewa mu ma za mu iya riƙe amincinmu ko da wane yanayi muke.” Wata ꞌyarꞌuwa da ita ma tana jin hakan ta rubuto cewa: “Waɗannan labaran suna ƙarfafa mu, suna ratsa zukatanmu kuma suna sa mu farin ciki. Rayuwar ꞌyanꞌuwanmu maza da mata tana da manufa sosai. Labaran suna sa in daɗa ƙwazo a yin waꞌazi kuma suna taimaka mini in ƙarfafa yarana su yi wa Jehobah hidima ta cikakken lokaci.”

Labaran nan za su iya sa mu ƙara himma a hidimarmu ga Jehobah, mu shawo kan kasawarmu kuma mu jimre matsalolinmu da farin ciki, ba tare da jin kunya ba. A ina ne za ka iya samun waɗannan labaran?

  • Ka duba jerin talifofin nan “Tarihin Shaidun Jehobah” a jw.org/⁠ha ko a JW Library®.

  • Ka duba “Life Stories of Jehovah’s Witnesses” a Watchtower ONLINE LIBRARY ko Watchtower Library a Turanci.