Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Wace Kyauta Ce Za Mu Ba Jehobah?

Wace Kyauta Ce Za Mu Ba Jehobah?

YESU ya taɓa cewa: “Ya fi albarka a bayar da a karɓa.” (A. M. 20:35) Abin da Yesu ya faɗa yana da alaƙa da dangantakarmu da Jehobah. Me ya sa? Domin Jehobah ya ba mu abubuwa da yawa da suke sa mu farin ciki sosai, amma za mu fi farin ciki idan muna ba Jehobah kyauta. Wace kyauta ce za mu ba Jehobah? Littafin Karin Magana 3:9 ya ce: Mu ‘girmama Yahweh da abin da muke da shi.’ Abubuwan da muke da su sun ƙunshi lokacinmu da baiwarmu da ƙarfinmu da kuma wadatarmu. Idan muna yin amfani da waɗannan abubuwan don mu tallafa wa bauta ta gaskiya, muna ba Jehobah kyauta ne kuma yin hakan yana sa mu farin ciki.

Mene ne zai taimaka mana mu ɗauki ba Jehobah kyauta da muhimmanci? Manzo Bulus ya gaya wa Kiristocin da ke Korinti cewa su riƙa ‘ajiye’ abin da za su ba Allah kyauta. (1 Kor. 16:2) Mene ne za ka yi idan kana son ƙarin bayani game da yadda ake ba da gudummawa a wurin da kuke? Don Allah ka duba akwatin da ke ƙasa.

Ba a iya ba da gudummawa ta Intane a wasu ƙasashe. Amma, akwai wasu hanyoyin ba da gudummawa da aka rubuta a shafin ba da gudummawa. A wasu ƙasashe, ana saka amsoshi ga tambayoyin da ake yawan yi game da batun ba da gudummawa a shafin.