Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Ku Rika Karfafa Juna

Ku Rika Karfafa Juna

“In kuna da wata maganar gargaɗi da za ku yi wa jama’a, ai, sai ku yi.”​—A. M. 13:15.

WAƘOƘI: 12145

1, 2. Me ya nuna cewa yana da muhimmanci mu riƙa ƙarfafa mutane?

WATA yarinya ‘yar shekara 18 mai suna Cristina ta ce: “Iyayena ba sa ƙarfafa ni sai dai su riƙa sūka na. Kalamansu suna da zafi sosai. Sun ce ba ni da wayo kuma ba zan taɓa canjawa ba, kuma wai ina da ƙiba sosai. Hakan yana sa ni kuka koyaushe kuma ba na so in riƙa magana da su. Ina ji kamar ba ni da amfani.” [1] Mutane ba za su ji daɗin rayuwa ba idan ba wanda yake ƙarfafa su!

2 Yana da muhimmanci mu riƙa ƙarfafa juna. Rubén ya ce: “Na yi shekaru da yawa ina ɗaukan kaina a matsayin wanda ba shi da amfani. Amma wata rana da na fita wa’azi tare da wani dattijo, sai ya lura cewa ba na farin ciki. Ya saurare ni da kyau sa’ad da nake bayyana masa abin da ke damu na. Bayan haka, sai ya gaya mini abubuwa masu kyau da nake yi kuma ya tuna mini abin da Yesu ya faɗa a cikin Littafi Mai Tsarki cewa mun fi tsuntsaye daraja sosai. A kowane lokaci ina tunawa da wannan nassin kuma yana taɓa zuciyata har yanzu. Kalaman wannan dattijon ya ƙarfafa ni sosai.”​—Mat. 10:31.

3. (a) Mene ne manzo Bulus ya ce game da ƙarfafa? (b) Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?

3 Ba abin mamaki ba ne da Littafi Mai Tsarki ya ce mu riƙa ƙarfafa juna. Manzo Bulus ya rubuta wa Kiristoci Ibraniyawa cewa: ‘Ku kula fa, ‘yan’uwa, kada wata muguwar zuciya marar gaskatawa ta wakana ga waninku, wadda za ta bauɗar da ku daga wurin Allah Rayayye. Sai dai kowace rana ku ƙarfafa wa juna zuciya . . . don kada kowannenku ya taurare, ta yaudarar zunubi.’ (Ibran. 3:​12, 13, Littafi Mai Tsarki) Idan ka tuna da ranar da wani ya ƙarfafa ka da kuma yadda ka ji bayan haka, hakan zai sa ka san cewa ƙarfafa tana da amfani sosai. Don haka, bari mu yi la’akari da waɗannan tambayoyin: Me ya sa ƙarfafa mutane take da muhimmanci? Mene ne za mu koya daga yadda Jehobah da Yesu da kuma Bulus suka ƙarfafa wasu? Ta yaya za mu ba da ƙarfafa a hanyar da ta dace?

DUKANMU MUNA BUKATAR ƘARFAFA

4. Su waye ne suke bukatar a yaba musu, amma me ya sa ba a yin hakan a yau?

4 Dukanmu muna bukatar ƙarfafa musamman ma sa’ad da muke girma. Wani malami mai suna Timothy Evans ya ce: “Kamar yadda shuke-shuke suke bukatar ruwa sosai, haka ma yara . . . suke bukatar a riƙa yaba musu. Idan aka yaba wa yaro, hakan yana sa shi farin ciki sosai.” Amma da yake muna rayuwa a kwanaki na ƙarshe, mutane ba sa nuna ƙauna, ba sa damuwa da juna, kuma saboda haka ba sa ƙarfafa juna. (2 Tim. 3:​1-5) Wasu iyaye ba sa yaba wa yaransu domin su ma iyayensu ba su yaba musu ba sa’ad da suke yara. Ma’aikata da yawa sun ce ba a yaba musu a wurin aikinsu.

5. Mene ne ƙarfafa mutane ya ƙunsa?

5 A yawancin lokaci ƙarfafa takan ƙunshi yaba wa mutum sa’ad da ya yi wani abu mai kyau. Muna iya ƙarfafa wasu ta wajen gaya musu cewa suna da halaye masu kyau ko kuma ta wurin gaya wa “masu-raunanan zukata” abin da zai sa su ƙarfin gwiwa. (1 Tas. 5:14) Asalin kalmar Helenanci da aka fassara zuwa “ƙarfafa” a Hausa tana nufin “ka gaya wa mutum ya zo ya tsaya kusa da kai ya tallafa maka kuma yi maka ta’aziyya” a Helenanci. Yayin da muke hidima tare da ‘yan’uwanmu, za mu sami damar ƙarfafa su. (Karanta Mai-Wa’azi 4:​9, 10.) Shin muna gaya wa ‘yan’uwanmu dalilin da ya sa muke ƙaunarsu a duk lokacin da muka sami damar yin hakan? Kafin mu amsa wannan tambayar, bari mu yi la’akari da wannan ƙarin maganar da ta ce: “Magana a kan kari, ina misalin kyaunta!”​—⁠Mis. 15:⁠23.

6. Mene ne Shaiɗan yake so mu yi? Ka ba da misali.

6 Shaiɗan yana so mu karaya don ya san cewa idan muka karaya, hakan zai iya sa ƙaunarmu ga Jehobah ta yi sanyi. Littafin Misalai 24:10 ta ce idan muka karaya a lokacin wahala, hakan zai sa ba za mu yi ƙarfi ba. Shaiɗan ya yi amfani da matsaloli da kuma zargi don ya sa Ayuba ya karaya, amma bai yi nasara ba. (Ayu. 2:3; 22:3; 27:5) Idan muna ƙarfafa iyalanmu da kuma ‘yan’uwanmu a cikin ikilisiya, za mu iya yaƙar Shaiɗan, kuma hakan zai sa mu kasance da farin ciki da kwanciyar rai a cikin iyalinmu da kuma ikilisiya.

MISALAI DAGA LITTAFI MAI TSARKI DA ZA MU IYA BI

7, 8. (a) Waɗanne misalai da ke cikin Littafi Mai Tsarki ne suka nuna cewa Jehobah ya ɗauki ba da ƙarfafa da muhimmanci sosai? (b) Ta yaya iyaye za su iya bin misalin Jehobah? (Ka duba hoton da ke shafi na 4.)

7 Jehobah. Wani marubucin zabura ya ce: ‘Ubangiji yana kusa da masu-karyayyar zuciya, yana ceton waɗanda suka yi [“sanyin gwiwa,” NW ].’ (Zab. 34:18) Sa’ad da Irmiya ya karaya, Jehobah ya ƙarfafa shi kuma ya ba shi ƙarfin zuciya. (Irm. 1:​6-10) Ka yi tunanin yadda annabi Daniyel ya ji sa’ad da Allah ya aika mala’ika don ya ƙarfafa shi. Mala’ikan ya kira Daniyel “mutum ƙaunatacce ƙwarai!” (Dan. 10:​8, 11, 18, 19) Hakazalika, kai ma za ka iya ƙarfafa masu shela da majagaba da ‘yan’uwa tsofaffi maza da mata da suka karaya.

8 Allah bai yi tunanin cewa tun da shi da Ɗansa sun yi shekaru da yawa suna aiki tare, ba ya bukatar ya ƙarfafa ko kuma ya yaba wa Yesu sa’ad da yake duniya ba. Maimakon haka, Jehobah ya yi magana sau biyu daga sama yana cewa: “Wannan Ɗana ne, ƙaunatacena, wanda raina na jin daɗinsa ƙwarai.” (Mat. 3:17; 17:⁠5) Ta hakan, Allah ya yaba wa Yesu kuma ya tabbatar masa cewa ya amince da abin da yake yi. Babu shakka, abin da Allah ya faɗa sa’ad da Yesu ya soma hidimarsa da kuma a ƙarshen hidimarsa a duniya ya ƙarfafa Yesu sosai. Ƙari ga haka, kafin mutuwar Yesu, Jehobah ya aika mala’ika ya ƙarfafa Yesu sa’ad da yake baƙin ciki. (Luk. 22:43) Iyaye, kuna bukatar ku bi misalin Jehobah ta wajen ƙarfafa yaranku a kai a kai da kuma yaba musu sa’ad da suka yi wani abu mai kyau. Kuna bukatar ku taimaka musu sa’ad da suke fuskantar matsaloli a makaranta.

9. Mene ne za mu koya daga yadda Yesu ya bi da manzanninsa?

9 Yesu. A daren da Yesu ya kafa taron tuna mutuwarsa, manzanninsa sun nuna girman kai. Cikin tawali’u, Yesu ya wanke ƙafafun manzanninsa. Duk da haka, sun ci gaba da yin jayyaya a kan wanda ya fi girma a cikinsu kuma Bitrus ya buga ƙirji cewa shi ba zai taɓa barin Yesu ba. (Luk. 22:​24, 33, 34) Amma Yesu ya yaba musu don sun kasance tare da shi har ma a lokacin da yake shan wahala. Ya gaya musu cewa za su yi aikin da ya fi na shi, kuma ya tabbatar musu da cewa Allah yana ƙaunarsu sosai. (Luk. 22:28; Yoh. 14:12; 16:27) Muna iya tambayar kanmu, ‘Maimakon in riƙa mai da hankali ga kurakuren yarana ko na wasu, ba zai fi kyau in bi misalin Yesu ta wajen yaba musu don abu mai kyau da suka yi?’

10, 11. Ta yaya manzo Bulus ya nuna cewa yana da muhimmanci ya ƙarfafa wasu?

10 Manzo Bulus. Bulus ya faɗi abubuwa masu kyau game da ‘yan’uwansa a cikin wasiƙunsa. Ya yi shekaru da yawa yana yin tafiya tare da su, don hakan ya san kasawarsu. Amma Bulus ya ambaci abubuwa masu kyau ne game da su. Alal misali, Bulus ya kwatanta Timotawus a matsayin “ɗansa cikin Ubangiji, ƙaunatacce, mai-aminci,” wanda zai iya kula da ‘yan’uwansa Kiristoci. (1 Kor. 4:17; Filib. 2:​19, 20) Manzon ya gaya wa ‘yan’uwa da ke koranti cewa Titus mutumin kirki ne. Ya ce: “Titus abokin tarayyana ne, da abokin aikina kuma zuwa gare ku.” (2 Kor. 8:23) Hakika, Timotawus da Titus za su yi farin ciki bayan sun ji abin da Bulus ya faɗa game da su!

11 Bulus da Barnaba sun koma wuraren da aka kusan kashe su don su ƙarfafa ‘yan’uwansu. Alal misali, duk da hamayyar da suka fuskanta a Listra, sun koma wurin don su ƙarfafa waɗanda ba su daɗe da zama Kiristoci ba. (A. M. 14:​19-22) Bayan haka, Bulus ya haɗu da wani taron jama’a da suke so su kashe shi a Afisus, amma ya zauna a wurin don ya ƙarfafa ‘yan’uwansa. Littafin Ayyukan Manzanni 20:​1, 2 sun ce: “Bayan hargowan . . . ta kwanta, Bulus ya kira masu bi, bayan ya ƙarfafa musu zuciya, ya yi ban kwana da su, ya tafi ƙasar Makidoniya. Da ya zazzaga lardin nan, ya kuma ƙarfafa musu zuciya ƙwarai, ya zo ƙasar Hellas.” (LMT) Bulus yana son ya ƙarfafa mutane sosai, kuma hakan yana da muhimmanci a gare shi.

KU RIƘA ƘARFAFA JUNA

12. Me ya sa yake da kyau mu riƙa halartan taro?

12 Wani dalilin da ya sa Ubanmu na sama ya ce mu riƙa halartan taro a kai a kai shi ne don mu riƙa ƙarfafa juna a wajen. (Karanta Ibraniyawa 10:​24, 25.) Kamar yadda mabiyan Yesu suka yi a ƙarni na farko, mu ma muna yin taro don mu koyi abubuwa game da Allah kuma mu ƙarfafa juna. (1 Kor. 14:31) Cristina, wadda aka ambata ɗazu ta ce: “Ina son zuwa taro domin yadda muke ƙauna da kuma ƙarfafa juna a wurin. Wasu lokuta nakan halarci taro ina baƙin ciki. Amma sa’ad da nake wurin, ‘yan’uwa mata suna zuwa wurina, su rungume ni kuma su ce na yi kyau sosai. Suna gaya mini cewa suna ƙaunata kuma suna farin ciki da yadda nake samun ci gaba a ibada ta ga Jehobah. Kalamansu suna sa ni farin ciki sosai!” Abin farin ciki ne idan dukanmu muna “ƙarfafa juna!”​—Rom. 1:​11, 12, LMT.

13. Me ya sa waɗanda suka daɗe suna bauta wa Jehobah suke bukatar ƙarfafa?

13 Ko waɗanda suka daɗe suna bauta wa Jehobah ma suna bukatar a ƙarfafa su. Ka yi la’akari da misalin Joshua. Ya yi shekaru da yawa yana bauta wa Allah. Duk da haka, Jehobah ya gaya wa Musa cewa ya ƙarfafa shi kuma ya ce: “Ka umurci Joshua, ka ba shi zuciya, ka ƙarfafa shi: gama shi za ya ƙetare a gaban wannan jama’a, za shi kuwa gadar masu ƙasan wadda za ka gani.” (K. Sha. 3:​27, 28) Joshua ne zai yi wa mutanen Isra’ila ja-gora zuwa Ƙasar Alkawari. Hakan babban aiki ne kuma zai fuskanci matsaloli. Ban da haka ma, zai yi yaƙi da mutane da yawa kuma a wani lokaci an ci nasara a kansa. (Josh. 7:​1-9) Babu shakka, Joshua yana bukatar ƙarfafa sosai! Hakazalika, mu ma muna bukatar mu ƙarfafa dattawan ikilisiya har da masu kula da da’ira don suna aiki tuƙuru a madadin mu. (Karanta 1 Tasalonikawa 5:​12, 13.) Wani mai kula da da’ira ya ce: “A wasu lokuta, ‘yan’uwa suna ba mu katin gaisuwa don su nuna mana cewa sun ji daɗin ziyarar da muka yi musu. Muna ajiye waɗannan katunan kuma muna karanta su sa’ad da muka soma sanyin gwiwa. Waɗannan abubuwan suna ƙarfafa mu sosai.”

Yaranmu za su yi farin ciki idan muka yaba musu (Ka duba sakin layi na 14)

14. Waɗanne misalai ne suka nuna cewa zai yi wa mutum sauƙi ya karɓi gyara idan aka yabe shi da kuma ƙarfafa shi?

14 Dattawa da kuma iyaye sun lura cewa ƙarfafa da yaba wa wasu yana taimaka musu su bi ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki. Sa’ad da Bulus ya yaba wa Kiristocin da ke Korinti don sun bi shawarar da ya ba su, hakan ya ƙara motsa su su yi abin da ya dace. (2 Kor. 7:​8-11) Andreas wanda yake da yara biyu ya ce: “Ƙarfafa yara tana taimaka musu su kusaci Allah kuma su manyanta. Bayan ka ba su shawara, sai ka ƙarfafa su. Ko da yake yaranmu sun san abin da ya dace, ƙarfafawar da muke yi musu tana taimaka musu su riƙa yin abin da ya dace a koyaushe.”

YADDA ZA A BA DA ƘARFAFA A HANYAR DA TA DACE

15. A wace hanya ce za mu iya ƙarfafa wasu?

15 Ku riƙa yaba wa ‘yan’uwanku don aikin da suke yi da kuma halayensu masu kyau. (2 Laba. 16:9; Ayu. 1:⁠8) Ko da yake ƙarfinmu ba ɗaya ba ne, Jehobah da Yesu suna farin ciki da abubuwan da kowannenmu yake yi a ƙungiyarsa. (Karanta Luka 21:​1-4; 2 Korintiyawa 8:12) Alal misali, wasu ‘yan’uwanmu tsofaffi suna fama sosai kafin su iya halartan taro ko kuma fita wa’azi a kai a kai. Zai dace mu riƙa ƙarfafa da kuma yaba wa waɗannan ‘yan’uwan.

16. Me ya sa bai kamata mu yi shiru sa’ad da muka sami damar ƙarfafa wasu ba?

16 Ku nemi damar ƙarfafa wasu. Idan wani ɗan’uwa ya yi abin da ya dace, kada mu yi shiru amma mu yaba masa nan da nan. Ku yi la’akari da abin da ya faru sa’ad da Bulus da Barnaba suka je Antakiya ta Bisidiya. Shugaban majami’ar ya gaya musu cewa: “ ’Yan’uwa, idan kuna da wata maganar gargaɗi domin jama’a, sai ku faɗi.” Sai Bulus ya yi amfani da wannan damar ya ƙarfafa su. (A. M. 13:​13-16, 42-44) Don haka, kada mu yi shiru idan muka sami damar ƙarfafa wasu. Mutane za su ƙarfafa mu idan mu ma muna ƙarfafa su.​—⁠Luk. 6:⁠38.

17. Mene ne zai sa ƙarfafar da muke yi ta ratsa zuciya sosai?

17 Ku faɗi gaskiya da kuma ainihin dalilin da ya sa kuke yaba musu. Yana da kyau a ƙarfafa da kuma yaba wa mutane. Amma yadda Yesu ya yaba wa Kiristocin da ke Tiyatira ya nuna cewa ya fi dacewa mu ambaci ainihin dalilin da ya sa muke yaba musu. (Karanta Ru’ya ta Yohanna 2:​18, 19.) Alal misali, iyaye suna iya yaba wa yaransu don ci gaban da suke samu a bautarsu ga Jehobah. Za mu iya gaya wa wata mahaifiya da take renon yaranta ita kaɗai cewa muna jin daɗin yadda take renon yaranta duk da matsalolin da take fuskanta. Irin wannan ƙarfafawar zai iya taimaka wa mutane sosai!

18, 19. Ta yaya za mu iya taimaka wa ‘yan’uwanmu?

18 Jehobah ba zai gaya mana cewa mu je mu ƙarfafa wani kamar yadda ya gaya wa Musa ya ƙarfafa Joshua ba. Amma Allah zai yi farin ciki idan muka ƙarfafa ‘yan’uwanmu. (Mis. 19:17; Ibran. 12:12) Alal misali, za mu iya gaya wa wani da ya ba da jawabi cewa mun ji daɗin darasin da muka koya daga jawabinsa ko kuma mun fahimci wani nassi daga jawabin da ya bayar. Wata ‘yar’uwa ta rubuta wa wani baƙo mai jawabi cewa: “Ko da yake mun yi magana na ‘yan mintoci ne kawai, amma kamar ka ga zuciyata kuma ka ƙarfafa ni da kalamanka. Ina so ka san cewa yadda ka yi magana a hanya mai daɗi sa’ad da kake jawabi da kuma sa’ad da muke tattaunawa da kai, na ji kamar Jehobah ne ya ba ni kyauta.”

19 Idan muka bi shawarar da Bulus ya bayar, za mu iya taimaka wa wasu su ƙarfafa dangantakarsu da Jehobah. Bulus ya ce: “Ku ƙarfafa wa juna zuciya, ku riƙa inganta juna, kamar dai yadda kuke yi.” (1 Tas. 5:​11, LMT) Dukanmu za mu faranta wa Jehobah rai idan muka ci gaba da “ƙarfafa juna” kowace rana.

^ [1] (sakin layi na 1) An canja sunayen.