Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

“Ka Sayi Gaskiya, Kada Ka Sayar” da Ita

“Ka Sayi Gaskiya, Kada Ka Sayar” da Ita

“Ka sayi gaskiya, kada ka sayar, ka kuma sami hikima da horarwa da ganewa.”​—K. MAG. 23:23.

WAƘOƘI: 94, 96

1, 2. (a) Mene ne ya fi tamani a rayuwarmu? (b) Waɗanne koyarwa ne muke ɗauka da tamani, kuma me ya sa? (Ka duba hoton da ke shafin nan.)

MENE NE ya fi tamani a gare ka? Kana shirye ka sadaukar da shi don ka sami wani abu da ba shi da tamani? Ba da amsoshin waɗannan tambayoyin zai yi wa bayin Jehobah sauƙi. Abin da ya fi tamani a gare mu shi ne dangantakarmu da Jehobah, kuma ba za mu sadaukar da ita don mu sami wani abu ba. Ƙari ga haka, muna son gaskiyar da ke cikin Littafi Mai Tsarki, don ita ce ke taimaka mana mu ƙulla abota da Jehobah.​—Kol. 1:​9, 10.

2 Jehobah yana koya mana abubuwa da yawa a cikin Littafi Mai Tsarki! A wurin ne ya bayyana mana ma’anar sunansa da kuma halayensa masu kyau. Ya sanar da mu cewa yana ƙaunar mu sosai shi ya sa ya aiko da Ɗansa ya mutu a madadinmu. Ban da haka, Jehobah ya gaya mana game da Mulkin Almasihu, kuma ya ba shafaffu begen zuwa sama, “waɗansu tumaki” kuma suna da begen yin rayuwa a cikin Aljanna a duniya. (Yoh. 10:16) Jehobah ya koya mana irin halayen da za mu kasance da su. Muna ɗaukan waɗannan koyarwa da tamani don suna taimaka mana mu kusaci Mahaliccinmu kuma suna sa rayuwarmu ta kasance da ma’ana.

3. Za mu iya sayan gaskiya da kuɗi? Ka bayyana.

3 Jehobah, Allah ne mai karimci sosai, kuma ya nuna hakan sa’ad da ya aiko da Ɗansa ya mutu a madadinmu. Ƙari ga haka, Jehobah yana taimaka wa masu neman su koyi gaskiya, kuma ba ya bukatar su biya kuɗi kafin su koyi gaskiya. Shi ya sa manzo Bitrus ya tsauta ma wani mutum mai suna Siman da ya ba shi kuɗi don ya sami ikon ba mutane ruhu mai tsarki. Bitrus ya ce masa: “Kai da kuɗinka, ku halaka! Kana tsammani da kuɗi ne za ka sami kyautar Allah?” (A. M. 8:​18-20) Mene ne wannan umurnin “ka sayi gaskiya” yake nufi?

ME YAKE NUFI A “SAYI” GASKIYA?

4. Me za mu koya a wannan talifin?

4 Karanta Karin Magana 23:23. Wajibi ne mu ƙoƙarta mu koyi gaskiyar da ke cikin Kalmar Allah kuma mu yi sadaukarwa sosai don mu san ta. Kamar yadda marubucin littafin Karin Magana ya ce, muddin mun “sayi” ko kuma mun sami “gaskiya,” ya kamata mu mai da hankali don kada mu “sayar” da ita ko kuma mu yi hasarar ta. Za mu tattauna abin da yake nufi mu “sayi” gaskiya da kuma adadin kuɗin da za mu biya don mu same ta. Hakan zai sa mu ɗauki gaskiya da tamani kuma mu ƙuduri niyyar cewa ba za mu “sayar” da ita ba. Za mu fahimci cewa sayan gaskiya ya fi duk wata sadaukarwa da za mu yi.

5, 6. (a) Ta yaya za mu sayi gaskiya ba tare da biyan kuɗi ba? Ka ba da misali. (b) Ta yaya gaskiya take amfanar mu?

5 Hakika ko da an ba mu wani abu kyauta, muna bukatar mu ɗauki mataki don ya zama namu. A Helenanci, kalmar nan “sayi” da ke littafin Karin Magana 23:23 tana iya nufin “samu.” Kalmomin nan biyu suna nuna cewa mutum zai ɗauki mataki ko kuma ya yi musanyar wani abu don ya sami abu mai tamani. Alal misali, a ce ana rarraba ayaba kyauta a kasuwa, za mu ga ayabar a kan teburinmu ne haka kawai? A’a. Za mu bukaci mu je kasuwar mu karɓi ayabar. Shin wannan ayabar kyauta ce? E, amma wajibi ne mu je kasuwa don mu karɓi ayabar. Hakazalika, ba ma bukatar kuɗi don mu sayi gaskiya, amma muna bukatar mu ɗauki mataki kafin mu same ta.

6 Karanta Ishaya 55:​1-3. Abin da Ishaya ya rubuta ya ba da ƙarin haske a kan abin da sayan gaskiya yake nufi. A waɗannan ayoyin, Jehobah ya kwatanta Kalmarsa da ruwa da madara da kuma ruwan inabi. Kamar ruwan sanyi, Kalmar Allah tana kwantar mana da hankali. Madara tana sa mu sami ƙarfi kuma tana taimaka wa yara su yi girma. Hakazalika, Kalmar Jehobah tana ƙarfafa mu da kuma taimaka mana mu ci gaba da manyanta. Ƙari ga haka, Kalmar Jehobah tana kamar ruwan inabi. A wace hanya? A cikin Littafi Mai Tsarki, an ce ruwan inabi yana sa mutum farin ciki. (Zab. 104:15) Saboda haka, sa’ad da Jehobah ya gaya wa mutanensa su “sayi ruwan inabi,” yana tabbatar musu da cewa yin rayuwa da ta jitu da ƙa’idodinsa zai sa su farin ciki. (Zab. 19:8) Hakika, wannan kwatanci ya nuna mana amfanin koyan gaskiya da kuma yin amfani da ita! Muna iya kwatanta ƙoƙarin da muke yi da kuɗin da muka biya don mu sayi gaskiya. Saboda haka, bari mu tattauna abubuwa biyar da za mu biya don mu sayi gaskiya.

ME KA SADAUKAR DON KA SAYI GASKIYA?

7, 8. (a) Me ya sa ya wajaba mu nemi lokaci don mu sayi gaskiya? (b) Wace sadaukarwa ce wata matashiya ta yi don ta koyi gaskiya, kuma mene ne sakamakon hakan?

7 Lokaci. Kowa yana bukatar ya nemi lokaci don ya saurari wa’azi da karanta Littafi Mai Tsarki da kuma littattafai da ke bayyana shi. Ƙari ga haka, muna bukatar lokaci don yin nazari da shirya taro da kuma halartan taro. Wajibi ne mu nemi lokaci daga abubuwan da ba su da muhimmanci. (Karanta Afisawa 5:​15, 16.) Sa’o’i nawa muke bukatar mu keɓe don mu san abin da ke cikin Littafi Mai Tsarki sosai? Hakan ya dangana da yanayinmu. Akwai abubuwa da yawa da za mu iya koya game da hikimar Jehobah da hanyoyinsa da kuma ayyukansa. (Rom. 11:33) A fitowa ta farko ta Hasumiyar Tsaro, an kwatanta gaskiya da “fure” kuma ta ce: “Kada ka gamsu da fure ɗaya na gaskiya. Da a ce ɗaya ya isa da ba mu samu ƙari ba. Ka ci gaba da tara furen.” Ya kamata mu tambayi kanmu, ‘Shin na koyi abubuwa da yawa game da Jehobah?’ Ko a lokacin da za mu yi rayuwa har abada, za mu ci gaba da koyan abubuwa da yawa game da Jehobah. A yau, yana da muhimmanci mu yi amfani da lokacinmu sosai don mu koyi abubuwa da dama. Ga misalin wata da ta yi hakan.

8 Wata matashiya ’yar Jafan mai suna Mariko * ta zo yin karatu a birnin New York City a Amirka. A lokacin, tana bin wani rukunin addini da aka kafa a Jafan a shekara ta 1959. Amma sa’ad da wata majagaba take wa’azi gida-gida, sai ta haɗu da ita. Mariko ta yi farin ciki sa’ad da ta soma koyan gaskiyar Littafi Mai Tsarki, kuma hakan ya sa ta gaya wa ’yar’uwar ta riƙa nazari da ita sau biyu a mako. Duk da cewa tana da ayyuka da yawa a makaranta kuma tana aiki na ɗan lokaci, Mariko ta soma halartan taron ikilisiya nan da nan. Ban da haka, ta daina yawan shaƙatawa domin ta sami lokacin koyan gaskiya da kyau. Yin irin wannan sadaukarwa ya sa ta samu ci gaba kuma kafin shekara guda aka yi mata baftisma. Sai ta soma hidimar majagaba bayan wata shida a shekara ta 2006 kuma tana hakan har yau.

9, 10. (a) Ta yaya sayan gaskiya yake shafan ra’ayinmu game da kayan duniya? (b) Mene ne wata matashiya ta sadaukar, kuma yaya take ji game da yin hakan?

9 Kayan duniya. Don mu sayi gaskiya, muna iya bukatar mu sadaukar da aikinmu ko kuma sana’armu. Sa’ad da Yesu ya gaya wa Bitrus da Andarawus masu aikin kamun kifi su zama “masu jawo mutane” wurinsa, sai “suka bar kayansu na kamun kifi.” (Mat. 4:​18-20) Hakika, yawancin mutane da suka koyi gaskiya a yau ba za su bar aikinsu ba domin suna bukatar su kula da iyalinsu. (1 Tim. 5:8) Amma sau da yawa, wajibi ne mutanen da suka koyi gaskiya su canja ra’ayinsu game da kayan duniya kuma su riƙa yin abin da ya fi muhimmanci. Yesu ya ce: “Kada ku tara wa kanku dukiya a duniya . . . Sai dai ku tara wa kanku dukiya a sama.” (Mat. 6:​19, 20) Abin da wata matashiya ta yi ke nan.

10 Maria tana jin daɗin yin wasan kwallon gora sa’ad da take ƙarama. Ta ci gaba da ƙware sosai a yin wasan a lokacin da take makarantar sakandare kuma daga baya ta samu sukaloshif na zuwa jami’a. Tana son buga kwallon gora sosai kuma burinta shi ne ya zama sana’arta. Sai Maria ta soma nazarin Littafi Mai Tsarki, kuma tana jin daɗin abin da take koya. Ƙari ga haka, ta yi farin ciki don canje-canjen da hakan ya taimaka mata ta yi a rayuwarta. Ta ce: “Ina farin ciki sosai yayin da nake canja halina da salon rayuwata don su jitu da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki.” Maria ta fahimci cewa zai yi mata wuya ta riƙa biɗan kayan duniya da kuma bauta wa Jehobah a lokaci ɗaya. (Mat. 6:24) Sai ta sadaukar da burinta na zama tauraruwa da yin arziki da kuma suna. Amma domin ta sayi gaskiya, tana hidimar majagaba yanzu kuma ta ce tana jin daɗin yin “rayuwa mai ma’ana sosai.”

11. Idan muka sayi gaskiya, mene ne zai faru da wasu abokanmu?

11 Yin abota da mutane. Yadda muke cuɗanya da abokanmu da danginmu yana iya canjawa sa’ad da muka zaɓi mu yi rayuwar da ta jitu da koyarwa Littafi Mai Tsarki. Me ya sa? Yesu ya yi addu’a don mabiyansa cewa: “Ka tsarkake su ta wurin gaskiya, gama kalmarka kuwa ita ce gaskiya.” (Yoh. 17:17) “Tsarkake su” yana iya nufin ware su, kuma sa’ad da muka koyi gaskiya, ana ware mu daga mutanen duniya domin ba ma yin abin da suke yi. Ra’ayin mutane game da mu yakan canja domin muna bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki. Ko da yake muna ƙoƙari mu yi cuɗanya da abokanmu da danginmu, wasu ba za su so mu kamar yadda suke yi a dā ba kuma suna iya tsananta mana don imaninmu. Hakan ba ya sa mu mamaki don Yesu ya ce: “Mutanen gidan mutum ne kuma za su zama abokan gābansa.” (Mat. 10:36) Ya kuma tabbatar mana da cewa ladar da za mu samu don sayan gaskiya ta fi sadaukarwar da muka yi.​—Karanta Markus 10:​28-30.

12. Wace sadaukarwa ce wani Bayahude ya yi don ya sayi gaskiya?

12 Wani mutum mai suna Aaron, Bayahude ne da kuma ɗan kasuwa. An koya masa cewa bai dace a furta sunan Allah ba. Amma Aaron yana so ya koyi gaskiya, kuma ya yi farin ciki sosai sa’ad da wani Mashaidi ya koya masa cewa yana iya furta sunan Allah “Jehobah” ta wajen saka wasula a sunan Allah da aka rubuta a Ibrananci. Abin da Aaron ya koya ya sa shi farin ciki sosai, sai ya je majami’arsu don ya gaya wa malamansu. Matakin da suka ɗauka ya ba shi mamaki. Maimakon su yi farin ciki, sun tofa masa miyau kuma suka kore shi daga majami’ar. Ƙari ga haka, dangin Aaron ba su yi farin ciki ba, duk da haka, ya ci gaba da sayan gaskiya kuma ya bauta wa Jehobah muddar ransa. Mutane da kuma iyalanmu suna iya daina cuɗanya da mu domin muna bauta wa Jehobah kamar yadda ya faru da Aaron.

13, 14. Waɗanne canje-canje muke bukatar mu yi domin mu sayi gaskiya? Ka ba da misali.

13 Hali da tunanin banza. Muna bukatar mu canja halinmu da tunaninmu sa’ad da muka koyi gaskiya kuma mu soma rayuwa da ta jitu da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki. Ka lura da abin da Bitrus ya ce game da waɗannan canje-canje: “Yanzu da kuke ’ya’ya masu biyayya, kada ku yarda abubuwan da kuke marmarinsu a dā su ɗauke muku hankali. A lokacin, ai, kuna zaman duhu ne. Amma . . . sai ku keɓe kanku da tsarki a cikin dukan ayyukanku.” (1 Bit. 1:​14, 15) Mutane da yawa a birnin Korinti na dā masu yin lalata ne. Saboda haka, suna bukatar su yi canje-canje sosai domin su zama masu tsarki. (1 Kor. 6:​9-11) Hakazalika, mutane da yawa a yau sun daina halin banza don su koyi gaskiya. Bitrus ya ƙara tuna wa Kiristoci na zamaninsa cewa: “Kun riga kun ɓata lokaci sosai a kan zaman da kuka yi a dā, wato zama iri wanda marasa sanin Allah suke jin daɗinsa, wato neman jin daɗi na rashin kunya, da sha’awa iri-iri ta jiki, da buguwa, da bukukuwan shaye-shaye, da fitar shan iska ta lalata, har da bautar gumaka, abin ƙyama ne.”​—1 Bit. 4:3.

14 Wani mai suna Devynn da budurwarsa Jasmine sun yi shekaru da yawa suna shaye-shaye. Ko da yake Devynn ƙwararren akanta ne, ana yawan korarsa daga wurin aiki domin shi mashayi ne. Jasmine kuma tana da zafin rai kuma tana son faɗa sosai. Wata rana da Jasmine ta sha ta bugu, sai ta haɗu da Shaidun Jehobah biyu da suke wa’azi a hanya. Suka ce za su riƙa nazari da ita, amma da suka je gidansu a mako na gaba, sai suka ga cewa Jasmine da Devynn sun bugu. Amma sun yi mamaki cewa masu wa’azin sun sake dawowa ko da yake su mashaya ne. Bayan wannan ranar, Jasmine da Devynn ba su sake buguwa ba. Sun soma nazarin Littafi Mai Tsarki kuma suka soma yin amfani da abin da suke koya. Bayan wata uku na yin nazari, sai suka daina shan giya kuma suka yi rajistar aurensu. Mutane da yawa a ƙauyensu da suka lura da yadda suka yi canje-canje a rayuwarsu suka soma nazarin Littafi Mai Tsarki.

15. Wane abu ne yakan yi wuya sosai mutum ya daina yi sa’ad da ya koyi gaskiya, kuma me ya sa?

15 Bukukuwa da al’adun da ba su dace ba. Ba shi da sauƙi mutum ya daina bukukuwa da al’adun ƙarya. Ko da yake yana iya yi ma wasu sauƙi su daina waɗannan ayyukan, wasu kuma suna iya jinkirin yin hakan domin matsi daga iyalinsu da abokan aikinsu da abokansu na kud da kud. Matsalar tana iya yin tsanani sosai musamman idan bukukuwan don tuna da wasu dangi ne da suka mutu. (M. Sha. 14:1) Misalan wasu masu ƙarfin zuciya zai taimaka mana mu yi canje-canjen da ya kamata. Za mu bincika abin da wasu mazaunan Afisa suka yi a ƙarni na farko.

16. Mene ne wasu a Afisa suka yi sa’ad da suka koyi gaskiya?

16 Yin sihiri ruwan dare gama gari ne a birnin Afisa na dā. Amma, mene ne wasu mutane da suka koyi gaskiya suka yi don su daina sihiri? Littafi Mai Tsarki ya ce: “Mutane da yawa kuwa masu yin sihiri, suka tattaro littattafansu suka ƙone su a gaban jama’a duka. Da suka yi lissafin kuɗin littattafan, sai suka ga ya kai azurfa dubu hamsin. Ta haka kalmar Ubangiji ta ƙara bazuwa, ta kuma yi ƙarfi sosai.” (A. M. 19:​19, 20) Waɗannan Kiristoci masu aminci sun yi sadaukarwa sosai kuma Jehobah ya albarkace su.

17. (a) Waɗanne abubuwa ne za mu iya sadaukarwa don mu koyi gaskiya? (b) Waɗanne tambayoyi ne za mu tattauna a talifi na gaba?

17 Mene ne muka sadaukar don mu koyi gaskiya? Dukanmu mun sadaukar da lokacinmu, wasu sun daina biɗan kayan duniya, wasu kuma sun yi hasarar abokansu. Mutane da yawa sun yi canje-canje don su daina hali da tunanin banza kuma sun daina yin bukukuwa da al’adun da ba su dace ba. Ko da wace sadaukarwa ce muka yi, mun tabbata cewa koyarwar Littafi Mai Tsarki tana da tamani fiye da kome da muka sadaukar. Ƙari ga haka, tana sa mu ƙulla dangantaka ta kud da kud da Jehobah. Idan muka yi tunanin albarkar da muka samu don mun koyi gaskiya, zai yi mana wuya mu fahimci dalilin da ya sa wasu za su so su sayar da ita. Ta yaya hakan zai iya faruwa? Ta yaya za mu guji yin irin wannan kuskure mai tsanani? Za mu tattauna waɗannan tambayoyi a talifi na gaba.

^ sakin layi na 8 An canja wasu sunaye a wannan talifin.