TARIHI
Na Ji Dadin Koya da Kuma Koyar da Wasu Game da Jehobah
A LOKACIN da nake girma a birnin Easton, a jihar Pennsylvania a ƙasar Amirka, na kafa maƙasudin zuwa makarantar jami’a domin in yi suna. Na ji daɗin koyan ilimin lissafi da kimiyya kuma na iya su sosai. A shekara ta 1956, wata ƙungiyar farar hula ta ba ni dala 25 domin na sami maki fiye da kowa a cikin ɗalibai baƙaƙe a makarantarmu. Daga baya, maƙasudina ya canja. Me ya sa?
YADDA NA KOYA GAME DA JEHOBAH
Ba da daɗewa ba bayan shekara ta 1940, iyayena sun soma nazarin Littafi Mai Tsarki da Shaidun Jehobah. Ba su ci gaba da yin nazarin ba, amma mahaifiyata ta ci gaba da karɓan mujallun Hasumiyar Tsaro da kuma Awake!. A shekara ta 1950, an yi taron ƙasashe a birnin New York City, kuma iyayena sun halarta.
Nan ba da daɗewa ba, Ɗan’uwa Lawrence Jeffries ya soma ziyartarmu. Ya yi ƙoƙari ya taimaka mini in koyi gaskiya. Da farko, ban yarda da matakin da Shaidun Jehobah suka ɗauka na ƙin saka hannu a siyasa da kuma shiga aikin soja ba. Na gaya masa cewa idan kowa ya ƙi shiga soja a Amirka, maƙiya za su zo su ƙwace ƙasar. Amma Ɗan’uwa Lawrence ya tambaye ni cewa: “Me kake gani Jehobah zai yi idan kowa a Amirka yana bauta masa kuma maƙiya suka kawo musu hari?” Abin da ya faɗa game da wannan batun da kuma wasu batutuwa ya taimaka mini in ga cewa tunanina ba daidai ba ne. Hakan ya sa na soma marmarin koya game da Littafi Mai Tsarki.
Na yi sa’o’i ina karanta tsofaffin Hasumiyar Tsaro da Awake! da mamata take ajiyewa a wani ɗaki. Da shigewar lokaci, na gane cewa ina koyon gaskiya, sai na amince Ɗan’uwa Jeffries ya yi nazari da ni, kuma na soma halartan taro a kai a kai. Na ji daɗin abin da nake koya, don haka, na zama mai shela. Maƙasudin da na kafa wa kaina ya canja sa’ad da na gane cewa “babbar Ranar Yahweh ta yi kusa.” (Zaf. 1:14) Maimakon in mai da hankali ga zuwa makarantar jami’a, na kafa maƙasudin koya wa mutane game da Jehobah.
Na kammala makarantar sakandare a ranar 13 ga Yuni, 1956, kuma kwana uku bayan haka, na yi baftisma a wani taron da’ira. Ban san cewa zan sami albarku da yawa daga wurin Jehobah domin
na yanke shawarar in bauta masa kuma in koyar da mutane game da shi ba.NA JI DAƊIN KOYA DA KUMA KOYARWA SA’AD DA NAKE MAJAGABA
Wata shida bayan na yi baftisma, na soma hidimar majagaba na kullum. An wallafa wani talifi a Hidimarmu ta Mulki na Disamba 1956 mai jigo “Can You Serve Where the Need Is Great?” Na gaya wa kaina cewa abin da ya kamata in yi ke nan. Na yanke shawarar taimakawa a wurin da babu masu shela sosai.—Mat. 24:14.
Sai na ƙaura zuwa garin Edgefield da ke jihar South Carolina. Masu shela huɗu ne kawai a ikilisiyar da ke garin kuma na zama na biyar. Mukan yi taro a zauren wani ɗan’uwa. A kowane wata, nakan yi sa’o’i 100 ina wa’azi. Na shagala da yin ja-goranci a wa’azi da kuma ba da jawabai a cikin ikilisiya. Amma yayin da nake yin hakan, ina daɗa koya game da Jehobah.
Wata mata da nake nazarin Littafi Mai Tsarki da ita, tana da wani ɗakin jana’iza a garin Johnston da ke da nisan ’yan mil daga wurin da muke zama. Ta ba ni aiki na ɗan lokaci kuma ta bar mu mu yi amfani da gininta a matsayin Majami’ar Mulki.
Ɗan’uwa Jolly Jeffries, yaron ɗan’uwan da ya yi nazari da ni, ya ƙaura zuwa ikilisiyarmu daga Brooklyn da ke jihar New York don mu yi hidimar majagaba tare. Mun zauna a wani ƙaramin gida da wani ɗan’uwa ya ba mu.
Ba a biyan albashi sosai a kudancin Amirka a lokacin. Dala biyu ko uku ake biyan mu a rana. Akwai ranar da na yi amfani da dukan kuɗin da nake da shi na sayi abinci a wani shago. Da na fito, wani mutum ya same ni kuma ya tambaye ni: “Kana son aiki? Zan biya ka dala ɗaya a awa.” A bayyane yake cewa Jehobah yana so in ci gaba da hidima a Edgefield. Na yi hakan, kuma na halarci taron ƙasashe da aka yi a shekara ta 1958 a birnin New York City.
A rana ta biyu na taron, wani abu mai muhimmanci ya faru. Na haɗu da wata ’yar’uwa mai suna Ruby Wadlington da take hidimar majagaba a birnin Gallatin da ke jihar Tennessee. Da yake mu biyu muna so mu yi hidima a ƙasar waje, mun halarci taron da ake yi don waɗanda suke so su je makarantar Gilead. Daga baya, mun soma tura wa juna wasiƙu. Sai aka gayyace ni zuwa birnin Gallatin in ba da jawabi. Na yi amfani da wannan damar na tambaye ta ko za ta yarda ta aure ni. Na ƙaura zuwa ikilisiyar su Ruby kuma a shekara ta 1959 muka yi aure.
NA JI DAƊIN KOYA DA KUMA KOYARWA A IKILISIYA
A lokacin da nake shekara 23, na zama bawan ikilisiya wanda yanzu ake kira (mai tsara ayyukan rukunin dattawa) a garin Gallatin. Ikilisiyarmu ce ta farko da Charles Thompson ya ziyarta sa’ad da ya soma hidimar mai kula da da’ira. Ya ƙware sosai, amma duk da haka, ya so ya ji ra’ayina game da abubuwan da ’yan’uwa suke bukata, da kuma yadda masu kula da da’ira da suka riga shi suka kula da waɗannan bukatun. Na koya daga wurinsa
cewa yana da kyau mutum ya yi tambayoyi kuma ya san gaskiyar batu kafin ya yanke shawara.A watan Mayu na 1964, an gayyace ni in halarci Makarantar Hidima ta Mulki da aka yi na wata ɗaya a birnin South Lansing da ke jihar New York. ’Yan’uwan da suka koyar da mu a makarantar sun taimaka mini in daɗa kusantar Jehobah da kuma son koya game da shi.
NA JI DAƊIN KOYA DA KUMA KOYARWA A HIDIMAR MAI KULA DA DA’IRA DA KUMA MAI KULA DA GUNDUMA
A watan Janairu 1965, an naɗa ni mai kula da da’ira. Da’irarmu ta farko tana da girma sosai, ta kai daga birnin Knoxville da ke jihar Tennessee, har zuwa kusan birnin Richmond da ke jihar Virginia. Ƙari ga haka, ya haɗa da ikilisiyoyi a jihohin North Carolina da Kentucky da kuma West Virginia. Ikilisiyoyin baƙaƙen fata ne kaɗai muke ziyarta domin a lokacin, a kudancin Amirka ana hana baƙaƙen fata yin cuɗanya da fararen fata. Don haka, baƙaƙe da farare ba sa iya yin taro a wuri ɗaya. Yawancin ’yan’uwan talakawa ne, don haka, mukan ba mabukata ɗan abin da muke da shi. Wani ɗan’uwa da ya daɗe yana yin hidimar mai kula da da’ira ya koya mini wani darasi mai muhimmanci. Ɗan’uwan ya ce: “Kada ka yi kamar kai shugaba ne idan ka je ziyartar ikilisiyoyi. Sai sun ɗauke ka a matsayin ɗan’uwansu ne za ka iya taimaka musu.”
Sa’ad da muke ziyartar wata ƙaramar ikilisiya, matata Ruby ta soma nazari da wata matashiya da ke da ’ya mai shekara ɗaya. Da yake ba mu sami wadda za ta yi nazari da ita bayan mun bar wurin ba, sai Ruby ta soma yin hakan da ita ta wajen wasiƙu. Da muka sake ziyartar ikilisiyar, matar ta soma halartan taro a kullum. Da aka turo majagaba na musamman guda biyu zuwa ikilisiyar, sun ci gaba da yin nazari da ita, kuma ba da daɗewa ba bayan hakan ta yi baftisma. Bayan wajen shekaru 30, wato a 1995, sa’ad da muke Bethel na Patterson sai wata ’yar’uwa ta zo ta sami matata Ruby. ’Yar’uwar ’yar matar da Ruby ta yi nazari da ita ce. Ita da mijinta sun zo su halarci aji na 100 na makarantar Gilead.
Da’ira na biyu da muka yi hidima yana tsakiyar Florida. A lokacin, mun bukaci mota. Don hakan, mun sayi mota mai araha. Amma da muka yi mako ɗaya da motar, wani abu ya lalace a injin motar. Ba mu da kuɗin da za mu gyara motar, sai na kira wani ɗan’uwa da ke gyaran mota. Ya sa ɗaya daga cikin ma’aikatansa ya gyara mana motar, kuma ya ƙi ya karɓi kuɗi. Ya ce ba ma bukatar mu biya shi. Ya ma ba mu kyautar kuɗi. Hakan ya nuna cewa Jehobah yana kula da bayinsa. Mun kuma koyi muhimmancin bayarwa.
A duk lokacin da muka ziyarci wata ikilisiya, mukan zauna a gidan ’yan’uwa kuma hakan ya sa mun sami abokai da dama. Wata rana, na soma rubuta rahoto game da ikilisiyar da muka ziyarta kuma na bar rahoton a kan tafiretana sa’ad da na fita. Da na dawo da yamma, sai aka gaya mini cewa, yaron ɗan’uwan da muke zama a gidansa mai shekara uku, ya “taimaka” mini wajen ƙarasa rahoton. Na yi shekaru ina zolayarsa game da hakan.
A 1971, an turo mini wasiƙa, kuma a wasiƙar an ce in soma hidimar mai kula da gunduma a birnin New York City. Mun yi mamaki sosai! Shekaruna 34 kawai sa’ad da muka isa wurin. ’Yan’uwan sun marabce ni sosai a matsayin mai kula da gundumarsu na farko wanda baƙin fata ne.
Sa’ad da nake hidimar mai kula da gunduma, na ji daɗin koyar da ’yan’uwa game da Jehobah a kowane ƙarshen mako a taron da’ira. Da yawa daga cikin masu kula da da’irar sun fi ni ƙwarewa. Ɗaya daga cikinsu ne ya ba da jawabin baftismana. Ɗaya kuma mai suna Theodore Jaracz, ya zama memban Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu daga baya. Ƙari ga haka, akwai ’yan’uwa da yawa masu hidima a Bethel a Brooklyn da sun ƙware sosai a gundumar. Na yi farin ciki sosai don yadda masu kula da da’ira da kuma ’yan’uwa da ke hidima a Bethel suka ba ni haɗin kai sosai. Na ga yadda waɗannan makiyaya masu ƙauna suka dogara ga Kalmar Allah kuma suka goyi bayan ƙungiyar Jehobah. Yadda suka nuna sauƙin kai ya sa ya yi mini sauƙi in yi hidimata a matsayin mai kula da gunduma.
MUN KOMA HIDIMAR MAI KULA DA DA’IRA
A 1974, Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu ta naɗa wasu masu kula da da’ira su zama masu kula da gunduma. Sai aka mayar da ni mai kula da da’ira kuma a karon nan an tura ni South Carolina. A lokacin, farare da baƙaƙen fata sun soma yin taro a wuri ɗaya kuma hakan ya sa ’yan’uwa farin ciki sosai.
A ƙarshen 1976, an tura ni hidima a wata da’irar da ke jihar Georgia tsakanin Atlanta da Columbus. Na tuna lokacin da na gudanar da jana’iza na wasu yara baƙaƙe guda biyar da suka mutu sa’ad da wasu suka cinna wa gidansu wuta. An kwantar da mamarsu a asibiti don raunukan da ta ji a harin. ’Yan’uwa da yawa sun yi ta zuwa asibitin don su ƙarfafa iyayen. Irin ƙaunar da suka nuna ya burge ni. Irin tausayin nan zai taimaka wa bayin Jehobah su jimre duk wani mummunan yanayin da suka shiga.
NA JI DAƊIN KOYA DA KUMA KOYARWA A BETHEL
A 1977, an ce mu zo Bethel don mu taimaka da wani aiki na ’yan watanni. Da muka yi kusan gama aikin, sai membobin Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu guda biyu sun tambaye ni ko ni da matata Ruby za mu yarda mu ci gaba da yin hidima a Bethel. Mun yarda da hakan.
Na yi shekaru 24 ina hidima a Sashen Kula da Hidima inda ’yan’uwa suke warware matsaloli masu wuya. Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu ta yi shekaru tana ba da umurnai da suka jitu da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki. Da umurnan ne ake warware matsaloli masu wuya, kuma muna yin amfani da su mu koyar da masu kula da da’ira da dattawa da kuma majagaba. Umurnan da suke bayarwa sun taimaka wa mutane da yawa su daɗa kyautata halayensu na Kirista. Hakan kuma na ƙarfafa ƙungiyar Jehobah.
Daga 1995 zuwa 2018, na ziyarci reshen ofisoshinmu da yawa. A dā ana kiran masu ziyara kamar haka, dattawa masu ziyartar ofishin reshe. Nakan tattauna da Kwamitin da Ke Kula da Ofishinmu na ƙasashe dabam-dabam, da ’yan’uwa da ke hidima a Bethel da kuma ’yan’uwan da ke hidima a ƙasashen waje don in ƙarfafa su kuma in taimaka musu da duk wani damuwar da suke fuskanta. Kuma ’yan’uwan da suka gaya wa ni da Ruby labaransu sun ƙarfafa mu. Alal misali, mun ziyarci ƙasar Ruwanda a shekara ta 2000. Jin labaran yadda ’yan’uwa maza da mata a ƙasar da kuma ’yan’uwa da ke hidima a Bethel suka yi rayuwa a lokacin kisan ƙare dangi na 1994 ya ƙarfafa mu sosai. Da yawa sun rasa iyalansu da abokansu. Duk da abubuwan da suka fuskanta, ’yan’uwan sun nuna bangaskiya da bege, kuma sun ci gaba da farin ciki.
Yanzu mun wuce shekaru 80. Na yi shekaru 20 yanzu ina hidima a matsayin memban Kwamitin da Ke Kula da Ofishinmu na Amirka. Ban taɓa zuwa makarantar jami’a ba, amma Jehobah da kuma ƙungiyarsa sun koyar da ni da kyau. Hakan ya sa ina iya koya wa mutane gaskiyar da ke Littafi Mai Tsarki da zai amfane su har abada. (2 Kor. 3:5; 2 Tim. 2:2) Na ga yadda gaskiyar Littafi Mai Tsarki ta taimaka wa mutane su kyautata rayuwarsu kuma su kafa dangantaka mai kyau da Mahaliccinsu. (Yak. 4:8) A duk lokacin da muka sami zarafi, ni da Ruby muna ƙarfafa mutane su ci gaba da koya game da Jehobah da kuma koya ma wasu gaskiyar da ke Littafi Mai Tsarki, hakan shi ne gata mafi girma da bawan Jehobah zai iya samu!