Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu
Mene ne manzo Bulus yake nufi sa’ad da ya ce yana “kamar mutum ne wanda an haifa a lokacin da bai kamata ba”? (1 Korintiyawa 15:8)
Bisa ga abin da ke 1 Korintiyawa 15:8, manzo Bulus ya ce: “Daga ƙarshe duka, ya bayyana gare ni, ko da yake ni kamar mutum ne wanda an haifa a lokacin da bai kamata ba.” A dā, mun saba bayyana cewa manzo Bulus yana magana ne game da abin da ya faru da shi a lokacin da ya ga wahayi game da Yesu a sama. Kamar dai an sake haifan sa ne ko kuma tā da shi daga mutuwa zuwa sama tun kafin lokacin da ya kamata, wato ɗarurruwan shekaru kafin a fara yin wannan tashin matattu. Amma bayan mun ƙara yin nazari a kan wannan ayar, mun ga cewa yana da muhimmanci mu canja yadda muka fahimci ayar.
Gaskiya ne cewa Bulus yana magana game da abin da ya faru sa’ad da ya zama Kirista. Me yake nufi sa’ad da ya ce shi “mutum ne wanda an haifa a lokacin da bai kamata ba”? Yana iya nufin abubuwa da dama.
Abin da ya faru jim kaɗan bayan ya zama Kirista ya faru ne ba zato kuma abin ya jijjiga shi sosai. Yaran da aka haife su ’yan bakwaini suna fitowa ne ba zato. Yayin da Shawulu, wanda daga baya an san shi da sunan nan Bulus, yake tafiya zuwa Dimashƙu don ya tsananta wa Kiristoci da ke wurin, bai yi zato cewa zai ga Yesu a cikin wahayi bayan an tā da Yesu ba. Yadda Bulus ya zama Kirista ya ba Bulus mamaki har da Kiristocin da yake shirin ya je ya tsananta musu a birnin. Ƙari ga haka, abin ya jijjiga shi sosai har ya makance na ɗan lokaci.—A. M. 9:1-9, 17-19.
Ya zama Kirista a lokacin da “bai kamata ba.” Ga yadda juyin The Jerusalem Bible ya fassara wannan furucin, ya ce: “Kamar dai an haife ni ne a lokacin da mutane ba su yi zato ba.” A lokacin da Bulus ya zama Kirista, Yesu ya riga ya koma sama. Bulus bai gan Yesu bayan da Yesu ya tashi daga mutuwa kafin ya haura sama ba. Amma mutanen da ya ambata su a wasu ayoyi kafin wannan ayar sun ga Yesu kafin ya koma sama. (1 Kor. 15:4-8) Sa’ad da Yesu ya bayyana ga Bulus ba zato, hakan ya ba shi damar ganin Yesu bayan tashinsa daga mutuwa, ko da yake hakan ya zama kamar “a lokacin da bai kamata ba” ne.
Yana magana ne da sauƙin kai a wannan ayar. Bisa ga wasu masana, furucin da Bulus ya yi a nan, yana iya nuna kamar ya rena kansa ne. Idan abin da Bulus yake nufi ke nan, to, yana cewa ne bai isa a ba shi damar zama manzo ba. Bayan haka, ya ce: “Ni ne mafi ƙanƙanta a cikin manzannin Yesu, ban ma isa a ce da ni manzo ba, saboda na tsananta wa jama’ar masu bin Allah. Amma saboda alherin Allah ne na zama yadda nake.”—1 Kor. 15:9, 10.
Saboda haka, furucin yana iya nufin cewa Bulus yana magana ne game da yadda Yesu ya bayyana masa ba zato, yadda ya zama Kirista a lokacin da bai zata ba ko kuma yadda bai cancanci ya sami irin wannan wahayin ba. Ko da mene ne Bulus yake nufi a nan, a bayyane yake cewa Bulus ya ɗauki wannan wahayin da muhimmanci sosai. Hakan ya tabbatar masa cewa an riga an tā da Yesu daga mutuwa. Shi ya sa a yawancin lokuta, yakan yi magana game da wannan wahayin da ya gani yayin da yake wa’azi ga mutane game da tashin Yesu daga mutuwa.—A. M. 22:6-11; 26:13-18.