Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Ka Yi Koyi da Yadda Jehobah Yake Nuna Adalci da Jin Kai

Ka Yi Koyi da Yadda Jehobah Yake Nuna Adalci da Jin Kai

“Ku hukunta shari’a ta gaskiya, ku nuna jin ƙai da juyayi.”​—ZAK. 7:9.

WAƘOƘI: 125, 88

1, 2. (a) Yaya Yesu ya ɗauki Dokar Allah? (b) Ta yaya malamai da Farisawa suka ɓata Dokar Allah?

YESU ya so dokar da aka bayar ta hannun Musa. Me ya sa? Don ya san cewa Ubansa Jehobah wanda yake ƙauna sosai ne ya kafa wannan dokar. An nuna yadda Yesu yake ƙaunar dokar Allah a annabcin da ke Zabura 40:8 cewa: “Murna nake yi in yi nufinka, ya Allahna, hakika, shari’arka tana cikin zuciyata.” Abubuwan da Yesu ya faɗa da kuma yi sun nuna cewa Dokar Allah ba ta da illa kuma tana da amfani. Ban da haka ma, ba wani abin da zai hana ta cikawa.​—Mat. 5:​17-19.

2 Yesu ya yi baƙin ciki sosai a lokacin da ya ga malamai da Farisawa suke taka dokar Allah. Sun mai da hankali ga bin wasu dokoki da ba su da muhimmanci, shi ya sa Yesu ya ce: “Kukan fitar da zakar na’ana’a, da anise, da lafsur.” To mene ne matsalarsu? Ya ƙara da cewa: “Amma kun yar da muhimman jigajigan Attuara, wato gaskiya, da jin ƙai, da aminci.” (Mat. 23:​23, Littafi Mai Tsarki) Halin Yesu ya yi dabam da Farisawa masu gani su masu adalci ne. A maimakon haka, Yesu ya fahimci dokar da kyau da kuma yadda dokar ta nuna halayen Allah.

3. Me za mu bincika a wannan talifin?

3 Kiristoci a yau ba sa bin Dokar alkawari. (Rom. 7:6) Duk da haka, Jehobah yana son mu san Dokar shi ya sa ya hure mutane su rubuta a Kalmarsa, Littafi Mai Tsarki. Ba ya son mu bi kowane abu da Dokar ta faɗa, amma mu fahimci “muhimman jigajigan,” wato, darussa da za mu koya daga dokar. Alal misali, waɗanne darussa muka koya daga biranen mafaka da aka yi tanadinsu? A talifin da ya gabata, mun koya darussan daga matakan da mai gudun hijiran yake ɗaukawa. Ban da haka ma, mun koyi darussa daga tanadin da Jehobah ya yi na biranen mafaka da yadda za mu yi koyi da halayensa. Amma a wannan talifin, za mu bincika amsoshin waɗannan tambayoyi uku: Ta yaya tanadin biranen mafaka suka nuna cewa Jehobah mai jin ƙai ne? Me suka koya mana a kan ra’ayin Jehobah game da rai? Ta yaya suka nuna cewa shi mai yin adalci ne? A kowace tambaya da za mu tattauna, ya kamata dukanmu mu mai da hankali ga darussan da za mu koya daga Ubanmu, Jehobah.​—Karanta Afisawa 5:1.

BIRANEN SUN NUNA CEWA JEHOBAH MAI JIN ƘAI NE

4, 5. (a) Ta yaya biranen mafaka suke da sauƙin zuwa ko shiga, kuma me ya sa? (b) Mene ne wannan tanadin yake koya mana game da Jehobah?

4 Mutane suna iya zuwa ko shiga biranen mafaka guda shida ɗin babu matsala. Jehobah ya ba Isra’ilawa doka cewa su raba biranen a kowane gefen Kogin Urdun. Me ya sa? Don duk wanda ya kashe wani ba da saninsa ba ya shiga birnin babu ɓata lokaci kuma ya zauna hankali kwance. (Lit. Lis. 35:​11-14) An gyara hanyoyin shiga biranen mafakan da kyau. (K. Sha. 19:3) Bisa al’adar Yahudawa, an saka alamu don su ja-goranci masu gudu zuwa waɗannan biranen. Da yake an yi tanadin biranen mafaka, wanda ya kashe wani da kuskure ba zai gudu zuwa wata ƙasa ba don wataƙila hakan zai iya sa ya soma bauta ma wasu alloli.

5 Ka yi la’akari da wannan: Jehobah ne ya ba da doka cewa a riƙa hukunta waɗanda suka kashe wasu da gangan. Amma ya ce za a iya nuna ma waɗanda ba su yi hakan da gangan ba jin ƙai kuma a kāre su. Wani masani ya ce: “Wannan tsarin da aka kafa bai da wuya. Haka Allah yake nuna alherinsa.” Jehobah ba marar tausayi ba ne wanda yake son ya riƙa yi wa bayinsa horo. A maimakon haka, shi mai “jin ƙai” ne sosai.​—Afis. 2:4.

6. Shin Farisawa suna nuna jin ƙai kamar Allah? Ka bayyana.

6 Amma Farisawa ba sa jin tausayin mutane. Alal misali, sun ce idan mutum ya yi maka laifi har sau uku a kan abu ɗaya, bai kamata ka gafarta masa ba. Shi ya sa Yesu ya nuna halinsu a kwatanci na wani Bafarisi da yake addu’a cewa: “Ya Allah, na gode maka ba kamar sauran mutane ni ke ba, azalumai, marasa-adalci, mazinata, ko irin wannan mai-karɓan haraji.” Me ya sa Farisawa ba sa nuna jin ƙai? Littafi Mai Tsarki ya ce don sun “mai da sauran mutane wofi.”​—Luk. 18:​9-14.

Kana gafarta wa mutane ne idan suka zo neman gafara? Ka zama mai sauƙin kai sa’ad da wani yake maka magana

7, 8. (a) Ta yaya za ka yi koyi da Jehobah idan wani ya yi maka laifi? (b) Me ya sa ya kamata mu kasance da tawali’u idan muna son mu riƙa gafarta wa mutane?

7 Ya kamata ka yi koyi da Jehobah mai jin ƙai ko tausayi ba Farisawa ba. (Karanta Kolosiyawa 3:13.) Hanya ɗaya da za ka yi hakan ita ce ta wurin gafarta wa mutane. (Luk. 17:​3, 4) Don haka, zai dace ka tambayi kanka: ‘Shin ina gafarta wa mutane ko da sun mini laifi sau da yawa? Ina shirye in sasanta da wani da ya min laifi ko kuma ɓata min rai?’

8 Idan muna da tawali’u, za mu riƙa gafarta wa mutane. Farisawa ba su yi hakan ba domin ba su ɗauki wasu a bakin kome ba. Amma ya kamata Kiristoci su nuna tawali’u suna ganin cewa wasu sun fi su kuma su riƙa gafarta musu. (Filib. 2:3) Shin za ka iya bin misalin Jehobah kuma ka kasance mai tawali’u? Ka riƙa gafarta wa mutane kana nuna musu jin ƙai kuma kada ka riƙa saurin fushi.​—M. Wa. 7:​8, 9.

IDAN KA ƊAUKI RAI DA TAMANI, BA ZA KA ƊAUKI ALHAKIN JINI BA

9. Ta yaya Jehobah ya taimaka wa Isra’ilawa su san muhimmanci rai?

9 Wani babban dalilin da ya sa aka yi tanadin biranen mafaka shi ne don a kāre Isra’ilawa daga ɗaukan alhaki. (K. Sha. 19:10) Jehobah yana ɗaukan rai da muhimmanci sosai, shi ya sa ya tsani “hannuwa masu-zub da jinin” marasa laifi. (Mis. 6:​16, 17) Da yake Allah mai adalci ne kuma yana da tsarki, yana ɗaukan ran wanda aka kashe da kuskure da muhimmanci. Ko da yake ana nuna ma wanda ya kashe wani da kuskure jin ƙai, sai ya je gaban dattawa don su tabbata cewa bai yi kisan da gangan ba. Bayan da suka tabbatar da hakan, sai mutumin ya ci gaba da zama a birnin mafaka har sai babban firist ya mutu kafin ya iya komawa garinsu. Amma idan firist ɗin bai mutu ba, zai riƙa zama a wurin har muddar ransa. Wannan tsarin ya nuna wa Isra’ilawa cewa rai yana da muhimmanci sosai a gaban Allah. Don haka, idan suna son su riƙa girmama Allah, ya kamata su guji wasu abubuwa da za su iya sa ran mutane cikin hadari.

10. Ta yaya Yesu ya nuna cewa malamai da Farisawa ba su damu da mutane ba?

10 Farisawa ba sa ɗaukan rai da muhimmanci kamar yadda Jehobah yake yi. Ta yaya suka yi hakan? Yesu ya gaya musu cewa: “Kuka ɗauki mabuɗin sani: ku da kanku ba ku shiga ba, masu shiga kuwa kuka hana su.” (Luk. 11:52) Ya kamata su koya wa mutane Kalmar Allah kuma su taimaka musu su sami rai na har abada. Maimakon su yi hakan, sai suka hana mutane gaskatawa da “Sarkin rai,” wato Yesu kuma suka ja-gorance su zuwa hanyar da za ta kai su ga hallaka. (A. M. 3:15) Malamai da Farisawa suna da fahariya kuma su masu son kai ne, ba su damu da wasu ba sam balle ma zaman lafiyarsu. Ba su da tausayi ko kaɗan balle ƙauna!

11. (a) Ta yaya manzo Bulus ya nuna cewa yana da ra’ayin Allah game da rai? (b) Mene ne zai taimaka mana mu bi misalin Bulus game da wa’azi?

11 Ta yaya za mu yi koyi da Jehobah kuma mu guji halin marubuta da Farisawa? Ya kamata mu riƙa ɗaukan rai da tamani. Manzo Bulus ya yi hakan ta wurin yin wa’azi sosai. Shi ya sa ya ce: “Ni kuɓutacce ne daga jinin dukan mutane.” (Karanta Ayyukan Manzanni 20:​26, 27.) Amma wa’azin da Bulus ya yi ba don kada ya ɗauki alhakin mutane ba ne ko kuma don kawai Jehobah ya ce ya yi hakan ba. A maimakon haka, ya yi wa’azin ne don yana ƙaunar mutane kuma ransu yana da muhimmanci a gare shi. (1 Kor. 9:​19-23) Saboda haka, ya kamata mu yi iya ƙoƙarinmu don mu kasance da ra’ayin Allah game da rai. Don yana so “duka su kai ga tuba.” (2 Bit. 3:9) Kai kuma fa? Idan kana jin tausayin mutane, hakan zai sa ka riƙa wa’azi da ƙwazo kuma za ka yi farin ciki idan kana hakan.

12. Me ya sa yake da muhimmanci bayin Allah su mai da hankali sa’ad da ake aiki?

12 Mu ma muna ɗaukan rai da muhimmanci kamar yadda Jehobah yake yi, shi ya sa muke guje wa abubuwan da za su sa rayukanmu cikin haɗari. Wajibi ne mu mai da hankali sosai sa’ad da muke aiki ko gini ko gyara har da lokacin da muke tuƙi zuwa taro ma. Rayukan mutane da lafiyarsu sun fi kuɗi da lokaci muhimmanci. Allah yana yin adalci a kowane lokaci kuma ya kamata mu yi koyi da shi. Don haka, ya kamata dattawa su yi ƙoƙari su mai da hankali sa’ad da suke aiki da wasu don kada mutane su ji rauni. (Mis. 22:3) Saboda haka, idan dattawa suka ce mu mai da hankali sa’ad da muke aiki, zai dace mu bi shawararsu. (Gal. 6:1) Ya kamata mu ɗauki rai da muhimmanci kamar yadda Allah yake ɗaukansa kuma bai kamata ka ɗauki “alhakin jini” ba.

KA YI SHARI’A “BISA GA WAƊANNAN SHARI’U”

13, 14. Me zai taimaka wa dattawa su riƙa adalci kamar Jehobah?

13 Jehobah ya umurci dattawan Isra’ilawa su riƙa yin adalci kamar yadda yake yi. Da farko, dattawan za su saurari batun kafin su ɗauki wani mataki. Ta yaya za su yi hakan? Za su yi bincike sosai don su fahimci dalilin da ya sa mutumin ya yi kisan da abubuwan da ya yi a dā kafin su san yadda za a nuna masa jin ƙai. Ƙari ga haka, za su bincika ko ya tsani mutumin kuma ya ƙulla ya kashe shi. (Karanta Littafin Lissafi 35:​20-24.) Ban da haka ma, sai shaidu biyu sun tabbatar da cewa ya yi kisan da gangan ne kafin a hukunta shi.​—Lit. Lis. 35:30.

14 Bayan dattawan sun fahimci abin da ya faru da gaske, sai su yi tunani game da halin mutumin ba kawai laifin da ya yi ba. Suna bukatar su kasance da basira, wato su fahimci dalilin da ya sa mutumin ya aikata hakan. Abu mafi muhimmanci da za su yi shi ne su roƙi ruhun Jehobah ya taimaka musu su kasance da basira da tausayi kuma su yi adalci kamar Jehobah.​—Fit. 34:​6, 7.

15. Ka bayyana yadda ra’ayin Yesu game da masu zunubi ya bambanta da na Farisawa.

15 Farisawa ba sa nuna jin ƙai sa’ad da suke bincika zunubin da wani ya yi domin suna mai da hankali ga zunubin ne ba halin mutumin ba. Shi ya sa a lokacin da suka ga Yesu yana cin abinci a gidan Matiyu, sai suka ce wa almajiransa: “Don me malaminku yana ci tare da masu-karɓan haraji da masu-zunubi?” Da Yesu ya ji, sai ya ce musu: “Lafiyayyu ba su da bukatar mai-magani, sai masu-ciwo. Amma ku tafi ku koya azancin wannan, Ni, jin ƙai nike so, ba hadaya ba: gama na zo ba domin in kira masu adalci ba, amma masu-zunubi.” (Mat. 9:​9-13) Shin wannan furucin da Yesu ya yi ya nuna cewa yana son abin da masu zunubi suke yi ne? A’a. Babban dalilin da ya sa Yesu ya zo shi ne don ya taimaka wa masu zunubi su tuba. (Mat. 4:17) Yesu ya gane cewa wasu cikin “masu-karɓan haraji da masu-zunubi” suna so su canja halinsu. Kuma ba cin abinci ne kawai ya kai waɗannan masu karɓan haraji gidan Matiyu ba. Me ya sa? Domin da yawa a cikinsu suna ‘bin’ Yesu. (Mar. 2:15) Amma abin baƙin ciki shi ne Farisawa ba sa daraja mutane kamar yadda Yesu yake yi. Halinsu ya bambanta da na Jehobah shi ya sa ba su gaskata cewa masu zunubi za su iya tuba ba. Don haka, suna ganinsu kamar waɗanda ba su da bege.

16. Wane bincike ne dattawa suke yi don su fahimci batun da kyau?

16 Ya kamata dattawa a yau su bi misalin Jehobah wanda yake “son shari’a” ko adalci. (Zab. 37:28) Amma da farko sai sun “yi bincike . . . a hankali,” sosai don su san gaskiyar al’amarin. Bayan sun yi hakan, sai su ɗauki mataki bisa abin da Littafi Mai Tsarki ya ce. (K. Sha. 13:​12-14) Idan suna yin shari’a, suna bincike su tabbata cewa wanda ya yi zunubin ya tuba da gaske. Bai da sauƙi a gane ko wani da ya yi zunubi ya tuba da gaske ko a’a. Yadda mutumin ya ɗauki zunubin da ya yi da kuma abin ke zuciyarsa ne yake nuna ko ya tuba da gaske. (R. Yoh. 3:3) Idan har wanda ya yi zunubi yana son a nuna masa jin ƙai, sai ya tuba da gaske. *

17, 18. Ta yaya dattawa za su san ko wanda ya yi zunubi ya tuba da gaske? (Ka duba hoton da ke shafi na 13.)

17 Dattawa ba za su iya sanin abin da ke zukatan mutane kamar yadda Jehobah da Yesu suke yi ba. Don haka, idan kai dattijo ne, ta yaya za ka san ko wani da ya yi zunubi ya tuba da gaske? Da farko, sai ka yi addu’a don Allah ya ba ka hikima da basira. (1 Sar. 3:9) Na biyu, ka bincika Kalmar Allah da littattafan da bawan nan yake wallafawa don ya taimaka mana mu san bambanci tsakanin “baƙin ciki kan al’amarin duniya” da “baƙin cikin nan da Allah ke so,” wato, tuba da gaske. (2 Kor. 7:​10, 11, LMT) Ka bincika labaran Littafi Mai Tsarki da suka nuna waɗanda suka tuba da gaske da waɗanda ba su yi hakan ba. Ta yaya Littafi Mai Tsarki ya kwatanta yadda suka ji da kuma halinsu?

18 A ƙarshe, ka bincika halin mutumin ba laifin da ya yi ba. Wato, ka yi ƙoƙari ka fahimce shi da kyau da dalilin da ya sa yake ɗaukan wasu matakai da wasu abubuwan da yake fuskanta. Littafi Mai Tsarki ya annabta game da shugaban ikilisiya, wato Yesu, cewa: “Ba za ya yi shari’a bisa ga abin da ya bayyana ga idanunsa ba, ba kuwa za shi yanka magana bisa ga abin da kunnensa ke ji ba: amma da adalci za ya yi wa talakawa shari’a, da daidaita kuma za ya yanka magana domin masu-tawali’u na duniya.” (Isha. 11:​3, 4) Da yake Yesu ne ya naɗa dattawa su riƙa kula da ikilisiya, zai taimaka musu su yi adalci kuma su nuna tausayi sa’ad da suke shari’a. (Mat. 18:​18-20) Shin ba ma farin ciki cewa dattawa suna yin hakan? Suna taimaka mana mu riƙa yin adalci kuma mu ji tausayin ’yan’uwanmu a ikilisiya, ko ba haka ba?

19. Wanne cikin darussa da muka koya daga tanadin biranen mafaka ne kake so ka yi amfani da shi?

19 Dokar da aka bayar ta hannun Musa ya ƙunshi “surar sani da surar gaskiya,” game da Jehobah da kuma ƙa’idodinsa. (Rom. 2:20) Tanadin biranen mafaka da aka yi ya koya wa dattawa yadda za su yi “shari’a ta gaskiya.” Ban da haka ma, ya koya mana yadda za mu “nuna jin ƙai da juyayi.” (Zak. 7:9) Ba ma bin dokar alkawari yanzu. Duk da haka, Jehobah bai canja ba kuma yin adalci da nuna jin ƙai suna da muhimmanci sosai. Muna da babban gata da yake muna bauta wa Allah. Don haka, bari dukanmu mu yi koyi da shi don mu sami kwanciyar hankali kuma ya ci gaba da kāre mu!

^ sakin layi na 16 Ka duba “Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu” a Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Satumba, 2006, shafi na 30 a Turanci.