Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 10

Mene ne Yake Hana Ni Yin Baftisma?

Mene ne Yake Hana Ni Yin Baftisma?

“Dukansu biyu suka sauka suka shiga cikin ruwan, sai Filibus ya yi wa mutumin nan baftisma.”​—A. M. 8:38.

WAƘA TA 52 Alkawarinmu ga Jehobah

ABIN DA ZA A TATTAUNA *

1. Adamu da Hauwa’u sun yi hasarar me, kuma wane sakamako ne hakan ya jawo?

WAYE NE ke da ikon gaya mana abin da ya dace da wanda bai dace ba? A lokacin da Adamu da Hauwa’u suka ci ’ya’yan itacen sanin nagarta da mugunta, sun nuna cewa ba su yarda da Allah da kuma ƙa’idodinsa ba. Sun kafa wa kansu ƙa’idodi a kan abin da ya dace da wanda bai dace ba. (Far. 3:22) Kuma hakan ya sa sun rasa abubuwa da dama, har da dangantakarsu da Jehobah. Sun rasa zarafin yin rayuwa har abada kuma dukan ’ya’yansu sun gāji zunubi da mutuwa. (Rom. 5:12) Babu shakka, zaɓinsu ya jawo baƙin ciki.

Bahabashen ya ce a yi masa baftisma da zarar ya koya game da Yesu (Ka duba sakin layi na 2-3)

2-3. (a) Wane mataki ne Bahabashen ya ɗauka sa’ad da Filibus ya yi masa wa’azi? (b) Waɗanne albarku ne muke samu sa’ad da muka yi baftisma, kuma waɗanne tambayoyi ne za mu amsa?

2 Bari mu gwada zaɓin da Adamu da Hauwa’u suka yi da wanda wani Bahabashe ya yi sa’ad da Filibus ya yi masa wa’azi. Bahabashen ya yi farin ciki sosai don alherin da Jehobah da Yesu suka yi masa, har hakan ya motsa shi ya gaggauta yin baftisma. (A. M. 8:​34-38) Idan mun yi alkawarin bauta wa Jehobah kuma muka yi baftisma yadda Bahabashen ya yi, muna nuna cewa muna godiya don abin da Jehobah da kuma Yesu suka yi mana. Muna kuma nuna cewa mun dogara ga Jehobah kuma mun amince cewa yana da ikon gaya mana abin da ya dace da wanda bai dace ba.

3 Ka yi tunani a kan albarkar da za mu samu idan muka bauta wa Jehobah! Abin farin ciki ne cewa lokaci na zuwa da za mu sami dukan abubuwan da Adamu da Hauwa’u suka yi hasara, har da zarafin yin rayuwa har abada. Hadayar da Yesu ya yi yana sa Jehobah ya gafarta zunubanmu kuma mu kasance da lamiri mai kyau. (Mat. 20:28; A. M. 10:43) Ya kuma sa mu kasance cikin iyalin Jehobah waɗanda za su sami albarka a nan gaba. (Yoh. 10:​14-16; Rom. 8:​20, 21) Duk da waɗannan amfanin da muka ambata, wasu da sun riga sun koya game da Jehobah suna jinkirin bin misalin wannan Bahabashen. Mene ne yake hana su yin baftisma? Ta yaya za su iya magance wannan matsalar?

ABUBUWAN DA KE HANA WASU YIN BAFTISMA

Ƙalubalen da wasu suka fuskanta kafin su yi baftisma

Rashin Gaba Gaɗi (Ka duba sakin layi na 4-5) *

4-5. Waɗanne ƙalubale ne wani matashi mai suna Avery da wata mai suna Hannah suka fuskanta?

4 Rashin gaba gaɗi. Akwai wani matashi mai suna Avery wanda iyayensa Shaidun Jehobah ne. Babansa dattijo ne mai kirki kuma ya manyanta. Duk da haka, Avery ya yi jinkirin yin baftisma. Me ya sa? Ya ce: “Ina ganin ba zan iya kasancewa kamar babana ba.” Ya kuma ji tsoro cewa ba zai iya yin ayyukan da za a ba shi a ikilisiya a nan gaba ba. “Na ji tsoro za a ce in yi jawabi ko addu’a ko kuma in ja-goranci ’yan’uwa a wa’azi.”

5 Wata ’yar shekara 18 mai suna Hannah ta yi fama da rashin gaba gaɗi. Iyayenta Shaidun Jehobah ne, duk da haka, ta yi shakka cewa za ta iya bin ƙa’idodin Jehobah. Me ya sa? Hannah ta rena kanta sosai. A wasu lokuta, tana yin baƙin ciki sosai har ta ji wa kanta rauni. Ta ce: “Ban taɓa gaya wa kowa abin da nake yi ba, har iyayena. Kuma na yi tsammani cewa Jehobah ba zai so in zama baiwarsa ba saboda abubuwan da nake yi.”

Rinjayar Abokai (Ka duba sakin layi na 6) *

6. Mene ne ya hana Vanessa yin baftisma?

6 Rinjayar abokai. Wata ’yar shekara 22 mai suna Vanessa ta ce, “Ina da wata ƙawa da muke abokantaka kusan shekara goma.” Amma wannan ƙawar Vanessa da ba ta bauta wa Jehobah ba ta so Vanessa ta yi baftisma. Hakan ya sa ta baƙin ciki kuma ta ce: “Samun sababbin ƙawaye yana min wuya kuma na ji tsoro cewa idan na daina yin cuɗanya da ita, ba zan iya yin wata ƙawa ba.”

Tsoron Yin Kuskure (Ka duba sakin layi na 7) *

7. Tsoron me wata mai suna Makayla take ji?

7 Tsoron yin kuskure. Wata mai suna Makayla tana ’yar shekara biyar sa’ad da aka yi wa yayanta yankan zumunci. Yayin da take girma, ta ga baƙin cikin da hakan ya jawo wa iyayenta. Makayla ta ce: “Ina jin tsoro cewa idan na yi baftisma, zan yi kuskure kuma hakan zai sa a yi mini yankan zumunci. A sakamako, hakan zai daɗa sa iyayena baƙin ciki.”

Tsoron Tsanantawa (Ka duba sakin layi na 8) *

8. Mene ne ya sa wani matashi mai suna Miles jin tsoro?

8 Tsoron tsanantawa. Akwai wani mai suna Miles wanda mahaifiyarsa ba Mashaidiya ba ce, amma babansa da matar babansa Shaidu ne. Miles ya ce: “Ni da mahaifiyata mun zauna tare har tsawon shekara 18, kuma na ji tsoron gaya mata cewa ina so in yi baftisma. Na ga abin da ta yi sa’ad da babana ya zama Mashaidi kuma hakan ya sa in ji tsoro cewa za ta tsananta mini.”

TA YAYA ZA MU MAGANCE WAƊANNAN MATSALOLIN?

9. Mene ne zai iya faruwa idan ka koyi yadda Jehobah yake nuna ƙauna da haƙuri?

9 Adamu da Hauwa’u ba su yi biyayya ga Jehobah ba domin ba su ƙaunace shi ba sosai. Amma duk da haka, Jehobah ya ƙyale su su rayu don su haifi yara kuma za su bukaci yanke shawara a kan yadda za su rene su. Sakamakon shawarar da Adamu da Hauwa’u suka yanke na ƙin bin ja-gorancin Jehobah ya nuna sarai cewa ba su da hankali. Kayinu, ɗansu na fari ya kashe ƙanensa, kuma sannu-a-hankali, mugunta da son kai ya zama ruwan dare gama gari. (Far. 4:8; 6:​11-13) Amma Jehobah ya shirya wata hanyar da zai ceci ’ya’yan Adamu da Hauwa’u da suke so su bauta masa. (Yoh. 6:​38-40, 57, 58) Yayin da kake koyon yadda Jehobah yake nuna ƙauna da haƙuri, za ka daɗa ƙaunar sa sosai. Ba za ka so yin irin zaɓin da Adamu da Hauwa’u suka yi ba, amma za ka yi alkawarin bauta wa Jehobah.

Yadda za ka iya magance ƙalubalen

(Ka duba sakin layi na 9-10) *

10. Me ya sa yin bimbini a kan Zabura 19:7 zai iya taimaka mana mu bauta wa Jehobah?

10 Ka ci gaba da koyo game da Jehobah. Yayin da kake koyo game da Jehobah, za ka daɗa kasancewa da tabbaci cewa za ka iya faranta masa rai. Avery da aka ambata ɗazu ya ce: “Karanta alkawarin da ke Zabura 19:7 (Karanta) da kuma yin bimbini a kansa yana ƙara min gaba gaɗi.” Avery ya daɗa ƙaunar Jehobah sa’ad da ya ga yadda ya cika wannan alkawarin. Ƙaunarmu ga Jehobah tana kuma taimaka mana mu tsani abubuwan da Jehobah ba ya so kuma mu bauta masa. Hannah da muka ambata ɗazu ta ce: “Karanta Littafi Mai Tsarki da kuma yin nazari ya taimaka mini in san cewa Jehobah ba ya farin ciki idan na ji wa kaina rauni.” (1 Bit. 5:7) Daga baya, Hannah ta soma “aikata kalmar Allah.” (Yaƙ. 1:22) Wane sakamako ne ta samu? Ta ce: “Ganin yadda na amfana daga yin biyayya ga Jehobah ya sa in daɗa ƙaunar sa. A yanzu, ina da tabbaci cewa Jehobah zai riƙa taimaka mini a duk sa’ad da nake bukatar taimakonsa.” Hannah ta daina ji wa kanta rauni. Daga baya, ta yi alkawarin bauta wa Jehobah kuma ta yi baftisma.

(Ka duba sakin layi na 11) *

11. Me ya taimaki Vanessa ta yi abokan kirki, kuma wane darasi ne hakan ya koya mana?

11 Ku zaɓi abokan kirki. Vanessa da muka ambata ɗazu ta gano daga baya cewa ƙawarta ce take hana ta bauta wa Jehobah. A sakamakon haka, sai ta daina cuɗanya da ita kuma ta samo wasu abokai a cikin ikilisiya. Ta ce misalin Nuhu da iyalinsa ne ya taimaka mata. Ta daɗa cewa: “Suna kewaye da mutanen da ba sa ƙaunar Jehobah, amma sun yi cuɗanya da junansu.” Bayan da Vanessa ta yi baftisma, ta soma hidimar majagaba. A yau Vanessa ta ce, “Matakin da na ɗauka ya taimaka mini in yi abokan kirki a ikilisiyarmu da kuma wasu ikilisiyoyi.” Kai ma za ka iya yin abokan kirki idan kana ƙwazo sosai a hidimar Jehobah.​—Mat. 24:14.

(Ka duba sakin layi na 12-15) *

12. Wane irin tsoro ne Adamu da Hauwa’u ba su da shi, kuma wane sakamako ne hakan ya jawo?

12 Tsoron da ya dace da wanda bai dace ba. Akwai wasu lokutan da jin tsoro ya dace. Alal misali, ya kamata mu riƙa jin tsoron ɓata wa Jehobah rai. (Zab. 111:10) Da a ce Adamu da Hauwa’u sun ji irin wannan tsoron, da ba su yi tawaye da Jehobah ba. Amma sun yi tawaye da Jehobah kuma bayan haka, idanunsu sun buɗe domin sun gane cewa sun yi zunubi. Sun soma jin kunya domin sun fahimci cewa suna tsirara. Daga baya, ’ya’yansu sun gāji zunubi da mutuwa.​—Far. 3:​7, 21.

13-14. (a) Kamar yadda 1 Bitrus 3:21 ya nuna, me ya sa bai kamata mu ji tsoron mutuwa ba? (b) Me ya sa ya kamata mu ƙaunaci Jehobah?

13 Gaskiya ne cewa muna bukatar mu riƙa jin tsoron Jehobah, amma bai kamata mu riƙa jin tsoron mutuwa ba. Jehobah ya riga ya yi mana tanadi don mu sami rai na har abada. Idan muka yi zunubi kuma muka tuba da gaske, Jehobah zai gafarta mana. Zai gafarta mana domin muna da bangaskiya cewa hadayar Yesu za ta sa mu sami ceto. Hanya ta musamman da muke nuna bangaskiya ita ce ta wajen yin alkawarin bauta wa Allah da kuma yin baftisma.​—Karanta 1 Bitrus 3:21.

14 Muna da dalilai da yawa na nuna ƙauna ga Jehobah. Jehobah yana tanadar mana da abubuwa masu kyau da muke mora a koyaushe kuma yana koya mana gaskiya game da kansa da kuma nufe-nufensa. (Yoh. 8:​31, 32) Ya yi mana tanadin ikilisiyar Kirista don ta ja-gorance mu kuma ta tallafa mana. Jehobah yana taimaka mana mu jimre da matsalolinmu kuma ya ce za mu rayu har abada a cikin aljanna a nan gaba. (Zab. 68:19; R. Yar. 21:​3, 4) Idan muka yi bimbini a kan abubuwan da Jehobah ya yi don yana ƙaunar mu, hakan zai sa mu ƙaunace shi. Kuma idan muna ƙaunar Jehobah, ba za mu riƙa yawan jin tsoro ba. Za mu ji tsoron ɓata wa Jehobah rai domin yana ƙaunar mu sosai.

15. Mene ne ya taimaka wa Makayla ta daina jin tsoro?

15 Makayla da muka ambata ɗazu ta daina jin tsoron yin kuskure sa’ad da ta fahimci cewa Jehobah yana gafarta wa mutane. Ta ce: “Na gano cewa dukanmu ajizai ne kuma muna yin kuskure. Na kuma fahimci cewa Jehobah yana ƙaunar mu kuma zai gafarta mana don Yesu ya mutu dominmu.” Ƙaunarta ga Jehobah ya motsa ta ta yi alkawarin bauta wa Jehobah kuma ta yi baftisma.

(Ka duba sakin layi na 16) *

16. Mene ne ya taimaka wa Miles ya daina jin tsoro tsanantawa?

16 Miles da muka ambata ɗazu cewa yana tsoro mahaifiyarsa za ta tsananta masa idan ya yi baftisma, ya nemi taimakon wani mai kula da da’ira. Miles ya ce: “Mahaifiyar mai kula da da’iran ma ba ta bauta wa Jehobah. Ya taimaka mini in yi tunanin yadda zan sa mahaifiyata ta yarda cewa ba babana ba ne yake tilasta mini in yi baftisma ba, amma zaɓina ne.” Ba ta yi farin ciki ba. Daga baya ya bar gidanta, amma duk da haka, bai yi watsi da shawarar da ya yanke ba. Ya daɗa cewa: “Ganin alherin da Jehobah ya yi mana ya ratsa zuciyata sosai. Yin tunani a kan hadayar da Yesu ya yi mana ya sa in fahimci cewa Jehobah yana ƙauna ta sosai. Hakan ya taimaka mini in yi alkawarin bauta wa Jehobah kuma in yi baftisma.”

KA TSAYA A KAN ZAƁIN DA KA YI

Za mu iya nuna cewa muna godiya don alherin da Jehobah ya yi mana (Ka duba sakin layi na 17)

17. Wane zarafi ne muke da shi?

17 Hauwa’u ta ƙi Jehobah a lokacin da ta ci ’ya’yan itacen lambun Adnin. Sa’ad da Adamu ya bi ta cin ’ya’yan itacen, bai nuna godiya don alherin da Jehobah ya yi musu ba. Dukanmu muna da zarafin nunawa ko muna goyon bayansu ko kuma muna godiya don alherin Jehobah. Idan mun yi baftisma, muna nuna wa Jehobah cewa yana da ikon gaya mana abin da ya dace da wanda bai dace ba. Muna kuma nuna cewa muna ƙaunar Ubanmu kuma mun dogara gare shi.

18. Me zai taimaka mana mu yi nasara a bautarmu ga Jehobah?

18 Bayan mun yi baftisma, muna fuskantar ƙalubalen bin ƙa’idodin Jehobah kowace rana. Miliyoyin mutane a faɗin duniya suna yin hakan. Za ka iya yin koyi da su idan ka ci gaba da yin nazarin Kalmar Allah da yin cuɗanya a kai a kai da ’yan’uwa da kuma gaya wa mutane abubuwan da ka koya game da Jehobah da ƙwazo. (Ibran. 10:​24, 25) Idan kana so ka yanke shawara, zai dace ka bi shawarar da ke Kalmar Allah da kuma wadda ƙungiyarsa ke bayarwa. (Isha. 30:21) Idan ka yi hakan, za ka yi nasara a dukan ayyukanka.​—K. Mag. 16:​3, 20.

19. Me ya kamata ka riƙa yin tunani a kai, kuma me ya sa?

19 Yin tunani a kan yadda kake amfana don bin ja-gorancin Jehobah zai taimaka maka ka so shi da kuma ƙa’idodinsa. A sakamako, Shaiɗan ba zai iya rinjayar ka ba. Ka yi tunanin yadda rayuwarka za ta kasance nan da shekara dubu. Za ka ga cewa shawarar da ka yanke na bauta wa Jehobah shawara ce mai kyau sosai!

WAƘA TA 28 Yadda Za Mu Zama Abokan Jehobah

^ sakin layi na 5 Zaɓi mafi muhimmanci da mutum zai iya yi shi ne yanke shawarar yin baftisma. Me ya sa wannan zaɓin yake da muhimmanci sosai? Za a amsa wannan tambayar a talifin nan. Talifin zai kuma taimaka wa mutanen da ke so su yi baftisma su daina yin jinkiri.

^ sakin layi na 56 BAYANI A KAN HOTO: Gaba gaɗi: Wani matashi yana tsoron yin kalami.

^ sakin layi na 58 BAYANI A KAN HOTO: Abokai: Wata Mashaidiya da ƙawarta ba ta bauta wa Jehobah ta ji kunya sa’ad da ta ga wasu Shaidu.

^ sakin layi na 60 BAYANI A KAN HOTO: Yin kuskure: Sa’ad da wata matashiya ta ga ɗan’uwanta yana barin gida don an yi masa yankan zumunci, sai ta soma tsoro cewa hakan zai iya faruwa da ita.

^ sakin layi na 62 BAYANI A KAN HOTO: Tsanantawa: Wani yaro na tsoron yin addu’a a gaban mahaifiyarsa da ba Mashaidiya ba ce.

^ sakin layi na 65 BAYANI A KAN HOTO: Gaba gaɗi: Wani matashi yana yin nazari sosai shi kaɗai.

^ sakin layi na 67 BAYANI A KAN HOTO: Abokai: Wata matashiya ta koyi cewa ya kamata ta yi alfaharin zama Mashaidiya.

^ sakin layi na 69 BAYANI A KAN HOTO: Yin kuskure: Wata matashiya ta ƙarfafa ƙaunarta ga Jehobah kuma ta yi baftisma.

^ sakin layi na 71 BAYANI A KAN HOTO: Tsanantawa: Wani yaro ya yi wa mahaifiyarsa da ba Mashaidiya ba wa’azi da ƙarfin zuciya.