TALIFIN NAZARI NA 39
An Rubuta Sunanka a Cikin “Littafin Rai”?
“A gabansa kuwa aka rubuta littafin tunawa da waɗanda suke tsoron Yahweh.”—MAL. 3:16.
WAƘA TA 61 Bayin Jehobah, Kar Mu Gaji!
ABIN DA ZA A TATTAUNA a
1. Wane littafi ne Jehobah ya daɗe yana rubutu a ciki? Mene ne ke cikin littafin?
JEHOBAH ya yi shekaru dubbai yana rubutu a cikin wani littafi na musamman. Wannan littafin yana ɗauke da sunayen mutane, kuma sunan mutum mai aminci na farko da aka fara rubutawa a littafin shi ne Habila. b (Luk. 11:50, 51) Tun daga lokacin, Jehobah ya ci gaba da rubuta ƙarin sunayen mutane a cikin littafin, kuma a yau littafin yana ɗauke da sunayen miliyoyin mutane. A Littafi Mai Tsarki, an kira littafin, “littafin tunasarwa” ko kuma “littafin rai.” A wannan talifin, za mu kira littafin, “littafin rai.”—Karanta Malakai 3:16; R. Yar. 3:5; 17:8.
2. Sunayen su wane ne aka rubuta a littafin rai, kuma mene ne za mu yi don a rubuta sunayenmu a littafin?
2 Wannan littafi mai muhimmanci yana ɗauke da sunayen waɗanda suke bauta wa Jehobah da daraja shi da kuma ƙaunar sunansa. Su ne za su sami damar yin rayuwa har abada. A yau, za a iya rubuta sunanmu a cikin littafin rai idan muna da dangantaka ta kud-da-kud da Jehobah bisa ga hadayar da Ɗansa Yesu Kristi ya bayar. (Yoh. 3:16, 36) Dukanmu muna so a rubuta sunanmu a wannan littafin, ko da muna da begen yin rayuwa a sama ko a nan duniya.
3-4. (a) Za mu rayu har abada idan sunanmu yana cikin littafin rai yanzu? Ka bayyana. (b) Mene ne za mu tattauna a wannan talifin da kuma na gaba?
3 Shin hakan yana nufin cewa dukan waɗanda sunayensu yana littafin nan suna da tabbacin samun rai na har abada? Amsar tana cikin abin da Jehobah ya gaya wa Musa a Fitowa 32:33. Jehobah ya ce: ‘Duk wanda ya yi mini zunubi, shi ne zan share sunansa daga littafina.’ Don haka, za a iya cire sunayen ko kuma a share su daga cikin littafin. Kamar dai a ce dama Jehobah ya rubuta sunan da fensir ne. (R. Yar. 3:5) Muna bukatar mu tabbata cewa sunayenmu sun ci gaba da kasancewa a cikin littafin, har sai an rubuta shi da biro.
4 Akwai wasu tambayoyi da za mu iya yi. Alal misali, mene ne Littafi Mai Tsarki ya faɗa game da waɗanda sunayensu yake cikin littafin rai da kuma waɗanda sunayensu ba sa cikin littafin? Yaushe ne waɗanda sunayensu sun ci gaba da kasancewa a cikin littafin za su sami rai na har abada? Waɗanda suka mutu ba tare da samun damar koya game da Jehobah ba kuma fa? Zai yiwu a rubuta sunayensu a cikin wannan littafin? Za a amsa waɗannan tambayoyin a wannan talifin da kuma na gaba.
SU WAYE NE SUNAYENSU KE CIKIN LITTAFIN RAI?
5-6. (a) Kamar yadda aka nuna a Filibiyawa 4:3 su waye ne sunayensu ke littafin rai? (b) Yaushe za a rubuta sunayensu a littafin rai na dindindin?
5 Su waye ne sunayensu ke cikin littafin rai? Don mu amsa wannan tambayar, za mu tattauna game da rukunonin mutane guda biyar. Daga cikin waɗannan mutanen, an rubuta sunayen waɗansu a cikin littafin rai, waɗansu kuma ba a rubuta sunayensu ba.
6 Rukuni na farko ya ƙunshi mutane da aka zaɓa su yi mulki tare da Yesu a sama. Shin sunayensu na cikin littafin rai a yanzu? E. Bisa ga abin da manzo Bulus ya gaya wa ‘abokan aikinsa’ a Filibi, sunayen waɗanda aka zaɓa su yi mulki tare da Yesu suna cikin littafin rai. (Karanta Filibiyawa 4:3.) Amma don sunayensu su ci gaba da kasancewa a cikin wannan littafin, suna bukatar su riƙe amincinsu. Bayan haka, idan aka saka musu hatimi a ƙarshe kafin su mutu ko kuma kafin ƙunci mai girma, za a rubuta sunayensu na dindindin a littafin.—R. Yar. 7:3.
7. Mene ne muka fahimta daga Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 7:16, 17 game da lokacin da za a rubuta sunayen taro mai girma na dindindin a littafin rai?
7 Rukuni na biyu shi ne babban taro ko taro mai girma. Sunansu yana cikin littafin rai yanzu? E. Sunansu zai ci gaba da kasancewa a littafin rai bayan sun tsira daga Armageddon? E. (R. Yar. 7:14) Yesu ya ce waɗannan tumakin, za su sami “rai na har abada.” (Mat. 25:46; Yoh. 10:16) Amma ba za su sami rai na har abada nan da nan ba. Sunansu zai ci gaba da kasancewa a littafin kamar da fensir aka rubuta. A lokacin Sarautar Yesu na Shekara Dubu, Yesu “zai zama makiyayinsu, zai bi da su zuwa maɓuɓɓugar ruwa mai ba da rai.” Waɗanda suka bi ja-gorancin Yesu, kuma Jehobah ya yi musu shari’a a matsayin masu aminci, za a rubuta sunayensu na dindindin a littafin rai.—Karanta Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 7:16, 17.
8. Mene ne zai faru da waɗanda sunayensu ba sa littafin rai?
8 Rukuni na uku ya ƙunshi awaki, waɗanda za a hallaka su a Armageddon. Sunayensu ba sa cikin littafin rai. Yesu ya ce za a hallaka su har abada. (Mat. 25:46) Bulus ya gaya mana cewa “za su sha hukuncin halaka ta har abada.” (2 Tas. 1:9; 2 Bit. 2:9) Haka ma yake da waɗanda suke saɓa wa ruhu mai tsarki da gangan. Su ma ba za su sami rai na har abada ba. Amma za a hallaka su har abada. (Mat. 12:32; Mar. 3:28, 29; Ibran. 6:4-6) Yanzu bari mu tattauna rukuni na biyu na mutanen da za a tā da su.
WAƊANDA ZA A TĀ DA SU
9. Kamar yadda aka nuna a littafin Ayyukan Manzanni 24:15, waɗanne rukunoni biyu ne za a tā da su a duniya, kuma mene ne ya bambanta rukunonin nan?
9 Littafi Mai Tsarki ya yi magana game da rukunoni biyu na mutanen da suke da begen yin rayuwa a nan duniya, wato “masu adalci” da “marasa adalci.” (Karanta Ayyukan Manzanni 24:15.) “Masu adalci” su ne waɗanda suka bauta wa Jehobah a lokacin da suke da rai. “Marasa adalci” kuma su ne waɗanda ba su sami damar koya game da Jehobah ba. Domin an tā da rukunoni biyu daga mutuwa, za mu iya cewa sunayensu na cikin littafin rai? Don mu amsa wannan tambayar, bari mu tattauna kowannensu.
10. Me ya sa za a tā da “masu adalci,” kuma wane gata ne wasunsu za su samu? (Ka kuma duba talifin nan “Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu” da ya yi magana game da waɗanda za a tā da su a duniya a wannan fitowar.)
10 “Masu adalci” su ne rukuni na huɗu. Kafin su mutu, an rubuta sunayensu a cikin littafin rai. Shin an cire sunayensu daga cikin littafin bayan sun mutu? A’a. Domin a wurin Jehobah, suna “rayuwa.” Jehobah “ba Allah na matattu ba ne, amma na masu-rai: gama duka suna rayuwa gareshi.” (Luk. 20:38, Tsohuwar Hausa a Sauƙaƙe) Hakan yana nufin cewa, sa’ad da aka tā da masu adalci a duniya, sunayensu za su kasance a cikin littafin rai ko da yake ba na dindindin ba. (Luk. 14:14) Babu shakka wasu daga cikin waɗanda aka tā da su za su sami damar zama “hakimai cikin dukan duniya.”—Zab. 45:16, New World Translation.
11. Mene ne “marasa adalci” za su bukaci su koya kafin a saka sunayensu a littafin rai?
11 Yanzu bari mu yi la’akari da rukuni na ƙarshe, wato na biyar. Su ne “marasa adalci.” Da alama ba su san game da ƙa’idodin Jehobah na adalci ba, don haka, ba su yi adalci sa’ad da suke rayuwa ba. Sunayensu ba sa cikin littafin rai, amma Allah zai tā da su daga matattu, domin su sami zarafin koya game da shi kuma a sa sunayensu a cikin littafin rai. ‘Marasa adalcin’ nan za su bukaci koyarwa sosai. Kafin su mutu, wasunsu sun aikata mugayen abubuwa. Don haka, za su bukaci a koyar da su game da ƙa’idodin Jehobah na adalci. Don a cim ma hakan, Mulkin Allah zai ja-goranci koyarwa mafi girma da ba a taɓa yi ba a duk tarihi.
12. (a) Su waye ne za su koyar da marasa adalcin? (b) Mene ne zai faru da waɗanda suka ƙi aikata abubuwan da suka koya?
12 Su waye ne za su koyar da “marasa adalci”? Su ne taro mai girma da kuma masu adalci da aka tā da su. Kafin a rubuta sunayen marasa adalcin a littafin rai, za su bukaci su ƙulla dangantaka mai kyau da Jehobah kuma su yi alkawarin bauta masa. Yesu da kuma shafaffu za su mai da hankali sosai don su ga ko mutanen nan suna aikata abubuwan da suke koya. (R. Yar. 20:4) Duk wanda ya ƙi aikata abubuwan da yake koya za a hallaka shi ko da ya kai shekaru 100 yana rayuwa. (Isha. 65:20, NWT) Jehobah da kuma Yesu za su iya sanin abin da ke zuciyarmu kuma ba za su bar wani da zai lalata duniya ya ci gaba da rayuwa ba.—Isha. 11:9; 60:18; 65:25; Yoh. 2:25.
TASHIN MATATTU ZUWA RAI DA KUMA SHARI’A
13-14. (a) A dā, ta yaya muka fahimci kalmomin Yesu da ke Yohanna 5:29? (b) Mene ne muke bukatar mu sani game da kalmomin nan?
13 Yesu ma ya yi magana game da waɗanda za a tā da su su yi rayuwa a nan duniya. Alal misali, ya ce: ‘Lokaci yana zuwa da duk waɗanda suke cikin kaburbura za su ji muryarsa, su fito. Waɗanda suka yi abu mai kyau za su tashi, su rayu, amma waɗanda suka yi rashin gaskiya, za su tashi a kuwa yi musu hukunci.’ (Yoh. 5:28, 29) Mene ne Yesu yake nufi?
14 A dā, mun ɗauka cewa kalmomin Yesu suna nufin abubuwan da mutanen za su yi bayan an tā da su daga mutuwa ne, wato wasu za su yi rayuwa mai kyau, wasu kuma za su yi rashin gaskiya. Amma ku lura cewa Yesu bai ce waɗanda aka tā da su daga matattu za su yi abubuwa masu kyau ko kuma za su yi abubuwa marasa kyau ba. Ya yi amfani da kalmomi da suka nuna cewa sun riga sun yi abubuwan. Ya yi magana game da ‘waɗanda suka yi abu mai kyau’ da kuma ‘waɗanda suka yi rashin gaskiya.’ Hakan ya nuna cewa sun yi abubuwan nan kafin su mutu ne. Wannan bayanin ya dace, ko ba haka ba? Domin ba za a bar wani ya yi rashin adalci a sabuwar duniya ba. Marasa adalcin sun yi rashin gaskiyar kafin su mutu. Don haka mene ne Yesu yake nufi sa’ad da ya yi magana game da tashin matattu na waɗanda za su rayu da waɗanda za a yi musu hukunci ko kuma shari’a?
15. Su wane ne za a tā da su su “rayu” kuma me ya sa?
15 Masu adalci da suka yi abubuwa masu kyau kafin su mutu “za su tashi, su rayu” domin an riga an rubuta sunayensu a cikin littafin rai. Hakan yana nufin cewa tashin matattu na “waɗanda suka yi abu mai kyau” da aka ambata a Yohanna 5:29, ɗaya ne da tashin matattu na “masu adalci” da aka ambata a Ayyukan Manzanni 24:15. Wannan bayanin ya jitu da abin da aka faɗa a Romawa 6:7 cewa: ‘Idan mutum ya mutu, ya sami ꞌyanci daga ikon zunubinsa ke nan.’ Don haka, sa’ad da masu adalcin nan suka mutu, Jehobah ya gafarta musu zunubansu, amma zai tuna da abubuwa masu kyau da suka yi sa’ad da suke a raye. (Ibran. 6:10) Dole ne masu adalcin su ci gaba da yin abubuwa masu kyau idan suna so sunayensu su ci gaba da kasancewa a cikin littafin rai.
16. Mene ne tashin matattu na waɗanda za a “yi musu hukunci” ko kuma shari’a yake nufi?
16 Waɗanda suka yi rashin gaskiya kafin su mutu kuma fa? Ko da yake an gafarta musu zunubansu bayan sun mutu, ba su bauta ma Jehobah da aminci kafin su mutu ba. Sunayensu ba sa cikin littafin rai. Don haka, tashin matattu na “waɗanda suka yi rashin gaskiya” ɗaya ne da tashin matattu na “marasa adalci” da aka ambata a Ayyukan Manzanni 24:15. Za “su tashi a kuwa yi musu hukunci” ko shari’a. c Hakan yana nufin cewa Yesu zai lura da yadda marasa adalcin za su yi rayuwa. (Luk. 22:30) Bayan wasu lokuta, Yesu zai yanke shawarar ko sun dace a rubuta sunayensu a cikin littafin rai ko kuma a’a. Sai marasa adalcin sun canja salon rayuwarsu kuma sun yi alkawarin bauta wa Jehobah da dukan zuciyarsu kafin a sa sunayensu a cikin littafin rai.
17-18. Mene ne dukan waɗanda aka tā da su su yi rayuwa a duniya za su bukaci su yi, kuma mene ne “abin da suka yi” da aka ambata a Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 20:12, 13 yake nufi?
17 Waɗanda aka tā da su daga matattu ko su masu adalci ne ko marasa adalci, za su bukaci su yi biyayya da sabon littafin da za a buɗe a lokacin Sarautar Yesu na Shekaru Dubu. Manzo Yohanna ya bayyana abin da ya gani a wahayi, ya ce: “Sai na ga matattu manya da ƙanana, suna tsaye a gaban kujerar mulkin, aka kuma buɗe littattafai. Sa’an nan aka buɗe wani littafi, wato Littafin Rai. Aka yi wa matattun shari’a bisa ga abin da suka yi, kamar yadda yake a rubuce a cikin littattafan.”—R. Yar. 20:12, 13.
18 Bisa ga waɗanne ayyuka ne za a shari’anta waɗanda aka tā da su daga matattu? Shin zai zama ayyukan da suka yi kafin su mutu ne? A’a. Ka tuna cewa, an ꞌyantar da su daga zunuban da suka yi kafin su mutu. Don haka, ayyukan ba za su zama ayyukan da suka yi kafin su mutu ba. A maimakon haka, ana nufin abubuwan da za su yi bayan an koyar da su a sabuwar duniya. Har mutane masu aminci kamar Nuhu da Sama’ila da Dauda da kuma Daniyel ma za su bukaci su koya game da Yesu kuma su ba da gaskiya ga hadayar da ya bayar, balle marasa adalci!
19. Mene ne zai faru da waɗanda suka yi watsi da dama mai muhimmanci da za a ba su?
19 Mene ne zai faru da waɗanda suka yi watsi da damar da aka ba su? Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 20:15 ta gaya mana cewa: “Duk wanda ba a sami sunansa a rubuce a cikin wannan Littafin Rai ba, an jefar da shi cikin tafkin wutar nan.” Hakika za a hallaka su har abada. Don haka, yana da muhimmanci mu tabbata cewa sunanmu yana cikin littafin rai kuma ya ci gaba da kasancewa a ciki!
20. Wane aiki mai muhimmanci ne za a yi a lokacin Sarautar Yesu na Shekara Dubu? (Ka duba hoton da ke shafin farko.)
20 Hakika, lokacin Sarautar Yesu na Shekara Dubu zai kasance lokaci mai muhimmanci sosai! A lokacin za a yi gagarumin koyarwa a dukan duniya irin wadda ba a taɓa yi ba a duk tarihi. A lokacin ne kuma za a bincika halayen masu adalci da marasa adalci. (Isha. 26:9; A. M. 17:31) Ta yaya za a yi wannan aikin koyarwar? Talifinmu na gaba zai nuna mana yadda za a yi wannan aiki mai muhimmanci.
WAƘA TA 147 Alkawarin Rai Na Har Abada
a Wannan talifin ya bayyana ƙarin haske da aka samu game da abin da Yesu ya faɗa a Yohanna 5:28, 29 a kan waɗanda za a tā da su su yi rayuwa da waɗanda za a tā da su a yi musu hukunci. Za mu koyi game da abin da tashin matattu guda biyun nan suke nufi da kuma waɗanda za a tā da su a waɗannan tashin matattun.
b An soma rubuta littafin ne “tun farkon duniya,” wato tun lokacin da aka soma samun mutanen da sun cancanci a ꞌyantar da su daga zunubi. (Mat. 25:34; R. Yar. 17:8) Don haka, Habila shi ne mutum na farko da aka rubuta sunansa a wannan littafin rai.
c A dā, mun bayyana cewa kalmar nan “hukunci” ko kuma shari’a tana nufin za a hallaka marasa adalcin. Ko da yake kalmar tana iya nufin hakan, amma a ayar nan, kamar dai Yesu ya yi amfani da kalmar nan shari’a don ya nuna cewa za a lura da marasa adalcin, ko kuma kamar yadda wani kamus ya faɗa yana nufin “binciken hali.”