Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Israꞌilawa a Zamanin Dā Sun Yi Yake-Yake​—Me Ya Sa Ba Ma Yi?

Israꞌilawa a Zamanin Dā Sun Yi Yake-Yake​—Me Ya Sa Ba Ma Yi?

“IDAN ɗaya daga cikinku ya ƙi yin faɗa da Faransa ko kuma Birtaniya, dukanku za ku mutu!” Abin da wani sojan Nazi ya gaya ma wasu rukunin Shaidun Jehobah a lokacin Yaƙin Duniya na Biyu ke nan. Ko da yake sojojin Nazi sun kewaye ꞌyan’uwanmu da makamai, babu ko ɗaya daga cikin ꞌyanꞌuwanmu da ya karya dokar Jehobah. Hakika ꞌyan’uwan sun nuna ƙarfin zuciya sosai! Wannan misalin ya nuna raꞌayin Shaidun Jehobah game da yaƙi. Ba ma saka hannu a cikin yaƙe-yaƙe da ake yi a duniyar nan. Ko da an yi barazanar kashe mu, ba ma yarda mu saka hanu a yaƙe-yaƙe da ake yi a duniya.

Amma ba dukan waɗanda suke kiran kansu Kiristoci ne suka yarda da hakan ba. Sun gaskata cewa ya dace Kirista ya yi yaƙi a madadin ƙasarsa. Suna iya yin tunani cewa, ‘Isra’ilawa a zamanin dā bayin Allah ne kuma sun yi yaƙe-yaƙe, me ya sa bai dace Kiristoci su yi yaƙe-yaƙe a yau ba?’ Ta yaya za ka amsa? Za mu iya bayyana musu cewa yanayin Isra’ilawa a zamanin dā ya bambanta da na bayin Allah a yau. Za mu tattauna hanyoyi biyar da yanayoyinsu ya bambanta.

1. DUKAN BAYIN ALLAH A DĀ SUNA CIKIN ƘASA ƊAYA

A zamanin dā, Jehobah ya zaɓi al’ummar Isra’ila kuma ya mai da su mutanensa. Ya kira Isra’ilawan jama’ata mafi daraja “daga cikin dukan kabilun duniya.” (Fit. 19:5) Ya kuma zaɓa musu ƙasa guda. Don haka, sa’ad da Allah ya umurci Isra’ilawa su yi yaƙi da wasu al’ummai, ba su yi yaƙi ko kuma kashe wasu bayin Allah ba. a

A yau, bayin Jehobah “sun fito daga kowace al’umma, da zuriya, da ƙabila, da yare.” (R. Yar. 7:9) Don haka, idan bayin Allah suka saka hannu a yaƙi, za su iya kashe wasu bayin Allah kamarsu.

2. JEHOBAH YA UMURCI ISRA’ILAWA SU YI YAƘI

A zamanin dā, Jehobah ne yake gaya wa Isra’ilawa lokaci da kuma dalilin da ya sa ya kamata su je yaƙi. Alal misali, Jehobah ya umurci Isra’ilawa su yi yaƙi don su zartar da hukuncinsa a kan Kan’aniyawa waɗanda an san su da bautar aljannu da yin lalata da kuma yin hadayu da yara. Jehobah ya umurci Isra’ilawa su halaka mutanen da suke yin miyagun ayyukan nan a Ƙasar Alkawari, domin kada Isra’ilawan ma su koyi waɗannan halayen. (L. Fir. 18:​24, 25) Bayan Isra’ilawan sun mallaki Ƙasar Alkawari, akwai lokutan da Jehobah ya gaya musu cewa su je yaƙi domin su kāre ƙasar daga maƙiya. (2 Sam. 5:​17-25) Amma, Jehobah bai taɓa barin Isra’ilawan su je yaƙi a lokutan da suka ga dama ba. A lokutan da suka yi hakan, sakamakon ya yi muni sosai.​—L. Ƙid. 14:​41-45; 2 Tar. 35:​20-24.

A yau, Jehobah ba ya gaya ma ꞌyan Adam su yi yaƙi. Ƙasashe sukan yi yaƙi saboda nasu son zuciya ba don abin da Allah yake so ba. Sukan yi yaƙi domin suna so su faɗaɗa ƙasarsu ko don su sami kuɗi ko kuma don dalilai na siyasa. Waɗanda suke yin da’awa cewa suna yin yaƙin don sunan Allah kuma fa, ko kuma don su kashe maƙiyan Allah? Jehobah zai kāre masu bauta masa da gaske kuma ba da daɗewa ba zai halaka maƙiyansa a Armageddon. (R. Yar. 16:​14, 16) Jehobah zai yi amfani da mala’ikunsa ya yi yaƙin, ba ꞌyan Adam da suke bauta masa ba.​—R. Yar. 19:​11-15.

3. ISRA’ILAWAN BA SU KASHE WAƊANDA SUKA BA DA GASKIYA GA JEHOBAH BA.

Shin a yau Allah yana yi ma wata ƙasa yaƙi kamar yadda ya yi wa Israꞌilawa a Yariko?

A zamanin dā, Isra’ilawa sukan nuna jinƙai ga waɗanda suka ba da gaskiya ga Allah, amma su kashe waɗanda Jehobah ya ce su kashe. Ka yi la’akari da misalai guda biyu. Duk da cewa Jehobah ya gaya wa Isra’ilawa su hallaka Yeriko, Isra’ilawan ba su kashe Rahab da iyalinta ba domin ta ba da gaskiya. (Yosh. 2:​9-16; 6:​16, 17) Bayan haka, Isra’ilawan sun nuna jinƙai ga Gibeyonawa gabaki ɗaya domin mutanen sun daraja Jehobah.​—Yosh. 9:​3-9, 17-19.

A yau, kasashe da suke faɗa, ba sa kāre waɗanda suka ba da gaskiya. Kuma a wasu lokuta akan kashe fararen kaya da ba su ci ba, ba su sha ba a yaƙe-yaƙen da ake yi.

4. ISRA’ILAWAN SUN BI DOKOKIN ALLAH GAME DA YAƘIN

A dā, Jehobah ya umurci Isra’ilawa su bi ƙa’idodin yaƙi da ya ba su. Alal misali, akwai lokutan da Jehobah ya gaya wa Isra’ilawa su aika wa maƙiyansu “saƙon neman zaman lafiya.” (M. Sha. 20:10) Jehobah ya kuma bukaci sojojin Isra’ila su tsabtace sansaninsu kuma su kiyaye dokokinsa game da ɗa’a. (M. Sha. 23:​9-14) Yayin da sojojin ƙasashe da ke kewaye da Isra’ilawan sukan yi fyaɗe da matan da suka kwato daga yaƙi, Jehobah ya hana sojojin Isra’ilawa yin hakan. Ba za su ma iya auran matan da suka kwato daga yaƙi ba, sai sun yi wata ɗaya da cin birnin da yaƙi.​—M. Sha. 21:​10-13.

A yau, yawancin ƙasashe sun yi yarjejeniya a kan yadda za a yi yaƙi. Ko da yake an yi hakan ne domin a kāre fararen kaya, amma abin baƙin ciki ne cewa ba a kiyaye dokokin.

5. JEHOBAH YA YI FAƊA A MADADIN AL’UMMARSA

Shin a yaƙe-yaƙen da ake yi a yau ana kāre masu aminci kamar yadda Jehobah ya kāre Rahab da iyalinta a yaƙin da ya yi a Yariko?

A zamanin dā, Jehobah ya yi yaƙi a madadin Israꞌilawa, kuma ya yi alꞌajibai domin su iya yin nasara. Alal misali, ta yaya Jehobah ya taimaka wa Israꞌilawa su yi nasara a kan birnin Yariko? Da Israꞌilawan suka bi umurnin Jehobah kuma “suka yi ihu, sai katangar birnin ta rushe.” Hakan ya sa ya yi musu sauƙi su ci birnin da yaƙi. (Yosh. 6:20) Kuma ta yaya suka yi nasara a yaƙin da suka yi da Amoniyawa? “Yahweh ya jefe su da manyan duwatsun ƙanƙara daga sama. Waɗanda suka mutu ta wurin duwatsun ƙanƙara sun fi waɗanda Isra’ilawa suka kakkashe da takobi.”​—Yosh. 10:​6-11.

A yau, Jehobah ba ya faɗa a madadin wata ƙasa. Mulkinsa da kuma Yesu wanda shi ne Sarkin Mulkin ‘ba na duniya ba ne.’ (Yoh. 18:36) A maimakon haka, Shaiɗan ne yake iko a kan dukan gwamnatocin ꞌyan Adam. Munanan yaƙe-yaƙen da ake yi a duniya, sun nuna irin halayensa.​—Luk. 4:​5, 6; 1 Yoh. 5:19.

KIRISTOCI NA GASKE MASU ZAMAN LAFIYA NE

Kamar yadda muka gani, yanayinmu a yau ya bambanta sosai da na Israꞌilawa a zamanin dā. Amma dalilan nan da muka ambata ba su ne kaɗai suka sa ba ma yin yaƙi ba. Akwai wasu ƙarin dalilai. Alal misali, Allah ya annabta cewa a kwanakin ƙarshe, bayinsa “ba za su ƙara koyon dabarar yaƙi kuma ba.” Balle ma su yi yaƙi. (Isha. 2:​2-4) Ban da haka, Yesu ya ce mabiyansa “ba na duniya ba ne,” wato ba za su taɓa saka hannu a harkokin wannan duniyar da yaƙe-yaƙenta ba.​—Yoh. 15:19.

Yesu ya kuma umurci mabiyansa su yi fiye da hakan. Ya gaya musu cewa su guji irin halayen da zai kai ga ƙiyayya, fushi da kuma yaƙi. (Mat. 5:​21, 22) Ƙari ga haka, ya umurci mabiyansa su zama masu “sada zumunci” kuma su ƙaunaci maƙiyansu.​—Mat. 5:​9, 44.

Ta yaya za mu iya yin hakan? Hakika ba za mu so mu yi yaƙi ba, amma shin akwai ƙiyayya a zuciyarmu da zai iya jawo faɗa ko kuma rashin jituwa a cikin ikilisiya? Bari mu ci gaba da yin iya ƙoƙarinmu don mu kawar da irin waɗanna halayen.​—Yak. 4:​1, 11.

A maimakon mu saka hannu a yaƙe-yaƙen da ake yi a duniya, muna yin iya ƙoƙarinmu domin salama da ƙauna su ci gaba da kasancewa a sakaninmu. (Yoh. 13:​34, 35) Bari mu kuɗiri niyyar kasancewa ba ruwanmu da harkokin duniyar nan yayin da muke marmarin lokacin da Jehobah zai kawo ƙarshen yaƙe-yaƙe har abada.​—Zab. 46:9.

a Akwai lokutan da Isra’ilawa sun yi faɗa da junansu, amma Jehobah bai ji daɗin hakan ba. (1 Sar. 12:24) Amma akwai lokutan da ya amince Isra’ilawan su yi faɗa da juna domin wata kabila ta yi masa zunubi mai tsanani.​—Alƙa. 20:​3-35; 2 Tar. 13:​3-18; 25:​14-22; 28:​1-8.