HASUMIYAR TSARO—NA NAZARI Nuwamba 2018

Wannan fitowar tana dauke da talifofin nazari da za a yi daga ranar 31 ga Disamba 2018 zuwa 3 ga Fabrairu, 2019.

“Ka Sayi Gaskiya, Kada Ka Sayar” da Ita

Mene ne yake nufi a sayi gaskiya? Me zai taimaka mana mu ci gaba da bin gaskiya muddin mun saye ta?

Zan “Yi Tafiya Cikin” Gaskiyarka

Ta yaya za mu karfafa kudurinmu na daukan gaskiya da Jehobah yake koya mana da muhimmanci?

Ka Dogara ga Jehobah Don Ka Rayu!

Littafin Habakkuk zai iya taimaka mana mu kasance da kwanciyar rai duk da matsalolinmu.

Wane ne Yake Sarrafa Tunaninka?

Ta yaya za ka bari ra’ayin Jehobah ya rika sarrafa tunaninka ba na mutum ba?

Kana da Irin Ra’ayin Jehobah Kuwa?

Mene ne muke bukatar mu yi don kada ra’ayin mutanen duniya ya shafe mu?

Nasiha​—Halin da Muke Nunawa ta Furuci da Ayyuka

Nasiha yana cikin ’ya’yan ruhu mai tsarki. Ta yaya za mu kasance da wannan hali mai kyau?

Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu

Su waye ne Masu Taimakon Mutane da Yesu ya ambata a daren da ya mutu, kuma me ya sa aka ba su wannan lakabin?

Wace Kyauta Ce Za Mu Ba Jehobah?

Mene ne “abin da kake da shi” da aka ambata a Misalai 3:​9, kuma ta yaya za mu iya amfani da shi wajen goyon bayan bauta ta gaskiya?