Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Kana da Irin Ra’ayin Jehobah Kuwa?

Kana da Irin Ra’ayin Jehobah Kuwa?

“Ku yarda Allah ya canja ku ya sabunta tunaninku da hankalinku.”​—ROM. 12:2.

WAƘOƘI: 56, 123

1, 2. Me muke koya yayin da muke manyanta? Ka ba da misali.

KA YI la’akari da wannan misalin. Wani mutum ya ba wani ƙaramin yaro kyauta, sai iyayensa suka gaya masa ya ce wa mutumin, “Na gode.” Sai yaron ya ce ya gode domin an gaya masa ya ce hakan. Yayin da yaron yake girma, ya soma fahimtar dalilin da ya sa yin godiya yake da muhimmanci. Yanzu da ya yi girma, yana yin godiya ba don an gaya masa ya yi hakan ba, amma domin ya san muhimmancin yin hakan.

2 Hakazalika, sa’ad da muka koyi gaskiya, mun koyi muhimmancin bin dokokin Jehobah. Amma yayin da muke manyanta a gaskiya, mun koyi ra’ayin Jehobah da abubuwan da yake so da waɗanda ba ya so. Idan mun ci gaba da barin ra’ayin Jehobah ya shafi zaɓinmu da ayyukanmu, hakan zai nuna cewa muna bin ra’ayinsa.

3. Me ya sa ba shi da sauƙi mu kasance da ra’ayin Jehobah?

3 Ko da yake muna jin daɗin koyan ra’ayin Jehobah, amma yin hakan ba shi da sauƙi domin mu ajizai ne. Alal misali, mun san ra’ayin Jehobah game da yin lalata da biɗan kayan duniya da yin wa’azin Mulki da karɓan ƙarin jini da dai sauransu. Amma wataƙila ba mu fahimci dalilan da suka sa yake da wannan ra’ayin ba. Saboda haka, mene ne zai taimaka mana mu koyi kasancewa da ra’ayin Jehobah? Kuma ta yaya hakan zai taimaka mana mu yi zaɓi mai kyau a yanzu da kuma a nan gaba?

YADDA ZA MU RIƘA BIN RA’AYIN ALLAH

4. Me yake nufi mu ‘yarda Allah ya canja mu ya sabunta tunaninmu da hankalinmu’?

4 Karanta Romawa 12:2. A wannan ayar, manzo Bulus ya bayyana abubuwan da muke bukatar mu yi don mu kasance da ra’ayin Jehobah. A talifin da ya gabata, mun koyi cewa wajibi ne mu nisanta kanmu daga ra’ayoyin mutanen duniyar nan idan ba ma so tunaninsu ‘ya bi da hankalinmu.’ Amma Bulus ya faɗi cewa muna bukatar mu ‘yarda Allah ya canja mu ya sabunta tunaninmu da hankalinmu.’ Hakan na nufin cewa za mu riƙa yin nazarin Kalmar Allah, mu fahimci ra’ayinsa, mu yi bimbini a kansa kuma mu yi iya ƙoƙarinmu don mu kasance da irin ra’ayinsa.

5. Mene ne yin nazari yake nufi?

5 Yin nazari ba ya nufin yin karatu da gaggawa da kuma jan layi a amsoshin tambayoyin da aka yi a littattafanmu. Idan muna nazari, muna bukatar mu yi tunani a kan abin da talifin ya koya mana game da Jehobah, dalilan da suka sa ya ɗauki wasu matakai da kuma ra’ayinsa. Muna bukatar mu fahimci dalilan da suka sa ya haramta wasu abubuwa, amma ya yarda a yi wasu. Muna tunani a kan canje-canjen da muke bukatar mu yi a rayuwarmu da kuma a tunaninmu. Ko da yake ƙila ba za mu iya yin dukan waɗannan abubuwan a duk lokacin da muka yi nazari ba, amma ya kamata mu yi amfani da aƙalla rabin lokacin da muke nazari wajen yin bimbini.​—Zab. 119:97; 1 Tim. 4:15.

6. Wane sakamako za mu samu idan muna bimbini a kan Kalmar Jehobah?

6 Idan muna bimbini a kan Kalmar Allah a kai a kai, za mu shaida wani abu na musamman. Me ke nan? Za mu “tabbatar” wa kanmu cewa ra’ayin Jehobah ne ya fi kyau. Ƙari ga haka, za mu soma fahimtar ra’ayinsa kuma mu so ra’ayin sosai. A sakamakon haka, za mu ‘sabunta tunaninmu da hankalinmu’ kuma za mu kasance da ra’ayin Jehobah.

TUNANINMU YANA SHAFAN AYYUKANMU

7, 8. (a) Yaya Jehobah yake ɗaukan kayan duniya? (Ka duba hotunan da ke shafi na 23.) (b) Mene ne zai fi muhimmanci a gare mu idan muna da ra’ayinsa?

7 Tunaninmu ba ya shafan yadda muke ji kaɗai, amma yana shafan ayyukanmu. (Mar. 7:​21-23; Yaƙ. 2:17) Bari mu tattauna misalan da za su taimaka mana mu fahimci hakan. Littafin Matiyu da Markus da Luka da kuma Yohanna sun sa mu san ra’ayin Jehobah game da kayan duniya. Allah ya zaɓi iyaye a duniya da za su kula da Ɗansa, Yesu kuma su talakawa ne. (L. Fir. 12:8; Luk. 2:24) Sa’ad da aka haifi Yesu, Maryamu ta “kwantar da shi a abin da ake ba dabbobi abinci a ciki, domin ba su sami ɗaki a masauki ba.” (Luk. 2:7) Da a ce Jehobah yana so, da ya sa a haifi Ɗansa a masauki mai kyau sosai. Amma, abin da ya fi muhimmanci a gare shi shi ne iyayen da suke da dangantaka mai kyau da shi da za su kula da Ɗansa a duniya.

8 Wannan misali na Littafi Mai Tsarki ya koya mana ra’ayin Jehobah game da kayan duniya. A yau, wasu iyaye suna so yaransu su yi wadata ko da hakan zai shafi dangantakar yaransu da Jehobah. Amma a bayyane yake cewa al’amura na ibada ne suka fi muhimmanci ga Jehobah. Kana da irin ra’ayin Jehobah kuwa? Mene ne ayyukanka suke nunawa?​—Karanta Ibraniyawa 13:5.

9, 10. Ta yaya za mu nuna cewa muna da irin ra’ayin Jehobah game da sa wani yin zunubi?

9 Wani misali kuma shi ne yadda Allah yake ji idan mun sa wani ya yi zunubi. Yesu ya ce: “Zai zama abin tausayi ga wanda ya sa ɗaya daga cikin yara ƙananan nan masu ba da gaskiya gare ni ya yi zunubi. Zai fi masa kyau a ɗaura masa babban dutsen niƙa a wuya, a jefa shi cikin teku.” (Mar. 9:42) Hakika, yin hakan laifi ne mai tsanani! Tun da Yesu yana da ra’ayi ɗaya da na Ubansa, muna da tabbaci cewa Jehobah ba ya so mu sa wani mabiyin Yesu ya yi zunubi saboda halayenmu.​—Yoh. 14:9.

10 Muna da irin ra’ayin Jehobah da na Yesu kuwa? Mene ne ayyukanmu suke nunawa? Alal misali, wataƙila muna saka wani irin tufafi ko kuma muna yin wani irin ado da wasu a cikin ikilisiya ba sa so ko kuma yake sa wasu su soma tunanin yin lalata. Ya kamata ƙaunarmu ga ’yan’uwanmu ta motsa mu mu daina saka irin tufafin ko kuma yin irin adon.​—1 Tim. 2:​9, 10.

11, 12. Ta yaya za mu kāre kanmu idan muka tsani munanan ayyuka kuma muna da kamun kai?

11 Misali na uku shi ne cewa Jehobah ya tsani munanan ayyuka. (Isha. 61:8) Ko da yake Jehobah ya san cewa yana mana wuya mu yi abin da ya dace a wasu lokuta saboda ajizancinmu, amma yana so mu tsani munanan ayyuka. (Karanta Zabura 97:10.) Yin bimbini a kan dalilan da suka sa Jehobah ya tsani munanan ayyuka zai taimaka mana mu guji yin su.

12 Kasancewa da ra’ayin Jehobah game da yin munanan ayyuka zai taimaka mana mu guji yin wasu ayyuka ko da Kalmar Allah ba ta ce yin su laifi ba ne. Alal misali, yin rawar iskanci a kan cinyar mutum. Irin wannan rawar ta soma zama ruwan dare gama gari a yau. Wasu suna iya cewa yin hakan ba lalata ba ne. * Amma yin irin wannan tunanin ya jitu da na Allah wanda ya tsani kowane irin ƙazanta kuwa? Bari mu nisanta kanmu sosai daga munanan ayyuka ta wajen kasancewa da kamun kai kuma mu tsani abubuwan da Jehobah ba ya so.​—Rom. 12:9.

KA YI TUNANI A KAN ZAƁIN DA ZA KA YI A NAN GABA

13. Me ya sa muke bukatar mu san ra’ayin Jehobah kafin mu fuskanci wani yanayi?

13 Sa’ad da muke yin nazari, ya kamata mu yi tunani a kan ra’ayin Jehobah domin yin hakan zai taimaka mana mu yanke shawara mai kyau a nan gaba. Idan muka yi hakan, za mu san shawarar da za mu yanke idan muka fuskanci yanayin da zai bukaci mu tsai da shawara da gaggawa. (K. Mag. 22:3) Bari mu tattauna wasu misalan da ke cikin Littafi Mai Tsarki.

14. Wane darasi ne muka koya daga yadda Yusufu ya ƙi yin lalata da matar Fotifar?

14 A lokacin da matar Fotifar ta so ta rinjayi Yusufu don ya yi lalata da ita, Yusufu ya yanke shawara da gaggawa. Babu shakka, Yusufu ya riga ya yi bimbini a kan ra’ayin Jehobah game da cika wa’adin aure. (Karanta Farawa 39:​8, 9.) Ƙari ga haka, Yusufu ya ce wa matar Fotifar: “Don me zan yi wannan babbar mugunta, in yi wa Allah zunubi?” Wannan amsar da Yusufu ya bayar ya nuna cewa yana da irin ra’ayin Jehobah. Mu kuma fa? Me za mu yi idan wani abokin aikinmu ya soma yin kwarkwasa da mu? Ko kuma idan an aika mana wani saƙon lalata ko hotunan batsa a waya? * Zai fi mana sauƙi mu riƙe amincinmu ga Jehobah idan mun riga mun yanke shawara a kan matakin da za mu ɗauka idan hakan ya faru da mu.

15. Ta yaya za mu iya yin koyi da waɗannan matasa Ibraniyawa uku?

15 Yanzu bari mu yi la’akari da misalin wasu Ibraniyawa uku. Sunayensu Shadrak, Meshak da Abednego. Sun ƙi bauta wa gunkin da Sarki Nebuchadnezzar ya ƙera. Amsar da suka bayar ya nuna cewa sun riga sun yi tunanin abin da za su yi don su kasance da aminci ga Jehobah. (Fit. 20:​4, 5; Dan. 3:​4-6, 12, 16-18) Mu kuma fa a yau? Me za ka yi idan shugaban aikinku ya ce ka ba da gudummawar kuɗi don wani bikin addinin ƙarya da ake so a yi? Zai fi dacewa ka yi tunani a kan matakin da za ka ɗauka tun yanzu, maimakon ka jira har sai ka fuskanci yanayin. Idan ka yi hakan, zai kasance maka da sauƙi ka san abin da za ka ce ko kuma abin da za ka yi, yadda waɗannan Ibraniyawan suka yi.

Ka riga ka yi bincike, ka cika takardun jinya kuma ka tattauna da likitanka kuwa? (Ka duba sakin layi na 16)

16. Ta yaya fahimtar ra’ayin Jehobah zai taimaka mana mu yi shiri don jinyar gaggawa?

16 Yin tunani yanzu a kan matakin da za mu ɗauka idan mun je yin jinya zai taimaka mana mu kasance da aminci ga Jehobah. Babu shakka, ba za mu yarda a yi mana ƙarin jini ba ko kuma ɗaya cikin gutsurori huɗu na jini ba, amma da akwai wasu irin jinyar da za mu bukaci yin amfani da ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki wajen yanke shawara. (A. M. 15:​28, 29) Hakika, ba zai dace mu yi tunani a kan wannan batun a lokacin da muke asibiti ba. Me ya sa? Domin a lokacin, za mu yanke shawara a garaje saboda zafin ciwon da muke fama da shi. Yanzu ne lokacin da ya fi dacewa mu yi bincike, mu cika takardun jinya da za su nuna zaɓinmu kuma mu tattauna da likitanmu. *

17-19. Me ya sa yake da kyau mu san ra’ayin Jehobah game da wasu batutuwa tun yanzu? Ka ba da misali.

17 Ka yi tunanin amsar da Yesu ya ba da sa’ad da Bitrus ya ce masa: “Allah ya sawwaƙe, Ubangiji!” Babu shakka, Yesu ya riga ya yi tunani sosai a kan abin da Allah yake so ya yi da kuma Nassosi da suka shafi rayuwarsa da mutuwarsa a duniya. Hakan ya ƙarfafa shi ya kasance da aminci ga Jehobah kuma ya ba da ransa a madadinmu.​—Karanta Matiyu 16:​21-23.

18 A yau, Allah yana so bayinsa su ƙulla dangantaka da shi kuma su yi ƙwazo a hidimarsa. (Mat. 6:33; 28:​19, 20; Yaƙ. 4:8) Amma wasu suna iya neman su sa mu sanyin gwiwa, yadda Bitrus ya yi wa Yesu. Alal misali, me za ka yi idan an ƙara maka mukami a wurin aiki da kuma albashi, amma hakan zai rage ƙwazonka a hidimar Jehobah? Ko kuma idan kai ɗalibi ne, me za ka yi idan aka ce ka ƙaura daga gida don ka sami ƙarin ilimi a wata makaranta? Shin a lokacin ne za ka je ka yi addu’a da bincike a littattafanmu ko kuma ka nemi shawara daga danginka da kuma dattawa kafin ka tsai da shawara? Zai fi dacewa ka san ra’ayin Jehobah game da batun yanzu kafin ka fuskanci jarrabawa. Idan ka yi hakan, za ka san zaɓin da za ka yi a duk lokacin da ka fuskanci jarrabawa domin ka riga ka yanke shawarar riƙe aminci ga Jehobah.

19 Za ka iya yin tunani a kan wasu yanayoyin da za su iya tasowa babu zato. Ko da yake ba za mu iya yin shiri don dukan matsalolin da za mu fuskanta ba, amma idan muna yin bimbini sosai sa’ad da muke nazari mu kaɗai, za mu iya yanke shawara mai kyau sa’ad da muka fuskanci matsala. Saboda haka, a duk lokacin da muke nazari, zai dace mu bincika ra’ayin Jehobah kuma mu yi tunani a kan yadda hakan zai taimaka mana mu yanke shawara mai kyau a nan gaba.

SAKAMAKON KASANCEWA DA RA’AYIN JEHOBAH

20, 21. (a) Me ya sa za mu ji daɗin ’yancinmu na yin zaɓi a ƙarƙashin Mulkin Allah? (b) Mene ne zai sa mu farin ciki a yau?

20 Babu shakka, dukanmu muna ɗokin yin rayuwa a ƙarƙashin Mulkin Allah. Wasu cikinmu na ɗokin yin rayuwa har abada a aljanna a duniya. A lokacin, ’yan Adam za su sami ’yanci daga baƙin cikin da muke fama da shi a wannan mugun zamanin. Kowannenmu zai ci gaba da yin amfani da ’yancinsa wajen zaɓan abin da yake so.

21 Amma hakan ba ya nufin cewa za mu kasance da ’yancin yin duk wani abin da muka ga dama ba. Idan adalai suna so su yanke shawara, za su yi amfani da dokokin Jehobah wajen yin hakan. Yin hakan zai sa mu riƙa farin ciki sosai kuma mu kasance da kwanciyar rai. (Zab. 37:11) Yayin da muke jiran wannan lokacin, za mu iya yin farin ciki idan muna yin la’akari sosai da ra’ayin Jehobah.

^ sakin layi na 12 A wannan rawar iskanci da ake yi a kan cinyar mutum, namiji ko ta macen da ta kusan yin tsirara tana zaunawa a cinyar kwastoma tana kaɗe jikinta. Dangane da yanayin, hakan zai iya zama lalata da zai bukaci a kafa wa mutum kwamitin shari’a. Duk Kiristan da ya taɓa yin irin wannan abu yana bukatar ya nemi taimakon dattawa a ikilisiya.​—Yaƙ. 5:​14, 15.

^ sakin layi na 14 Aika saƙonnin batsa ta waya ko hotunan tsiraici ko bidiyo ne ake kiran sexting a Ingilishi. Dangane da yanayin, za a iya kafa wa mutumin da ya yi hakan kwamitin shari’a. A wasu yanayi, hukuma ta hukunta ƙananan yaran da suka yi wannan laifin. Don samun ƙarin bayani, ka karanta talifin nan “Me Ya Kamata In Sani Game da Aika Sakon Tsiraici ta Wayar Salula?” a dandalin jw.org. (Ka duba ƙarƙashin KOYARWAR LITTAFI MAI TSARKI > MATASA.) Ko kuma ka duba talifin nan “How to Talk to Your Teen About Sexting” a Awake! ɗin Nuwamba 2013, shafuffuka na 4-5.

^ sakin layi na 16 An tattauna wasu ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki a littattafanmu. Alal misali, ka duba littafin nan Ku Tsare Kanku Cikin Ƙaunar Allah, shafuffuka na 215-218.