Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Abin da Ke Sa Mu Bauta wa Allah Cikin Tsari

Abin da Ke Sa Mu Bauta wa Allah Cikin Tsari

“Ubangiji bisa ga hikima ya kafa duniya: Bisa ga fahimi kuma ya ƙarfafa sammai.”​—MIS. 3:19.

WAƘOƘI: 105107

1, 2. (a) Yaya wasu suke ji idan an gaya musu cewa Allah yana da ƙungiya? (b) Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?

SHIN Allah yana da ƙungiyar da take bauta masa cikin tsari? Wasu za su ce: “Ba ka bukatar wata ƙungiya da za ta ja-gorance ka muddin kana da dangantaka mai kyau da Allah.” Wannan ra’ayin daidai ne? Mene ne Littafi Mai Tsarki ya koyar game da hakan?

2 A wannan talifin, za mu tattauna abubuwan da suka nuna cewa Jehobah shi ne Allah Mai tsarin da babu kamarsa. Ƙari ga haka, za mu tattauna abin da ya kamata mu yi sa’ad da ƙungiyar Jehobah ta ba mu umurni. (1 Kor. 14:​33, 40) Ja-gorar da ke cikin Littafi Mai Tsarki ya taimaka wa bayin Jehobah su yi wa’azi a faɗin duniya a ƙarni na farko da kuma zamaninmu. Idan muna bin umurnin da ke cikin Littafi Mai Tsarki da kuma ja-gorar da ƙungiyar Jehobah take ba mu, hakan zai sa ƙungiyar ta kasance da tsabta da salama da kuma haɗin kai.

JEHOBAH ALLAH NE MAI TSARI DA BABU KAMARSA

3. Me ya sa ka tabbata cewa Jehobah Allah mai tsari ne da babu kamarsa?

3 Abubuwan da Allah ya halitta sun nuna cewa shi Mai tsari ne sosai. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ubangiji bisa ga hikima ya kafa duniya: Bisa ga fahimi kuma ya ƙarfafa sammai.” (Mis. 3:19) Abubuwan da muka sani “kaɗan ne kawai daga cikin al’amuran [Allah]. Ɗan ƙis kaɗai muke ji a kansa.” (Ayu. 26:​14, Littafi Mai Tsarki) Duk da haka, wannan ɗan ilimin da muke da shi a kan duniyoyi da kuma damin-damin taurarin da ke sama sun nuna mana cewa halittun Allah suna da tsari ba kaɗan ba. (Zab. 8:​3, 4) Kowane damin taurari yana ɗauke da miliyoyin taurarin da suke tafiya bisa ga tsari. Duniyoyin da suke kewaye rana suna bin tsarin da aka kafa musu kamar dai suna biyayya ne ga dokokin hanya! Hakika, yadda aka tsara sama da ƙasa ya nuna cewa Jehobah, wanda ya yi duniya da kuma “sammai bisa ga fahimi” ya cancanci mu ba shi yabo da ɗaukaka da girma.​—⁠Zab. 136:​1, 5-9.

4. Me ya sa kimiyya ta kasa ba da amsoshin tambayoyi da yawa?

4 Ilimin kimiyya ya taimaka mana mu san abubuwa da yawa game da sama da duniya, kuma ya inganta rayuwarmu a wasu fannoni. Amma akwai tambayoyi da yawa da masanan kimiyya sun kasa ba mu amsoshinsu. Alal misali, masanan taurari sun kasa gaya mana ko ta yaya ne sama da ƙasa suka soma wanzuwa da kuma abin da ya sa ‘yan Adam da dabbobi da kuma shuke-shuke suke rayuwa a duniya. Ƙari ga haka, yawancin mutane sun kasa bayyana dalilin da ya sa mutane ba sa so su mutu. (M. Wa. 3:11) Me ya sa mutane sun kasa samun amsoshi ga tambayoyi masu muhimmanci kamar waɗannan? Wani dalili shi ne, ‘yan kimiyya da yawa da kuma wasu mutane suna koyar da juyin halitta da kuma ra’ayin da ya saɓa wa abin da Allah ya faɗa. Amma Jehobah ya ba da amsoshi ga tambayoyin da mutane a ko’ina suke yi a cikin Littafinsa.

5. A waɗanne hanyoyi ne rayuwarmu ta dangana ga bin dokokin da ke sarrafa sama da ƙasa?

5 Rayuwarmu ta dangana ne ga bin dokokin da Jehobah ya kafa don sarrafa sama da ƙasa kuma waɗannan dokokin ba sa canjawa. Masu gyaran wuta da masu gyaran famfo da injiniyoyi da matuƙan jirgin sama da likitoci masu fiɗa suna bin waɗannan dokokin yayin da suke aikinsu. Alal misali, likitoci masu fiɗa sun san inda zuciyar ɗan Adam a jikinsa. Saboda haka, ba za su je suna neman zuciyar marar lafiya a wani wuri dabam ba. Dukanmu mu san cewa bin dokokin da ke sarrafa sama da ƙasa yana da amfani sosai kuma idan muka yi banza da su, za mu sha wuya. Alal misali, mun san cewa idan muka yi tsalle daga wani wuri mai tsayi sosai, muna iya mutuwa.

ABUBUWAN DA ALLAH YA TSARA

6. Me ya sa Jehobah yake son bayinsa su bauta masa cikin tsari?

6 Jehobah ya tsara sama da ƙasa sosai. Saboda haka, ba abin mamaki ba ne cewa Allah yana son bayinsa su bauta masa cikin tsari. Shi ya sa ya ba mu Littafi Mai Tsarki don ya yi mana ja-gora. Za mu sha wahala idan muka ƙi bin ƙa’idodinsa da kuma ja-gorar ƙungiyarsa, kuma ba za mu ji daɗin rayuwa ba.

7. Me ya nuna cewa an tsara Littafi Mai Tsarki sosai?

7 Littafi Mai Tsarki ba tarin littattafan Yahudawa da na Kiristoci da ba su jitu da juna ba ne. Akasin haka, littafi ne da Allah ya tsara da kyau. Dukan littattafan da suke cikin Littafi Mai Tsarki suna da alaƙa da juna. Daga Farawa zuwa Ru’ya ta Yohanna, saƙon da aka fi mai da hankali a kai shi ne, Jehobah ne yake da iko ya mallaki sama da ƙasa, kuma zai mai da duniyar nan ta zama aljanna ta wurin yin amfani da Mulkinsa, wanda Kristi, “zuriyar” macen ne zai zama sarkinsa.​—⁠Karanta Farawa 3:15; Matta 6:10; Ru’ya ta Yohanna 11:⁠15.

8. Me ya sa za mu iya cewa an tsara Isra’ilawa da kyau sosai?

8 Jehobah ya tsara al’ummar Isra’ila da kyau sosai. Alal misali, bisa ga Dokar da Allah ya ba Musa, an tsara “mata waɗanda suke yin hidima a bakin ƙofar tanti na taruwa.” (Fit. 38:⁠8) Isra’ilawa suna bin tsarin da Jehobah ya kafa game da yadda za su yāɗa zango da kuma warware mazauni. Ƙari ga haka, Sarki Dauda ya tsara Lawiyawa da Firistoci su yi ayyuka dabam-dabam. (1 Laba. 23:​1-6; 24:​1-3) A duk lokacin da Isra’ilawa suka yi biyayya ga Jehobah, suna kasancewa da tsari da salama da kuma haɗin kai.​—⁠K. Sha. 11:​26, 27; 28:​1-14.

9. Me ya nuna cewa Kiristoci a ƙarni na farko sun bauta wa Allah cikin tsari?

9 Jehobah ya tsara Kiristoci a ƙarni na farko kuma ya kafa hukumar da za ta kula da ayyukansu, wadda ta ƙunshi manzannin kaɗai a dā. (A. M. 6:​1-6) Daga baya, an zaɓi ƙarin ‘yan’uwa maza su yi hidima a ƙarƙashin wannan hukumar. (A. M. 15:⁠6) Mambobin hukumar ko kuma ‘yan’uwan da suka zaɓa su yi aiki tare da su sukan rubuta wasiƙun da ke ɗauke da gargaɗi da kuma ja-gora daga wurin Jehobah don ƙarfafa ‘yan’uwan. (1 Tim. 3:​1-13; Tit. 1:​5-9) Ta yaya ikilisiyoyi suka amfana daga bin umurnin hukumar da ke kula da ayyukan Kiristoci a ƙarni na farko?

10. Me ya faru sa’ad da Kiristoci na farko suka bi umurnin da hukumar da ke kula da ayyukan Kiristoci ta bayar? (Ka duba hoton da ke shafi na 9.)

10 Karanta Ayyukan Manzanni 16:​4, 5Hukumar da ke kula da ayyukan Kiristoci a ƙarni na farko ta zaɓi ‘yan’uwa maza su je ikilisiyoyi dabam-dabam don su kai musu umurnin da “manzanni da dattiɓai da ke cikin Urushalima suka” ba su. Yayin da ikilisiyoyi suke bin waɗannan umurnin da aka ba su, sun sami “ƙarfafa cikin imani” kuma sun ci gaba da ƙaruwa kowace rana. Wannan misalin da ke cikin Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa bin ja-gorar ƙungiyar Jehobah a yau yana da amfani sosai, ko ba haka ba?

KANA BIN JA-GORAR DA ƘUNGIYAR JEHOBAH TAKE MANA?

11. Mene ne waɗanda Jehobah ya naɗa su yi ja-gora a cikin ikilisiya za su yi da umurnin da ƙungiyar Jehobah take bayarwa?

11 Membobin Kwamitin da ke Kula da Ofishin Shaidun Jehobah da masu kula da da’ira da kuma dattawa suna bukatar su riƙa bin ja-gorar da ƙungiyar Jehobah take bayarwa. Ban da haka ma, Littafi Mai Tsarki ya umurci dukanmu mu riƙa yin biyayya ga waɗanda suke mana shugabanci. (K. Sha. 30:16; Ibran. 13:​7, 17) Waɗanda suke so su kasance da aminci ga Jehobah ba sa nuna halin tawaye ko kuma suna gunaguni game da umurnin da aka ba su. Hakika ba ma so mu zama kamar Diyoturifis, wanda ba ya daraja waɗanda suke yin ja-gora a cikin ikilisiya. (Karanta 3 Yohanna 9, 10.) Muna iya tambayar kanmu: ‘Shin ina ƙarfafa ‘yan’uwana su kasance da aminci ga Jehobah? Ina saurin bin shawarar da ƙungiyar Jehobah take bayarwa?’

12. Wane canji ne aka yi game da yadda za a riƙa naɗa dattawa da kuma bayi masu hidima?

12 Ka yi la’akari da wani canjin da Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah suka yi kwana kwanan nan. Talifin nan “Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu” da ke Hasumiyar Tsaro na 15 ga Nuwamba 2014, ya ambata wasu canjin da aka yi game da yadda za a riƙa naɗa dattawa da kuma bayi masu hidima. Talifin ya ambata cewa a ƙarni na farko, hukumar da ke kula da ayyukan Kiristoci sun ce masu ziyara kaɗai ne za su iya naɗa dattawa da kuma bayi masu hidima. Saboda haka, tun daga ranar 1 ga Satumba ta shekara ta 2014, masu kula da da’ira ne suke naɗa dattawa da kuma bayi masu hidima. Mai kula da da’ira yana yin iya ƙoƙarinsa don ya san mazan da ake so a naɗa kuma ya yi wa’azi tare da su. Mai kula da da’ira zai kuma lura da yadda iyalinsa suke yi a ibadarsu ga Jehobah. (1 Tim. 3:​4, 5) Bayan haka, dattawa da kuma mai kula da da’ira za su yi taro. Za su duba abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da halin da mutum da ya cancanci a naɗa shi dattijo ko kuma bawa mai hidima zai kasance da shi.​—⁠1 Tim. 3:​1-10, 12, 13; 1 Bit. 5:​1-3.

13. Ta yaya za mu nuna cewa muna bin ja-gorar da dattawa suke bayarwa?

13 Muna bukatar mu bi ja-gorar da dattawa suke bayarwa bisa ga Littafi Mai Tsarki. Waɗannan dattawa masu aminci suna barin “sahihan” umurnin da ke cikin Kalmar Allah ya yi musu ja-gora. (1 Tim. 6:⁠3) Ka tuna da abin da Bulus ya faɗa game da waɗanda ba sa bin tsarin da ake yi a cikin ikilisiya. Waɗansu a cikinsu ‘ba sa yin aiki ko kaɗan’ sai dai su riƙa yin ‘shishigi’ a kan abin da bai shafe su ba. Dattawa sun yi musu magana amma sun ƙi ji. Mene ne ‘yan’uwa ya kamata su yi game da irin waɗannan mutanen? Bulus ya ce: “Ku shaida wannan mutum, kada ku yi ma’amala da shi.” Umurnin da ya ba su shi ne, su daina yin tarayya da irin waɗannan mutanen, amma kada su ɗauke su a matsayin maƙiyansu. (2 Tas. 3:​11-15) Hakazalika, dattawa suna iya taimaka wa wanda yake yin abin da bai dace ba kamar fita zance da wanda ba Mashaidi ba. Idan mutumin ya ƙi jin abin da suka ce, dattawa suna iya ba da jawabi a kan yadda irin wannan halin zai iya sa mutane su riƙa magana marar kyau game da ƙungiyar Jehobah. (1 Kor. 7:39) Mene ne za ka yi idan dattawa suka ba da irin wannan jawabin a ikilisiyarku? Idan ka san cewa akwai mutumin da yake da irin wannan halin a cikin ikilisiya, shin za ka daina yin tarayya da shi? Idan ka yi hakan, za ka taimaka masa ya fahimci cewa abin da yake yi ba shi da kyau kuma hakan zai iya sa ya canja halinsa. [1]

KU KASANCE DA TSABTA DA SALAMA DA HAƊIN KAI A CIKIN IKILISIYA

14. Ta yaya za mu iya sa ikilisiya ta kasance da tsabta?

14 Za mu iya sa ikilisiya ta kasance da tsabta idan muna bin ja-gorar da ke cikin Littafi Mai Tsarki. Ku yi la’akari da abin da ya faru a Koranti na dā. Bulus ya yi iya ƙoƙarinsa a yin wa’azi a wurin kuma yana ƙaunar ‘yan’uwansa “tsarkakakku” da suke wajen. (1 Kor. 1:​1, 2) Ku yi tunanin yadda Bulus ya ji sa’ad da ya gano cewa akwai wani da yake yin lalata kuma dattawan ba su yi kome game da wannan mutumin ba! Bulus ya gaya wa dattawan cewa su yi masa yankan zumunci. Dattawa suna bukatar su kawar da ‘yistin’ da zai iya ɓata ikilisiyar. (1 Kor. 5:​1, 5-7, 12) Idan muka goyi bayan dattawa sa’ad da suka yi wa wani yankan zumunci, hakan zai sa ikilisiyar ta kasance da tsabta kuma zai iya sa mutumin ya nemi gafarar Jehobah.

15. Ta yaya za mu ci gaba da kasancewa da salama a cikin ikilisiya?

15 Akwai wata matsala kuma da ake bukatar a magance ta a Koranti. Wasu ‘yan’uwa suna kai ƙarar ‘yan’uwansu a kotu. Bulus ya yi musu wannan tambayar: ‘Ba gwamma ka yi haƙuri da zalunci ba?’ (1 Kor. 6:​1-8) Irin wannan matsala tana faruwa a yau. A wasu lokuta, ‘yan’uwa sun yi harkokin kasuwanci da juna amma daga ƙarshe, an yi asarar kuɗi ko kuma wataƙila wani ya cuci wani. Hakan ya sa sun kai ƙara a kotu. Amma Kalmar Allah ta taimaka mana mu fahimci cewa gwamma mu yi haƙuri da asarar da muka yi da mu yi abin da zai ɓata sunan Allah ko kuma ya sa ‘yan’uwanmu su ƙi kasancewa da salama. [2] Wajibi ne mu bi shawarar da Yesu ya ba da idan muna so mu magance irin wannan matsalolin. (Karanta Matta 5:​23, 24; 18:​15-17.) Idan muka yi hakan, za mu kasance da salama a matsayinmu na bayin Allah.

16. Me ya sa ya kamata mutanen Allah su kasance da haɗin kai?

16 Littafi Mai Tsarki ya nuna dalilin da ya sa ya kamata bayin Allah su kasance da haɗin kai. Marubucin wannan zaburar ya ce: “Duba, me ya fi wannan kyau da kuwa daɗi ‘yan’uwa su yi zaman jiyayya!” (Zab. 133:⁠1) Sa’ad da Isra’ilawa suka yi biyayya ga umurnin Jehobah, hakan ya sa sun kasance da tsari da kuma haɗin kai. Allah ya yi annabci game da yadda mutanensa za su kasance a nan gaba kuma ya ce: “Zan haɗa su tare kamar tumaki a garke.” (Mi. 2:​12, LMT) Ƙari ga haka, Jehobah ya gaya wa annabi Zafaniya cewa: “Sa’annan zan juya wa al’ummai da harshe mai-tsarki [koyarwar Littafi Mai Tsarki], domin dukansu su kira sunan Ubangiji, su bauta masa da zuciya ɗaya.” (Zaf. 3:⁠9) Abin farin ciki ne mu kasance da gatan bauta wa Jehobah tare da ‘yan’uwanmu!

Ya kamata dattawa su yi iya ƙoƙarinsu wajen taimaka wa wanda ya yi abin da bai dace ba (Ka duba sakin layi na 17)

17. Don ikilisiya ta kasance da haɗin kai da kuma tsabta, wane mataki ne dattawa za su ɗauka a kan wanda ya yi zunubi?

17 Idan dattawa suna so a kasance da tsabta da kuma haɗin kai a cikin ikilisiya, wajibi ne su ɗauki mataki nan da nan sa’ad da wani ya yi zunubi mai tsanani. Bulus ya san cewa ko da yake Jehobah yana ƙaunar mu ba ya yin shiru sa’ad da mutum ya yi zunubi. (Mis. 15:⁠3) Domin Bulus yana ƙaunar ‘yan’uwan da ke Koranti, ya rubuta musu gargaɗin da ke cikin littafin Korintiyawa na Ɗaya. Bayan wasu watanni, ya sake rubuta musu littafin Korintiyawa na Biyu, kuma abin da ke cikin saƙon ya nuna cewa dattawan sun bi shawarar da ya ba su kuma suna samun ci gaba. Idan mutum ya yi abin da bai dace ba, ya kamata dattawa su yi iya ƙoƙarinsu don su taimaka masa, kuma su yi hakan cikin ƙauna.​—⁠Gal. 6:⁠1.

18. (a) A wace hanya ce Kalmar Allah ta taimaka wa Kiristoci a ƙarni na farko? (b) Mene ne za mu tattauna a talifi na gaba?

18 Mun ga cewa Kalmar Allah ta taimaka wa Kiristocin da ke Koranti da kuma wasu wurare a ƙarni na farko su kasance da tsabta da salama da kuma haɗin kai a cikin ikilisiya. (1 Kor. 1:10; Afis. 4:​11-13; 1 Bit. 3:⁠8) Kuma hakan ya sa ‘yan’uwanmu a lokacin su yi wa’azi da ƙwazo. Shi ya sa Bulus ya ce sun yi wa’azin bishara ga “dukan halitta da ke ƙarƙashin sama.” (Kol. 1:23) A yau ma, ana yi wa mutanen da ke faɗin duniya wa’azi game da nufin Allah, kuma hakan ya faru ne don muna da haɗin kai a ƙungiyar Jehobah. A talifi na gaba, za mu ga abubuwan da suka nuna cewa bayin Allah suna daraja Littafi Mai Tsarki kuma sun ƙuduri niyyar cewa za su ci gaba da ɗaukaka Jehobah Allah Maɗaukaki.​—⁠Zab. 71:​15, 16.

^ [1] (sakin layi na 13) Ka duba littafin nan Organized to Do Jehovah’s Will, shafuffuka na 134-136.

^ [2] (sakin layi na 15) Ku duba littafin nan “Ku Tsare Kanku Cikin Ƙaunar Allah” shafi na 223 da kuma ƙarin bayani da ke shafin don ku ga abubuwan da za su iya sa Kirista ya yi tunanin kai ɗan’uwansa ƙara a kotu.