TALIFIN NAZARI NA 41
Za Ka Iya Yin Farin Ciki na Kwarai
“Masu albarka ne dukan masu tsoron Yahweh, masu tafiya cikin hanyarsa.”—ZAB. 128:1. a
WAƘA TA 110 ‘Farin Cikin’ da Jehobah Yake Bayarwa
ABIN DA ZA A TATTAUNA b
1. Mene ne ake nufi da sanin kāsawarmu ta ruhu kuma wace alaƙa ce ke tsakanin hakan da farin ciki?
FARIN ciki na ƙwarai ya wuci yin murna na ɗan lokaci. Mutum zai iya yin farin ciki na ƙwarai a duk rayuwarsa. Ta yaya hakan zai iya yiwu? Yesu ya bayyana hakan a Huɗubarsa Na Kan Dutse cewa: “Masu albarka ne waɗanda suka san kāsawarsu ta ruhu, gama mulkin sama nasu ne.” (Mat. 5:3) Yesu ya san cewa an halicci ꞌyan Adam da marmarin sani da kuma bauta wa Mahaliccinsu, wato Jehobah. Abin da ake nufi da ‘sanin kāsawarmu ta ruhu’ ke nan. Kuma da yake Jehobah shi ne “Allah mai albarka” ko kuma farin ciki, waɗanda suke bauta masa za su iya farin ciki su ma.—1 Tim. 1:11.
2-3. (a) Bisa ga abin da Yesu ya faɗa su waye ne kuma za su iya yin farin ciki? (b) Me za mu tattauna a wannan talifin kuma me ya sa muke bukatar mu yi hakan?
2 Sai ba mu da matsaloli ne za mu iya farin ciki na ƙwarai? Aꞌa. A huɗubarsa, Yesu ya faɗi wani abu da zai iya ba mu mamaki. Ya ce: “Masu baƙin ciki” domin suna nadama a kan zunubansu na dā, ko domin suna da matsaloli da yawa, ko “masu shan tsanani saboda adalci” ko waɗanda ake zaginsu don su mabiyan Yesu ne, duk za su iya farin ciki. (Mat. 5:4, 10, 11) Amma me zai taimake mu mu yi farin ciki a yanayoyin nan?
3 Yesu yana so mu gane cewa ba rashin matsaloli ne za su sa mu farin ciki a rayuwa ba. Amma kyautata dangantakarmu da Jehobah da kuma kusantarsa ne za su sa mu farin ciki. (Yak. 4:8) Me zai taimake mu mu yi hakan? A wannan talifin za mu tattauna abubuwa uku da za su taimake mu mu yi farin ciki na gaske.
KA KARANTA DA KUMA YI NAZARIN LITTAFI MAI TSARKI
4. Wane abu na farko ne ya kamata mu yi idan muna so mu yi farin ciki na ƙwarai? (Zabura 1:1-3)
4 MATAKI NA 1: Idan muna so mu yi farin ciki na ƙwarai, wajibi ne mu karanta da kuma yi nazarin Kalmar Allah. Yesu ya kwatanta Kalmar Allah da abinci. ꞌYan Adam da kuma dabbobi suna bukatar abinci don su rayu. Amma ꞌyan Adam ne kaɗai za su iya karanta Kalmar Allah. Kuma suna bukatar su yi hakan. Shi ya sa Yesu ya ce: “Ba da abinci kaɗai mutum zai rayu ba, sai dai da kowace kalmar da take fitowa daga wurin Allah.” (Mat. 4:4) Don haka, bai kamata mu bar kwana ɗaya ya wuce ba tare da mun karanta Kalmar Allah ba. Wani marubucin Zabura ya ce: ‘Mai albarka ne mutumin da yana jin daɗi ya kiyaye Koyarwar Yahweh, yana tunanin Koyarwar dare da rana.’—Karanta Zabura 1:1-3.
5-6. (a) Me za mu iya koya daga Littafi Mai Tsarki? (b) A waɗanne hanyoyi ne karanta Littafi Mai Tsarki zai taimaka mana?
5 Da yake Jehobah yana ƙaunarmu, a cikin Kalmarsa ya nuna mana abin da za mu iya yi don mu yi farin ciki na ƙwarai. A ciki, mun koyi abin da ya sa Allah ya halicce mu. Mun koyi yadda za mu kusace shi da abin da za mu yi don ya gafarta mana. Kuma mun koyi abubuwa da yawa da ya yi alkawari cewa zai yi mana a nan gaba. (Irm. 29:11) Waɗannan abubuwa da muka koya daga Littafi Mai Tsarki suna sa mu farin ciki sosai!
6 Mun san cewa Littafi Mai Tsarki yana cike da shawarwarin da za su iya taimaka mana kowace rana. Idan muna bin shawarwarin nan, za mu yi farin ciki na ƙwarai. A duk lokacin da matsalolin rayuwa sun sa ka sanyin gwiwa, ka ƙara lokacin da kake karanta Littafi Mai Tsarki da kuma yin tunani a kan abin da ka karanta. Yesu ya ce: “Albarka ta fi tabbata ga waɗanda suke jin kalmar Allah, suke kuma kiyaye ta!”—Luk. 11:28.
7. Me zai taimaka maka ka amfana sosai daga karatun Littafi Mai Tsarki?
7 Yayin da kake karanta Kalmar Allah, kada ka yi hakan da sauri-sauri, amma ka yi shi yadda za ka ji daɗin karantawa. Ga wani misali, a ce wani ya dafa abincin da kake so sosai. Mai yiwuwa don hanzari ko don kana tunanin wani abu dabam, ka cinye abincin da sauri-sauri ba tare da tauna abincin da kyau don ka ji daɗin ɗanɗanonsa ba. Bayan ka gama cin abincin ne ka gaya wa kanka cewa da ka sani da ba ka cinye shi da sauri-sauri ba don ka ji daɗin ɗanɗanon da kyau. Abu makamancin haka zai iya faru da mu yayin da muke karanta Littafi Mai Tsarki. A wasu lokuta, mukan yi karatun a cikin hanzari har mu kasa fahimtar abin da muka karanta. Idan kana karanta Kalmar Allah, kada ka yi hakan cikin hanzari don ka ji daɗin karatun; ka yi tunanin abubuwan da ke faruwa, ka ɗauka kamar kana jin muryoyin mutanen da ke magana, kuma ka yi tunani a kan abin da ka karanta. Hakan zai sa ka farin ciki.
8. Ta yaya “bawan nan mai aminci, mai hikima” yake cika hakkin da Yesu ya ba shi? (Ka duba ƙarin bayani.)
8 Yesu ya naɗa “bawan nan mai aminci, mai hikima” don ya tanadar mana da abubuwan da za su ƙarfafa dangantakarmu da Jehobah a lokacin da ya kamata, kuma bawan yana yin hakan sosai. c (Mat. 24:45) Littafi Mai Tsarki ne musamman bawan nan yake amfani da shi ya koyar da mu. (1 Tas. 2:13) Wannan koyarwa ce take taimaka mana mu san yadda Jehobah yake tunani, kamar yadda aka bayyana a cikin Littafi Mai Tsarki. Abin da ya sa muke karanta mujallunmu na Hasumiyar Tsaro da Awake!, da kuma talifofin da ke dandalin jw.org ke nan. Kuma muna shirya taron tsakiyar mako da kuma na ƙarshen mako. Ƙari ga haka, muna kallon shirin Tashar JW da ke fitowa kowane wata, idan muka sami dama. Karanta da kuma yin nazarin Littafi Mai Tsarki zai taimaka mana mu yi abu na biyu da zai sa mu farin ciki.
KA YI RAYUWAR DA TA JITU DA ƘAꞌIDODIN LITTAFI MAI TSARKI
9. Mene ne abu na biyu da za mu yi don mu yi farin ciki na ƙwarai?
9 MATAKI NA 2: Idan muna so mu yi farin ciki na ƙwarai dole ne mu bi ƙaꞌidodin Jehobah. Wani marubucin Zabura ya ce: “Masu albarka ne dukan masu tsoron Yahweh, masu tafiya cikin hanyarsa.” (Zab. 128:1) Jin tsoron Jehobah yana nufi cewa muna girmama shi a zuciyarmu, shi ya sa muke iya ƙoƙarinmu kada mu yi abin da zai ɓata masa rai. (K. Mag. 16:6) Muna iya ƙoƙarinmu don mu ci gaba da bin ƙaꞌidodinsa game da abin da ya dace da abin da bai dace ba kamar yadda Littafi Mai Tsarki ya bayyana mana. (2 Kor. 7:1) Za mu yi farin ciki idan muna yin abubuwan da Jehobah yake so kuma muna guje wa abubuwan da ba ya so.—Zab. 37:27; 97:10; Rom. 12:9.
10. Wane hakki ne muke da shi bisa ga Romawa 12:2?
10 Karanta Romawa 12:2. Mutum zai iya sanin cewa Jehobah ne yake da iko ya kafa doka game da abin da ya dace da wanda bai dace ba, amma dole ne ya yarda ya bi dokokin. Alal misali, mutum zai iya sanin cewa gwamnati tana da iko ta kafa doka a kan iyakan gudun da mutum zai iya yi da mota a kan hanya. Amma yana iya yiwu cewa mutumin ba ya so ya yarda ya bi dokokin. Kuma yakan yi gudu da mota fiye da yadda ya kamata. Ta wurin halinmu ne za mu nuna cewa mun yarda cewa ƙaꞌidodin Jehobah ne suka fi dacewa da mu. (K. Mag. 12:28) Yadda Dauda ya ji ke nan shi ya sa ya faɗa game da Jehobah cewa: “Kana nuna mini hanya, hanyar da za ta kai ga rai, kasancewarka tare da ni, cikakken farin ciki ne, zama a hannun damanka, jin daɗi ne har abada.”—Zab. 16:11.
11-12. (a) A kan me ya kamata mu mai da hankali idan wani abu na daminmu ko mun yi sanyin gwiwa? (b) Ta yaya abin da ke Filibiyawa 4:8 zai taimaka mana idan muna so mu zaɓi nishaɗin da za mu yi?
11 Idan wani abu yana damunmu ko mun yi sanyin gwiwa, za mu iya ji kamar ya kamata mu yi wani abu da zai sa mu manta da matsalolinmu. Hakan ba laifi ba ne amma ya kamata mu mai da hankali don kada mu yi abin da Jehobah ya tsana.—Afis. 5:10-12, 15-17.
12 A wasiƙarsa ga Filibiyawa, manzo Bulus ya ƙarfafa Kiristocin da ke wurin su ci gaba da tunani a kan abubuwan da suke “daidai, . . . da tsabta,” da ke “jawo ƙauna,” da kuma “mafi kyau.” (Karanta Filibiyawa 4:8.) Ko da yake wannan ƙarfafa da Bulus ya bayar ba game da nishaɗi ba ne, amma abin da ya faɗa zai iya taimaka mana mu san irin nishaɗin da ya kamata mu yi. Ka gwada wannan: A duk inda aka rubuta “abin da,” ka canja shi da “waƙoƙi” da “fina-finai” da “littattafai” da “wasannin bidiyo.” Yin hakan zai taimaka maka ka san waɗanda Allah yake so da waɗanda ba ya so. Muna so mu yi rayuwar da za ta jitu da ƙaꞌidodin Jehobah. (Zab. 119:1-3) Ta hakan za mu iya ɗaukan mataki na gaba da zai taimake mu mu yi farin ciki na ƙwarai.—A. M. 23:1.
KA SA IBADA TA ZAMA ABU NA FARKO A RAYUWARKA
13. Mene ne mataki na uku da zai taimaka mana mu yi farin ciki na ƙwarai? (Yohanna 4:23, 24)
13 MATAKI NA 3: Ka tabbata ka sa ibada ga Jehobah ta zama abu na farko a rayuwarka. A matsayin Mahalicci, Jehobah ya cancanci mu bauta masa. (R. Yar. 4:11; 14:6, 7) Shi ya sa abin da ya kamata ya zama farko a rayuwarmu shi ne, bauta wa Jehobah a hanyar da yake so, wato “cikin ruhu, da kuma gaskiya.” (Karanta Yohanna 4:23, 24.) Muna so ruhu mai tsarki ya ja-gorance mu yayin da muke yi ma Allah ibada don mu bauta masa a hanyar da ta jitu da gaskiya kamar yadda take a cikin Kalmarsa. Dole ne mu sa ibadarmu ta zama farko a rayuwarmu ko da muna zama ne a inda aka hana aikinmu ko ana taƙura mana. Yanzu haka ꞌyanꞌuwanmu fiye da 100 suna kurkuku don suna bauta wa Jehobah. d Duk da haka, suna iya ƙoƙarinsu su yi adduꞌa, su yi nazari, kuma su yi waꞌazi game da Allah da kuma Mulkinsa. Za mu iya farin ciki ko da ana tsananta mana ko zaginmu domin mun san cewa Jehobah yana tare da mu kuma zai yi mana albarka.—Yak. 1:12; 1 Bit. 4:14.
LABARIN WANI ƊANꞌUWA
14. Me ya sami wani ɗanꞌuwa matashi a Tajikistan kuma me ya sa?
14 Labaran wasu ꞌyanꞌuwa sun nuna cewa matakai uku da muka tattauna a baya suna kai ga farin ciki na ƙwarai ko da wane yanayi ne mutum yake ciki. Ka yi laꞌakari da abin da ya faru da wani Ɗanꞌuwa mai suna Jovidon Bobojonov don ya ƙi ya shiga soja. Shekarun ɗanꞌuwan 19 ne kuma shi ɗan Tajikistan ne. A ranar 4 ga Oktoba, 2019, an kama shi daga gidansu aka kai shi kurkuku na tsawon watanni kuma sun bi da shi kamar wani mai laifi. Kafofin yaɗa labarai a ƙasashe da yawa, sun yaɗa labarin wannan rashin adalcin. Sun sanar da cewa an yi masa dūka sosai domin ana so a tilasta masa ya yi rantsuwan zama soja kuma ya saka rigar soja. Bayan haka, aka kama shi da laifi kuma an kai shi wani sansani inda aka tilasta masa ya riƙa yin aiki mai wuya, daga baya shugaban ƙasar ya sa a sake shi. Saꞌad da abubuwan nan suke faruwa, Jovidon ya riƙe amincinsa kuma ya ci gaba da farin ciki. Me ya taimake shi ya yi hakan? Abin da ya taimaka masa shi ne saka bautar Jehobah farko a rayuwarsa.
15. Ta wace hanya ce Jovidon ya iya koya game da Jehobah saꞌad da yake kurkuku?
15 A lokacin da Jovidon yake kurkuku, ya ci gaba da koya game da Jehobah duk da cewa bai da Littafi Mai Tsarki ko littattafanmu. Ta yaya ya yi hakan? ꞌYanꞌuwa a yankinsu sukan kai masa abinci kuma su rubuta nassin yini na ranar a jikin jakunkuna abincin. Ta hakan, ya iya karanta Littafi Mai Tsarki da kuma yin tunani a kansa kowace rana. Bayan an sake shi daga kurkuku, ga shawara da ya ba wa waɗanda ba a soma tsananta musu ba. Ya ce: “Yana da muhimmanci mutum ya koya game da Jehobah sosai ta wurin karanta Kalmarsa da kuma littattafanmu tun kafin a soma tsananta masa.”
16. Mene ne Jovidon ya mai da hankali a kai?
16 Ɗanꞌuwanmu ya yi rayuwar da ta jitu da ƙaꞌidodin Jehobah. Bai mai da hankali ga shaꞌawoyi marar kyau da za su kai shi ga yin abin da bai dace ba, a maimakon haka, ya mai da hankali ga Jehobah da kuma abubuwan da Jehobah yake so ya yi. Jovidon ya lura da yadda halittun Jehobah suke da kyau sosai. Kowace safe yakan saurari kukan tsuntsaye. Da dare kuma, yakan kalli taurari da kuma wata. Ya ce: “Waɗannan abubuwan da Jehobah ya ba mu kyauta, sun sa ni farin ciki.” Idan muna gode wa Jehobah domin abubuwan da yake tanada mana, da kuma koyarwa da muke samu daga Littafi Mai Tsarki, za mu yi farin ciki. Kuma farin cikin, zai taimaka mana mu iya jimre matsaloli.
17. Ta yaya abin da ke 1 Bitrus 1:6, 7 zai taimaka wa mutumin da ya shiga irin yanayin da Jovidon ya shiga?
17 Jovidon ya kuma sa bautar Jehobah farko a rayuwarsa. Ya san muhimmancin kasancewa da aminci ga Allah na gaskiya. Yesu ya ce: “Ka yi wa Ubangiji Allahnka sujada, kuma shi kaɗai za ka bauta masa!” (Luk. 4:8) Sojoji da kuma shugabanninsu sun so Jovidon ya daina bauta wa Jehobah. A maimakon ya yi hakan, ya yi adduꞌa ga Jehobah dare da rana kuma ya roƙi Jehobah ya taimaka masa kada ya yi watsi da bangaskiyarsa. Duk da rashin adalci da aka yi wa Jovidon, ya ci gaba da kasancewa da aminci. A sakamakon haka, yanzu yana da bangaskiya mai ƙarfi fiye da dā domin an gwada bangaskiyarsa.—Karanta 1 Bitrus 1:6, 7.
18. Ta yaya za mu iya ci gaba da yin farin ciki?
18 Jehobah ya san abin da muke bukata don mu yi farin ciki na ƙwarai. Idan ka bi hanyoyi uku da suke sa mu yi farin ciki na ƙwarai, za ka iya ci gaba da farin ciki duk da matsalolin da kake fuskanta. Da hakan kai ma za ka iya cewa: “Masu albarka ne mutanen da Yahweh ne Allahnsu.”—Zab. 144:15.
WAƘA TA 89 Mu Ji, Mu Yi Biyayya Don Mu Sami Albarka
a Kalmar Ibrananci da aka fassara zuwa “masu albarka” a wannan ayar da kuma wasu ayoyi a wannan talifin tana nufin “masu farin ciki.”
b Mutane da yawa ba sa farin ciki na ƙwarai domin sun ɗauka cewa abubuwa kamar rayuwar jin daɗi da kuɗi da suna da kuma iko zai sa su farin ciki. Amma a lokacin da Yesu yake duniya ya gaya wa mutane abin da zai sa su farin ciki. A wannan talifin za mu tattauna abubuwa uku da za su taimaka mana mu yi farin ciki na ƙwarai.
c Ka duba talifin nan “Kana Samun ‘Abinci a Lotonsa’ Kuwa?” a Hasumiyar Tsaro na 15 ga Agusta, 2014.
d Don ƙarin bayani, ka nemi “An Kai Su Kurkuku Saboda Imaninsu” a jw.org.
e BAYANI A KAN HOTUNA: A wannan misalin, ꞌyanꞌuwa suna nuna goyon baya ga wani ɗanꞌuwa da aka kama za a kai shi kotu don a hukunta shi.