Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu
Mene ne Yesu yake nufi sa’ad da ya ce: “Kada ku yi tsammani na zo in kawo salama ne a duniya”?
Yesu ya koya wa mutane su yi zaman lafiya da juna. Amma akwai lokacin da ya gaya wa manzanninsa cewa: ‘Kada ku yi tsammani na zo in kawo salama ne a duniya. Ba domin in kawo salama na zo ba, sai dai faɗa. Gama na zo ne, in sa ɗa ya yi gāba da babansa, ’ya kuma da mamarta, matar ɗa kuma da mamar mijinta.’ (Mat. 10:34, 35) Mene ne Yesu yake nufi a nan?
Ba wai Yesu yana so ya raba kan iyalai ba ne, amma ya san cewa abubuwa da yake koyarwa za su iya raba kan iyali. Shi ya sa waɗanda suke so su zama almajiran Kristi kuma su yi baftisma, suna bukatar su san cewa a wasu lokuta, membobin iyalinsu ba za su yi farin ciki ba don matakin da suka ɗauka. Idan abokin aurensu ko wani a iyalinsu ya yi adawa da su, zai iya yi musu wuya su ci gaba da bin koyarwar Kristi.
Littafi Mai Tsarki ya ƙarfafa Kiristoci su “yi zaman lafiya da kowa.” (Rom. 12:18) Amma koyarwar Yesu zai iya jawo “faɗa” a wasu iyalai. Hakan yana iya faruwa ne idan wani ya soma bin koyarwar Yesu amma wasu a iyalinsa sun ƙi koyarwar. Idan hakan ya faru, waɗanda suka ƙi koyarwar suna mai da kansu ‘abokan gāban’ wanda yake koyan gaskiya.—Mat. 10:36.
Almajiran Kristi da suke zama a gida ɗaya da waɗanda ba sa bauta wa Jehobah za su iya fuskantar yanayin da zai bukaci su zaɓa ko za su faranta wa Jehobah da Yesu rai ko su faranta wa danginsu rai. Alal misali, danginsu da ba Shaidu ba za su iya ƙoƙarin tilasta musu su yi bukukuwa da ke da alaƙa da addinan ƙarya. Idan suka fuskanci irin wannan yanayin, wa za su zaɓa su faranta wa rai? Yesu ya ce: “Duk wanda ya fi son mamarsa ko babansa fiye da ni, bai isa ya zama nawa ba.” (Mat. 10:37) Hakika, Yesu ba ya nufin cewa mutum yana bukatar ya rage yadda yake ƙaunar iyayensa kafin ya zama almajirinsa. Amma yana koya musu ne yadda za su zaɓi abubuwa mafi muhimmanci a rayuwa. Idan danginmu da ba Shaidu ba suna ƙoƙarin hana mu mu bauta wa Jehobah, ba za mu daina ƙaunar su ba, amma mun san cewa abin da ya fi muhimmanci shi ne mu ƙaunaci Allah.
Babu shakka idan wani danginmu yana adawa da mu don muna bauta wa Jehobah, hakan zai iya sa mu baƙin ciki sosai. Duk da haka, dole ne almajiran Yesu su tuna abin da ya faɗa cewa: “Duk wanda bai ɗauki [‘gungumen azabarsa,’ NWT] ya bi ni ba, bai isa ya zama nawa ba.” (Mat. 10:38) Kiristoci sun san cewa ɗaya daga cikin abubuwa da za su bukaci su jimre shi ne yadda danginsu za su iya ƙin su domin suna bin Kristi. Amma suna sa rai cewa halinsu mai kyau zai sa danginsu su canja ra’ayinsu kuma su soma nazarin Littafi Mai Tsarki.—1 Bit. 3:1, 2.