Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Kada Ka Bar Wani Abu Ya Hana Ka Samun Ladar

Kada Ka Bar Wani Abu Ya Hana Ka Samun Ladar

“Kada kowane mutum ya raba ku da ladanku.”​—KOL. 2:18.

WAƘOƘI: 122, 139

1, 2. (a) Wace lada ce bayin Allah suke begensa? (b) Me zai taimaka mana mu sa rai a kan ladarmu? (Ka duba hoton da ke shafin nan.)

KIRISTOCI shafaffu suna da begen samun ‘ladar nasara ta maɗaukakiyar kira ta Allah.’ (Filib. 3:14) Suna da begen yin rayuwa tare da Yesu Kristi a sama don su sa ’yan Adam su zama kamiltattu. (R. Yoh. 20:6) Wannan gata ne mai kyau da shafaffu suke jira, ko ba haka ba? Amma waɗansu tumaki suna da wani bege kuma da suke jira. Wane bege ke nan? Su ma suna da begen yin rayuwa a duniya har abada kuma wannan ba ƙaramin gata ba ne.​—2 Bit. 3:13.

2 Don a taimaka wa shafaffu su ci gaba da kasancewa da aminci kuma su sami ladar, manzo Bulus ya ce: ‘Ku ƙwallafa ranku ga abubuwan da ke bisa.’ (Kol. 3:2) An ce su ƙwallafa ransu ga ladar da za su samu na yin rayuwa a sama. (Kol. 1:​4, 5) Idan muka yi tunani a kan alkawarin da Allah ya yi wa bayinsa, hakan zai sa mu sa rai a kan wannan ladar ko muna da begen zuwa sama ko kuma zama a duniya.​—1 Kor. 9:24.

3. Wane gargaɗi ne Bulus ya yi wa Kiristoci game da abubuwan da za su iya hana su samun ladar?

3 Bulus ya sake yi wa Kiristoci gargaɗi a kan wasu abubuwa da za su iya hana su samun ladar nan. Alal misali, ya ja kunnen Kiristoci da ke Kolosi game da wasu Kiristoci da suke so su faranta wa Allah rai amma suna bin Dokar da aka ba da ta hannun Musa maimakon su ba da gaskiya ga Kristi. (Kol. 2:​16-18) Ban da haka ma, ya yi magana a kan wasu abubuwan da za su iya hana mu a yau samun ladar nan. Alal misali, ya nuna yadda za mu guji tunanin banza da yadda Kiristoci za su sasanta matsalolinsu da kuma abin da za mu yi idan muna da matsala a iyali. Wannan shawarar tana da amfani har wa yau. Don haka, bari mu bincika wasu cikin gargaɗin da Bulus ya yi a wasiƙar da ya rubuta wa Kiristocin da ke Kolosi.

KA MATAR DA SHA’AWOYIN YIN LALATA

4. Ta yaya sha’awoyin banza za su iya hana mu samun wannan ladar?

4 Bayan da ya tuna wa ’yan’uwa game da bege mai kyau da suke da shi, sai ya ce: “Ku matar da gaɓaɓuwanku fa waɗanda ke a duniya; fasikanci, ƙazanta, kwaɗayi, mugun guri, da sha’awa.” (Kol. 3:5) Sha’awoyin lalata za su iya shawo kanmu har su sa mu ɓata dangantakarmu da Allah kuma mu kāsa samun ladar. Wani ɗan’uwa da ya taɓa yin lalata aka masa horo kuma ya tuba aka dawo da shi, ya ce: “Sha’awoyin sun shawo kaina sosai shi ya sa ban iya kame kaina ba har sai da na ɓata dangantakata da Allah.”

5. Ta yaya za mu kāre kanmu daga yanayi mai haɗari?

5 Zai dace mu mai da hankali sosai sa’ad da muka sami kanmu a wani yanayin da zai iya sa mu tāka dokar Allah. Alal misali, zai dace waɗanda suke fita zance su tattauna tun da wuri matakan da za su ɗauka don kada su wuce gona da iri sa’ad da suke rungumar juna ko sumba da kuma a lokacin da suke wani wuri su kaɗai. (Mis. 22:3) Wani yanayi kuma da zai iya sa Kirista cikin haɗari shi ne sa’ad da wata ko wani ma’auraci ya yi tafiya ko kuma sa’ad da wani yake aiki da wadda ba matarsa ba. (Mis. 2:​10-12, 16) Idan ka sami kanka a irin wannan yanayin, zai dace ka sa su sani cewa kai Mashaidin Jehobah ne kuma ka kasance da basira sa’ad da kake sha’ani da su. Ƙari ga haka, kada ka manta cewa idan kana kwarkwasa, za ka shiga matsala sosai. Ban da haka ma, zai dace mu mai da hankali sa’ad da muke baƙin ciki ko kuma muka kaɗaita. Domin yanayin zai iya sa mu nemi kowane irin mutum da zai sa mu farin ciki kuma hakan yana da haɗari sosai. Idan ka sami kanka a irin wannan yanayin, zai dace ka nemi taimakon Jehobah da kuma mutanensa don su taimaka maka don kada wani abu ya haka ka samun wannan ladar.​—Karanta Zabura 34:18; Misalai 13:20.

6. Me ya kamata mu tuna sa’ad da muke zaɓan nishaɗi?

6 Idan muna son mu daina sha’awoyin banza, zai dace mu guji nishaɗi da ke ɗaukaka halin banza. Abubuwan da masu shirya fina-finai da masana’antun nishaɗi suke gabatar wa mutane sun yi kama da waɗanda ake yi a Saduma da Gwamarata a dā. (Yahu. 7) Kuma waɗanda suke tsara waɗannan abubuwan suna ɗaukaka lalata, don haka mutane ba sa ganin cewa yana da muni. Saboda haka, ya kamata mu riƙa zaɓan abubuwan da muke karantawa da kallo don kada su janye hankalinmu kuma su hana mu samun ladar.​—Mis. 4:23.

KA ZAMA MAI ƘAUNA DA ALHERI

7. Waɗanne matsaloli ne za mu iya fuskanta a ikilisiya?

7 Muna farin cikin kasancewa a cikin ikilisiyar Kirista. Muna nazarin Kalmar Allah a taronmu kuma muna tallafa ko ƙarfafa juna. Kuma hakan yana taimaka mana mu mai da hankali ga samun ladar. Amma a wasu lokuta, za mu iya samun saɓani da ’yan’uwanmu. Kuma idan ba mu sasanta matsalar ba, hakan zai iya jawo ƙiyayya.​—Karanta 1 Bitrus 3:​8, 9.

8, 9. (a) Waɗanne halaye ne za su taimaka mana mu sami ladar? (b) Me zai taimaka mana mu ci gaba da kasancewa da haɗin kai a ikilisiya ko da wani ya ɓata mana rai?

8 Me ya kamata mu yi don kada mu sa ƙiyayya ya hana mu samun wannan ladar? Bulus ya gaya wa ’yan’uwa da ke Kolosi cewa: “Domin ku zaɓaɓu na Allah ne, masu-tsarki, ƙaunatattu kuma, ku yafa zuciya ta tausayi, nasiha, tawali’u, ladabi, jimrewa; kuna haƙuri da juna, kuna gafarta ma juna, idan kowane mutum yana da maganar ƙara game da wani; kamar yadda Ubangiji ya gafarta maku, hakanan kuma sai ku yi: gaba da dukan waɗannan kuma ku yafa ƙauna, gama ita ce magamin kamalta.”​—Kol. 3:​12-14.

9 Idan muna nuna ƙauna da alheri, za mu riƙa gafarta wa juna. Alal misali, idan wani ɗan’uwa ko wata ’yar’uwa ta ɓata mana rai, zai dace mu tuna cewa a wasu lokuta mu ma mun taɓa yin magana ko wasu abubuwan da suka ɓata ma wasu rai. Babu shakka, mun yi farin ciki cewa a lokacin, ’yan’uwa sun nuna mana ƙauna da alheri kuma suka gafarta mana, ko ba haka ba? (Karanta Mai Wa’azi 7:21, 22.) Ban da haka ma, muna farin ciki cewa Kristi ya sa mu kasance da haɗin kai. (Kol. 3:15) Dukanmu muna ƙaunar Jehobah, muna wa’azin game da shi kuma muna fuskantar matsalolin da ’yan’uwanmu suke fama da shi. Don haka, idan muka gafarta wa juna, za mu kasance da haɗin kai a ikilisiya kuma ba za mu manta da ladar rai na har abada da ke jiranmu ba.

10, 11. (a) Me ya sa kishi ba shi da kyau? (b) Wane mataki za mu ɗauka don kada kishi ya hana mu samun ladar nan?

10 Akwai wasu labarai da yawa a Littafi Mai Tsarki da suka nuna cewa kishin mutane zai hana mu samun ladar. Alal misali, kishi ne ya sa Kayinu ya kashe ɗan’uwansa Habila. Korah da Datan da Abiram sun yi kishin Musa kuma suka masa taurin kai. Ƙari ga haka, Sarki Saul ya yi kishin Dauda don nasarar da yake yi shi ya sa ya yi ƙoƙari ya kashe shi. Wannan dalilin ne ya sa Littafi Mai Tsarki ya ce: “Wurin da kishi da tsaguwa suke, nan akwai yamutsai da kowane irin mugun al’amari.”​—Yaƙ. 3:16.

11 Idan muka yi iya ƙoƙarinmu don mu kasance da ƙauna da alheri, ba za mu yi kishin wasu ba. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ƙauna tana da yawan haƙuri, tana da nasiha; ƙauna ba ta jin kishi.” (1 Kor. 13:4) Idan ba ma son mu yi kishin mutane, wajibi ne mu kasance da ra’ayin Jehobah muna ganin kanmu duka a ikilisiya cewa mu ’yan’uwan juna ne. Hakan zai taimaka mana mu riƙa tausayin mutane don Kalmar Allah ta ce: “Idan . . . gaɓa ɗaya ya sami girma, dukan gaɓaɓuwa suna murna tare da shi.” (1 Kor. 12:​16-18, 26) Saboda haka, maimakon mu yi kishin wasu don abubuwan da suke da su, zai yi kyau mu taya su murna. Bari mu bincika labarin ɗan Sarki Saul mai suna Jonathan. Bai yi kishi ba sa’ad da aka ce Dauda ne zai gāji sarautar babansa, a maimakon haka, ya ƙarfafa Dauda. (1 Sam. 23:​16-18) Zai dace mu yi koyi da misali mai kyau na Jonathan.

KU YI ƘOƘARI A IYALINKU KU SAMI LADAR

12. Bin wace shawara ce za ta taimaka wa iyalai su sami ladar?

12 Bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki zai sa iyali su yi zaman lafiya kuma su riƙa farin ciki. Ƙari ga haka, zai sa su sami ladar. Wace shawara ce da za ta taimaka wa iyalai Bulus ya ba ’yan’uwa da ke ikilisiyar Kolosi? Ya ce: “Ku mata, ku yi zaman biyayya da maza naku, abin da ya kamata ke nan cikin Ubangiji. Ku mazaje, ku yi ƙaunar matayenku, ka da kuwa ku yi fushi da su. Ku ’ya’ya, ku yi biyayya da iyayenku cikin kowane abu, gama wannan abin yarda ne cikin Ubangiji. Ku ubanni, ka da ku yi wa ’ya’yanku cakuna, domin ka da ransu ya karai.” (Kol. 3:​18-21) Babu shakka, bin shawarar Bulus zai taimaka wa magidanta da mata da kuma yara a zamaninmu.

13. Ta yaya ’yar’uwa za ta taimaka wa mijinta ya soma bauta wa Jehobah?

13 Idan kina da aure kuma kina ganin mijinki da ba Mashaidi ba ne yana wulaƙanta ki kuma fa? Yanayin zai gyaru ne idan kuna jayayya da juna a kullum? Ko da kin yi nasara kuma ya yi abin da kike so, shin hakan zai sa ya soma bauta wa Jehobah? Amma idan kika yi masa ladabi, za ku yi zaman lafiya kuma ku ɗaukaka Jehobah har wataƙila ya soma bauta wa Jehobah. Ta hakan dukanku za ku sami ladar.​—Karanta 1 Bitrus 3:​1, 2.

14. Mene ne maigida zai yi idan matarsa da ba Mashaidiya ba, ba ta yi masa ladabi?

14 Idan matarka da ba Mashaidiya ba, ba ta maka ladabi fa? Za ka iya sa ta soma yi maka biyayya ne idan kana tsauta mata don ka nuna mata cewa kai ne mai iko a iyalin? A’a! Allah yana son ka riƙa ƙaunar matarka kamar yadda Yesu ya yi. (Afis. 5:23) Yesu ya yi ƙaunar ikilisiya kuma ya bi da su da haƙuri. (Luk. 9:​46-48) Idan maigida ya bi da matarsa kamar yadda Yesu ya yi, wataƙila matar ta soma bauta wa Jehobah.

15. Ta yaya maigida zai nuna cewa yana ƙaunar matarsa?

15 Littafi Mai Tsarki ya umurci mazaje cewa: “Ku yi ƙaunar matayenku, kada kuwa ku yi fushi da su.” (Kol. 3:19) Maigida da yake ƙaunar matarsa yana yin la’akari da ra’ayinta kuma ya tabbatar mata cewa yana son shawarar da take ba shi. (1 Bit. 3:7) Ko da yake ba zai iya bin kowace shawara da ta bayar ba, idan yana sauraron ta, hakan zai taimaka masa ya riƙa tsai da shawara mai kyau. (Mis. 15:22) Duk wani maigida da ke ƙaunar matarsa ba zai riƙa gaya mata ta masa ladabi ba, a maimakon haka, zai yi wasu abubuwa masu kyau da za su sa matar da riƙa masa ladabi. Idan maigida yana ƙaunar matarsa da yaransa, dukansu za su bauta wa Jehobah da kyau kuma za su sami ladar rai na har abada.

Ta yaya za mu guji barin matsaloli na iyali su hana mu samun ladar? (Ka duba sakin layi na 13-15)

MATASA, KADA KU BAR WANI ABU YA HANA KU SAMIN LADAR!

16, 17. Ta yaya matashi zai guji yin fushi ainun da iyayensa?

16 Wane mataki za ka ɗauka idan kai matashi ne da kake gani cewa iyayenka ba sa fahimtarka ko kuma suna taƙura maka? Hakan zai iya ɓata maka rai har ka riƙa ganin cewa bauta wa Jehobah ba shi da wani muhimmanci. Amma idan har hakan ya sa ka daina bauta wa Jehobah, daga baya za ka fahimta cewa babu wanda ya fi ƙaunarka kamar ’yan’uwa da kuma iyayenka.

17 Idan iyayenka ba sa yi maka gyara, ta yaya za ka sani ko sun damu da kai? (Ibran. 12:8) Shin yadda iyayenka suke maka horo ne yake ba ka haushi? Maimakon hakan yana ɓata maka rai, zai dace ka tuna cewa iyayenka ajizai ne. Don haka, ya kamata ka kasance da ra’ayi mai kyau kuma ka daina kushe su. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Mutumin da ya tabbata yana da gaskiya ba zai cika yawan magana ba, natsattsen mutum yana da basira ƙwarai.” (Mis. 17:​27, Littafi Mai Tsarki) Ka yi ƙoƙari ka riƙa karɓan shawararsu amma kar ka bar yadda suka ba ka shawarar ya dame ka. (Mis. 1:8) Idan kana da iyayen da suke bauta ma Jehobah, hakan albarka ce sosai don za su so taimaka maka ka sami ladar rai na har abada.

18. Me ya sa ka ƙuduri aniya samun ladar rayuwa har abada a nan gaba?

18 Ko da muna da begen zuwa sama ko kuma yin rayuwa a duniya har abada. Muna da bege mai kyau domin Mahaliccinmu ne ya yi wannan alkawarin game da Aljanna a duniya cewa: “Duniya za ta cika da sanin Ubangiji.” (Isha. 11:9) Jehobah ne zai riƙa koyar da kowane mutum a duniya a lokacin. Babu shakka, ya kamata mu yi ƙoƙari sosai don mu sami wannan ladar. Saboda haka, ka riƙa tunanin alkawarin da Jehobah ya yi maka, kuma kada ka bar wani abu ya hana ka samun wannan ladar!