Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Wata Kalma da Take Ratsa Zuciya!

Wata Kalma da Take Ratsa Zuciya!

YESU yakan yi amfani da kalmar nan “mace” a wasu lokatai sa’ad da yake yi wa mata magana. Alal misali, a lokacin da yake warkar da wata mata da ta yi shekara 18 a tanƙware, Yesu ya ce: “Mace, an sake ki daga kumamancinki.” (Luk. 13:​10-13) Yesu ya yi amfani da wannan kalmar da ake yin amfani da ita a zamaninsa sa’ad da yake yi wa mahaifiyarsa magana, kuma a lokacin wannan kalma ce da ake amfani da ita idan ana so a daraja mutum. (Yoh. 19:26; 20:13) Amma akwai wata kalmar da ta fi wannan daraja mutum.

An yi amfani da wata kalma da ke daraja mutum a cikin Littafi Mai Tsarki sa’ad da ake magana game da wasu mata. Yesu ya yi amfani da wannan kalmar sa’ad da yake magana da wata mata da ta yi shekara goma sha biyu tana zubar da jini. Dokar da Allah ya ba da ta hannun Musa ta hana mutumin da yake cikin irin yanayinta zuwa kusa da mutane, amma matar ta karya wannan Dokar sa’ad da ta zo wurin Yesu. (Lev. 15:​19-27) Amma tana bukatar taimako, saboda “ta sha wahala da yawa kuwa ga hannuwan masu-magani da yawa, ta ɓatar da dukan abin da ke wurinta, ba ta amfana komi ba, amma cuta ta riƙa daɗuwa.”​—Mar. 5:​25, 26.

Ta shiga cikin mutane a hankali, kuma ta zo ta bayan Yesu ta taɓa bakin rigarsa. Nan da nan ta daina zubar da jini! Matar tana gani ba zai sani ba, amma sai Yesu ya yi tambaya: “Wane ne ya taɓa ni?” (Luk. 8:​45-47) Da ta ga hakan sai ta tsorata tana rawan jiki kuma “ta faɗa masa gaskiya duka.”​—Mar. 5:33.

Saboda Yesu yana so ya kwantar mata da hankali, sai ya ce mata: “Ɗiya, ki yi farinciki.” (Mat. 9:22) Masanan Littafi Mai Tsarki sun ce, ana iya amfani da kalmar Ibrananci da na Hellenanci da take nufin “ɗiya” don a nuna “tausayi da kuma ƙauna.” Don ta kasance da tabbaci, Yesu ya sake ce mata: “Bangaskiyarki ta warkar da ke; ki tafi lafiya, ki rabu da azabarki.”​—Mar. 5:34.

Boaz wani Baisra’ile mai kuɗi ya kira uth ‘yar Moab “Ɗiyata.” Ita ma tana shakkar yin kālar hatsi a gonar mutumin da ba ta sani ba. Amma Boaz ya ce mata, ‘ki ji ɗiyata,’ sai ya gaya mata cewa ta ci gaba da yin kāla a gonarsa. Ruth ta rusuna da fuskarta har ƙasa, ta tambaye shi mai ya sa yake nuna mata alheri a matsayinta na baƙuwa. Boaz ya amsa tambayarta kuma ya ƙarfafa ta, ya ce: “An bayyana mini sarai dukan abin da kika yi wa surukuwarki [Na’omi gwauruwa] . . . Ubangiji ya sāka miki aikinki.”​—Ruth 2:​8-12.

Yesu da Boaz sun kafa wa dattawan ikilisiyar Kirista misali mai kyau. A wasu lokuta dattawa biyu suna iya yin amfani da Littafi Mai Tsarki don su ƙarfafa wata ‘yar’uwa da take bukatar taimako. Bayan sun yi addu’a ga Jehobah ya yi musu ja-gora kuma sun saurari abin da ‘yar’uwar ta faɗa, hakan zai ba su damar yin amfani da Kalmar Allah su ƙarfafa ta.​—Rom. 15:4.