Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu
Su waye ne za a tā da su daga mutuwa kuma wane irin tashin matattu ne za a yi musu?
Ka yi la’akari da yadda Littafi Mai Tsarki ya amsa tambayoyin nan.
Ayyukan Manzanni 24:15 ta gaya mana cewa ‘za a tā da matattu, masu adalci da marasa adalci duka.’ Masu adalcin su ne waɗanda suka yi biyayya ga Allah kafin su mutu. Don haka sunayensu na cikin littafin rai. (Mal. 3:16) Marasa adalcin kuma sun haɗa da mutanen da sun mutu ba tare da samun damar koya game da Jehobah ba. Don haka, sunayensu ba sa cikin littafin rai.
Yohanna 5:28, 29 sun yi magana game da rukunonin nan biyu da aka ambata a Ayyukan Manzanni 24:15. Yesu ya ce ‘waɗanda suka yi abu mai kyau za su tashi, su rayu, amma waɗanda suka yi rashin gaskiya, za su tashi a kuwa yi musu hukunci.’ Masu adalcin sun yi abubuwa masu kyau kafin su mutu. Za a tā da su su rayu domin sunayensu na cikin littafin rai. Amma marasa adalcin sun yi abubuwa marasa kyau kafin su mutu, don haka, za a tā da su zuwa ga hukunci ko shari’a. Ba a rubuta sunayensu a cikin littafin rai ba, don haka, za a yi musu shari’a, wato za a ba su lokaci a ga ko za su koya game da Jehobah, su bauta masa kuma a saka sunayensu a cikin littafin rai.
Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 20:12, 13 sun bayyana cewa dukan waɗanda aka tā da su daga matattu za su bukaci su yi biyayya da dukan abubuwan da ke “rubuce a cikin littattafan,” wato sabbin dokokin da Allah zai ba mu a sabuwar duniya ke nan. Za a kawar da waɗanda suka ƙi yin biyayya da dokokin.—Isha. 65:20.
Daniyel 12:2 ta annabta cewa waɗanda suka mutu za a tā da su, “waɗansu zuwa rai madawwami, waɗansu kuwa zuwa kunya da madawwamin ƙasƙanci.” Wannan ayar tana magana game da abin da zai faru bayan an yi musu shari’a. Za su sami ‘rai madawwami’ ko ‘madawwamin ƙasƙanci.’ Saboda haka, a ƙarshen Shekara Dubu na Sarautar Yesu, wasu za su sami rai na har abada, wasu kuwa za a hallaka su har abada.—R. Yar. 20:15; 21:3, 4.
Ka yi la’akari da wannan kwatancin. Abin da zai faru da rukunoni biyu da za a tā da su daga matattu yana kama da mutanen da suke so su zauna a wata ƙasa. Masu adalcin suna kama da waɗanda aka ba su izinin zama a wata ƙasa ko izinin yin aiki a ƙasar. Hakan zai sa a san da su kuma su ɗan sami ’yanci, amma marasa adalci suna kama da waɗanda aka ba su izinin zama a ƙasar na ɗan lokaci. Dole ne irin waɗannan baƙin su nuna cewa sun cancanci zama a ƙasar kafin a bar su su ci gaba da zama a ƙasar. Haka ma, marasa adalcin da za a tā da su za su bukaci su yi biyayya da dokokin Jehobah kuma su nuna cewa sun cancanci su ci gaba da yin rayuwa a aljanna a duniya. Amma ko da wace irin izini na zuwa wata ƙasa aka ba mutum, a ƙarshe, wasu za a ba su ’yancin zama ’yan ƙasar, wasu kuma a kore su daga ƙasar. Za a yanke hukuncin ne bisa ga irin halayen da suka nuna a ƙasar. Haka ma, bayan shekara dubu, hukuncin da za a yanke ma dukan waɗanda aka tā da su daga mutuwa zai dangana ga irin halaye da kuma bangaskiyar da suka nuna a sabuwar duniya.
Jehobah Allah ne mai ƙauna da kuma adalci. (M. Sha. 32:4; Zab. 33:5) Zai nuna ƙaunarsa ta wajen tā da masu adalci da marasa adalci. Amma zai bukaci dukansu su bi ƙa’idodinsa na adalci. Waɗanda suka ƙaunace shi kuma suka yi rayuwa bisa ga ƙa’idodinsa na adalci ne kaɗai za a bar su su ci gaba da yin rayuwa a sabuwar duniya.