Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 11

Ku Saurari Jehobah

Ku Saurari Jehobah

“Wannan shi ne Ɗana . . . Ku saurare shi!”​—MAT. 17:5.

WAƘA TA 89 Mu Ji, Mu Yi Biyayya Don Mu Sami Albarka

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1-2. (a) A waɗanne hanyoyi ne Jehobah yake magana da mutane? (b) Me za mu tattauna a wannan talifin?

JEHOBAH yana so mu san shi. A dā ya yi amfani da annabawa da mala’iku da kuma Ɗansa Yesu Kristi don ya sa mu san ra’ayinsa. (Amos 3:7; Gal. 3:19; R. Yar. 1:1) A yau, Jehobah yana yin hakan ta wurin Kalmarsa. Ya ba mu Littafi Mai Tsarki don mu san ra’ayinsa kuma mu fahimci hanyoyinsa.

2 Sa’ad da Yesu yake duniya, Jehobah ya yi magana da shi daga sama sau uku. Bari mu tattauna abin da Jehobah ya ce sa’ad da ya yi magana a waɗannan lokutan. Ƙari ga haka, za mu ga darasin da za mu koya daga abin da ya ce, da kuma yadda za mu amfana.

‘KAI ƊANA NE WANDA NAKE ƘAUNA’

3. Kamar yadda aka ambata a littafin Markus 1:​9-11, me Jehobah ya ce sa’ad da aka yi wa Yesu baftisma, kuma waɗanne abubuwa masu muhimmanci ne wannan furucin ya nuna?

3 Littafin Markus 1:​9-11 ya nuna lokaci na farko da Jehobah ya yi magana daga sama. (Karanta.) Ya ce: ‘Kai Ɗana ne wanda nake ƙauna. Ina jin daɗinka ƙwarai.’ Babu shakka, abin da Jehobah ya ce ya sosa zuciyar Yesu don ya ce yana ƙaunarsa kuma ya amince da shi! Abin da Jehobah ya ce ya nuna abubuwa uku masu muhimmanci game da Yesu. Na farko, Yesu ne Ɗansa. Na biyu, Jehobah yana ƙaunar Ɗansa. Na uku, Jehobah ya amince da Ɗansa. Bari mu bincika kowanne cikin waɗannan furucin sosai.

4. Wace dangantaka ce Yesu ya ƙulla da Allah sa’ad da aka yi masa baftisma?

4 ‘Kai Ɗana ne.’ Ta wannan furucin, Jehobah ya nuna cewa Ɗansa ƙaunatacce ya ƙulla wata dangantaka da shi. Sa’ad da Yesu yake sama, shi ɗan Allah ne. Amma sa’ad da ya yi baftisma, an shafe shi da ruhu mai tsarki. A wannan lokacin, Allah ya nuna cewa Yesu yana da begen komawa sama don ya zama Babban Firist da kuma Sarkin Mulkin Allah. (Luk. 1:​31-33; Ibran. 1:​8, 9; 2:17) Saboda haka, da aka yi wa Yesu baftisma, ya dace da Jehobah ya ce: “Kai ne Ɗana.”​—Luk. 3:22.

Mukan ƙara ƙwazo idan aka yaba mana kuma aka ƙarfafa mu (Ka duba sakin layi na 5) *

5. Ta yaya za mu nuna ƙauna kuma mu riƙa ƙarfafa mutane kamar Jehobah?

5 “Wanda nake ƙauna.” Yadda Jehobah ya ce yana ƙaunar Yesu kuma ya amince da shi ya koya mana cewa ya dace mu riƙa neman zarafin ƙarfafa mutane. (Yoh. 5:20) Mukan ƙara ƙwazo sa’ad da abokinmu ya nuna yana ƙaunarmu kuma ya yaba mana don abubuwa masu kyau da muke yi. Hakazalika, ya kamata mu riƙa ƙauna da ƙarfafa ’yan’uwa a cikin ikilisiya da kuma membobin iyalinmu. Idan muna yaba musu, hakan zai ƙarfafa bangaskiyarsu kuma zai taimaka musu su riƙa bauta wa Jehobah da aminci. Ya dace iyaye su riƙa ƙarfafa yaransu kuma su nuna suna ƙaunarsu. Idan suka yi hakan da dukan zuciyarsu, yaran za su ci gaba da bauta wa Jehobah.

6. Me ya sa za mu iya tabbata da Yesu Kristi?

6 “Ina jin daɗinka ƙwarai.” Wannan furucin ya nuna cewa Jehobah ya amince da Yesu kuma ya tabbata cewa Yesu zai yi nufinsa. Tun da Jehobah yana da wannan tabbacin, mu ma za mu kasance da tabbaci sosai cewa Yesu zai cika dukan alkawuran Jehobah. (2 Kor. 1:20) Idan muka yi tunani a kan misalin Yesu, za mu ƙuduri niyya mu koya daga wurinsa kuma mu bi misalinsa. Jehobah yana da tabbaci cewa bayinsa za su ci gaba da koyo daga wurin Ɗansa.​—1 Bit. 2:21.

“KU SAURARE SHI!”

7. Kamar yadda littafin Matiyu 17:​1-5 ya nuna, a wane lokaci ne Jehobah ya yi magana daga sama, kuma me ya ce?

7 Karanta Matiyu 17:​1-5. Lokaci na biyu da Jehobah ya yi magana daga sama shi ne lokacin da ‘kamanin’ Yesu ya canja. Yesu ya gaya wa Bitrus da Yakub da kuma Yohanna su bi shi zuwa kan wani tudu mai tsawo. Sun ga wani wahayi mai ban mamaki sa’ad da suke wurin. Fuskar Yesu ta yi haske kamar rana kuma rigarsa ta yi fari fat. Sai wasu mutane da suke wakiltar Musa da Iliya suka soma yin magana da Yesu game da mutuwar da zai yi da kuma yadda zai tashi daga mutuwa. Duk da cewa manzannin uku “suna barci,” sun ga wannan wahayi mai ban al’ajabi a lokacin da suka farka. (Luk. 9:​29-32) Bayan haka, sai girgije mai haske ya rufe su kuma suka ji murya tana magana daga cikin girgijen, wannan muryar Allah ce. Kamar yadda Jehobah ya yi sa’ad da Yesu ya yi baftisma, ya nuna cewa ya amince da Ɗansa kuma yana ƙaunar sa. Jehobah ya ƙara cewa: “Wannan shi ne Ɗana, wanda nake ƙauna, ina jin daɗinsa ƙwarai.” Amma a wannan lokacin Jehobah ya daɗa cewa: “Ku saurare shi!”

8. Ta yaya wahayin ya shafi Yesu da manzaninsa?

8 Wannan wahayin ya nuna ɗaukaka da ikon da Yesu zai samu sa’ad da ya zama Sarkin Mulkin Allah. Babu shakka, wannan wahayin ya ƙarfafa Kristi, hakan zai taimaka masa ya jimre da wahala da mutuwar azaba da zai yi. Ƙari ga haka, wannan wahayin ya sa almajiransa su ƙarfafa bangaskiyarsu don jarrabawar da za su fuskanta a nan gaba da kuma aiki mai wuya da za su yi. Bayan misalin shekara 30, manzo Bitrus ya yi maganar wannan wahayi da Yesu ya canja kamanni, kuma hakan ya nuna cewa ya tuna da abin da ya faru sosai.​—2 Bit. 1:​16-18.

9. Wace shawara mai kyau ce Yesu ya ba almajiransa?

9 “Ku saurare shi!” Jehobah ya nuna cewa yana son mu saurari Ɗansa kuma mu riƙa yi masa biyayya. Me Yesu ya ce sa’ad da yake duniya? Ya koyar da abubuwa da yawa da suke da muhimmanci mu saurara! Alal misali, ya koya wa mabiyansa yadda za su riƙa wa’azi kuma ya tuna musu a kai a kai su zauna da shiri. (Mat. 24:42; 28:​19, 20) Ban da haka, ya gaya musu su riƙa yin ƙwazo sosai, kuma ya ƙarfafa su kada su karaya. (Luk. 13:24) Yesu ya kuma nuna wa mabiyansa cewa yana da muhimmanci su riƙa ƙaunar juna, su kasance da haɗin kai kuma su riƙa bin umurninsa. (Yoh. 15:​10, 12, 13) Wannan shawarar da Yesu ya ba almajiransa ta dace! Kuma tana da muhimmanci a yau kamar yadda take sa’ad da Yesu ya ba da shawarar.

10-11. Ta yaya za mu nuna muna saurarar Yesu?

10 Yesu ya ce: “Duk wanda yake na gaskiya, yakan saurari muryata.” (Yoh. 18:37) Muna saurarar Yesu ta “yin haƙuri da juna.” (Kol. 3:13; Luk. 17:​3, 4) Ƙari ga haka, muna saurarar sa ta yin wa’azi da ƙwazo “ko da zarafi ko babu zarafi.”​—2 Tim. 4:2.

11 Yesu ya ce: “Tumakina sukan yi biyayya da abin da nake faɗa.” (Yoh. 10:27) Mabiyan Kristi suna saurarar sa ta wurin yin abin da ya ce da kuma bin umurninsa. Ba sa barin “damuwar rayuwar duniya” ta raba hankalinsu. (Luk. 21:34) Maimakon haka, bin umurnin Yesu ya fi muhimmanci a gare su har a lokacin da suke shan wahala. ’Yan’uwa da yawa suna fuskantar jarrabawa sosai don masu hamayya suna kai musu hari. Ban da haka, suna fama da talauci da kuma bala’i. Duk da waɗannan abubuwan da suke fuskanta, suna da aminci ga Jehobah. Yesu ya tabbatar wa irin waɗannan cewa: “Duk wanda ya san umarnaina, yana binsu kuma, shi ne yake ƙaunata. Wanda ya ƙaunace ni kuwa, Ubana zai ƙaunace shi.”​—Yoh. 14:21.

Hidimar mu tana taimaka mana mu ci gaba da saurarar Yesu (Ka duba sakin layi na 12) *

12. A wace hanya ce kuma za mu saurari Yesu?

12 Wata hanyar da muke saurarar Yesu ita ce ta yin biyayya ga waɗanda suke ja-goranci a tsakaninmu. (Ibran. 13:​7, 17) Ƙungiyar Allah ta yi wasu canje-canje kwanan nan, hakan ya ƙunshi sababbin kayayyaki da hanyoyin yin wa’azi. An canja yadda ake taron tsakiyar mako da yadda ake gina da gyara da kuma kula da Majami’un Mulki. Ana yin waɗannan abubuwa don mu amfana, kuma hakan ya nuna cewa ’yan’uwa a ƙungiyar Allah suna ƙaunar mu. Babu shakka muna godiya don hakan! Muna da tabbaci cewa Jehobah zai albarkace mu idan muka bi umurnin ƙungiyarsa.

13. Ta yaya za mu amfana idan muka saurari Yesu?

13 Za mu amfana idan muka yi biyayya ga dukan abubuwan da Yesu ya koyar. Yesu ya yi wa almajiransa alkawari cewa koyarwarsa za ta ƙarfafa su. Ya ce: “Za ku sami hutu a zuciyarku. Gama gungumena yana da sauƙi, umarnaina kuma ba nauyi.” (Mat. 11:​28-30) Kalmar Allah wadda ta ƙunshi labaran rayuwar Yesu da hidimarsa a littafin Matiyu da Markus da Luka da kuma Yohanna tana ƙarfafa mu kuma tana sa mu zama masu hikima. (Zab. 19:7; 23:3) Yesu ya ce: “Albarka ta fi tabbata ga waɗanda suke jin kalmar Allah, suke kuma kiyaye ta!”​—Luk. 11:28.

‘ZAN ƊAUKAKA SUNANA’

14-15. (a) Kamar yadda aka ambata a littafin Yohanna 12:​27, 28, a wane lokaci na uku ne Jehobah ya yi magana daga sama? (b) Me ya sa furucin Jehobah ya ƙarfafa Yesu?

14 Karanta Yohanna 12:​27, 28. Littafin Yohanna ya ambata lokaci na uku da Jehobah ya yi magana daga sama. ’Yan kwanaki kafin Yesu ya mutu, yana Urushalima don ya yi idi na ƙarshe, wato idin Kafara, sai ya ce: “Ina jin nauyi a raina.” Kuma ya yi addu’a cewa: “Ya Uba, ka ɗaukaka sunanka.” Sai Jehobah ya yi magana daga sama, ya ce: “Ai, na riga na ɗaukaka shi, zan ƙara ɗaukaka shi kuma.”

15 Yesu ya damu don yana da babban hakkin kasancewa da aminci ga Jehobah. Ya san cewa zai sha matsananciyar wahala kuma zai yi mutuwar azaba. (Mat. 26:38) Abin da ya fi muhimmanci ga Yesu shi ne ya ɗaukaka sunan Ubansa. An zargi Yesu cewa shi mai saɓo ne, kuma ya damu cewa mutuwarsa za ta sa a zargi sunan Allah. Babu shakka, furucin Jehobah ya ƙarfafa Yesu sosai don ya tabbata cewa za a ɗaukaka sunan Jehobah. Ƙari ga haka, furucin Ubansa ya ƙarfafa Yesu ya jimre da wahalar da zai sha. Ko da yake wataƙila Yesu ne kaɗai ya fahimci abin da Ubansa ya ce a wannan lokacin, Jehobah ya tabbatar da cewa an rubuta furucinsa don mu amfana.​—Yoh. 12:​29, 30.

Jehobah zai ɗaukaka sunansa kuma ya ceci mutanensa (Ka duba sakin layi na 16) *

16. A wasu lokuta, me ya sa za mu riƙa damuwa game da yadda ake zargin sunan Allah?

16 Kamar Yesu, mai yiwuwa mu ma muna damuwa game da yadda ake zargin sunan Jehobah. Wataƙila an taɓa yi mana rashin adalci kamar Yesu. Ko kuma mun damu don masu hamayya sun yaɗa ƙarya game da mu. Ƙari ga haka, muna iya yin tunanin yadda wannan ƙaryar za ta sa a zargi sunan Jehobah da kuma ƙungiyarsa. A irin waɗannan lokutan, furucin Jehobah zai ƙarfafa mu sosai. Bai kamata mu riƙa damuwa ainun ba. Ya kamata mu kasance da tabbaci cewa Allah zai ba mu ‘salama iri wadda ta wuce dukan ganewar ɗan Adam, za ta kuma tsare zukatanmu da tunaninmu cikin Almasihu Yesu.’ (Filib. 4:​6, 7) Jehobah zai ci gaba da ɗaukaka sunansa. Zai yi amfani da Mulkinsa don ya kawar da dukan matsalolin da Shaiɗan da duniyarsa suka jawo wa bayin Jehobah.​—Zab. 94:​22, 23; Isha. 65:17.

ZA MU AMFANA IDAN MUKA SAURARI JEHOBAH

17. Kamar yadda yake a littafin Ishaya 30:​21, ta yaya Jehobah yake mana magana a yau?

17 Har ila Jehobah yana yi mana magana a yau. (Karanta Ishaya 30:21.) Hakika, Allah ba ya yi mana magana daga sama. Amma ya tanadar mana da Littafi Mai Tsarki da ke ɗauke da umurninsa. Ƙari ga haka, ruhun Jehobah yana sa “bawan nan mai aminci” ya riƙa ba bayinsa abinci a daidai lokaci. (Luk. 12:42) Kuma muna samun isashen abinci, wato littattafai da aka buga da waɗanda ake amfani da su a na’urori da bidiyoyi da kuma waɗanda ake saurarawa!

18. Ta yaya abubuwan da Jehobah ya faɗa za su sa ka ƙarfafa bangaskiyarka kuma ka kasance da gaba gaɗi?

18 Mu riƙa tuna abin da Jehobah ya faɗa sa’ad da Ɗansa yake duniya! Bari Kalmar Allah ta sa mu kasance da tabbaci cewa Jehobah zai magance dukan matsalolin da Shaiɗan da mutanensa suka jawo mana. Ƙari ga haka, mu ƙuduri niyyar yin biyayya ga Jehobah. Idan muka yi hakan, za mu iya jimre duk wata matsalar da muke fuskanta a yanzu da kuma waɗanda za su iya tasowa. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ya kamata ku jimre, domin ta yin haka ne za ku aikata nufin Allah. Bayan haka kuma ku karɓi abin da aka yi muku alkawari.”​—Ibran. 10:36.

WAƘA TA 4 “Jehobah Makiyayina Ne”

^ sakin layi na 5 Sa’ad da Yesu yake duniya, Jehobah ya yi magana da shi sau uku. A sau ɗaya cikin waɗannan lokutan, Jehobah ya gaya wa almajiran Yesu su saurari Ɗansa. A yau, Jehobah yana yin amfani da Kalmarsa, wadda ta haɗa da koyarwar Yesu da kuma ƙungiyarsa don ya yi mana magana. A wannan talifin, za mu tattauna yadda za mu amfana idan muka saurari Jehobah da kuma Yesu.

^ sakin layi na 52 BAYANNAI A KAN HOTO: Wani dattijo ya lura cewa wani bawa mai hidima yana taimakawa wajen kula da Majami’ar Mulki da kuma yin aiki a kantar littattafai. Sai dattijon ya yaba masa sosai.

^ sakin layi na 54 BAYANI A KAN HOTO: Wasu ma’aurata a ƙasar Saliyo suna gayyatar wani mai kamun kifi zuwa taro.

^ sakin layi na 56 BAYANI A KAN HOTO: Shaidu da ke ƙasar da aka saka takunkumi a aikinmu suna yin taro a wani gida. Ba su yi ado sosai ba don kada su jawo hankalin mutane.