Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

TALIFIN NAZARI NA 40

‘Sa Mutane Su Juya Zuwa Rayuwar Adalci’

‘Sa Mutane Su Juya Zuwa Rayuwar Adalci’

‘Waɗanda kuma suke sa mutane su juya zuwa rayuwar adalci, za su haskaka kamar taurari har abada abadin.’​—DAN. 12:3.

WAƘA TA 151 Zai Kira Su

ABIN DA ZA A TATTAUNA a

1. Wane abu mai ban sha’awa ne zai faru a lokacin Sarautar Yesu na Shekara Dubu?

 BA ƘARAMIN farin ciki ba ne za a yi sa’ad da aka soma tā da matattu a nan duniya a lokacin Sarautar Yesu na Shekara Dubu! Dukan waɗanda ƙaunatattunsu suka mutu suna marmarin ganin su. Yadda Jehobah ma yake ji ke nan. (Ayu. 14:15) Ka yi tunanin yadda kowa zai yi farin ciki a duniya sa’ad da aka tā da matattu. Kamar yadda muka gani a talifi na baya, “masu adalci” wato waɗanda aka rubuta sunayensu a littafin rai “za su tashi, su rayu.” (A. M. 24:15; Yoh. 5:29) Mai yiwuwa za a tā da waɗanda muke ƙauna da wuri a lokacin da za a yi tashin matattu a nan duniya. b Ƙari ga haka, “marasa adalci,” wato waɗanda ba su sami damar sanin Jehobah da kyau ko kuma bauta masa kafin su mutu ba za su tashi a kuwa “yi musu hukunci,” wato shari’a.

2-3. (a) Kamar yadda aka nuna a Ishaya 11:​9, 10, wane gagarumin aikin koyarwa ne za a yi? (b) Me za mu tattauna a wannan talifin?

2 Dukan waɗanda aka tā da su daga mutuwa za su bukaci a koyar da su. (Isha. 26:9; 61:11) Don haka, za a koyar da mutane a gagarumar hanyar da ba a taɓa yi ba tun farkon duniya. (Karanta Ishaya 11:​9, 10.) Me ya sa? Domin marasa adalci da aka tā da su za su bukaci su koya game da Yesu, da Mulkin Allah, da fansar Yesu, da muhimmancin sunan Allah da kuma dalilin da ya sa shi kaɗai ne ya isa ya yi mulki a sama da ƙasa. Masu adalci da aka tā da su ma za su bukaci su koyi abubuwa da Jehobah ya bayyana wa mutanensa a hankali game da nufinsa. Wasu daga cikin masu amincin nan sun mutu tun kafin a rubuta Littafi Mai Tsarki. Hakika, akwai abubuwa da yawa da za a koya wa masu adalci da marasa adalci da aka tā da su.

3 A wannan talifin, za mu tattauna tambayoyin nan: Ta yaya za a yi wannan gagarumin aikin koyarwa? Ta yaya halayen mutane za su nuna ko za a rubuta sunayensu a littafin rai har abada ko ba za a rubuta ba? Ya kamata amsoshin waɗannan tambayoyin su kasance da muhimmanci a gare mu. Kamar yadda za mu gani, wasu annabce-annabce masu ban sha’awa da ke littafin Daniyel da Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna za su taimaka mana mu kyautata yadda muka fahimci abin da zai faru sa’ad da aka tā da matattu. Da farko bari mu soma da tattauna abubuwan da aka ambata a annabcin Daniyel 12:​1, 2.

“WAƊANDA SUKA YI BARCI CIKIN ƘURAR ƘASA ZA SU TASHI”

4-5. Mene ne Daniyel 12:1 ta bayyana game da kwanakin ƙarshe?

4 Karanta Daniyel 12:1. Littafin Daniyel ya bayyana yadda abubuwa za su faru ɗaya bayan ɗaya a kwanakin ƙarshe. Alal misali Daniyel 12:1 ya nuna cewa Mika’ilu, wato Yesu Kristi, “zai tashi ya ɗauki mataki” a madadin mutanen Allah. Sashe na wannan annabcin ya soma cika ne a 1914 a lokacin da Allah ya naɗa Yesu a matsayin Sarkin Mulkinsa a sama.

5 Amma, an gaya wa Daniyel cewa Yesu “zai tashi” ya ɗauki mataki a “kwanakin azaba iri wadda ba a taɓa yi ba tun” da aka yi duniya. Waɗannan “kwanakin azaba” su ne ƙunci mai girma ko “azaba mai zafi” da aka ambata a Matiyu 24:21. Yesu zai tashi ya ɗauki mataki ko kuma zai kāre mutanen Allah a ƙarshen kwanakin azabar, wato a Armageddon. Littafin Ru’uyar da Aka Yi Wa Yohanna ya kira mutanen da Yesu zai kāre babban taro ko kuma taro mai girma “waɗanda suka fito daga azabar nan mai zafi.”​—R. Yar. 7:​9, 14.

6. Me zai faru bayan babban taro ko taro mai girma sun tsira daga azaba mai zafi? Ka bayyana. (Ka kuma duba “Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu” game da tashin matattu a fitowar nan.)

6 Karanta Daniyel 12:2. Mene ne zai faru bayan babban taro sun tsira daga kwanakin azaba? A dā mun ɗauka cewa annabcin nan yana nufin ci gaban da aka samu a aikin wa’azi bayan da maƙiya suka kusan hana aikin a 1918. c Amma yanzu, mun fahimci cewa waɗannan kalmomin suna nufin tashin matattu ne da zai auku a sabuwar duniya. Me ya sa muka faɗi hakan? A Ayuba 17:​16, an yi amfani da furucin nan “ƙurar ƙasa” kuma yana nufin abu ɗaya ne da “kabari.” Hakan yana nufin cewa Daniyel 12:2 yana nufin tashin matattu na zahiri ne da za a yi bayan kwanaki na ƙarshe da kuma bayan yaƙin Armageddon.

7. (a) A wace hanya ce za a tā da wasu zuwa “rai madawwami”? (b) A wace hanya ce wannan zai zama tashin matattu “mafi kyau”?

7 Amma mene ne Daniyel 12:2 take nufi sa’ad da ta ce, waɗansu za su tashi zuwa “rai madawwami”? Yana nufin cewa waɗanda aka tā da su kuma suka koya ko suka ci gaba da koya game da shi, suka yi biyayya ga Jehobah da Yesu a lokacin sarautar Yesu na shekara 1000, za su sami rai na har abada. (Yoh. 17:3) Wannan zai zama tashin matattu mafi kyau, kuma zai fi tashin matattu da aka yi a zamanin dā. (Ibran. 11:35) Me ya sa? Domin mutanen da aka tā da su a zamanin dā sun sake mutuwa.

8. Me ake nufi da za a tā da wasu “zuwa kunya da madawwamin ƙasƙanci”?

8 Amma ba dukan waɗanda aka tā da su daga mutuwa ne za su so su koya game da Jehobah ba. Annabcin Daniyel ya ce za a tā da wasu “zuwa kunya da madawwamin ƙasƙanci.” Hakan yana nufin cewa ba za a rubuta sunayensu a cikin littafin rai ba kuma ba za su sami rai na har abada ba domin tawayensu. A maimakon haka, za su fuskanci “ƙasƙanci” ko kuma hallaka. Don haka, Daniyel 12:2 tana magana ne game da abin da zai faru da dukan waɗanda aka tā da su daga mutuwa bisa ga abin da za su yi bayan an tā da su. d (R. Yar. 20:12) Wasu za su sami rai madawwami wasu kuma ba za su samu ba.

‘SA MUTANE SU JUYA ZUWA RAYUWAR ADALCI’

9-10. Me kuma zai faru bayan ƙunci mai girma kuma su waye ne “za su haskaka kamar sararin sama”?

9 Karanta Daniyel 12:3. Me kuma zai faru bayan “kwanakin azaba”? Ƙari ga abin da aka rubuta a Daniyel 12:​2, abin da aka rubuta a aya ta 3 tana magana ne game da abin da zai faru bayan ƙunci mai girma.

10 Su waye ne za su “haskaka kamar sararin sama”? Abin da Matiyu 13:43 ta faɗa zai taimaka mana mu san ko su waye ne ake maganar su. Wurin ya ce: ‘A lokacin ne masu adalci za su haskaka kamar rana a cikin Mulkin Ubansu.’ Idan muka duba abin da Yesu ya faɗa a nan, za mu ga cewa yana nufin “ ’ya’yan mulkin,” wato ’yan’uwansa shafaffu, waɗanda za su yi sarauta tare da shi a sama. (Mat. 13:38) Saboda haka, Daniyel 12:3 tana magana ne game da shafaffu da kuma aikin da za su yi a lokacin Sarautar Yesu na Shekara Dubu.

Shafaffu 144,000 za su haɗa hannu tare da Yesu Kristi don su ja-goranci aikin koyarwa da za a yi a lokacin Sarautar Yesu na Shekara Dubu (Ka duba sakin layi na 11)

11-12. Wane aiki ne shafaffu 144,000 za su yi a lokacin Sarautar Yesu na Shekara Dubu?

11 A wace hanya ce shafaffu za su ‘sa mutane su juya zuwa rayuwar adalci’? Shafaffu za su haɗa hannu tare da Yesu Kristi don su ja-goranci aikin koyarwa da za a yi a cikin shekaru 1000. Shafaffun nan 144,000 za su zama firistoci da kuma sarakuna. (R. Yar. 1:6; 5:10; 20:6) Ta hakan, za su taimaka wajen warkar da dukan al’ummai, wato taimaka ma ’yan Adam a hankali su sake zama kamiltattu. (R. Yar. 22:​1, 2; Ezek. 47:12) Wannan aikin zai sa shafaffu farin ciki sosai.

12 Su waye ne mutanen da za su “juya zuwa rayuwar adalci”? Za su haɗa da waɗanda za a tā da su daga mutuwa, da kuma waɗanda suka tsira wa Armageddon, da alama tare da yaran da za a haifa a sabuwar duniya. A ƙarshen shekara 1000, dukan waɗanda suke rayuwa a duniya za su zama kamiltattu. Amma a wane lokaci ne za a rubuta sunayensu a cikin littafin rai na dindindin, wato kamar an rubuta da biro, ba da fensir ba?

GWAJI NA ƘARSHE

13-14. Mene ne ya zama dole dukan kamiltattu su yi kafin su sami rai na har abada?

13 Wajibi ne mu tuna cewa idan mutum kamiltacce ne, hakan ba ya nufin cewa zai sami rai na har abada haka kawai. Ka yi tunanin misalin Adamu da Hauwa’u. Su kamiltattu ne a lokacin da aka yi su, amma ya kamata su nuna cewa suna biyayya ga Allah kafin su sami rai na har abada. Amma abin baƙin ciki, sun yi rashin biyayya.​—Rom. 5:12.

14 Yaya yanayin mutane a duniya zai zama a ƙarshen shekara 1000? Kowa zai zama kamiltacce. Shin kowa zai goyi bayan sarautar Jehobah a lokacin? Ko kuma wasu za su bi sawun Adamu da Hauwa’u waɗanda suka yi zunubi duk da cewa su kamiltattu ne? Muna bukatar mu san amsoshin tambayoyin nan. Amma ta yaya?

15-16. (a) A wane lokaci ne dukan ꞌyan Adam za su sami damar nuna amincinsu ga Jehobah? (b) Me zai faru a ƙarshen wannan gwajin?

15 Za a ɗaure Shaiɗan na tsawon shekara 1000. A lokacin, ba zai iya ruɗin kowa ba. Amma a ƙarshen shekara 1000, za a ɗan sake Shaiɗan. Zai yi ƙoƙari ya ruɗi kamiltattun mutane. A lokacin gwajin, dukan kamiltattu a duniya za su sami damar nuna ko suna ɗaukaka sunan Allah kuma suna goyon bayan sarautarsa ko a’a. (R. Yar. 20:​7-10) Abin da za su yi a lokacin zai nuna ko sun cancanci a rubuta sunayensu na dindindin a cikin littafin rai.

16 Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa wasu za su yi tawaye kamar yadda Adamu da Hauwa’u suka yi kuma za su ƙi sarautar Jehobah. Me zai faru da su? Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 20:15 ta gaya mana cewa: “Duk wanda ba a sami sunansa a rubuce a cikin wannan Littafin Rai ba, an jefar da shi cikin tafkin wutar nan.” Hakika, za a hallaka ꞌyan tawayen gabaki ɗaya har abada. Amma yawancin kamiltattu za su goyi bayan sarautar Jehobah. Saboda haka, za a rubuta sunayensu kamar da biro a cikin littafin rai.

A “KWANAKIN ƘARSHE”

17. Mene ne aka gaya wa Daniyel cewa zai faru a zamaninmu? (Daniyel 12:​4, 8-10)

17 Yin tunanin abubuwan da za su faru a gaba yana ratsa zuciyarmu sosai! Amma akwai wasu bayanai masu muhimmanci kuma da wani mala’ika ya ba Daniyel game da zamaninmu, wato, “kwanakin ƙarshe.” (Karanta Daniyel 12:​4, 8-10 e; 2 Tim. 3:​1-5) Mala’ikan ya gaya wa Daniyel cewa “Ilimi kuma za ya ƙaru.” Hakika a lokacin, bayin Allah za su fahimci annabcin da ke littafin Daniyel sosai. Mala’ikan ya kuma ƙara da cewa a lokacin “miyagu za su aika mugunta; daga cikin miyagu kuma babu fahimta.”

18. Me zai faru da mugaye nan ba da daɗewa ba?

18 A yau, za mu iya ganin kamar ba a hukunta mugaye don abubuwa marasa kyau da suke yi. (Mal. 3:​14, 15) Amma nan ba da daɗewa ba, Yesu zai hukunta waɗanda aka kwatanta da awaki kuma zai wāre su daga tumaki. (Mat. 25:​31-33) Ba za su tsira daga ƙunci mai girma ba, kuma ba za a tā da su daga mutuwa a sabuwar duniya ba. Ba za a rubuta sunayensu a cikin “littafin tunawa” da aka ambata a Malakai 3:16 ba.

19. Mene ne ya kamata mu yi a yanzu, kuma me ya sa? (Malakai 3:​16-18)

19 Yanzu ne ya kamata mu nuna cewa babu ruwanmu da masu mugunta. (Karanta Malakai 3:​16-18.) Jehobah yana tattara waɗanda yake ɗaukan su a matsayin ‘mutanensa mafi daraja.’ Hakika mu ma muna so ya ɗauke mu a matsayin masu daraja.

Ba ƙaramin farin ciki ne za mu yi ba a lokacin da muka ga Daniyel da ƙaunatattunmu da suka mutu sun “tashi” domin su karɓi rabonsu a sabuwar duniya! (Ka duba sakin layi na 20)

20. Wane alkawari ne aka yi wa Daniyel a ƙarshe, kuma me ya sa kake ɗokin ganin cikar alkawarin?

20 Hakika, muna farin ciki cewa muna rayuwa a lokacin da annabce-annabcen Littafi Mai Tsarki suke cika. Amma jim kaɗan, abubuwa masu ban mamaki da suka fi waɗannan za su faru. Za mu ga yadda za a hallaka mugaye. Bayan haka, za mu ga yadda alkawarin da Jehobah ya yi wa Daniyel zai cika, da ya ce: “A ƙarshen kwanaki kuwa za ka tashi ka karɓi naka rabon gādo.” (Dan. 12:13) Shin kana marmarin ganin ranar da Daniyel da ƙaunatattunka da suka mutu ‘za su tashi’? Idan haka ne, ka yi iya ƙoƙarinka ka riƙe amincinka. Ta hakan, za ka iya tabbata cewa sunanka zai ci gaba da kasancewa a cikin littafin rai.

WAƘA TA 80 ‘Mu Ɗanɗana, Mu Gani, Jehobah Nagari Ne’

a Wannan talifin ya ba da bayanai game da yadda muka fahimci gagarumin aikin koyarwar da aka kwatanta a Daniyel 12:​2, 3. Za mu tattauna lokacin da za a yi wannan koyarwar da waɗanda za su yi koyarwar. Za mu kuma ga yadda wannan koyarwar za ta taimaka ma waɗanda za su kasance a duniya a lokacin gwaji na ƙarshe, a ƙarshen Sarautar Yesu na Shekara Dubu.

b Mai yiwuwa za a soma tā da mutane masu aminci da suka mutu a kwanakin ƙarshe. Bayan haka za a tā da waɗanda suka mutu kafin su, zamani bayan zamani. Idan haka ne zai faru, kowa zai sami damar marabtar waɗanda suka sani da suka mutu. Ko da wace hanya ce za a yi tashin matattu, Littafi Mai Tsarki ya ce za a tā da waɗanda suka mutu zuwa sama “bi da bi.” Don haka, za mu iya cewa tashin matattu a nan duniya ma zai kasance bi da bi.​—1 Kor. 14:33; 15:23.

c Wannan bayanin ya canja yadda muka fahimci batun nan a dā kamar yadda yake a littafin nan Pay Attention to Daniel’s Prophecy! babi na 17, da kuma Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Yuli, 1987, shafuffuka na 21-25.

d Akasin haka, kalmomin nan “masu adalci” da “masara adalci” da aka rubuta a Ayyukan Manzanni 24:15 da kuma kalmomin nan “waɗanda suka yi abu mai kyau” da “waɗanda suka yi rashin gaskiya” da aka rubuta a Yohanna 5:29 suna magana ne game da abubuwan da waɗanda aka tā da su suka yi kafin su mutu.

e Daniyel 12:​4, 8-10 (THS) : “Amma kai, ya Daniyel, ka kulle zantattukan, ka rufe littafin da hatimi, har kwanakin ƙarshe; mutane da yawa za su kai da kawo a guje, ilimi kuma za ya ƙaru. Na ji, amma ban gane ba: sa’annan na ce, Ya ubangijina, ina mafitan waɗannan al’amura? Ya ce, Yi tafiyarka, ya Daniyel, gama an kulle zantattukan, an hatimce su har kwanakin ƙarshe. Waɗansu da yawa za su tsarkake kansu, su maida kansu farare, su tsabtata; amma miyagu za su aika mugunta; daga cikin miyagu kuma babu mai-fahimtawa; amma waɗanda su ke da hikima za su gane.”