Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Ka Guji Tunanin Mutanen Duniya

Ka Guji Tunanin Mutanen Duniya

“Ku yi hankali kada kowa ya cuce ku ta wurin iliminsa da ruɗinsa na banza . . . na duniya.”​—KOL. 2:8.

WAƘOƘI: 38, 31

1. Wane gargaɗi ne manzo Bulus ya yi wa ’yan’uwansa masu bi? (Ka duba hoton da ke shafin nan.)

MANZO BULUS ya rubuta wa Kiristoci da ke Kolossi wasiƙa sa’ad da yake fursuna a Roma a misalin shekara 60 zuwa 61 bayan haihuwar Yesu. Ya ambata muhimmancin samun “fahimta na ruhu.” (Kol. 1:​9, Littafi Mai Tsarki) Bulus ya ƙara cewa: “Wannan nake faɗi, domin kada kowa ya ruɗe ku da magana mai-rinjayarwa. Ku yi hankali kada kowa ya cuce ku ta wurin iliminsa da ruɗinsa na banza, bisa ga ta’adar mutane, bisa ga rukunai na duniya, ba bisa ga Kristi ba.” (Kol. 2:​4, 8) Sai Bulus ya ci gaba da bayyana dalilin da ya sa wasu ra’ayoyi ba su dace ba da kuma abin da ya sa mutane da yawa suke son su. Alal misali, waɗannan ra’ayoyin suna iya sa mutane su ga suna da hikima kuma sun fi wasu. Saboda haka, Bulus ya rubuta wasiƙar don ya taimaka wa ’yan’uwa su ƙi tunanin mutanen duniya da ayyukan banza.​—Kol. 2:​16, 17, 23.

2. Me ya sa za mu bincika wasu ra’ayoyin mutanen duniya?

2 Tunanin mutanen duniya zai iya sa mutum ya ƙi bin ƙa’idodin Jehobah, kuma hakan a hankali yana zai iya sa mutumin ya daina kasancewa da bangaskiya ga Allah. Dukanmu muna ji ko ganin ra’ayin mutanen duniya a talabijin ko intane ko a wurin aiki ko kuma a makaranta. A wannan talifin, za mu bincika abin da za mu yi don mu guji irin wannan tunanin da zai ɓata zuciyarmu. Ƙari ga haka, za mu tattauna misalai biyar na ra’ayin mutanen duniya da kuma yadda za mu guje su.

ZAI DACE NE MU GASKATA DA ALLAH?

3. Wane ra’ayi ne mutane da yawa suke so, kuma me ya sa?

3 “Zan iya zama mutumin kirki ba tare da yin imani ga Allah ba.” A ƙasashe da yawa, mutane da yawa suna da wannan ra’ayin. Wataƙila mutanen da suke da irin wannan ra’ayin ba su yi tunani sosai ko Allah yana wanzuwa ba amma mai yiwuwa suna jin daɗin ’yanci da suke da shi na yin duk abin da suka ga dama. (Karanta Zabura 10:4.) Wasu kuma suna ganin suna da basira sosai idan suka ce: “Zan iya kasancewa da hali mai kyau ba tare da yin imani ga Allah ba.”

4. Ta yaya za mu iya tattauna da wanda yake da’awa cewa babu Mahalicci?

4 Zai dace ne mutum ya gaskata cewa babu mahalicci? Wasu mutane sukan rikice sa’ad da suka nemi amsoshi daga kimiyya. Amma amsar ba ta da wuya. Idan har gida yana da magini, babu shakka wani ne ya halicci abubuwa masu rai! Har abubuwa masu rai mafi ƙanƙanta suna iya haifan irinsu, amma gida ba zai taɓa iya gina kansa ba. Hakan yana nufin cewa ƙwayoyin rai suna iya riƙe wani bayani kuma su sanar wa sababbin ƙwayoyin rai don su ma su haifi irinsu. Wane ne yake sa waɗannan ƙwayoyin rai su riƙa yin waɗannan abubuwa? Littafi Mai Tsarki ya ba da amsar: “Kowane gida akwai mai-kafa shi; amma wanda ya kafa dukan abu Allah ne.”​—Ibran. 3:4.

5. Ta yaya za mu tattauna da mutum da yake da ra’ayin cewa muna iya sanin abin da ya dace ba tare da gaskata da Allah ba?

5 Ta yaya za mu tattauna da mutum da yake da ra’ayin cewa mutum zai iya sanin abin da yake da kyau ba tare da gaskata da Allah ba? Kalmar Allah ta ce waɗanda ba su yi imani da Allah ba suna da wasu halaye masu kyau. (Rom. 2:​14, 15) Alal misali, suna iya daraja iyayensu kuma su riƙa ƙaunarsu. Amma, idan mutum ba ya bin ƙa’idodin Jehobah, yana iya tsai da shawarwarin da ba su dace ba. (Isha. 33:22) Mutane da yawa masu basira sun tabbata cewa muna bukatar taimakon Allah don a magance mugun matsaloli da ake fuskanta a duniya a yau. (Karanta Irmiya 10:23.) Saboda haka, bai kamata mu riƙa tunani cewa za mu iya sanin abin da ya dace ba tare da gaskata da Allah da kuma bin ƙa’idodinsa ba.​—Zab. 146:3.

WAJIBI NE MU BI WANI ADDINI?

6. Yaya mutane da yawa suke ji game da addini?

6 “Za ka yi farin ciki ba tare da bin wani addini ba.” Mutane da yawa suna da wannan ra’ayin ne domin bin addini ba ya faranta musu rai kuma a ganinsu hakan ba shi da amfani. Wasu kuma sun juya wa addini baya domin ana koya musu cewa Allah zai ƙona mutane a cikin wuta, kuma addinan suna tilasta wa mutane su ba da zakka kuma su goyi bayan ’yan siyasa. Shi ya sa mutane suna cewa za su iya yin farin ciki ba tare da bin wani addini ba! Irin waɗannan mutane sukan ce, “Ina son yin ibada ga Allah, amma ba na son in bi wani addini.”

7. Ta yaya bauta ta gaskiya take sa mutum ya yi farin ciki?

7 Da gaske ne cewa mutum zai yi farin ciki ba tare da bin wani addini ba? Hakika, mutum zai yi farin ciki idan bai bi addinin ƙarya ba, amma mutum ba zai yi farin ciki ba idan bai ƙulla dangantaka da Jehobah ba, domin shi mai farin ciki ne. (1 Tim. 1:11) Kome da Allah yake yi yana taimaka ma wasu. Bayinsa suna farin ciki domin suna taimaka ma wasu. (A. M. 20:35) Alal misali, ka yi la’akari da yadda bauta ta gaskiya take taimaka wa iyalai su riƙa farin ciki. Kuma ma’aurata sun koya su riƙa daraja juna kuma su kasance da aminci ga juna. Ban da haka ma, za mu guji yin zina kuma mu koyar da yaranmu su riƙa daraja mutane kuma muna ƙaunar juna a cikin iyali. Saboda haka, bauta ta gaskiya tana sa mutane su kasance da haɗin kai da salama a cikin ikilisiyoyi da ke faɗin duniya.​—Karanta Ishaya 65:​13, 14.

8. Ta yaya Matta 5:3 ta taimaka mana mu fahimci abin da ke sa mutane farin ciki?

8 Da gaske ne cewa mutum zai yi farin ciki ba tare da bauta wa Allah ba? Ka yi tunanin wannan tambayar, Me ke sa mutane farin ciki? Wasu suna jin daɗin sana’arsu ko wasanni ko kuma wani abu da suke son yi. Wasu kuma suna farin cikin kula da iyalinsu da abokansu. Dukan waɗannan abubuwa suna iya sa mutum farin ciki, amma da akwai abubuwa da suka fi muhimmanci a rayuwa da za su sa mu yi farin ciki na dindindin. Ba kamar dabobbi ba, za mu iya koya game da Mahaliccinmu kuma mu bauta masa da aminci. Don ya halicce mu yadda za mu yi farin ciki idan muna bauta masa. “Masu albarka [“farin ciki,” NW ] ne masu ladabi a ruhu, gama mulkin sama nasu ne.” (Mat 5:3) Alal misali, muna farin ciki da kuma samun ƙarfafa idan muka halarci taro tare da ’yan’uwanmu don mu bauta wa Jehobah. (Zab. 133:1) Ƙari ga haka, muna farin cikin kasancewa cikin ’yan’uwanmu da ke faɗin duniya, muna rayuwa mai kyau da kuma kasancewa da bege don nan gaba.

MUNA BUKATA MU BI WASU ƘA’IDODI GAME DA ƊABI’A NE?

9. (a) Wane ra’ayi game da jima’i ne ya zama ruwan dare a duniya? (b) Me ya sa aka hana mutum yin jima’i da wadda ba matarsa ba?

9 “Me ya sa aka hana mutum ya yi jima’i da wadda ba matarsa ba?” Mutane suna iya gaya mana: “Ya kamata mutum ya ji daɗin rayuwarsa. Me zai sa a hana mutum ya yi jima’i da wadda ba matarsa ba?” Shawarar nan cewa kada Kirista ya yi lalata ya dace. Me ya sa? Domin Kalmar Allah ta ce kada a yi hakan. * (Karanta 1 Tasalonikawa 4:​3-8.) Jehobah yana da ikon kafa mana dokoki domin shi ne ya halicce mu. Ya ce mata da miji ne kawai za su yi jima’i da juna. Allah ya ba mu dokoki domin yana ƙaunarmu, kuma za mu amfana idan muka bi su. Ƙari ga haka, iyalai da suke bin dokokin Allah za su riƙa ƙauna da kuma daraja juna. Ban da haka, za su kasance da kwanciyar rai. Allah zai hukunta waɗanda suka san dokokinsa kuma suka ƙi bin su da gangan.​—Ibran. 13:4.

10. Ta yaya Kirista zai guji lalata?

10 Kalmar Allah ta umurce mu kada mu yi lalata. Hanya mai muhimmanci da za mu yi hakan ita ce ta wurin guje wa kallon abubuwan da ba su dace ba. Yesu ya ce: “Dukan wanda ya dubi mace har ya yi sha’awarta, ya rigaya ya yi zina da ita cikin zuciyarsa. Kuma idan idonka na dama yana sa ka yi tuntuɓe, ka cire shi, ka yar.” (Mat. 5:​28, 29) Saboda haka, Kirista zai guji kallon batsa ko kuma sauraron kaɗe-kaɗe da ake kalmomin lalata. Manzo Bulus ya gaya wa ’yan’uwansa Kiristoci cewa: “Ku matar da gaɓaɓuwanku fa waɗanda ke a duniya; fasikanci.” (Kol. 3:5) Ƙari ga haka, ya kamata mu guji maganganu da tunanin banza.​—Afis. 5:​3-5.

ZAI DACE NE MU BI RA’AYIN DUNIYA GAME DA AIKI?

11. Mene ne zai iya sa mu tattara hankalinmu ga neman aiki mai kyau kawai?

11 “Yin aiki mai kyau zai sa ka farin ciki.” Mutane da yawa suna iya gaya mana mu mai da hankalinmu ga neman aiki mai kyau kawai, musamman wanda zai sa mu yi suna ko mu zama masu iko ko kuma masu arziki. Tun da yake mutane da yawa suna ganin yin aiki mai kyau ne zai sa su farin ciki, Kiristoci suna iya soma bin irin wannan ra’ayin.

12. Shin aiki mai kyau ne zai sa mutum farin ciki?

12 Da gaske ne cewa yin aiki mai kyau da zai sa mu zama masu iko ko mu yi suna ne zai sa mu yi farin ciki? A’a. Ka tuna cewa Shaiɗan yana so ya zama mai iko da kuma sananne. Babu shakka, ya yi nasara amma waɗannan abubuwan ba su sa shi farin ciki ba. (Mat. 4:​8, 9; R. Yoh. 12:12) Akasin haka, ka yi tunanin yadda muke farin ciki sa’ad da muke taimaka wa mutane su koya game da Allah da kuma abubuwa masu kyau da ya yi alkawari zai yi a nan gaba. Babu sana’a ko aikin da zai sa mu yi irin wannan farin ciki. Ƙari ga haka, don mutane su samu sana’a ko aiki sukan yi gasa da fushi ko kuma kishin wasu. Amma, har ila ba sa yin farin ciki. Littafi Mai Tsarki ya ce suna “cin iska kawai.”​—M. Wa. 4:4.

13. (a) Yaya ya kamata mu ɗauki aikinmu? (b) Bisa ga wasiƙar da Bulus ya rubuta wa Tasalonikawa, me ya sa shi farin ciki sosai?

13 Hakika, ba laifi ba ne mu yi aiki mai kyau da zai taimaka mana mu biya bukatunmu. Amma bai kamata aikinmu ya fi muhimmanci a rayuwarmu ba. Yesu ya ce: “Ba wanda ke da iko shi bauta wa ubangiji biyu: gama ko shi ƙi ɗayan, shi ƙaunaci ɗayan: ko kuwa shi lizimci ɗayan, shi rena ɗayan. Ba ku da iko ku bauta wa Allah da dukiya ba.” (Mat. 6:24) Za mu yi farin ciki sosai idan muka mai da hankali ga bauta wa Jehobah da kuma koya wa mutane game da Kalmarsa. Manzo Bulus ya shaida hakan, don sa’ad da yake matashi ya mai da hankali ga yin aiki mai kyau, amma ya fi farin ciki sa’ad da ya zama mai wa’azi kuma ya ga yadda Kalmar Allah ta gyara rayuwar mutane da yake musu wa’azi. (Karanta 1 Tasalonikawa 2:​13, 19, 20.) Don haka, babu aiki a duniya da zai sa mu farin ciki kamar bauta wa Jehobah da kuma koya ma wasu game da shi.

Za mu yi farin ciki sosai idan muka taimaka wa mutane su fahimci Kalmar Allah (Ka dubi sakin layi na 12, 13)

ZA MU IYA MAGANCE MATSALOLIN ’YAN ADAM NE?

14. Me ya sa wasu za su iya son ra’ayin nan cewa mutane za su iya magance matsalolinsu?

14 “ ’Yan Adam za su iya magance matsalolinsu da kansu.” Mutane da yawa suna son wannan ra’ayin. Me ya sa? Don idan gaskiya ne, ba sa bukatar ja-gorancin Allah kuma za su iya yin duk abin da suka ga dama. Ban da haka ma, mutane suna iya tunani cewa da gaske ’yan Adam za su iya magance matsalolinsu don wani bincike ya nuna cewa yaƙi da mugunta da cututtuka da kuma talauci suna raguwa. A wani rahoto da aka ba da, an ce: “Abin da ya sa duniya take yin kyau shi ne don ’yan Adam sun tsai da shawara su gyara ta.” Irin wannan furuci ya nuna cewa mutane sun soma sanin yadda za su magance matsalolin duniya? Bari mu bincika waɗannan matsalolin sosai.

15. Me ya nuna cewa matsalolin ’yan Adam suna ƙaruwa sosai a duniya?

15 Yaƙi: Yaƙoƙi guda biyu da aka yi a duniya sun kwashi rayukan mutane fiye da miliyan 60. Tun daga Yaƙin Duniya na Biyu, mutane ba su daina yin yaƙi ba. A shekara ta 2015, yaƙi ko tsanantawa sun sa mutane miliyan 65 su bar gidajensu. Bincike ya nuna cewa a shekara 2015 kawai, mutane wajen miliyan goma sha biyu da dubu ɗari huɗu ne suka rasa gidajensu. Aikata laifi: Ko da yake an daina yin wasu laifuffuka a wasu wurare, amma aikata laifi ta kwamfuta ko intane da faɗa tsakanin ma’aurata da kuma ta’addanci suna ƙaruwa sosai. Ban da haka ma, mutane sun san cewa cin hanci da rashawa na ci gaba sosai. Don haka, mutane ba za su iya kawar da aikata laifi ba. Cututtuka: Da gaske ana iya warkar da wasu cututtuka, amma a shekara ta 2013, wani rahoto ya nuna cewa a kowace shekara mutane miliyan tara da ba su kai shekara 60 ba suna mutuwa sanaddiyar ciwon zuciya da shanyewar jiki da kansa da kuma ciwon sukari. Talauci: Bankin duniya ta ba da rahoto cewa, adadin mutanen da suke fama da talauci a Afirka ya ƙaru daga miliyan 280 a shekara ta 1990 zuwa miliyan 330 a shekara ta 2012.

16. (a) Me ya sa Mulkin Allah ne kawai zai kawar da matsalolin ’yan Adam? (b) Wane annabci ne Ishaya da marubucin Zabura suka yi game da yadda Allah zai albarkaci mutane?

16 Mutane masu son kai ne suke iko da ƙungiyoyin tattalin arziki da kuma na siyasa. Kuma waɗannan mutanen ba za su iya magance matsalar yaƙi da aikata laifi da cututtuka da talauci ba, Mulkin Allah ne kaɗai zai iya yin hakan. Bari mu bincika abin da Mulkin Allah zai yi wa mutane. Yaƙi: Mulkin Allah ne zai kawar da abubuwan da yaƙi ya jawo kamar su son kai da rashawa da nuna bambanci da addinin ƙarya da kuma Shaiɗan da kansa. (Zab. 46:​8, 9) Aikata laifi: Mulkin Allah yana koya wa miliyoyin mutane su riƙa ƙaunar juna kuma su amince da juna, amma ba wata gwamnatin ’yan Adam da zai yi hakan. (Isha. 11:9) Cututtuka: Jehobah zai albarkaci mutanensa da koshin lafiya. (Isha. 35:​5, 6) Talauci: Jehobah zai kawar da talauci kuma ya sa bayinsa su yi farin ciki. Ban da haka ma, zai sa su kasance da dangantaka mai kyau da shi domin wannan shi ne abu mafi muhimmanci.​—Zab. 72:​12, 13.

“KU SANI YADDA ZA KU AMSA TAMBAYAR KOWA”

17. Ta yaya za mu guji ra’ayin duniya?

17 Idan ka ji wani ra’ayin duniya game da wani batu da yake son ya shafi bangaskiyarka, ka nazarta Kalmar Allah kuma ka nemi shawara daga wani da ya manyanta. Ƙari ga haka, ka yi ƙoƙari ka san dalilin da ya sa mutane suke son ra’ayin da dalilin da ya sa ra’ayin bai dace ba da kuma yadda za mu guje wa ra’ayin. Babu shakka, dukanmu za mu iya guje ma wannan ra’ayin idan muka bi shawarar da manzo Bulus ya ba wa ’yan’uwa da ke ikilisiyar Kolosi cewa: “Ku yi tafiya cikin hikima wajen waɗanda ke waje . . . domin ku sani yadda za ku amsa tambayar kowa.”​—Kol. 4:​5, 6.

^ sakin layi na 9 Mutane sun ce abin da ke Yohanna 7:53–8:11 yana nufin cewa kamiltaccen mutum ne kawai zai iya kama wani da laifin yin zina. Amma ba su san cewa waɗannan ayoyin ba sa cikin Littafi Mai Tsarki na asali ba. Wannan dalilin ne ya sa aka cire waɗannan ayoyin a cikin sabuwar fassarar New World Translation na Turanci.