Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Nagarta​—Ta Yaya Za Mu Koyi Nuna Wannan Halin?

Nagarta​—Ta Yaya Za Mu Koyi Nuna Wannan Halin?

DUKANMU muna son a ce mu mutanen kirki ne. Amma yana da wuya mu zama masu nagarta domin mutane da yawa a yau “masu ƙin nagarta” ne. (2 Tim. 3:3) Suna ƙin ƙa’idodin Jehobah. Suna mayar da abin “kirki” “mugunta,” “mugunta” kuma abin “kirki.” (Isha. 5:20) Yana da wuya mu nuna nagarta domin ajizancinmu yana shafanmu sosai. Don haka, muna iya kasancewa da irin ra’ayin wata mai suna Anne. * Duk da cewa ta yi shekaru tana bauta wa Jehobah, ta ce: “Ya mini wuya na yarda cewa ina da nagarta.”

Dukanmu za mu iya nuna nagarta domin ruhu mai tsarki ne yake sa mu kasance da wannan halin. Ruhu mai tsarki ya fi duk wani tunani marar kyau na mutanen da ke kewaye da mu da kuma duk wani irin tunanin da muke da shi. Bari mu koyi abin da nagarta ke nufi kuma mu ga yadda za nuna wannan halin.

ABIN DA NAGARTA KE NUFI

Nagarta yana nufin kasancewa mai alheri ko kirki. Ya ƙunshi kasancewa mai ɗabi’u masu kyau. Ana sanin mutumin kirki ta wajen abubuwan da yake yi don mutane su amfana. Mutumin kirki yana neman hanyoyin da zai taimaka wa mutane kuma yana yi musu alheri a kowane lokaci.

Za ku lura cewa mutane sukan yi wa ’yan iyalinsu da abokansu nagarta. Amma su kaɗai ne kawai za mu nuna wa nagarta? A gaskiya, babu wani a cikinmu da zai iya nuna nagarta a kowane lokaci. Littafi Mai Tsarki ya ce, “babu mutum mai adalci a duniyar nan mai aikata abin da yake daidai a kowane lokaci, ba tare da yin zunubi ba.” (M. Wa. 7:20) Manzo Bulus ya ce: “Na sani cewa ba wani abu mai kirki wanda yake zama a cikina.” (Rom. 7:18) A bayyane yake cewa idan muna son mu nuna nagarta, daga Jehobah ne za mu koyi yin hakan.

JEHOBAH “MAI ALHERI NE”

Jehobah ne yake kafa mizanin abin ya dace da wanda bai dace ba. Littafi Mai Tsarki ya ce game da Jehobah: “Kai mai alheri ne, kana kuwa yin alheri, koya mini ƙa’idodinka.” (Zab. 119:68) Bari mu bincika hanyoyi biyu da Jehobah yake nuna nagarta da aka ambata a wannan ayar.

Jehobah mai alheri ne. Jehobah mai nagarta ne sosai kuma ba zai taɓa daina nuna wannan halin ba. Ka yi la’akari da abin da ya faru sa’ad da Jehobah ya gaya wa Musa cewa: “Zan sa dukan darajar alherina ta wuce a gabanka.” Jehobah ya nuna wa Musa ɗaukakarsa har da yadda yake nuna nagarta. Musa ya ji wata murya tana magana cewa: “Ni ne Yahweh, ni ne Yahweh! Allah mai jinƙai ne, mai alheri, marar saurin fushi, mai yawan ƙauna marar canjawa, cike da aminci kuma, mai kiyaye ƙauna marar canjawa ga ’ya’ya har zuwa tsara ta dubu, mai gafarta laifi, da zunubin ganganci, da kowane irin zunubi. Duk da haka ba mai kāsa hukunta mai laifi ba ne.” (Fit. 33:19; 34:​6, 7) Wannan ya nuna mana cewa Jehobah yana nuna nagarta a dukan abin da yake yi. Sa’ad da Yesu yake duniya, duk da cewa shi mutumin kirki ne, ya ce: “Ai, ba wani mai kirki sai Allah kaɗai.”​—Luk. 18:19.

Muna ganin yadda Jehobah yake nuna nagarta ta abubuwan da ya halitta

Ayyukan Jehobah suna da kyau. Dukan abubuwan da Jehobah ya halitta suna nuna cewa shi mai nagarta ne. “Yahweh mai alheri ne ga kowa, tausayinsa yana a kan dukan halittunsa.” (Zab. 145:9) Jehobah ba ya nuna son kai, shi ya sa ya yi tanadin abubuwan da za su sa ’yan Adam su ci gaba da rayuwa. (A. M. 14:17) Yana nuna cewa shi mai nagarta ne sa’ad da ya gafarta mana zunubanmu. Wani marubucin Zabura ya ce: “Ubangiji, mai alheri ne kuma mai yin gafara.” (Zab. 86:5) Muna da tabbaci cewa “babu abu mai kyau wanda Yahweh yake hana wa waɗanda suke tafiya da gaskiya a zuci.”​—Zab. 84:11.

“KU KOYI YIN ABIN DA YAKE DAIDAI”

Jehobah ya halicce mu da irin halayensa, don haka, muna iya zama mutanen kirki kuma mu riƙa nuna alheri. (Far. 1:27) Duk da haka, Littafi Mai Tsarki ya ƙarfafa bayin Allah su “koyi yin abin da yake daidai.” (Isha. 1:17) Amma ta yaya za mu koyi nuna nagarta? Bari mu tattauna hanyoyi uku da za mu iya yin hakan.

Da farko, muna iya roƙan Jehobah ya ba mu ruhu mai tsarki. Ruhu mai tsarki yana taimaka wa Kiristoci su riƙa nuna nagarta. (Gal. 5:22) Zai taimaka mana mu soma ƙaunar abin da Allah yake so kuma mu guji abin da ba ya so. (Rom. 12:9) Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Jehobah yana iya “ƙarfafa mu cikin kowane kyakkyawan aiki da kyakkyawar magana.”​—2 Tas. 2:​16, 17.

Na biyu, mu riƙa karanta Kalmar Allah. Idan muna yin hakan, Jehobah zai sa mu “gane kowace hanya mai kyau” kuma yana shirya mu don “kowane irin kyakkyawan aiki.” (K. Mag. 2:9; 2 Tim. 3:17) Idan muka karanta Littafi Mai Tsarki kuma muka yi bimbini a kai, hakan zai taimaka mana mu cika zuciyar mu da abubuwa masu kyau da za su taimaka mana a nan gaba.​—Luk. 6:45; Afis. 5:9.

Na uku, mu riƙa yin iya ƙoƙarinmu don mu “bi gurbin kirki.” (3 Yoh. 11) Akwai misalai da yawa na mutanen kirki a Littafin Mai Tsarki da za mu iya yin koyi da su. Amma misalin da ya fi muhimmanci shi ne na Jehobah da kuma Yesu. Muna iya bincika rayuwar mutanen kirki da aka ambata a Littafi Mai Tsarki. Mutane biyu da za mu iya yin tunani a kan labarinsu su ne Tabita da kuma Barnaba. (A. M. 9:36; 11:​22-24) Kana iya amfana sosai idan ka yi nazarin abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da su. Sa’ad da kake yin nazarin, ka lura da abin da Littafi Mai Tsarki ya ce sun yi don su taimaka wa mutane. Ka yi tunanin hanyoyin da za ka iya taimaka ma wasu a iyalinka da kuma a ikilisiya. Ƙari ga haka, ka lura da sakamakon da Tabita da kuma Barnaba suka samu domin sun nuna wa mutane nagarta. Kai ma kana iya amfana ta yin hakan.

A yau, mukan tuna wasu da suke da kirki. Ka yi tunanin dattawa masu “son nagarta,” da suke aiki tuƙuru a ikilisiyoyi. Akwai kuma ’yan’uwa mata amintattu da suka “koyar da abin nagari” ta furucinsu da kuma misalansu. (Tit. 1:8; 2:3) Wata ’yar’uwa mai suna Roslyn ta ce: “Abokiyata takan yi ƙoƙari sosai don ta taimaka ma wasu a ikilisiya. Tana yin tunani game da yanayinsu kuma ta ba su kyauta ko da kaɗan ne. A gaskiya, ita mai kirki ce.”

Jehobah yana ƙarfafa mutanensa su “nema yin abin kirki.” (Amos 5:14) Idan muka yin hakan, za mu so abin da Jehobah ya ce yake da nagari kuma zai taimaka mana mu so yin nagarta.

Muna ƙoƙarin yin nagarta da kuma kirki

Ba ma bukatar mu ba mutane kyauta mai tsada kafin a san cewa mu masu kirki ne. Alal misali, idan muna son shuka ya yi girma, ba za mu zuba ruwa da yawa sau ɗaya kawai ba. Amma za mu riƙa zubawa kaɗan-kaɗan. Hakazalika, ƙanana abubuwa da muke yi don mu taimaka wa mutane zai nuna cewa mu masu nagarta ne.

Littafi Mai Tsarki ya ƙarfafa mu mu kasance a “shirye” don mu taimaka wa ’yan’uwanmu. (2 Tim. 2:21; Tit. 3:1) Idan muka mai da hankali don mu san irin matsalolin da ’yan’uwa suke fuskanta, hakan zai taimaka mana mu ga hanyoyin da za mu iya tallafa musu da kuma ƙarfafa su. (Rom. 15:2) Taimaka wa ’yan’uwa ya ƙunshi ba su abin da muke da shi. (K. Mag. 3:27) Muna iya gayyatar su gidanmu don mu ci abinci tare ko kuma don mu ƙarfafa juna. Ban da haka, muna iya ziyartar marar lafiya ko kuma mu kira shi ta waya. Hakika da akwai hanyoyi da yawa da za mu iya yin “magana da take da amfani domin ƙarfafawar juna bisa ga bukatarku. Ta haka maganarku za ta zama da amfani ga masu jinta.”​—Afis. 4:29.

Kamar Jehobah, muna yin iya ƙoƙarinmu don mu taimaka wa mutane. Saboda haka, ba ma nuna son kai. Hanya ta musamman da muke nuna muna ƙaunar mutane ita ce ta wajen yi musu wa’azi. Yesu ya umurce mu cewa mu yi nagarta har ga waɗanda suka tsane mu. (Luk. 6:27) Ba laifi ba ne mu nuna wa mutane alheri da kuma yi masu abin kirki don “babu dokar da ta hana waɗannan abubuwa.” (Gal. 5:​22, 23) Idan muka ci gaba da yin nagarta har a lokacin da ake tsananta mana, hakan zai sa mutane su bauta wa Jehobah kuma su ɗaukaka shi.​—1 Bit. 3:​16, 17.

ZA MU AMFANA IDAN MUNA NUNA NAGARTA

“Mutumin kirki kuma yakan sami ladan aikinsa.” (K. Mag. 14:14) Waɗanne lada ne zai samu? Idan muka nuna wa mutane nagarta, hakan zai sa su ma su yi mana kirki. (K. Mag. 14:22) Ko da mutane ba sa bi da mu yadda ya kamata, mu ci gaba da yi musu nagarta. Hakan yana iya sa su canja halinsu kuma su soma bi da mu yadda ya dace.​—Rom. 12:20.

Idan muna yin nagarta, za mu amfana sosai. ’Yan’uwa da yawa sun ce abin da ya faru da su ke nan. Ka yi la’akari da labarin Nancy. Ta ce: “Ni ’yar iska ce a lokacin da nake matashiya kuma ba na daraja mutane, amma sa’ad da na koyi abubuwan da Jehobah ya ce sun dace kuma na soma biyayya a gare shi, na yi farin ciki sosai. Yanzu ina da mutunci da kuma daraja.”

Dalili na musamman da ya sa muke bukatar mu riƙa nuna nagarta shi ne domin haka yana faranta wa Jehobah rai. Ko da mutane ba sa ganin abin da muke yi, Jehobah yana gani. Ya san duk lokacin da muka nuna wa mutane nagarta kuma muka yi tunanin kirki. (Afis. 6:​7, 8) Wane sakamako ne za mu samu? “Mai kirki yana samun farin jini a wurin Yahweh.” (K. Mag. 12:2) Bari mu ci gaba da zama masu nagarta. Jehobah ya yi alkawari cewa “duk mai aikata nagarta zai sami ɗaukaka da girma da salama.”​—Rom. 2:10.

^ sakin layi na 2 An canja wasu sunayen.