Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 44

Ka Ci Gaba da Karfafa Begenka

Ka Ci Gaba da Karfafa Begenka

“Sa zuciya ga Yahweh.”​—ZAB. 27:14.

WAƘA TA 144 Mu Riƙa Ɗokin Samun Ladan!

ABIN DA ZA A TATTAUNA a

1. Wane bege ne Jehobah ya ba mu?

 JEHOBAH ya ba mu begen yin rayuwa har abada. Wasu suna da begen yin rayuwa har abada a sama da rai marar mutuwa. (1 Kor. 15:​50, 53) Amma yawancinmu muna da begen yin rayuwa har abada a nan duniya cikin koshin lafiya da kuma farin ciki. (R. Yar. 21:​3, 4) Ko da muna da begen yin rayuwa a sama ne ko a duniya, begenmu yana da daraja sosai.

2. Me ya sa muke da bege, kuma me ya sa muka faɗi hakan?

2 Kalmar nan bege, tana nufin “sa zuciya ga wani abu mai kyau da zai faru” kamar yadda aka yi amfani da shi a cikin Littafi Mai Tsarki. Za mu iya kasancewa da tabbaci cewa abubuwan da muke sa rai a kai za su faru domin Jehobah ne ya yi mana alkawarinsu. (Rom. 15:13) Mun san alkawuran da ya yi mana kuma mun san cewa ba ya fasa cika alkawuransa. (L. Ƙid. 23:19) Mun gaskata cewa Jehobah yana da niyya da kuma ikon yin duk wani abin da ya yi alkawarin cewa zai yi. Don haka, begenmu ba abu ne da muke fatan cewa zai faru ba, amma abu ne da muke da tabbacin cewa zai faru.

3. Mene ne za mu tattauna a wannan talifin? (Zabura 27:14)

3 Ubanmu na sama yana ƙaunar mu kuma yana so mu gaskata da shi. (Karanta Zabura 27:14.) Idan begenmu yana da ƙarfi, za mu iya jimre matsaloli kuma mu yi farin ciki, mu kasance da ƙarfin zuciya ko da mene ne ya faru. Bari mu tattauna yadda begenmu yake kāre mu. Za mu ga yadda begenmu yake kama da anka da kuma hular kwano. Sa’an nan za mu tattauna yadda za mu iya ƙarfafa begenmu.

BEGENMU YANA KAMA DA ANKA

4. Ta yaya begenmu yana kama da anka? (Ibraniyawa 6:19)

4 A wasiƙar da ya rubuta wa Ibraniyawa, manzo Bulus ya kwatanta begenmu da anka. (Karanta Ibraniyawa 6:19. b) Da yake manzo Bulus yana yawan yin tafiya ta jirgin ruwa, ya san cewa akan yi amfani da anka a riƙe jirgin ruwa domin kada iska ya tafi da shi. Akwai wani lokacin da manzo Bulus yake tafiya a cikin ruwa, sai aka soma iska mai ƙarfi. Sa’ad da ake iskar, ya ga yadda matuƙan jirgin ruwan suka jefa anka a cikin ruwa domin kada iska ya hura jirgin ya buga dutse. (A. M. 27:​29, 39-41) Kamar yadda anka yake riƙe jirgin ruwa, begenmu yana sa mu yi kusa da Jehobah don kada mu bijire a lokacin da muke fuskantar matsaloli kamar iska mai ƙarfi. Begenmu yana sa mu kasance da kwanciyar hankali sa’ad da muke fuskantar matsaloli, domin mun san cewa abubuwa za su yi kyau nan ba da daɗewa ba. Ka tuna cewa Yesu ya gaya mana cewa za a tsananta mana. (Yoh. 15:20) Don haka, yin tunani a kan alkawuran da Allah ya yi mana yana taimaka mana mu ci gaba da bauta ma Jehobah.

5. Ta yaya bege ya taimaka wa Yesu sa’ad da ya san cewa zai mutu?

5 Ka yi la’akari da yadda bege ya sa Yesu ya ci gaba da kasance da aminci ko da yake ya san cewa za a kashe shi. A ranar Fentakos ta 33 bayan haihuwar Yesu, manzo Bitrus ya yi ƙaulin wani nassi daga littafin Zabura da ya kwatanta yadda Yesu ya kasance da kwanciyar hankali da kuma tabbaci. Ya ce: “Jikina zai zauna da sa rai. Gama ba zai bar raina a kabari ba, ko ya bar Mai Tsarkinsa ya ruɓa ba. . . . Za ka cika ni da farin ciki ta wajen kasancewarka tare da ni.” (A. M. 2:​25-28; Zab. 16:​8-11) Ko da yake Yesu ya san cewa zai mutu, amma yana da bege cewa Jehobah zai tā da shi, kuma zai yi farin ciki don zai sake haɗuwa da Ubansa a sama.​—Ibran. 12:​2, 3.

6. Mene ne wani ɗan’uwa ya faɗa game da bege?

6 Begen da muke da shi ya taimaka ma ꞌyanꞌuwanmu da yawa su jimre matsaloli. Ka yi la’akari da misalin wani ɗan’uwa mai suna Leonard Chinn daga ƙasar Ingila. A lokacin Yaƙin Duniya na Farko, an saka shi a kurkuku domin ya ƙi ya shiga aikin soja. A kurkukun, an kulle shi a wani ɗaki shi kaɗai har na tsawon watanni biyu kuma bayan hakan, an sa shi ya yi aiki mai tsanani. Daga baya ya rubuta cewa: “Abin da na fuskanta ya nuna min cewa muna bukatar bege sosai don mu iya jimrewa. Muna da misalai masu yawa kamar na Yesu da manzanninsa da wasu annabawa da kuma alkawuran da ke Littafi Mai Tsarki. Dukansu suna ba mu bege da kuma tabbatar mana cewa abubuwa za su yi kyau a nan gaba.” Kamar yadda anka yake taimaka ma jirgin ruwa, bege ya taimaka wa Leonard kuma zai iya taimaka mana.

7. Ta yaya matsaloli suke sa begenmu ya yi ƙarfi? (Romawa 5:​3-5; Yakub 1:12)

7 Sa’ad da muka jimre matsaloli kuma muka ga yadda Jehobah yake taimaka mana, hakan zai tabbatar mana cewa Jehobah ya amince da mu. (Karanta Romawa 5:​3-5; Yakub 1:12.) Kuma begenmu zai yi ƙarfi fiye da lokacin da muka soma bauta ma Jehobah. Shaiɗan yana so matsalolinmu su sa mu sanyin gwiwa, amma da taimakon Jehobah, za mu iya jimre su.

BEGENMU YANA KAMA DA HULAR KWANO

8. Ta yaya bege yake kama da hular kwano? (1 Tasalonikawa 5:8)

8 Littafi Mai Tsarki ya kwatanta begenmu da hular kwano. (Karanta 1 Tasalonikawa 5:8.) Soja yakan saka hular kwano domin ya kāre kansa daga hari da maƙiyinsa zai kawo masa. Haka ma, a yaƙin da muke yi da Shaiɗan, muna bukatar mu kāre tunanin zuciyarmu daga harin Shaiɗan. Yakan yi amfani da abubuwa dabam-dabam domin ya gurɓata tunaninmu. Kamar yadda hular kwano take kāre kan soja, haka ma begenmu yake kāre tunanin zuciyarmu domin mu ci gaba da bauta ma Jehobah da aminci.

9. Mene ne zai faru idan mutane ba su da bege?

9 Begen da muke da shi na yin rayuwa har abada zai taimaka mana mu yanke shawarwarin da suka dace. Amma idan begenmu ya yi sanyi kuma muka soma mai da hankali ga sha’awoyin jiki, za mu iya manta da begenmu. Ka yi la’akari da misalin wasu Kiristoci da suka yi rayuwa a Korinti. Sun manta da alkawari mai muhimmanci da Allah ya yi, wato tashin matattu. (1 Kor. 15:12) Manzo Bulus ya rubuta musu cewa waɗanda ba su da begen tashin matattu sukan mai da hankali ga sha’awoyin jikinsu ne kawai. (1 Kor. 15:32) A yau ma, mutane da yawa da ba su da bege game da alkawuran da Allah ya yi mana, sukan yi iya ƙoƙarinsu domin su ji daɗin rayuwa a yanzu. Amma mu muna mai da hankali game da alkawarin da Allah ya yi mana game da nan gaba. Begenmu yana kama da hular kwano da ke kāre tunanin zuciyarmu kuma yana taimaka mana kada mu mai da hankali ga sha’awoyin jikinmu kawai don hakan zai ɓata dangantakarmu da Jehobah.​—1 Kor. 15:​33, 34.

10. Ta yaya bege zai taimaka mana mu guji yin tunani marar kyau?

10 Begenmu zai taimaka mana mu guji yin tunani cewa ba za mu iya faranta wa Allah rai ba. Alal misali, wasu za su iya cewa: ‘Ba zan iya samun rai na har abada ba domin ban cancanta ba. Ba zan taɓa iya yin abubuwan da Allah ya ce in yi ba.’ Ka tuna cewa abin da abokin Ayuba na ƙarya, wato Eliphaz ya gaya wa Ayuba ke nan. Eliphaz ya ce: “Wane ɗan Adam ne zai iya kasance marar laifi?” Ya kuma ce game da Jehobah: “Allah bai ma amince da halittunsa masu tsarki ba, ko sammai ma ba su kasance marasa laifi a gabansa ba.” (Ayu. 15:​14, 15) Wannan ƙarya ne ba kaɗan ba! Ka tuna cewa Shaiɗan ne yake so ka yi tunani kamar haka. Ya san cewa idan ka ci gaba da yin tunani kamar haka, za ka rasa begenka. A maimakon haka, ka guji irin ƙaryar nan kuma ka mai da hankali ga alkawuran da Allah ya yi. Kada ka yi shakkar cewa yana so ka yi rayuwa har abada kuma zai taimaka maka ka iya yin hakan.​—1 Tim. 2:​3, 4.

KA CI GABA DA ƘARFAFA BEGENKA

11. Me ya sa ya dace mu yi haƙuri yayin da muke jiran Allah ya cika alkawuran da ya yi mana?

11 A wasu lokuta, yana yi mana wuya mu ci gaba da ƙarfafa begenmu. Za mu iya gajiya yayin da muke jiran Allah, amma da yake Jehobah yana rayuwa tun filꞌazar, yadda yake ɗaukan lokaci ya bambanta da mu. (2 Bit. 3:​8, 9) Zai cika alkawarinsa a lokacin da ya dace, amma mai yiwuwa ba a lokacin da muke sa rai ba. Me zai taimaka mana mu ci gaba da ƙarfafa begenmu yayin da muke jira Jehobah ya cika alkawuran da ya yi mana?​—Yak. 5:​7, 8.

12. Bisa ga Ibraniyawa 11:​1, 6, wane alaƙa ne yake tsakanin bege da bangaskiya?

12 Za mu iya ƙarfafa begenmu idan mun ci gaba da kasancewa kusa da Jehobah domin shi ne zai iya cika alkawuran da ya yi mana. Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa don mu kasance da bege, dole ne mu ba da gaskiya cewa Allah yana wanzuwa kuma “yana ba da lada ga duk waɗanda suke nemansa.” (Karanta Ibraniyawa 11:​1, 6.) Idan mun ba da gaskiya cewa Allah yana wanzuwa, hakan zai taimaka mana mu kasance da tabbaci cewa zai cika alkawuran da ya yi mana. Bari mu tattauna abubuwan da za mu iya yi don mu kyautata dangantakarmu da Jehobah kuma mu ci gaba da ƙarfafa begenmu.

Yin addu’a da kuma bimbini za su sa begenmu ya ci gaba da yin ƙarfi (Ka duba sakin layi na 13-15) c

13. Ta yaya za mu yi kusa da Allah?

13 Ka yi addu’a ga Jehobah kuma ka karanta Kalmarsa. Ko da yake ba za mu iya ganin Jehobah ba, za mu iya yin kusa da shi. Za mu iya yin addu’a gare shi da tabbacin cewa zai saurare mu. (Irm. 29:​11, 12) Za mu iya sauraran Allah ta wajen karanta Kalmarsa Littafi Mai Tsarki kuma mu yi bimbini a kai. Yayin da muke karanta game da yadda Jehobah ya kula da waɗanda suka dogara gare shi a zamanin dā, begenmu zai daɗa ƙarfi. Duk abin da ke cikin Kalmar Allah “an rubuta ne domin a koyar da mu, domin mu zama da sa zuciya ta wurin jimrewa da ƙarfafawa.”​—Rom. 15:4.

14. Me ya sa yake da muhimmanci mu yi tunani a kan abin da Allah ya yi ma wasu?

14 Ka yi bimbini a kan yadda Allah ya cika alkawuransa. Ka yi la’akari da abin da Jehobah ya yi wa Ibrahim da Saratu. Sun tsufa sosai da ba za su iya haifan yara ba. Duk da haka, Allah ya yi musu alkawari cewa za su haifi ɗa. (Far. 18:10) Mene ne Ibrahim ya ce game da hakan? Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ya gaskata zai zama uban al’ummai da yawa.” (Rom. 4:​18, Mai Makamantu Ayoyi) Ko da yake Ibrahim bai san yadda Allah zai cika alkawarin da ya yi ba, ya ba da gaskiya cewa Allah zai cika alkawarin. Kuma Allah ya cika alkawarin da ya yi wa Ibrahim. (Rom. 4:​19-21) Wannan labarin ya nuna mana cewa a ko yaushe, za mu iya gaskata cewa Jehobah zai cika alkawarinsa, ko da muna ganin kamar hakan ba zai yiwu ba.

15. Me ya sa ya dace ka yi tunani a kan abubuwan da Allah ya riga ya yi maka?

15 Ka yi la’akari da abin da Jehobah ya yi maka. Ka yi tunanin yadda ka amfana daga alkawuran da ke cikin Littafi Mai Tsarki. Alal misali, Yesu ya yi alkawari cewa Jehobah zai tanadar mana da abubuwan da muke bukata. (Mat. 6:​32, 33) Yesu ya kuma gaya mana cewa Jehobah zai tanada mana ruhu mai tsarki idan muka roƙe shi. (Luk. 11:13) Jehobah ya cika alkawuran nan. Mai yiwuwa za ka iya tuna da wasu alkawuran da ya yi maka kuma yake cika su. Alal misali, ya yi alkawari cewa zai gafarta maka, zai ƙarfafa ka kuma zai tanadar maka da abubuwan da za su ƙarfafa bangaskiyarka. (Mat. 6:14; 24:45; 2 Kor. 1:3) Idan ka yi bimbini a kan abubuwan da Allah ya riga ya yi maka, hakan zai sa ka daɗa gaskata da alkawuran da ya yi game da nan gaba.

KU YI FARIN CIKI DON BEGENKU

16. Me ya sa bege kyauta ne mai kyau daga wurin Allah?

16 Begen da muke da shi game da nan gaba kyauta ne mai kyau daga gun Allah. Muna marmarin lokacin da Allah zai cika alkawuransa kuma mun gaskata cewa zai yi hakan. Begenmu yana kama da anka domin yana sa mu jimre matsaloli, mu saya da ƙarfi sa’ad da ake tsananta mana, kuma mu ci gaba da bauta ma Jehobah ko da an yi barazanar kashe mu. Yana kama da hular kwano domin yana kāre tunanin zuciyarmu don mu iya guje wa mugunta kuma mu so nagarta. Begen da muke da shi yana sa mu yi kusa da Allah kuma yana tabbatar mana da irin ƙaunar da yake yi mana. Muna amfana sosai yayin da muke ci gaba da ƙarfafa begenmu.

17. Me ya sa begenmu yana sa mu farin ciki?

17 A wasiƙarsa ga Romawa, manzo Bulus ya ƙarfafa su cewa “Ku yi farin ciki a cikin sa zuciyarku.” (Rom. 12:12) Bulus ya yi farin ciki domin ya tabbata cewa idan ya ci gaba da bauta ma Jehobah da aminci, zai sami rai na har abada a sama. Mu ma za mu iya yin farin ciki domin begenmu. Kamar yadda mai zabura ya rubuta, “mai albarka ne . . . wanda Yahweh Allahnsa ne sa zuciyarsa, . . . wanda yakan kiyaye gaskiya har abada.”​—Zab. 146:​5, 6.

WAƘA TA 139 Rayuwa a Cikin Aljanna

a Jehobah ya ba mu bege mai kyau. Begen nan yana ƙarfafa mu kuma yana taimaka mana kada mu mai da hankali ga matsalolin da muke fuskanta a yau. Yana ba mu ƙarfi da muke bukata don mu ci gaba da bauta ma Jehobah ko da wane matsaloli ne muke fuskanta. Kuma yana kāre mu daga abubuwan da za su iya lalata tunaninmu. Waɗannan dalilai ne suka sa ya kamata mu ci gaba da ƙarfafa begenmu.

b Ibraniyawa 6:19 (THS) : “Wanda muna da shi kamar anka (anchor) na rai, tabbatacen bege mai-tsayawa mai-shiga kuma cikin abin da ke daga cikin labulen.”

c BAYANI A KAN HOTUNA: Kamar yadda hular kwano take kāre kan soja, kuma anka take sa jirgin ruwa ya saya da kyau, begenmu yana kāre tunanin zuciyarmu kuma ya sa mu ci gaba da bauta ma Jehobah a lokacin da muke fuskantar matsaloli. Wata ꞌyarꞌuwa tana yin adduꞌa ga Jehobah da tabbacin cewa zai amsa mata. Wani ɗanꞌuwa yana bimbini a kan yadda Allah ya cika alkawarin da ya yi wa Ibrahim. Wani ɗanꞌuwa kuma yana tunawa da yadda Allah ya albarkace shi.